Showing 129001 words to 132000 words out of 133788 words

Chapter 44 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA

ta sannan kin ga ba sanarwa za mu shiga ai babu dad'i" girgiza kai Afifah tai ta na sake jan ta tace "kai a'a babu abin da take mu je" har Zainab za ta sake magana sai kuma ta yi shiru shiga su kai suka same ta a parlor tare da Daddy suna zaune abin da Zainab ta yi gudu kenan ga shi kuwa ya faru Husnah ta na gefe ta na rubutu 'kwace hannun ta Zainab ta yi da sauri za ta juya Afifah ta ri'ke ta ta na cewa.

"Haba dan Allah Aunty Zee ki tsaya ku gaisa man bayan ga shi har da Daddy" tsayawa tai tana juyowa ta yi sallama amma ta'ki yarda ta fito normal su gan ta tana bayan Afifah kamar wacce tai laifi ko ta ke jin tsoro murya 'kasa-'kasa tace "Afifah ban san Daddyn ku yana nan ba ke kuma baki fad'a min ba me ya sa za ki min haka? Kin sa naji kunya wallahi" 'yar dariya Afifah tai zatai magana Momy tace.

"A'a malama Zainab kin shigo kenan ai Afifah ta fad'a min zaki zo tun d'azu"? Dur'kusawa Zainab tai tana gaida su amma dai ta'ki fitowa daga bayan Afifan sai kare kan ta take kamar mara gaskiya murmushi Momy tai tana cewa

"Ya kike ra'bewa ki shigo sosai mana karaso nan" Zainab na dur'kushe a gurin murya a nutse tace "Daddy ina kwana"? sai a lokacin Daddy ya d'ago shima yana kallon yadda take faman jan Afifah tana 6oyewa kai ya girgiza yana cewa "nidai bazan kar'ba daga nan ba" jin abinda yace yasa dole ta mi'ke tana d'an karasawa cikin parlon ta d'an zauna a kasan carpet ta gaida su da fara'ar su suka amsa mata lallai yarinyar nan akwai nutsuwa sanadin ra6arta da Afifah keyi a islamiyya yasa itama ta kasance mai hankali suna godiya da samunta matsayin 'kawar 'yar su.

"Zee-zee taso mu je part d'in mu" Afifah ta fad'a tana kallon yadda ta sunkuyar da kai 'kasa ta'ki d'agowa saida tai magana sannan ta mi'ke suka fita da kallo Momy ta bisu tana d'an yin murmushi bayan sun fita Daddy ya kalli Momy da Asma'u ta mi'ko mata rubutun datai tana duba mata yace "ni dai ina yiwa Aliyu kwad'ayin yarinyar nan sai dai kin san jiki da jini ba lallai shi kuma tai masa ba" numfasawa Momy itama ta yi ta na cewa "haka ne amma ai ba shi zamu biya ba mezai hana kawai muyi magana a junan mu damu da iyayen ta a aura masa ita ba dole sai yana sonta ba kyawawan halayenta sune zasu sanya ya damu da ita idan ma dai yana da wacce yake so daga baya saiya aureta" jinjina kai Daddy ya yi ya na cewa "haka ne kema kin kawo magana amma bana son abinda zai zama damuwa a tare dasu damu gara a fara tuntubar sa idan yana ra'ayi shikenan idan yace a'a sai a 'kyale shi ni Ina ganin kamar hakan zaifi sau'ki akan mu je gurin iyayen ta kai tsaye".

"Ai ko nasan Aliyu da son mace mai tarbiyya bazaice a'a ba domin yasha fad'a min kud'i ba su bane samun mace ta gari shi yake so saboda tarbiyyar 'ya'yan sa kuma ma bayan haka yace min yana da wacce ya ke so".

"Wacce ya ke so kuma a ina take"? "Ni kaina ban sani ba domin bai fad'a min ba sai dai na sake tambayar sa".

