Showing 9001 words to 12000 words out of 47415 words
Chapter 4 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf
har da irin
doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a
d'aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa.
Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta'ba kallon
kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun
kafar.
A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji
muryarsa cike da wani irin amo!! "Tashi zaune."
Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara'a yace." Zanja
ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin
gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya.
Kuka tasa tana kallonsa da fadin." Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine
zaka had'a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad'ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana
iya faruwa da rayuwata."
Yace." Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had'ari shiyasa
na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali."
Ta girgiza kai tana shakar hanci tace."Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo
bayanku."
Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta.
Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi'kewa. "Na fad'a miki abinda yake da akwai kina kuka
ko."?
Hannu ta d'aga masa da fadin." Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba." Tana gama
maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali."
"Ki tsaya nan nace."! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi.
Ya karasa inda take da fadin." Kar'bi wannan ki rufe jikinki dashi." ba tayi musu ba ta kar'ba, ta
lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana 'bata masa
lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d'aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a
kafar ba.
Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama'arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa
tare da ita ya basu mamaki! amma babu wanda yayi magana a cikinsu, yayi gaba suka rufa
masa baya.
karnuka wasu a gaba wasu a baya, sai kuma bushe-bushe da gangi! da ya cika dajin!
*Free pege ya kusa 'karewa a hanzarta biyan kudin karatu.*
*0542382124...Binta umar gtbank* a tura sheda ta wannan number...... 07084653262
*Ayi kokari a duba wannaní ½í±‡í ¼í¿»*
_Mijina baya bani_ kulawa bayan kafin muyi aure yana bani kulawa da duk wata soyayya
___________
*Watakila kece kika janyo faruwar hakan, na farko dai namiji yana da bukatar kulawa, ta kowane
fanni, watakila kafin kuyi aure ke din 'yar gayu ce mai tsafta, bakya rabo da kwalliya kamshin
turare ako da yaushe, sai bayan auranki kuma ki mayar da kanki jakar mata, da kuruciyar da
komai ki shiririce wanka ma sai kiyi kwana biyu ko uku ba kiyi ba mussaman a cikin wannan
lokacin, sai kiyi kwaskwarima ki shafa mai akan dauda kina tsamin hammata! to me zai hana
namiji bai kyamace ki ba, babu mummunar mace, kuma komai shekarunki mutukar kina da miji
to kada ki zauna a lalace domin hakan zai janyo miki bacin rai mai tsanani mussaman idan kina
da abokiyar zama to zaki zama koma baya ta kowane fanni, tsafta jigo ne a cikin
zamantakewar aure don haka ki kula da wannan abubuwan.*
*1- Wanka sau biyu a rana*
*-2 yawan aske sassan dake fitar da gashi a jikinki*
*4-Zama cikin kamshin turare mai sanyi da sanyaya zuciya*
*3-Kitso duk bayan sati ko kwana goma kuma kafin ayi kitson a wanke kan*
*5-Wanke baki sau biyu ko uku mussaman idan zaki kwanta*
*6- Taraiyaya da iya kalami mai dadi a lokacin da kike tare da mijinki*
*7-Sauya kalolin abinci masu inganci*
*8- Sanya kaya na mussaman domin zuwa turaka*
*9- Shagwaba wata abace mai muhimmanci*
*10- Banda yawan dariya mara ma'ana a gaban miji murmushi zaki yawaita yi masa kina sarrafa
kwayar idonki a kansa kina bashi labarai masu dadi.*
_Mutukar kin kula da wannan to zaki kama mijinki a hannu kuma zai baki kulawa ta mussaman_
