Showing 90001 words to 93000 words out of 133788 words
Chapter 31 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA
kwance har da amai ki ke".
"Uhm zazza'bi ne".
"Yaya Sameer ya duba ki"?"eh tun safen ya duba ni na samu sau'ki ba kamar d'azu da ko zama gagara ta ya yi ba" zaro ido waje Afifah tai ta na cewa "zama ya gagare ki? Caf Allah ya rufa asiri Allah ya kawo sauki".
"Amin" Umma ce ta fito daga d'aki ta na cewa "Afifah ashe ke ce ki ka zo"?.
"Ni ce Umma ina yini"? "Lafiya kalau ya mutan gidan na ku"?.
"Lafiya kalau su ke ya me jikin"?.
"Ga ta nan da sauki".
"Allah ya 'kara sau'ki" "Amin an gode sosai Allah ya yi albarka" Umma ta fad'a ta na wucewa ta d'auki buta za ta yi alwalar sallar magriba kallon Zainab Afifah tai ta na mi'kewa ta ce "Aunty Zee bari na tafi kin ji an fara kiran sallah" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "to Afifah na gode ki gaida Momy"?.
"To in sha Allahu za ta ji sai da safe" ta fad'a ta na fita bayan Umma ta yi alwalar dawowa gurin ta ta yi tana cewa "zaki iya tashi ki yi alwalar ne"? "Eh zan iya" ta fad'a ta na tashi tsaye duk da har lokacin ba ta jin 'karfin jikin ta ko kad'an shimfid'ar Umma ta d'auke ta mayar mata d'aki sannan ta fito ta shiga na ta ita kuma Zainab ta yo alwalar ta zo ta shiga za ta yi sallar.
Afifah ta na komawa gida ta tarar da Momy a parlor ta na zaman jiran dawowar ta ganin ta shigo ya sa Momy kallon ta tana cewa "Afifah a ina ki ka tsaye ne sai yanzu ki ka shigo gida har an fito daga masallaci bayan ba ki saba yin hakan ba"? Kai Afifah ta d'aga ta na cewa "tun lokacin da aka taso na taho Momy na wuce gidan su Zainab na dubo ta ne".
"Ba ta da lafiya"?.
"Eh ashe tun safe ta ke zazza'bin ni ban sani ba da yake na kira wayar ta a kashe na d'auka ba ta da caji ne ashe ba ta jin dad'i ma ita".
"Ayya Allah ya sauwake idan na samu lokaci ko gobe ne zan je har gida na duba ta Allah ba ta lafiya".
"Amin" Afifah ta ce tana wucewa part d'in su Momy ma tashi ta yi ta koma na ta dama dalilin fitowar da ta yi rashin ganin shigowar Afifan a lokacin da ta saba ne amma tun da ta dawo kuma ta ji inda ta je ba matsala.
Da yake tun da daren da Zainab su kai waya da Aunty Murjah ta fad'a mata ba ta da lafiya shi ya sa washe gari da safe wajen 'karfe goma da rabi na safe ta sake kiran ta, ta duba ta sannan ta ce mata da dare za su shigo tare da Auwal su sake duba ta Afifah ma ta sake shigowa da safen kafin ta tafi school ta duba ta harda Fati da Elham su ka zo da kayan dubiya.
Sakamakon shi ma Yaa Sayyidi bai san ba ta da lafiyar ba a jiyan ya ga yau ma still ba ta le'ko islamiyyar ba shi ya sa ya tambayi Afifah ko lafiya ta fad'a masa ai ba ta jin dad'i ne tun daren shekaran jiya sosai ya yi kewar rashin zuwan ta musamman ajin da ta ke d'auka dole jiya da yau duk shi ya ke shiga mu su..............
