Showing 81001 words to 84000 words out of 133788 words
Chapter 28 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA
rayuwar da mu kai a Spain gwanin burgewa".
"Da kyau ki huta lafiya" ya fad'a ya na 'ko'karin kashe wayar da sauri ta ce "ahh Aliyu wai har ka gaji da yin wayar da ni"?.
"A'a me ki ka gani"?.
"Na ji kuma ka na shirin kashewa"?.
"Eh zan sauka akwai abin da zan yi kuma kira na ake yi daga wajen aiki na yau daji za mu shiga" kai ta d'aga ta na sake sabon juyi ta ce "ok ba damuwa Allah ya fito da ku lafiya" "Amin thank" ya na fad'in haka ta ji d'it d'it aje wayar ta yi a gefen filon da take kwance akai ta na sauke numfashi ta yi shiru kamar me tunani sai kuma ta saki murmushi ita kad'ai ta fara magana.
"Aliyu kai ne mafarki na lokaci ya yi da zan fito na bayyana maka soyayya ta tun da naga kamar kai ba ka da ra'ayin furta min ba da wanda na dace na zama matar sa sai kai kuma in sha Allahu kai zan aura" tashi zaune ta yi ta na kallon agogo ganin har sha biyu na rana ta san yanzu ta na fita Mama fad'a za ta yi mata shi yasa ta mi'ke ta je tayi wanka da ta fito sai ta dau'ki takardun jarrabawar ta kamar gaske ta fita da su parlor ba Mama ba Nansy murmushi ta yi ta na samun kujera kawai ta zauna tana aje takardan a kusa da ita ta bud'e wayar ta ta hau WhatsApp ta fara chatting da 'kawayen ta.
** **
Sakamakon yau weekend ba aiki ga shi Baby ta kwana ta na mafarkin Shareef hakan ya sa da gari ya waye ta yi tunanin zuwa har gida ta gan shi har ta gaisar da Mami amma me? Tuna ya ce mata kar ta 'kara zuwa gidan su ya sa ta ja dogon numfashi tana d'auko wayar ta ta zubawa number sa ido ta dad'e daga baya ta danne kiran sa amma har ta katse bai d'aga ba ta sake kiran sa nan ma bai d'aga ba ji ta yi hankalin ta ya d'an fara tashi sake kiran sa ta yi karo na uku sai ta ji d'it alamar ya katse zaro ido ta yo firgice ta na kallon secreen d'in sai kuma ta ga na sa kiran ya shigo d'agawa ta yi ta na cewa.
"Hello barka da safiya Shareef ya ka ke"?.
"Lafiya ki na kira ina wanka ne shi ya sa ban d'aga ba yanzu na fito" jin abin da ya ce yasa ta sauke ajiyar zuciya cikin jin dad'i ashe ba 'kin d'aga mata ya yi ba baya kusa ne tace "ok ba damuwa dama abu zan tambaye ka".
"Me ne"?.
"Shareef dan Allah idan ba damuwa ka zo ina jiran ka za mu yi magana"?.
"A ina kenan"?.
"A inda ka ke so mu had'u".
"Kamar ya ban gane ba"?.
"Ina nufin ko gidan mu ne zaka iya zuwa dan girman Allah ka ji wallahi muhimmiyar magana za mu yi".
"Ok ba damuwa amma yanzu ba zan samu lokaci ba akwai in da zan je maybe sai wajen 'karfe uku ko biyar zan zo idan na kusa shigowa zan kira ki na fad'a miki" cikin farin ciki Baby ta ce "wayyo na gode Shareef sai na gan ka".
"Ok" ya fad'a yana aje wayar shiryawa ya fara yi sai da ya gama sannan ya d'auki wayar ta sa yana fita saukowa daga stairs ya ke yi yana kallon agogon dake d'aure a hannun sa ganin ba Mami yasa ya nufi hanyar kitchen yasan ba zai wuce ta na can ba iya Rabi ya tarar ta na aiki ba Mami fitowa ya yi ya dawo parlon kenan ya gan ta ta shigo ta na cire mayafin da ke kan ta tare da sauke numfashi ta na kallon sa ta ce.