*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Dala dari Katin Airtal ko Mov
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*í ¼í¿¹
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í±‘í ½í²«_)
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONí ½í¶Šï¸í ½í³š_*
_____________________
*_KADAN DAGA CIKIN IRIN SAKKONIN DA NAKE CIN KARO AKO DA YAUSHE_*
_*1-* Mijina baya bani kulawa bayan kafin muyi aure yana masifar sona_
_*2-* Mijina baya iya biya min bukatata._
_*3-* Mijina baya hira dani kullum idan ya dawo daga aiki ko kasuwa wayarsa ce abokiyar
hirarsa_
_*4-* Mijina kazami ne sai yayi sati ko kwana goma beyi wanka ya wanke bakinsa ba._
_*5-* Dangijin mijina sun matsa min basa kaunata saboda bana haihuwa._
_*7-* Bana jin dadi a duk sanda mijina zai kusanceni da kyar nake amincewa saboda zafi._
_*8-* Mijina yana cutar dani baya sauke hakkina dake kansa bayan Allah ya hore masa._
_*9-* Mijina mazinaci ne yana neman mata bayan ina iyakacin bakin kokarina gurin ganin na
dauke masa bukata._
_*10* Mu biyu ko uku ko hudu ne a gurin mijinmu amma baya adalci a tsakaninmu._
_*11-* Mijina yana da taurin kai da wani irin hali baya sarrafuwa._
_*12-* Mijina Miskili ne kullum babu mu'amular arziki a tsakaninmu sai muyi kwana da kwanaki
babu magana._
_*13-* Ina fama da rashin nutsuwa da kwanciyar hankali a gidan aurena bayan ta kowane
bangare bani da matsala._
_*14-* Mijina shaye-shaye yake nayi - nayi ya daina yaki baya sallah a kan lokaci sannan idan
mukayi mu'amula ta aure baya wankan tsarki._
_*15-* Mijina baya dogon zango yake release kuma bai damu dani ba, haka zai tashi ya barni
cikin halin damuwa._
FREE PEGE
*13&14*
Sosai yayi namijin kokarin tunkarar inda take kafin ya karasa ya cire duk wani kawazucin dake
cikin zuciyarsa yana isa ya bude mata wuta sosai yana mata fada tare da nuna mata illar
abinda ta aikata.
Tsaye ta mike tana masa wani irin kallo kafin tace."Wai shin ubana ne kai da zaka zo kana min
tsawa ina ruwanka da rayuwata, idan har baka san ganina a haka to kayi gaggawar mayar
dani inda ka daukoni."
Ya nuna ta da yatsa kamar zai tsole mata ido Yace." Banyi ra'ayin haka ba kuma ke baki isa
kisa na tafi ba tare dana shirya tafiya ba, idan kina san kanki da arziki ki dauki rigarki kasa a
jikinki."
Ta nuna masa jikakkiyar rigar dake yashe a gefe, ya kalleta da fadin." Meye manufarki na jika
rigarki da ruwa ko kinyi hakane don kija ra'ayina akanki.?
Wulakantaccen kallo tayi masa kafin tace."Allah ya kiyaye meye abin sha'awa a tattare da kai
da har kake wannan maganar."
Ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallo, ta gyada kanta idonta a soye a kansa tana kara
tabbatar masa da maganarta.
Yace."Idan babu abin sha'awa a tattare dani to ni naga abinda ya burgeni a jikinki kuma ke zaki
janyo na aikata abinda ba shikkenan ba."
Gabanta ya fadi da jin furucinsa, amma bata saduda ba, ta ya mutsa fuska da fadin.'' Da kuwa
nayi maka illah! domin ka kuskura ka keta min haddi wallahi sai ka dawwama a daure. a
kurkuku."
Leb'ansa yasa a bakinsa ya dan ciza kafin ya furzar da wani irin huci! yace."Baki san ni bana
d'auruwa ba? ko ba kiji sunana ba *GOJE!* nake ko kuma ki kira ni da *MAI DAWA!* Babu wani
mahalukin da ya isa ya tunkari inda nake ban ci Uwarsa ba!"
Sai ta tsargu! ta nuna kirjinta da hannu da fadin." Ni kake zagi ko? shin ka san su waye iyayena
a fadin kasar nan kuwa"?
Ya gyda kansa da fadin" Babu ruwana da ko su waye iyayenki ni na fada miki wanene ni! babu
wanda ya isa ya daureni ba tare dana rikirkita masa al'amuraba."
Ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa, babu wanda ya isa ya daureshi ba tare da ya
rikirkita masa al'amuraba ba."
"Kana nufin kafi karfin hukuma kenan."? tafada idonta a tsaye a kansa.
Tsaki! yaja mai karfi kafin ya nuna kirjinsa da fadin." Ni nan! ni ne hukuma! duk wani mai
bukatar kwanciyar hankali a kasar nan to kada ya ta'boni."!
