Showing 87001 words to 90000 words out of 133788 words

Chapter 30 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA

ta ya na rawa ta fita ta ga waje ma har lokacin 'yan matan gidan su na kofar sun yi tsit kowa jira ya ke yaji salatin Hajiya ko na Asabe cewa cikin ne da Zainab ganin ta fito ta yi hanyar band'aki yasa suka bi ta da kallo har ta fito ta zo ta sake wucewa ta kai masa komawa ta yi ta kwanta ta na addu'a a zuciyar ta Umma ma gabadaya ta rud'e PT Abdul-Razza'k ya d'auka ya d'an saka ya dagwalo ya d'ago shi ya zuba ido kafin ya ja tsaki me 'karfi ya na mi'kawa Sameer ya ce.

"Kalli da idon ka, ka gani na rasa me ya ke damun 'yan gidan nan kamar rashin tarbiyya a kan su ta 'kare" kar'ba Sameer ya yi shi ma yaga dai layi d'aya PT d'in ya nuna ba layi biyu ba kai ya jinjina ya na cewa "Allah na gode maka d'an ba'kin ciki sai ya mutu duk wanda ya ke son ganin ba'kin cikin Zainab sai dai ya ci kan sa Allah ya fitar da ita daga zargi kuma sai Allah ya saka mata sharrin da akai 'yan ba'kin ciki kuma sai su yi tono su binne kan su alkaba'in da suke nema bai samu ba" kallon sa Hajiya ta yi tana cewa.

"Uban wa yace maka ba'kin ciki ake mata uban me ku ka gani a jikin wannan d'an siririn abun munafikai har ku ke fad'awa mutane magana" mi'kewa Abdul-Razza'k ya yi yana cewa "ba kin ce a duba miki idan ta na da ciki ba? To bata da shi" ya na fad'in haka ya juya zai fita Hajiya ta ce "kai Abdul-Razza'ku ba na son 'karya ka fad'a min gaskiyar abin da ka gani".

"Ai Hajiya gaskiyar abin da na gani na fad'a miki daga 'kin gaskiya kuma kowa ya san sai 6ata wallahi tallahi na rantse da Allah wanda ya halicce ni Zainab ba ta da ciki zazza'bin malaria ne ya kama ta sosai shi ya sa ku ka ga tana amai" sauke ajiyar zuciya Hajiya ta yi tana cewa "shikenan na yarda na san kana da hankali ba za ka min rantsuwa akan 'karya ba shi ya sa nasa aka kira ka amma da Samar ne ya fad'a min ba zan ta'ba yarda ba".

"Humm Allah ya rufa asiri Allah ya shiryar da 6atacce" Abdul-Razza'k ya na fad'in haka ya fita daga d'akin cike da takaicin jin ba ciki ba ne malaria ce Asabe ta harari Umma wacce ke gefe ta na goge hawayen fuskarta kamar za ta ja tsaki amma saboda kar ace ta na daga cikin 'yan ba'kin cikin gidan yasa ta saki labulen dake ri'ke a hannun ta tun d'azu ta fice fuuuu daga d'akin su ma na wajen jin abun da Abdul-Razza'k d'in ya fad'a yasa d'aya bayan d'aya su ke mi'kewa su na fita kowa murna ta koma ciki.

"Kin gani ko Hajiya kin ga irin abin da nake fad'a muku wai ana zuwa idan aka fad'a muku magana ba bincike sai ku hau ku zauna yanzu gashi kun zarge ta akan abin da bata aikata ba sai ku nemi yafiyar ta" Sameer ya yi maganar ya na tattare kayayyakin sa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "uban na nemi yafiyar ta dama ni ce nayi mata sharrin ina d'aki a zaune aka je akai kira na nazo kuma dan na sa an bincike ta meye abun laifi a nan har zan nemi wata yafiya"? Mi'kewa Sameer ya yi yana cewa "shikenan tun da ba ki ga abun neman yafiyar ba ni dana gani na fad'a miki amma tun da kin ce ke ba ki yi komai ba, ba damuwa" shi ma yana fad'in haka ya fita mi'kewa Hajiya ta yi ita ma zata fita ta kalli Umma ta na cewa.