"To ki tambaye shi ina fata ta kasance wannan yarinyar ce ina so ta zama d'aya daga cikin ahli na" hannu Momy ta d'aga tana cewa "Amin Alhaji Allah ya amshi ro'kon ka" murmushi Daddy yayi yana kallon ta ya ce "ya amsa ma in sha Allahu yanzu idan ya shigo kiyi min magana da shi kice ina neman sa idan kina ganin kamar a naki 6angaren da matsala".

"Ba wata matsala amma dai gara ka tambaye shi da kanka".

"Ok shikenan idan ya shigo ki fad'a masa ya same ni a part d'ina yanzu zan fita ko zuwa dare ne idan na dawo za mu yi magana da shi" ya fad'a yana mi'kewa itama Momy mi'kewar tayi suka fita tare tayi masa rakiya suka bar iya Asma'u a parlon tana ci gaba tracing d'in rubutun da take yi.

Su Zainab kam suna fita parlor ta mayar da nikaf d'inta kan fuskarta kamar yadda yake dariya Afifah tai tana kallonta tace "kai dan Allah a gida ma bazaki cire ba nan fa ba layi bane ko dama haka kike zama ko a gidan ku"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa.

"A'a".

"Oh meyasa anan ba za ki cire ba kodan saboda akwai samari a gidan"? "Eh" shine amsar da ta bata "to ai kuma iya Yaya discipline ne a gidan shi kuma ya riga ya sanki Afif ne ma dai zan ce da sau'ki kuma shi da baya nan garama ki cire abin ki kisha iska".

"A'a basai na cire ba".

"Kai wai da gaske ki ke, me ya sa bakya son a kalli fuskar ki ne Zainab"? "Saboda na tsare kai na daga shiga fitina ina yiwa wanda zai aure ni tattalin kai na da taya shi kishi kar kowanne d'a namiji ya ga fuskata sai shi" dariya sosai Afifah keyi tana tafi tare da jinjina kai tace.

"Gaskiya ne Zainab ni kai na da nake mace kuma 'kawar ki zan iya 'kirga sau nawa naga fuskar ki ba dan kina yin alwala ba kuma saboda mutane kar su gani bakya yin alwala sai kowa ya gama shima ba dan nasan muryar ki ba fuskar dai zai min wahalar ganewa ko dan ina ganin ta a islamiyya lokaci zuwa lokaci ko Yaa Sayyidi shima alwala za ki yi kika cire nikaf ya ga fuskar ki shikenan ya rud'e ya kamu da son ki haka ne"? "Hummm" kawai shi ne abin da Zainab ta ce wanda yasa Afifah dariya tana cewa "humm me"?

"Ba komai" ta fad'a daidai Fati da Elham sun fito ganin har tazo yasa suka karaso suna cewa "Aunty Zainab ina kwana"? A sake tace "lafiya kalau ya ku ke"? "Muna lafiya" Fati ta d'ora da cewa "dan Allah Aunty Zainab na d'auko littafi na, na d'an biya ki ji ko ina da gyara"? Tun kafin Zainab ta yi magana Afifah ta harari Fati ta na cewa.

"Ke ba d'ori ta zo yi muku ba kar ku takura ta ki bari sai kin je islamiyyar man" murmushi Zainab tai tana cewa "a'a bari na d'ora mata d'auko Fati" jin zata biya mata yasa Elham ma tashi kowa ta d'auko na ta al-qur'anin su ka dawo d'age nikaf d'in Zainab tayi sannan ta fara gyara musu Afifah dake gefe tana murmushi so take ta yi dariya tasan tana yi indai Zainab ta fahimta yanzun nan zata mayar da nikaf d'in ta yadda yake Aliyu kam daga kofar gidan su tashi yayi domin ya shigo gida zai d'auki abu kawai tun yana wajen kofar parlon su kafin ya bud'e yake jiwo tashin karatun ta tsam ya tsaya a guri d'aya yayi shiru yana saurarar ta daga baya kuma ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "alhamdulillah" sannan ya bud'e kofar ya shigo idon sa ne ya sauka akan kyakkyawar fuskar ta da ke bayyane rabon da yaga fuskar ta a fili kamar haka har ya manta wani abu yaji ya sake dira a cikin zuciyar shi ji yake ina ma yadda take zaunen nan ace ba zuwa ta yi zata tafi ba kyan abun ace ta riga ta zama matar sa a gidan sa take ya aure ta kawai abin da ya kawo a ransa ke nan Zainab bata lura da wucewar sa ba saida ya d'auko abinda zai d'auka ya dawo zai fita jin 'karar bud'e 'kofa yasa ta d'ago karaf su ka had'a ido da sauri ta d'auke kai gaban ta na fad'uwa ta mayar da kallon ta kan al-qur'anin da'kyar tace.