Cike da Izzah! da jin kai ya fadi maganar, kai daga jin yanda yake magana kasan akwai abinda
da ya taka.
Ta sunkuyar da kanta tana mamakin furucinsa wato shi bai yarda ma akwai hukuma ba! to bari
ta ta'bashi taga abinda zai yi.
Yanke shawarar zaginsa tayi, ta dago kai suka hada ido, yana tsaye kikam! a kanta, tsoro ta cire
Cikin turanci ta fara zazzzaginsa tana kiransa da sunayen dabbobi........ Iyakacinsa secondary
skull turancin nata yayi tsayi sosai da kyar ya fahimci wasu kalmomin mussaman sunayen
dabbobin da take kiransa dashi.
Bahagon mari! ya kifa mata a fuska a take taurari masu haske suka gilma, ta rintse idonta
hawayen azaba na zuba!
Tana cire hannunta daga gurin shatin yatsunsa suka fito radau!
Ta tsira masa ido gabanta sai faduwa yake, tunda take a duniya babu wanda ya taba fitar da
hannu ya tsinka mata mari sai shi.
Ta dinga bin sassan jikinsa da kallo, shi kuma yana dogare a kanta yana tsuma! da alama
tsumin ne ya tashi.
Kafin kiftawa da bismillah tayi wani tsalle sai kace aljanna ta fizge kaifaffar wukar dake soke a
gaban rigarsa.
Ta rike da kyau! tana kallonsa da fadin" Sai na zubar maka da jini yau! *GOJE!* kake ko? har
kana Ikirarin cewa wuka bata huda ka, bayan haka yaranka suna kumbura maka kai kana
d'aukar kanka wata tsiya! to yau ni zanyi ajalinka."!!
Da gaske take domin hannu bibbiyu ta ri'ke wukar da kyau sai huci take! tana mazari! kanshi
tayi da wukar zata yankeshi, ya kauce! tabi iska! a sukwane ta sake kai masa sarah! ya kauce
ta sake bin iska! dariya ta kusa kufce masa ganin yanda ta dage! wai dole sai ta yankeshi da
wukar wanda duk kokarin da take a banza bata samu damar saka wukar a jikinsa bama
ballanatana ta fitar mai da jini.
Haka suka dinga bugawa ya dinga watangaririya da ita yana bata wahala! ta galabaita mutuka
gumi duk ya jika mata jiki shi kanshi tsumman data daure cinyoyinta dashi ya kwance,ribbon din
data d'aure gashinta dashi ya cire ya fadi kasan gurin, kafafunta sunyi bududu! amma saboda
tsabar karfin hali taki saduda!.
Yana sane ya dinga bata wahala sai da ya tabbatar data galabaita sannan ya murde hannunta
ya kwace wukar! faduwa tayi a gurin tana wani irin kukan bakin ciki!
Tausayi ta bashi! wannan artabun da sukayi koda namiji ne zai ji jiki ballantana mace irinta da
bata saba da wahala ba, yayi mamakin karfin halinta mutuka.
Kusa da ita ya tsuguna yana duba kafafunta duk ta taka k'ananun k'ayoyi, hannu yasa domin
cire mata k'ayoyin ta harbeshi da kafa daya, kallonta yayi cikin zafin nama! ta ciko hannu da
kasa zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, ta watsawa iska. tana daga kwance tana nishi ta
cigaba da cin mutuncinsa da turanci, hakan be dameshi ba tunda ya kaita kasa bukatarsa ta
biya.
Duk buge-bugen da take bai hanashi ciccire mata kayoyin da suka huda kafafunta ba, ya cire
rigar jikinsa ya rufa mata a jiki.
Da sauri ta cire ta jefar da ita.
Yace." Ni zan iya kawar da kwadayina akanki amma kika yarda wata dabbar ta gilma ta hangi
tsaraicinki ba zaki kai labari ba, bayan dabbobi akwai aljanu a gurin nan kiyi hattara."
Jin maganar aljanu yasa jikinta mutuwa idan akwai abinda take tsoro a duniya aljan ne! hakura
tayi kan dole ta karbi rigar sa tasa.