"Hauwa Allah ya rufa miki asiri yau da ace ciki ne da yarinyar nan daga ke har ita yau sai dai ku yi kwanan D'an Yana dan wallahi ba ku isa ta haifa mana shege a gida ba to amma tun da maleriya ce Allah ya kawo sau'ki" ta fad'a ta na shirin fita sai kuma ta juyo ta na kallon kwalin sweet dake can gefen Umma ta ce "Hauwa me ye a cikin nan"? Kallon kwalin Umma ta yi tana cewa..

"Chocolates ne a ciki da biscuits" dawowa ciki Hajiya ta yi tana cewa "chocolates da biscuits mi'ko min bibiyu" bud'ewa Umma ta yi ta d'ebo mata ta d'auko leda ta saka a ciki ta mi'ko mata kar6a Hajiya ta yi tana cewa "saura lemuka da pure water nima yau Allah ya rubuta zan ci arzikin duk da ran ku bai so ba bud'e ki d'ibo min tun da aka kawo mata firizar nan daga ke har ita ba ku ta'ba tunanin d'aukar wani abu ku kai min ba sai yau da rabo ya shigo da ni" Umma ba tayi magana ba duk dan a rabu lafiya nan ma ta sake tashi ta bud'e fridge d'in ta d'ebo mata kai Hajiya ta jinjina ta na cewa.

"Ahh lallai kam ta yaya Zainab za ta yi aure bayan ba ta rasa komai ba ga sana'o'i ga kuma wadannan gatan da take samu daga aljanin ta tun da nasan da mutum ne yake bata wadannan abubuwan da yanzu ya bayyana mata kan sa Allah yasa ba ba'kin aljani ne ya aure ta ba kar ya hana ta aure" ta fad'a ta na zaro alawa d'aya ta 6are ta saka a baki ta na cewa "garin dad'i ba kusa ba ana shan irin wannan dad'in a gidan nan amma ban sani ba humm! Na gode ni zan tafi Allah ya sauwake zan dawo anjima na sake duba ki lokacin na shanye alawar sai na 'kara kar6ar wata tun da na gani ai na daina barin ku, ku huta" ita dai Umma tari da bai kamata ba ba ta yi ba har Hajiya ta bar 'kofar ta na fita Asabe ta bankad'o labule ta koma d'akin ta na kallon Umma ta ce.

"Na san 'karya Sameer da Abdul-Razza'k su ke yi da suka ce Zainab ba ta da ciki dan su kare ta ne amma ai duk inda cikin gaskiya ya ke baya 6uya mu nan mu na zuba ido duk wani motsin ku muna hankalce da shi duk ranar da na ga Zainab ta fita daga gidan nan ko biyu bana rabawa asibiti ki ka tura ta taje a zubar da cikin humm ga sakamakon kwad'ayi nan kun fara gani in dai nadama ce ba ku fara shiga ba sai nan gaba ma aure dama ba ku so ta yi ba kuma ba za ta ta'ba yi ba" ta na fad'in haka ta juya ta fita kai Umma ta girgiza ta na cewa "bakin ki ya fad'i a 'kasa in sha Allahu Zainab za ta yi aure duk daren dad'ewa" ta fad'a ta na sake jan bargo ta lullu'be ta kafin ta koma ta zauna ta yi shiru ta na kallon ta cike da tausaya mata kullum addu'ar ta Ubangiji ya ba ta miji na gari wanda zai ri'ke ta tamkar 'yar da ya haifa ya nuna mata gata domin wannan damuwar da ta sha ta gushe fatan ta Allah ya sa kafin ta bar gidan nan kar ba'kin ciki ya saka ta kamu da hawan jini.