"Ina kwana"? K'ofar fita ya nufa can 'kasa ta ji muryar sa yace "lafiya" numfashin da ya tsaya mata a 'kirji ta samu ta fito da shi tana d'an daidaita nutsuwar ta ta ci gaba da yi musu gyaran saida suka gama Afifah ta tashi tana cewa "Zainab ta so mu koma bedroom d'in mu tun da gashi tun ba'a je ko'ina ba abun da kike gudu ya faru taso mu je" kai ta girgiza tana mi'kewa ta ce "a'a tafiya zan yi na baro d'inkunan mutane da dama kuma an kusa bikin".

"Kai dan Allah Aunty Zee please mu karasa ki wuni man" zaro ido Zainab tayi tana kallon ta tace "wuni fa ki kace? A'a tafiya zan yi" ta fad'a tana yun'kurin nufar kofar fita da sauri Afifah ta ri'ko hijab d'in ta tana girgiza mata kai tace "wai dan Allah Zainab me ya sa bakya son zuwa gidan mu kuma yau ina ta murna kin zo sai ki ce tafiya za ki yi................

Muryar Momy ce ta katse maganar da Afifah ke yi "Ina zata je amma ba har gida za ta tafi ba"? Kai Afifah ta d'aga tana cewa "eh wai sai ta tafi nace ta tsaya ta wuni ta'ki"

"A'a haba Zainab daga zuwan ki ki bari man ko zuwa jimawa sai ki tafi"

"Nima fa abun da nace kenan ta tsaya ta wuni".

"Ko bata wuni ba amma tunda yanzu 'karfe sha biyu tayi ta bari idan tayi sallah taci abinci sai ta tafi bari na zo" ta fad'a tana nufar wata 'kofa kallon yadda Zainab ta yi shiru Afifah tai tana cewa "kin ji ko Zainab dan Allah ki dawo ki zauna kin ga Momy ma ta saka baki baza ta ji dad'i ba idan ki ka tafi" dole babu yadda Zainab ta iya duk da ta na son tafiyar amma tun da har da Momy ita ma ta saka baki ya za ta yi bedroom suka wuce acan ma da'kyar ta cire hijab d'in jikin ta gabadaya tafi so ta koma gida ko dan kar a kai gulmar ta gurin Hajiya jan ta Afifah ta yi tayi da hira har ta d'an ware sukai zance da aka 'kare lunch ta je ta d'ebo musu yin duniya Zainab taci abincin nan ta'ki saida Afifah ta rantse cewa indai bata ci ba sai ta zuba mata a cooler ta tafi da shi jin haka yasa taci abincin su na gamawa ta yi alwala tayi sallah shaf-shaf ta d'aura nikaf ta tashi daga kan sallayar Afifah data fito daga toilet ita ma tayo alwalar ganin yadda har ta gama shiri yasa ta saki murmushi ta na girgiza kai batare da ta ce komai ba ta d'auki hijab d'in ta ta saka.