ZUCIYAR ALIYU CE
STORY WRITTEN ND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR✨
@YUSRAH YMA DUTSE
PAGE 57
POV. YAA SAYYIDI
Da ya koma gida bayan sallar magriba ya shigo anguwar ta su amma a d'an nesa da gidan ya tsaya saboda haske kiran ta ya yi a waya ta fito ya duba ta ba ta ta'ba tunanin zai zo har gida ba ta d'auka tun da ya kira ta d'azu shikenan idan gobe ta koma islamiyyar ya duba ta.
A lokacin ta na kan sallaya ta yi sallah kenan ya yi kiran ta, tashi ta yi ta d'auki Nikaf ta d'aura ta shiga d'akin Umma ta sanar mata sannan ta fita had'uwa su kai da Sameer da mamaki ya kalle ta ya na cewa "Zainab ina zuwa haka ke da ba ki da lafiya"? Numfashi ta sauke a hankali ta ce "Yaa Sayyidi ne ya kira ni a waya ya ce na fito ya na waje ya zo duba ni" jin abin da ta ce ya sa Sameer ya kalle ta da sauri cike da mamaki ya ce.
"Wai Yaa Sayyidin dama har yanzu bai daina zuwa gurin ki ba"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh ya na zuwa amma ba koda yaushe ba sai lokaci zuwa lokaci" 'kak'karfan numfashi Sameer ya sauke ya na kallon ta ya ce "tabd'ijan amma akwai............... Koda shikenan je ki kawai idan kin dawo gida sai mu yi maganar kar na tsayar da ke shi kuma ya na jiran ki ba damuwa je ki kawai" ya fad'a ya na wucewa shiru Zainab ta yi a ran ta, ta na cewa "tabbas akwai abin da Yaya Sameer ya hango min wanda ni ban gano ba amma bari idan na dawo zan tambaye shi" bud'e 'kofa ta yi ta fita a inda ya saba tsayawa idan ya zo anan ta same shi yasha wankan jallabiyya shi yasa mutumin nan ya ke burge ta kuma ta ke jin cewa za ta iya auren sa ko mata uku ne da shi ta shiga gidan matsayin ta hud'u ta amince sallama ta yi su ka gaisa ya kalle ta shi ma cike da burgewa ko'ina a rufe ya ce.
"Fatan kin samu sau'ki ko ashe ba ki ji dad'i ba"?.
"Wallahi ban ji dad'i ba jiya a kwance na wuni shi ya sa ban samu na shigo islamiyya ba yau ma kuma na tashi babu 'karfin jiki shi ya sa ban zo ba na bari sai gobe".
"To Allah ya kai mu ai haka Afifah Ahmad ta ke fad'a min yau da na tambaye ta ki na ina na san dama ba za ki ta'ba yin tafiya ba ki fad'a min ba".
"Ba tafiya na yi ba zazza'bi ne ya same ni".
"Shikenan ba damuwa Allah ya 'kara lafiya dama kawai cewa na yi bari na shigo na duba ki daga nan sai na je gurin wani malami da ya ke bayan layin ku mu gaisa da shi ga wannan" ya 'karasa maganar ya na d'auko ba'kar ledar da ke gefen sa ya mi'ko mata kai ta girgiza ta na cewa "lah a'a ka barshi ba komai iya duba ni da ka zo ka yi ma na ji dad'i sosai".
"A'a ki kar'ba ai niyya na yi ba saka ni ki kai ba sannan kin san ba kyau mai da hannun kyauta baya ko"? Shiru ta yi ya ci gaba "dan Allah Zainab ki kar'ba na tafi" ya fad'a ya na sake mi'ko mata da'kyar ta saka hannu ta d'an risina ta kar6a ba don ran ta ya so ba sai dai dan kawai ba ta son musu.
"Na gode sosai Yaa Sayyidi Allah ya saka da alkhairi".