💓ZUCIYAR ALIYU CE💓

@YUSRAH MUSA
PAGE 55
Koda lokacin tafiya islamiyya ya yi ma bata samu lokaci ba sakamakon zazza'bin bai sauka ba waje Umma ta fito mata da shimfid'a ta kwanta a 'kofar d'akin ta tana nan a kwance ganin Bilki ta fito daga d'aki da shirin islamiyya ya sa Zainab tashi zaune tana jingina da jikin bango ta ce.

"Bilkisu islamiyya za ki je"? Jin abin da tace ya sa Bilki hararar ta tana cewa "a'a gidan rawa zan je" numfashi Zainab ta sauke sakamakon jin irin amsar da ta bata da har za ta 'kyale sai kuma ta ce "dan Allah idan kin je ki fad'awa Yaa Sayyidi ba ni da lafiya" taki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi ba zan fad'a ba ina ruwa na da wani Yaa Sayyidi" ta fad'a ta na shirin fita da kallo Zainab ta bita tana cewa.

"Bilkisu yanzu ba za ki fad'a masa ba ni da lafiya ba"? Kai ta jinjina tana cewa "eh ba zan fad'a ba sai akai ya"? Shiru Zainab ta yi ba ta sake magana ba tsaki Bilki ta ja ta na ficewa tana fita Asabe ta fito daga d'aki ta kai kwanuka gurin wankewa sannan ta juyo tana zuwa kan Zainab ta tsaya tare da kallon ta tace "ke a tunanin ki Bilkisu 'yar aiken ki ce? Tsabar rainin hankali ita ce za ta fad'awa wani Yaa Sayyidi ba ki da lafiya? Ai da tace za ta fad'a masa na fito sai na yi mata dukan ala tsine a gidan nan yadda ba ki d'auke ta 'kanwa a gidan nan ba har abada ba za ta yi miki kallon yaya ba ai ba ita kad'ai ce take zuwa islamiyya a gidan nan ba da za ki ba ta wani banzan sa'kon ki uban wa ya hana ki zuwa ai ba zazza'bin gaskiya ki ke ba wannan zazza6in na ciki ne kuma in sha Allahu sai kin haife shi" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin Zainab kam dama tun da ta fara magana kan ta yake 'kasa har ta gama ta juya kuwa ba ta d'ago ba domin ta tabbata ko Umma da ta na nan ba za ta tankawa Asaben ba balle ita da ta ke matsayin 'yar cikin ta kuma ko ba haka bama yadda Sameer ya ke son ta ya ke kula da ita bai kamata ace ta na yiwa Asabe rashin kunya ba duk ranar daya shigo ya tarar da hakan ba zai dad'i ba wannan dalilin ya sa ko Asabe za ta rufe ta da duka ba za tace ma ta komai ba..................

Kiran wayar ta da akai ta mayar da hankalin ta gurin Sameer ne d'agawa ta yi tana cewa "assalamu-alaikum Yaya Sameer ina yini"? Jin ta ambaci Sameer ya sa Asabe daina wanke-wanken da ta ke ta tsaya tare da juyowa ta na kallon ta, ta ji me za tace Zainab kam hankalin ta ba'a kan Asaben ya ke ba balle ta san me ya ke faruwa kawai da Sameer ya ce mata ya jiki ta ce.

"Da sau'ki".

"Zazza'bin ya sauka ko har yanzu da saura"?.

"A'a ya sauka ba zafin jikin sai juwa da na ke ji idan na mi'ke tsaye".

"Ba ki ci abinci bane"?.

"Eh".

"Me ya sa to ba'a yi bane"?.