"Afifah zan tafi" taji muryar Zainab juyowa inda take ta yi tana cewa "ok bari na yi sallah sai na raka ki" tana fad'in haka ta juya ta fara sallah tsaye Zainab tai har Afifan ta idar tayi addu'a sannan ta tashi ta d'auke sallayar tana cewa "mu je to" sauke numfashi Zainab ta yi tana bud'e kofar suka fito daga part d'in su Afifah duk sauran suna dining Momy Aliyu Elham Fati da Asma'u suna cin abinci sallama ta yiwa Momy da sauri ta fita saboda ta ga yadda Aliyu ya ke bin ta da wani kallo wanda yake firgita mata lissafi a ranta tana tunanin watakil baza ta sake shigowa gidan ba sai dai idan Aliyu ne ba ya nan tsayar da Afifah Momy ta yi tana cewa.

"A cikin dogayen rigunan nan guda biyu da Daddy ya siya miki kwanan baya naga baki saka su ba ki d'auko mata d'aya ai za ta yi mata daidai" kai Afifah ta d'aga tana cewa "to" tare da juyawa ta koma bedroom d'in su ta d'auko harda turare ma ta had'o mata guda d'aya ta sa'ko su a wata 'yar jaka da nufin daga baya ta kawo mata jakar fitowa tayi tacewa Momy "bari na je ta raka ta" ta fad'a tana bud'e 'kofar parlon ta fito harabar gida amma abun mamaki duk zaton ta Zainab tana harabar gidan tana jiran ta sai ta ga bata nan wucewa ta yi ta fita ko alamar ta babu humm Zainab kenan har ta gudu gida bari na bita wucewa tayi ta bi bayan ta a lokacin da ta shiga da Rasheedat suka fara karo ta na tsaye tare da Zakiyyah da sauri cikin shishshigi tace

"Lah Afifah ina yini"? "Lafiya kalau ya kike"? Ta fad'a tana d'an tsayawa kad'an cikin cushi Rasheedat tace "ina lafiya kwana biyu ban gan ki ba fatan ki na lafiya"?.

"Eh lafiya alhamdulillah" tana fad'in haka ta wuce da kallo Rasheedat ta bita tana cewa "wallahi a rayuwa ina so mu yi mutunci da wannan Afifan ko dan na ri'ka shiga gidan su amma sam daga gaisuwa bata tsayawa ayi wani zance da ita" dariya Zakiyyah tayi tana kallon Rasheedat tace "eh idan kin duba ita da masu aji take harkar ta".

"Su wa ye masu ajin"?.

"Zainab man a gidan nan da wa take 'kawance bayan ita gurin wa kika ta'ba gani ta tako ta zo idan ba ita ba"? Ta'be baki Rasheedat ta yi tana cewa "ai itan ma a shishshigin ne ya sa tayi suna a gurin ta idan ba haka ba tana matsayin 'yar mai kud'i zata zo har gida neman ta ne"?.

"To indai da shishshigi Zainab ta samu suke 'kawancen ke wa ya hana ki yi mata ke ma kuyi"? Zakiyyah ta fad'a tana kallon Rasheedat wacce ta ce "ai ina mata kawai har yanzu ban samu 'kofa bane".

"Hummm" kawai shine abinda Zakiyyah tace domin ita kam har ga Allah bata ga abun shishshigi a wanda ba ta kai yake ba duniya da fad'i idan wani ya'ki kuyi 'kawancen wani kana zaune zai zo ya kawo maka katin gayyatar ka yi abotar to meye a ciki.

Afifah kam tana shiga da sallama d'akin Zainab ta shiga ta same ta har ta hau kan keke tana d'inki murmushi ta yi tana cewa "kaga Hajiya chef Tailor mad'inkiya tsakani da Allah Zee-Zee baki kyauta min ba daga bari na zo na raka ki shikenan nan ki ka gudo"? "Eh akwai dalilin da yasa na yi hakan"?.

"Wanne dalili"?.

"A'a basai na fad'a miki ba".

"Ok shi ke nan Momy tace a fad'a miki ta gode sannan ga wannan" ta fad'a tana fito da doguwar rigar da turare ta aje mata zaro ido Zainab ta yi tana girgiza kai tace "a'a Afifah na gode dan Allah ki mayar mata" da mamaki Afifah tace "kamar ya na mayar mata"?.