Tana share hawaye ta mike tsaye, ya kalleta yana jimanta karfin halinta, wai dashi za tayi fada,
dariya yayi wacce ta dauki hankalinta ta kalleshi tsantsar kyawunshi ne ya bayyana a lokacin,
ganin tana kallonsa yasa ya gimtse fuska yaje ya dauki rigarta da tsumman ya bar gurin dasu a
hannunsa,
*********
Yau ma da wuri ta isa gidan, ta sameta ta shirya tsaf domin fita! A gabanta sabbin atampopi ne
irinsu nicham hartget da makamantasu, cike da ladabi suka gaisa, tace."Kinga sabbin
atampopi ne Rakiya ta kawo min na saya wai itama a cikin gari ne aka bata su shine nakeso
nayi musu kudi a ganinki duk daya za tayi nawa."?
Hamra'u ta kalli atampopin kafin tace."Uwale ke kin kasa yi musu kudi ballanatani ni da ba
sana'ata ba."
'Yar dariya tayi kafin tace."Don kar nace da ita dubu uku taga kamar wulakanci ne abun amma
iyakacin abinda zan iya siya kenan.''
Cike da mamaki tace."Uwale dubu uku a tamfa turmi hudu haba Uwale kiyi adalci mana shiyasa
jama'a suke zaginki har suna kiranki da mummunan suna."
Ta 'bata rai da fadin." Sun jima basu zageni ba! ai Hamra'u a wannan duniyar idan zaka dauki
maganar mutane to wallahi babu abunda zaka tsinana, amma meye laifina don na saya dubu
uku, itama ai kyautarsu a ka bata.
Tace."Duk da haka dai sunyi arha da yawa duka cotton ne babu leda a ciki maimakon ki saya
dubu biyar gabadaya."
Tace."Aa ba zan iya saya dubu biyar duka ba, dubu uku zan saya kuma ke da kike surutu ai
idan na saya to tanadi nake miki kayan lefanki ne."
Murmushi tayi kafin tace."Uwale nifa jikina yayi sanyi sai nake ganin kamar burina ba zai cika
ba."
Murya na rawa ta karashe maganar.
Tace."Aa ki daina sanya damuwa a ranki insha Allahu ba zakiyi zaman banza ba UMARU zai
aureki koda baya sonki to ni zan umarceshi ya aureki.
Tace."Aa Uwale ni nafi so ya aureni dan yana sona bana so muyi irin wannan auran da iyaye
suke hadawa daga baya a samu matsala."
Tace."Insha Allahu ba za'a samu matsala ba, domin ni kaina na gaji da ganinsa a haka babu
aure sa'anninsa sun jima da aure da 'ya'yansu amma shi yana zaune a haka, idan za'a biye
masa to zai kare rayuwarsa a haka wannan dalilin yasa zan tilasta masa auranki."
Hawaye ta share tana girgiza kai, itafa kwata-kwata bata son irin wannan auran tafi so da
bakinsa ya furta mata kalmar so, amma dole haka zata hakura tunda yaki gane irin son da take
masa. watakila idan Allah ya kaddara auran nasu Allah ya sanya masa kaunarta a cikin
zuciyarsa.
Tace."Ki goge hawayenki ki daina kuka mutukar ina raye to kamar kin auri UMARU kin gama,
shiyasa duk tsumi da tanadina ya kare akanki gashi cikin ikon Allah na kusa kammala hada
miki lefe, kinga sai komai yazo da sauki."
Tace."Nagode Uwale Allah ya tabbatar mana da alkairi" Ta amsa da "ameen" tana kokarin tashi,
Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin." Yanzu nake maganarki a
cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki."
Tace."To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba."
Ta ya mutse fuska da fadin." Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin
naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke."
Rakiya ta mika hannu da fadin." Ban siyar a hakaba bani na kai inda za'a saya da mutunci."
Baki ta bude da fadin." Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika
kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta."
Taja tsaki da fadin." Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku
duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu
biyar gabadaya."
Tace." Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka."
Jim tayi kafin tace."Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif."
Tace."Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba
ai ba zan karbi kayanki ba."
Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune
yawanci duk 'yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra'u tasa hannu suka lissafa dubu hudu
kudin me kayan ta mika mata da fadin." Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san
halinki kada ki dawo kice min basu cika ba." Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa
kudin ta kalleta da fadin "Sun cika." Tace."To masha Allah idan an samu wasu kayan ina
bukata." Tana kokarin fita tace." To shikkenan