"An yi shinkafa ce da wake salad ne babu shi ya sa ban ci ba" jin abin da ta ce ya sa yace "ok ina zuwa" ya na fad'in haka ya katse aje wayar Zainab ta yi Asabe da ta gama wanke kwanukan ta na shirin barin gurin ta ce "to munafika gadon 'karya da sharri inji uban waye ya ce ba'a siyo salad ba har ki ka fad'a masa kodan dama 'karya abincin ki ce" shiru Zainab ta yi ba tai magana ba Asabe data shiga kitchen ta d'auko salad a leda ta wurgo mata ta na cewa "kin ce masa ba salad saboda ga gidan fatararru yanzu wannan uban meye a ledar inace uwar ki ce ta yi abinci da shi jiya tsabar ba'kin hali ta'ki yanka shi yadda zai isa ta 6oye kuma gashi asirin ta ya tonu har salad d'in ya fara zama yellow ba ta d'auke ba" tafa hannu Asabe ta yi tana cewa "kai jama'a gaskiya akwai azzalumai a gidan nan ni dai ana zalunta ta ba abin da zan ce sai Allah ya saka min daga ke har uwar taki idan an gan ku shiru-shiru ba'a san lunbu-lunbu ne ba uwar 'kai'kayi sai mutum ya zauna da ku zai ga sharruka iri-iri gashi a haka gani ake kamar ni ce na ke cutar ku saboda ni ina da baki hummm kowanne shege haka nan zai gan ni ya, barni dan na zama ciwon ido zama da ni sai ha'kuri" ta fad'a tana komawa cikin kitchen d'in ita dai Zainab har lokacin ko tari ba ta yi ba sai dai ta ji mamakin ya akai da salad d'in amma ba'a yanka ba ai duk zaton ta babu shi ya sa ta'ki cin abincin da ta san da akwai koda kan ta za ta iya yankawa tun da Umman ba ta nan sallama Sameer ya yi yana shigowa ya zo ya aje leda a kusa da ita sannan ya shiga kitchen Asabe ta na tsaye ya gaida ita ba ta amsa ba sai tambaya da ta jefo masa ganin ya d'auki plate da wu'ka da cokali tace.

"Kai uban me za ka yi da su"?.

"Zan yankawa Zainab salad ne ta ci abinci".

"Humm dama na san sai dai Zainab d'in da nice nake jinyar nan Sameer ko kallo na ba za ka yi ba amma da ya ke Zainab 'kanwar uwar ka ce daga tace maka ba za ta ci abinci idan ba salad ba shine har ka rarumo ru'kui-ru'kui jiki na rawa ta kawo mata kuma hakan bai isa ba saboda ta mayar da kai bawan ta sai ka yanka mata" kallon ta Sameer ya yi yana cewa.

"Umma wannan fa duk ba abun fad'a ba ne dan na kyautatawa 'yar uwa ta".

"Sannu me 'yar uwa sakaran banza da an yi magana ka ce 'yar uwar ka zan ga tsiyar da za ta tsinana maka nan gaba da ka nace sai ita aikin banza kawai" juyawa ta yi ta bar gurin Sameer dai bai sake magana ba ya yanka mata salad d'in ya d'ebo gishiri kad'an ya wanke mata ya yanka mata cocumber tumatur da albasa ya aje mata ledar da ya shigo da ita ya bud'e ya d'auko wani 'katon kifi a ciki ya 6are shi ya fitar mata da 'kayar sannan ya zuba mata abincin ya shiga d'akin ta ya d'auko mata pure water a fridge ya kawo mata tare da zama a gefen shimfid'ar ya na cewa.

"Ki ci man ki ka tsaya ki na kallon abincin"? Kai ta d'an girgiza ta na cewa "ba zan iya ci ba" da mamaki Sameer ya ce "ba za ki iya ce ba kuma"? Nan ma kai ta sake d'agawa ta na d'an zamewa daga zaunen da take zata kwanta ganin haka ya sa Sameer cewa.