"Saboda ni ban je dan na saka ta wahala ba"

"Kuma amfad'a miki dama ita ce ta ba ki rigar tawa ce fa Daddy ne ya siya mana kowa bibbiyu kwanan baya shine na d'auko miki".

"Duk da haka ki koma da ita na gode" mi'kewa Afifah ta yi tana kallon ta tace "wallahi tunda na kawo miki ita bazan koma da ita ba saidai ki mayarwa Momyn da kan ki ni na tafi sai zuwa jimawa idan mun je islamiyya" tana fad'in haka ta fita ta saka takalmin ta ta koma gida.

Aliyu kam sakamakon Momy ta ce masa Daddy yana neman sa shiyasa ya fasa zuwa in da zai je ya jira shi tukuna ya dawo idan su kai maganar ya tafi kar yazo yana neman sa Daddy kuwa bai dawo ba tun sha biyu da ya bar gida sai dare bayan sallar isha ya shigo shiyasa Aliyu ya bari da yayi wanka ya huta ya je a lokacin shi kad'ai ne yana garden a zaune sakamakon ko'ina da haske tarrr kamar da rana yana karkashin wata bishiya akan kujera da securities mutum biyu a tsaye suna gadin sa da sallama Aliyu ya je gurin amsa masa Daddy yayi yana nuna masa d'ayar kujerar dake gurin zama yayi shi kuma Daddy yayi wa securities d'in nuni su d'an basu guri za suyi magana matsawa su kai d'an nesa da su kafin su yi abin da za su yi kallon Aliyu Daddy yayi yana cewa "Aliyu dama tambayar ka nake so na yi magana ce akan aure shin ka shirya yi yanzu kana da wacce kake so"? Aliyu bai ta'ba kawowa a ransa wannan tambayar da Daddyn zai yi masa ba shiyasa ya d'ago yana kallon sa kai Daddy ya d'aga ya na cewa "eh kalle ni da kyau na ce akwai wacce kake so ko a'a idan baka da wacce kake so ni na samo maka" jin abinda Daddy ya ce daga 'karshe ya sa cikin fargaba Aliyu yace "a ina take Daddy"?.

"Ba ruwan ka da inda ta ke da farko ka fad'a min wacce kake so ko babu"? shiru Aliyu ya yi zuciyar sa na harbawa addu'a kad'ai yake Allah yasa ba Amirah Daddy ya hango masa ba Allah yasa ba ita zai ce ba.......................

"Aliyu".

"Na'am Daddy".

"Nace ka fad'a min in da yarinya take 'yar waye a wacce anguwa ta ke"? Numfashi da huci ya fitar lokaci guda yana d'an rufe ido ya bud'e tare da girgiza kai duk Daddy na hankalce da shi yace "uhum ina jin ka"? "Daddy a nan anguwar ta ke".

"A nan anguwar ta wajen ina"?.

"Gidan su Sameer 'kanwar sa ce".

"K'annin nasa mata guda nawa ne"? "Su biyu ne Bilkisu da Zainab".

"Ok na gane wacce daga ciki ka ke so"? "Zainab ce" baki Daddy ya bud'e yana kallon sa da mamaki ya ce "bayan neman ka da Momyn ku ta ce ina yi ta fad'a maka wani abu ne"? "A'a babu abin da ta fad'a min kawai cewa ta yi ka na nema na".
"Ok shikenan dama dalilin kiran kenan tun da na ji a inda take ya wadatar tashi ka je" har ya mi'ke zai tafi ya sake tsayawa yace "amma Daddy ban fad'a mata ba".

"Me ya sa zaman jiran me ka ke "?.
"Lokaci na ke jira".

"Oh! nan d'in baka fad'a mata ba idan kuma da wanda zata aura fa"? "Babu Daddy ai tasan da zama na saidai ba ta san ni bane kar ku shiga maganar har sai naje na same ta da kaina" murmushi Daddy yayi yana cewa "Ok yayi ba damuwa je ka" wucewa Aliyu yayi ya fita daga garden d'in sosai Daddy yayi mamakin jin abinda ya ke so ya tarar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login