"Wannan wanka haka ina za ka je"?.
"Gurin 'yar ki" jin abinda yace yasa ta saki murmushi ta na cewa "humm dama na san sai dai can d'in Allah ya sa rabon ka ce".
"Amin Mami daga ina ki ke ko dai anguwa ki ka je"?.
"Eh na je asibiti ne an kai Tasnin ba ta da lafiya" d'an zaro ido ya yi yana cewa "Subanallahi cousin sister na ba lafiya me ya same ta"? "Tasnin 'yar gidan 'kanwar Mami ce".
"Ina ganin ko haihuwa ce ko kuma lokaci bai 'karaso ba bana ce ba na baro su yanzu dai jikin da sauki".
"Ok alhamdulillah bari na je ni ma na duba sister na ta ya zan iya nutsuwa abokiya ta tana can a gadon asibiti Mami na tafi" murmushi Mami ta yi tana bin sa da kallo ta ce "ok sai ka dawo ka gaida min surukar ta wa".
"Za ta ji Mami" ya fad'a ya na fita motar sa ya d'auka daga gida gidan su Neehal ya fara zuwa su ka tafi tare asibitin a lokacin Tasnin ta na zaune da Umman ta su na ta zance kamar ba ita ce majinyaciya ba ganin Shareef ya sa ya murje ido ta na cewa "mu gudu ko mu tsaya mafarki na ke ne jama'a d'an uwa rabin jiki yau kai na ke gani yaushe rabon duniya da ayyaraye"? D'an hararar ta ya yi yana cewa.
"Kuma tsakanin ni da ke waye za'a wa irin wannan murje idon"?.
"Kai man rabon da na saka ka a ido na har na manta".
"Yau kin gan ni ai kema kin san ba zan je gidan auren ki ba tun da ni ne babba kuma ni namiji ne ko"?.
"Duk da haka amma kamata ya yi a sati ko sau d'aya ne ka ri'ka zuwa".
"Ba zan zo ba" ya fad'a ya na mayar da hankalin sa kan Umman ta ya ce "barka da safiya Umma ya mai jikin"?.
"Lafiya kalau Shareef ga ta nan alhamdulillah".
"Allah ya 'kara sau'ki".
"Amin wannan fa ko rakiya ta yo maka"?.
"Eh ta rako ni na duba gawa ta'ki rami ne" ya fad'a ya na kallon Tasnin wacce ta yi dariya ta na cewa "wace gawa ta'ki rami amma dai ba da ni kake ba"?.
"Eh da ke nake yarinya ga matar da zan aura nan" zaro ido waje Tasnin ta yi tana duba Neehal da mamaki tace "kai dan Allah da gaske kake babban Yaya"?.
"Da gaske man Auntyn ki ce".
"Wow masha Allah dad'i kashe ni kaji har na daina jin zazza'bin da na ke ji saboda farin ciki alhamdulillah sannu Aunty in-law ya kike"?.
"Lafiya kalau ya jikin na ki"?.
"Jiki alhamdulillah na samu sau'ki Yaya Shareef ashe kwanan nan zamu sha biki"?.
"A'a ba kwanan nan ba".
"saboda me"?.
"Saboda ba na so baki haihu ba ayi bikin na fi so sai kin samu lafiya dad'in yadda zaki je ki yi shagali a biki na ko"? Kai ta d'aga tana cewa "yauwa babban Yaya haka nake son ji Allah ya kai mu da alkhairi".
"Amin bari mu tafi" jin abinda ya ce yasa Tasnin 6ata fuska tana cewa "haba dan Allah ya tafiya kuma daga zuwan ku".
"Eh zan je na mayar da ita gida ne".
"Amma dan Allah idan an bani sallama za ka kai mun ita har gida mu sake gaisawa"?.
"Ok in sha Allahu".