"A'a la'asar ta yi koma ki zauna kar ki kwanta rana ta yi 'kasa" d'agowa ta yi ta dawo zaune yadda ta ke duk da ta na son kwanciyar abincin Sameer ya gauraya mata cikin kulawa da lallami na mara lafiya ya soma ba ta ya na cewa "kin ga ki d'an kar6a ki ci ko loma d'aya ce" idan yaga ta kar6a sai ya sake d'ebowa ya ce "yauwa 'kara d'aya" da haka kamar da wasa har ta ci da yawa ya bata pure water ta sha murmushi ya yi yana kallon ta ya ce.

"Yauwa to alhamdulillah" mi'kewa ya yi ya na cewa "idan an jima ki d'auki d'ayan kifin da ya ke ledar ki cinye shi kafin na shigo bari na koma na baro chemist d'in a bud'e" kai ta d'aga a hankali ta ce "na gode Yaya Sameer Allah ya saka da mafificin alkhairi" "Amin ya ce ya na fita daga 'kofar ta su Asabe da ta yi shiru ta na kallon su ganin ya fita ya sa ta taso da gudu ta na zuwa ta yi wuff kamar shaho ta d'auke ledar kifin ta na hararar Zainab ta ce.

"Mayya ba ni wato bayan wanda ki ka ci harda saura ya rage miki zuwa jimawa ki ci, humm ni dai wannan abu ya na ba'kanta min zuciya amma ba komai in dai asiri ku kai masa zan je awarware daga ranar asirin munafiki zai tonu" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin ta shige d'akin ta numfashi Zainab ta sau'ke tare da rufe ido kawai ta yi shiru kamar me barci...............................

ZUCIYAR ALIYU CE

@YUSRAH MUSA
PAGE 56
Ganin da Afifah ta yi Zainab ba ta je islamiyya ba har aka tashi shi ya sa da taga tawagar su Bilki za su tafi gida ta tare su ta na cewa "am dan Allah yau ya akai Zainab ba ta zo islamiyya ba"? Dukkan su Bilki su ke kallo ganin ta'ki magana ya sa Rasheedat cewa "sai dai ki tambayi Bilki ita ce 'kofar su d'aya" jin abin da Rasheedat ta ce ya sa Bilki zafga mata harara ta na cewa "ni ma ban san dalilin ta na 'kin zuwan ba".

"Ok ba ta gidan ne ko ta yi tafiya"? Afifah ta sake tambaya kai Zakiyyah ta girgiza ta na cewa "in dai ba d'azu ta tafi ba gaskiya Zainab ta na nan da yake bata da lafiya tun safe ta ke amai ina ga shi yasa ba ta zo ba" d'an zaro ido Afifah ta yi ta na cewa "Subanallahi wayyo Aunty Zee-Zee dama ba ta da lafiya? Allah sarki Zainab d'ina shi ya sa na yita kiran ta a waya na ji a rufe ashe ita ta kan ta, ta ke yi bari na wuce na dubo ta" jin abin da Afifan ta ce ya sa suka fara kallon kallo tsakaninsu su na ta6e baki Bilki kuwa ji ta yi kamar ta d'auke Afifah da mari tsabar takaicin yadda ta damu da Zainab d'in, tare su ka shiga gidan Bilki da Afifah su ka wuce can 'kofar har lokacin Zainab ta na waje ba ta koma d'aki ba Abba ya na kusa da ita ya na mata sannu dawowar sa kenan daga gurin sana'ar sa ko d'aki bai shiga ba ganin ta yi ba'kuwa ya sa ya mi'ke dur'kusawa Afifah ta yi ta gaida shi ya amsa ya na nufar 'kofar d'akin sa zama Afifah ta yi tana kallon ta ta ce.

"Sannu Aunty Zeey ya jikin na ki"? D'aga kai Zainab ta yi ta na cewa "da sau'ki Afifah", "Allah ya 'kara lafiya ashe tun safe ba ki da lafiya ban sani sai yanzu da mu ka taho na ke tambayar 'yan gidan nan suka ce min tun safe ki na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login