"Amin ba damuwa sai da safe na tafi" ya na fad'in haka ya juya ya tafi ita kuma ta shiga gida ba ta samu Sameer ba domin har ya gama abin da zai yi a lokacin ya fita d'aki ta koma ta jira sallar isha lokacin ta ya 'karaso ta yi sannan ta d'an kwanta kafin su Aunty Murjah su zo kwanciyar ta ke da wuya barci ya fara d'aukar ta, ta ji sallamar su tashi zaune ta yi ta na kallon kofar shigowa d'akin ta gani ta yi an bud'o labule Ikram ta shigo da murnar ta, ta zo ta zauna a kusa da ita ta na cewa.
"Aunty Zainab ina wuni"? Murmushi Zainab ta yi tana d'aukar ta, ta d'ora ta akan cinya ta ce "lafiya kalau Ikiki na ina ki ka bar Daddyn ki"? D'aga yatsa ta yi ta na cewa "a can"?.
"A can gida ku ka baro shi"? Ikram na wasa da kayan 'kyallayen d'inki ta ce "eh Aunty Zainab za ki d'inkawa baby na kayan ta"?.
"Aw Baby ce da ke"?.
"Eh Daddy ne ya siyo min".
"Lallai Daddyn nan na ki ya na son ki to ina Momyn na ki"?.
"Ta na d'akin Umman ta" d'an zaro ido Zainab ta yi tana kallon ta tace "ke ba Umman ki ba ce"?
"Eh ni Momy ce Momy na" kai Zainab ta jinjina ta na d'auko biscuit mi'ka mata daidai Aunty Murjah ta shigo da sallama ganin ta a zaune yasa ta ce "ahh masha Allah ashe kin samu lafiya"? Ta fad'a ta na zama kusa da ita ta ce "sannu ya jikin"? Murmushi Zainab ta yi tana kallon ta tace.
"Da sauki ina yini"?.
"Lafiya kalau ya 'karfin jikin"?.
"Na samu lafiya wai ku kad'ai ku ka zo ban da Abban Ikram"? Kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "tare mu ka zo man"
"Kai amma Ikki ta ce min iya ku ne"?.
"A'a ba mu kad'ai ba ne ya na gurin Abban mu" mi'kewa Zainab ta yi tana d'aukar mayafi ta ce "bari na je mu gaisa da shi" tashi Aunty Murjah ta yi tana cewa "mu je ina son za mu gaisa da Hajiya" kallon ta Zainab ta yi kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa su ka fita ganin takalman Auwal a 'kofar d'akin Abban su ya sa ta fahimci har lokacin ya na d'akin waje su ka nufa Aunty Murjah ta shiga 'kofar Hajiya ita kuma ta tsaya tare da Ikram har Auwal ya fito Aunty Murjah ta na ciki 'karasowa inda Zainab ta ke ya yi yana cewa.
"Sannu 'yar 'kanwa ta ashe ba ki da lafiya ai ban sani ba sai da na dawo princess ta ke fad'a min kuma gashi ke da baki da lafiya amma ki ka fito rakiya"? D'an murmushi Zainab ta yi daidai Aunty Murjah ta fito ta ce "ai da ya ke zazza'bin dare na yi daga shekaran jiya zuwa yau ne".
"Allah ya kawo sau'ki ko dan ya kawo ma tun da gashi kin ware" kallon Aunty Murjah ya yi yana cewa "mu je dare ya na dad'a yi" kai ta d'aga su na fita a lokacin Ikram ta na kafad'ar Zainab ta yi barci jikin motar su ka zo Aunty Murjah ta bud'e baya ta shiga da mamaki Zainab ta kalle ta za ta yi magana ta ga an bud'e murfin gaban motar an fito zaro ido ta yi tare da d'auke numfashi ganin da wanda su ka zo...............
Ya na ri'ke da murfin motar ya kalle ta da murmushi ya ce "barka da dare malama Zainab ya jikin na ki"? Har lokacin numfashin ta bai dawo daidai ba da'kyar ta iya ce wa.
"Da sau'ki".
"Masha Allah Ubangiji ya 'kara afuwa".
"Amin na gode".
"Na so ace mun d'an samu zama ni da ke mu tattauna amma ba lokaci sai dai idan na ji ni free zan sake dawowa in sha Allahu sai mu yi magana ko"?.