"Ka yi alkawari"?.
"Kar ki damu zan cika miki ke dai Allah ya baki lafiya shine burin mu".
"Amin na gode Aunty na kin gaida gida sai na gan ki".
"To Allah ya sauwake" Neehal ta fad'a ta na gyara glass d'in fuskar ta kud'i Shareef ya ajewa Tasnin da d'an fruits kayan 'karin jini na mai ciki sannan su ka tafi ya mayar da Neehal gida su ka gama maganar da za su yi sannan ya koma gida....................
ZUCIYAR ALIYU CE
@YMA DUTSE
PAGE 52
Kamar yadda ya cewa Baby sai wajen 'karfe uku bai samu dama ba sai bayan sallar la'asar ya je gidan su humm samu yayi ta yi masa hidima ta kece raini abubuwa kala-kala ta d'au wanka ta na zaune ta na jiran sa ta ga kiran sa ya shigo alamar ya 'karaso tashi ta yi tana d'aukar mayafin ta ta fita yana waje a tsaye jikin motar sa hum kamar a mafarki haka ta ke gani wai yau Shareef ne ya zo gurin ta har gidan su day sallama ta karasa ta na kallon yadda ya d'au wanka ta ce.
"Sannu da zuwa Shareef bismilllah 'karaso ciki"? Kai ya girgiza ba tare da ya kalle ta ba yace "no ki barshi ba sai na shiga ciki ba za mu iya yin maganar mu anan".
Kai Shareef dan girman Allah ka zo mu shiga ciki".
"Me wai kina nufin gidan ku zan shiga"?.
"Eh amma ai ba cikin gidan ba sashin saukar ba'ki za mu je baya ala'ka da cikin gidan".
"Ok".
"Yauwa mu je" ta fad'a jiki na mazari ta yi gaba lock ya sakawa motar sa sannan ya bi bayan ta tsayawa ta yi tana cewa "ka shigo da motar ta ka harabar gidan man idan zaka tafi shikenan" kai ya girgiza ya na cewa "a'a bar shi kawai ai ba zama zan yi ba" jin abinda yace ya sa ta sauke numfashi duk da dama ta san sa'a taci ya zo mai gari ta 'kwallawa kiran ya fito da sauri ya zo yana cewa "ga ni Hajiya".
"Ka fita waje ka kula da motar da ta ke 'kofar gidan nan kafin me ita ya fito".
"To Hajiya" ya fad'a ya na juyawa ya fita "mu je Shareef" Baby ta ce tana ci gaba da tafiya kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa suka shiga ya ga yadda ta had'a abubuwa na alfarma iri-iri duk saboda shi zama yayi Baby data kasa nutsu jiki na rawa ta ce.
"Barka da zuwa gidan mu Shareef me zan yi serving d'in ka komai da ya ke nan na yi ne saboda kai" murmushi ya yi yana d'an girgiza kai tare da kallon ta yace "na gode da kulawa".
"Kar ka damu Shareef ko me na yi maka ban fad'i ba zaman tare ne ya kawo haka".
Kai ya jinjina bai sake magana ba juice ta zuba a cup tana mi'ko masa har zai girgiza mata kai amma sakamakon na dad'i ya sa ya kar'ba ya d'an kur6a ya na cewa "thank you" ajewa ya yi yana cewa.
"Uhum ina jin ki maganar me ki ke so mu yi da ke"? Gyara zama Baby ta yi tana sauke numfashi me nauyi tare da yin shiru ta na tunanin ta ina zata fara da wacce kalma za ta yi masa bayani yadda zai fahimce ta sosai..............
"Baby" taji ya kira sunan ta da sauri ta d'ago ta na barin tunanin da ta ke yi tace "na'am".