"To" ta sake cewa muryar ta bai fita sosai kai ya jinjina yana komawa cikin motar ya zauna murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tare da mi'ko hannu ta ce "kawo ta mu tafi" kai Zainab ta girgiza ta na d'an 6ata fuska ta ce "Aunty Murjah dan Allah ki bar Ikram a nan tun da gobe asabar ce ba school jibi zan kawo mi ki ita har gida da kai na Yaya Sameer ne zai rako ni".
"Ai kuma akwai islamiyya"? Zainab za ta yi magana Sameer ya karaso gurin sakamakon ba ya nan su ka zo fitowa Auwal ya yi yana bashi hannu suka gaisa cikin tsokana ya ce.
"A'a me gida Alhaji Sameer kana sha'anin ka sai yaushe za mu zo biki ne ko ba rana"? Dariya Sameer ya yi yana cewa "wanne biki amma ba nawa ba"?.
"Na ka mana yaushe ne"?.
"Tab ba rana ni da ko gini ban fara ba ka ga ina batun aure a gu na"? Da mamaki Auwal ya ce "kai haba dai"?.
"Wallahi da gaske ne ke maka iya fili na ke da shi sai daga baya zan fara aikin sa" kai Auwal ya jinjina ya na cewa "ok Allah ya taimaka Allah ya kai mu lokacin".
"Amin na gode" ya fad'a ya na juyawa inda Zainab ta ke tsaye ya ce "ya jikin na ki gaskiya ke 'yar gata ce sai zuwa duba ki ake uhm mu je a bani nawa abun dubiyar na san ya nan a d'aki jibgi-jibgi" dariya Aunty Murjah ta yi ta na cewa "tabbas ya na nan lodi-lodi ku je ka kar'bi rabon ka".
"Hum ki ji fa har albishir ake min please Zainab mu je dan Allah" ita kuma Aunty Murjah ta ke kallo tare da cewa "to Aunty Murjah dan Allah na tafi da ita kwana biyu kawai kin ga fa ta yi barci"? Tun kafin Aunty Murjah ta yi magana Auwal ya ce "ba damuwa je ki da ita".
"Yauwa Yaya na gode in sha Allahu jibi da kai na zan kawo ta sai da safe Yaya Sameer mu je ku gaida gida" ta na fad'in haka ta juya su ka shiga gida tare da Sameer saboda ya kar'bi Ikram tun da ta yi barci kuma Zainab d'in ba lafiya ce da ita ba har d'aki ya shiga ya kwantar da ita ganin dare ya d'an fara yi yasa daya fito ya d'auki bokitin da zai yi wanka ya fita daga 'kofar ta su.
Sosai Zainab ta sha mamakin ganin babbar leda a ajiye a kusa da katifar ta kenan Aunty Murjah ce ta shigo da ita d'aukowa ta yi ta na shirin bud'ewa ta duba sai kuma ta ga kiran Aunty Murjan ya shigo d'agawa ta yi ta na cewa "hello Aunty Murjah wannan ledar ke ce ki ka shigo da ita"?.
"Eh ni ce dama na manta ban fad'a miki ba shi ya sa na kira ki duba ledar nan za ki gan ta a d'akin ki kayan 'karamar ledar na mu ne na babbar kuma na masoyin ki ne Mukhtar" ta na fad'in haka ta yi dariya tare da kashe wayar dan ta san in ba haka ta yi ba sai ta yi mata 'korafi shiru Zainab ta yi hankalin ta a tashe ta kasa saka hannu ma ta bud'e ledar balle ta ga abin da ya ke ciki matsawa ta yi daga gurin ta koma kan katifa ta cirewa Ikram kayan ta sannan ta gyara mata kwanciya kafin ta tashi ta fita daga d'akin.....................