"Na ce me kike son fad'a min ki ke nema na har gidan ku"? Zazzafan huci ta sake fitarwa ta na kallon sa a sanyaye ta ce "duk da ban san ta inda zan fara yi maka bayani ka fahimta ba amma Shareef ina cikin matsananciyar damuwa a kan ka na rasa sukuni na rasa walwala duk saboda kai kullum ina tunanin yaushe ne zan daina shiga wannan halin amma na duba babu rana idan har ba samun ka na yi na fad'a maka ba" shiru ta yi ta kasa ci gaba Shareef da ya 'kure ta da kallo ya ce "uhum ina jin ki ci gaba" kai ta girgiza tana dafe goshin ta tare da runtse ido ta bud'e ta na cewa.
"Shareef ina son ka".
Bai yi mamakin jin hakan daga gare ta ba domin dama tun da tace za su yi magana abin da ya kawo a ran sa kenan gashi kuwa hasashen sa ya tabbata kai ya jinjina bai yi magana ba Baby ta sake cewa.
"Shareef ina son ka kasan tun yaushe na ke son ka? Huuuuuhhh ta sauke numfashi muryar ta ya fara rawa ta ce "tun lokacin da na fara ganin ka wannan dalilin ya sa na dage sai da ka san ni sannan na 'kulla ala'kar mutunci da kai a tunani na ta wannan hanyar ce kai ma za ka ji kana so na amma na ga tsawon shekaru ba wani canji shiyasa na kasa ha'kuri na fallasa maka asirin zuciya ta wallahi Shareef kai ne buri na kai na ke so ka zamo miji gare ni dan Allah kar ka ce a'a" ta fad'a ta na had'e hannun ta gurin d'aya alamar ro'ko kai ta ga ya girgiza ya na cewa.
"Dole na ce a'a".
A zabure ta ce "me ya sa"?.
"Saboda ni ban ta'ba jin hakan a rai na ba".
"A'a Shareef dan Allah ka daina cewa ba ka ta'ba ji ba zaka ji daga baya indai ka amince min zaka tsinci kan ka kamar yadda na ke a yanzu ina son ka son me mugun 'karfi wanda ban ta'ba yiwa wanin ka ba tun da nake ban ta'ba had'uwa da wanda na ji zan iya auren sa na zauna da shi ba sai kai please Shareef ka ce zaka aure ni kana sona"? Cije lips ya yi yana sake girgiza ma ta kai yace.
"Baby bazan iya soyayya dake ba balle rayuwar aure bana ra'ayi dan Allah ki fahimta bazan iya za6arki matsayin uwar 'ya'yana ba idan nayi hakan banyi musu adalci ba" rud'e Baby tace "haba Shareef me kake fad'a ne haka meyasa ba za ka iya soyayya dani ba balle ka aure ni ina da tauya ne"? Kai ya jinjina yana cewa "tawaya me girma ma kuwa ke ba ki gani ba ne"? jin abinda yace yasa ba arziki Baby ta fara kallon jikinta taga ta inda tauyar da yake fad'a take amma dai bata gani ba d'agowa tai tana kallon sa sai taga ya saki murmushi yana girgiza mata yatsar hannunsa alamar ba daidai ne abinda take hasashe bashi bane yace.
"Ba tauya a halittar jikinki ba nake magana tauya a dabi'un ki da mu'amalar ki da mutane ina hankalce dake sannan ina lura da duk wani motsin ki na gama karantar halayyan ki tabbas idan na aure ki ban yiwa yaran dazan haifa adalci ba ko kad'an".
"Me ye da dabi'un nawa Shareef"?.
"Wannan kuma kanki zaki yiwa wannan tambayar ba ni ba domin kinfi kowa sanin wacece ke nima na fahimce ki balle kuma ke kanki".
"Indai nice bana jin ina da wata matsala Shareef kawai ka fito fili kace so na ne baka yi bawai baza ka iya soyayya dani ba".
"Ba haka bane kar kiyi min gurguwar fahimta na fad'a miki gaskiyar abinda yake cikin raina ne ko mace yanzu ba ai mata auren dole balle namiji".
"Me hakan yake nufi"?.
"Bazan aure ki ba kuma kar fad'ar hakan ya sa ki kawo wani abu daban a ran ki".