💓 ZÜÇÏYÄR ÄLÏYÜ ÇË💓
♣Y♠ü♥s♣r♠ä♥h♣
♣M♠ü♥s♣ä♣
♣Ä♠b♥ü♣b♠ä♥k♣ä♠r♥.
@YUSRAH MUSA
₱AGE 58
Washe garin ranar asabar da yake ba school za ta je ba islamiyya ce shiyasa ta dafa ruwa da wuri ta yiwa Ikram wanka ga shi ba'a zo mata da kaya ba dad'in abun ma akwai irin wanda idan sun zo su ke barin sa shi ta birkito a cikin kayan ta, ta saka ma ta.
Su na d'aki Momy ta shiga tare da Husnah ta yi sallama Umma dake waje ta na shara ganin wacce ta shigo ya sa ta mi'ke tsaye cike da mamaki ta ce "a'a Hajiya Barakah ke ce a gidan na mu yau da kan ki"? Murmushi Momy ta yi tana cewa "wallahi ni ce ai dole in zo na duba 'yata ta na ina"? Aje tsintsiyar Umma ta yi tana cewa "bismilllah 'karaso" shiga d'akin Umma ta yi suka gaisa ta na cewa.
"Ya mai jikin kuma ai jiya ina ta jiran Afifah na ga ba ta koma gida da wuri ba ashe nan ta zo duba ta fatan ta warware"? Kai Umma ta d'aga tana cewa "alhamdulillah jikin ta ya yi sau'ki sosai ya kwanan yaran".
"Masha Allah haka ake so yara su na lafiya ta na ina yanzu"?.
"Ta na d'akin ta tare da Ikram" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "ok bari na je na duba ta Husnah tashi mu je" fita su kai Umma ta bud'e labulen 'kofar d'akin Zainab ta na cewa "Zainab ki na ciki ne ga Maman Afifah ta zo duba ki" sakin labulen Umma ta yi tana cewa "bismilllah Hajiya Barakah ki shiga ta na nan" komawa Umma ta yi ta ci gaba da shara Momy kuma ta shiga d'akin Zainab da 'yar fara'a Zainab ta ce.
"Lah Momy ke ce sannu da zuwa" ta fad'a tana tashi ta d'auko sallaya ta shimfid'a mata zama Momy ta yi bayan sun gaisa ta ce "ya jikin na ki da sau'ki ko"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh na samu sau'ki ina kwana"?.
"Lafiya 'kalau Zainab Allah ya 'karo miki lafiya kin ji".
"Amin Momy na gode" ta fad'a ta na ri'ko hannun Husnah ta ce "Husnah har da ke aka zo ina su Elham da Fati"?.
"Su na gida Aunty Zainab ya jikin"? "Jiki alhamdulillah Husnah da sauki" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "Auta tashi mu je" tashi Husnah ta yi su ka fita daga d'akin a lokacin har Umma ta gama sharar da ta ke yi ganin su ya sa ta ce "kun fito"?.
"Eh za mu tafi Allah ya sauwake".
"Amin Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi".
"A'a ba komai Zainab ai 'ya ta ce dan na zo duba ta dad'i na ji yara su na yabon ta sosai kuma su na matu'kar jin dad'in karatun ta a islamiyya kullum sai sun fad'a shi ya sa ni ma har ta shiga rai na sosai" murmushi Umma ta yi cikin jin dad'i daidai Momy ta juya za su fita a 'kofar ta ce "sai anjima a sake yi mata sannu idan ta fito".
"To in sha Allahu Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a ta na shirin shiga d'aki Asabe ta fito tana kallon ta tace "oh! Ni 'yasu na shiga d'aka ni jikar mutum hud'u anya Hauwa ki na neman zaman lafiya kuwa ashe asirin naki har ya bar kan mu 'yan gida ya koma kan masu kud'in anguwar nan meye had'in biri da gada ki fad'a min in dai ba sharrin asiri ba ko a mafarki wannan matar ba za ta tako gidan nan ba balle har ta yi magana da ke ta na matsayin matar minister ke kuma matar me