"Dalilin ka nake son sani kawai ba abin da zan kawo a rai na ba".
"Bana maimaita magana saboda na fad'a miki hujja ta kin gane"? Shiru tai ta zuba masa ido zuciyarta tana tafasa da yasan yadda take azabtuwa da tsananin sonsa da baiyi mata jayayya akan son da tace tana yi masa ba taya zai fahimta taya zata gwada masa ya gane wacce hanya zata bi ita fa bata jin koda duniya ne suka taru akan ta rabu da shi zata iya..............
Maganar da kika kira ni muyi kenan ko da wata"? Taji ya katse mata tunani d'agowa tai tana kallon sa ta kasa cewa komai sai da ido take binsa gira ya d'auke yana cewa "ki huta lafiya" yana fad'in haka ya juya zai bar gurin da sauri ita ma ta mi'ke muryarta kamar zai fashe tace.
"Shareef dakata" tsayawa yayi ba tare daya juyo ba yace "uhum" ajiyar zuciya ta sauke tana takowa inda yake ta zagayo ta tsaya a gabansa yadda zai ganta ta fara magana "Shareef ya kamata ka tausayawa rayuwa ta ka dubi son da nake maka karka barni na fad'a gagari dan Allah ka samu lokaci ko nan da wata guda ne ko shekara ka zauna kayi nazari a kaina komai kake so nayi alkawari zanyi maka zan gyara halaye na".
Kaiya girgiza yana kallon ta kamar yadda ta kafe shi da ido yace "maganar zaki canza halayen ki wannan ba gaskiya bane domin hali tamkar zanen dutse ne bashi shafuwa koda kinyi kokarin canzawar daga baya zaki koma kan halin ki da ace zaki canza Baby da yanzu kin canza shekara ta nawa dake a hospital d'in nan ina fad'a miki abinda ya kamata ina miki nasiha amma bakya d'auka na gwada ki ta hanyoyi da yawa amma baki iya cinye jarrabawar da nayi miki ba some times nakan yi wani abu saboda naji me zaki ce a kai saina tarar kin 'kalubalancin abun koda ya kasance gyara ne ga rayuwarki sannan idan naga kuskure na nuna miki maimakon ki min godiya saidai ki nuna kinji haushi da tunatarwar da nayi miki yanzu Baby me irin wadannan halayen ce kike so na aura a tunani na ko baki furta min ba ni nazo miki da kalmar soyayya zaki ce a'a baki dace dani ba naje na nemi mace ta gari wacce idan na fad'a mata magana zata ji idan na bata umarni zata yi aiki dashi yanzu tsaya nayi miki misali kamar wannan budurwar da kika bugeta ranar da naje da basket hospital kece da laifi gashi wayarta ya 6aci maimakon ki bata ha'kuri sai bala'i kike mata harda marinta kuma ina miki magana kina dad'a daga muryarki akan tawa hakan gani kike ado ne? Na fad'a miki wani abu da zai baki mamaki kwanan baya mun had'u da ita a wani wuri abinda tace min tana sake bani ha'kuri akan wannan abun daya faru tsakanin ki da ita gashi ke da muka shiga office ina miki fad'a sai kika nuna abinda kikai shine daidai ko"? Hankali tashe ta ce.
"Ban yi tunanin hakan wani abu bane"?.
"Baki tunanin hakan wani abu bane ashe idan yayan ki yana miki fad'a a gidan ku bakya tunanin kiyi shiru ki saurare shi sannan ki bashi ha'kuri ko kece da gaskiya"? Shiru tayi jikinta yana tsumma ta sunkuyar dakai hawaye sai faman zuba mata yake da tasan Shareef yana komai dan ya gwada tane da ta zama cikin mata masu ha'kuri data kame kanki ta danne kowanne irin abu idan ya taso gashi yanzu tana gani duk yadda take son shi ya nuna halinta bazai barshi ya aure ta ba kuka ta fashe dashi tana girgiza kai ta kasa magana.
"Kuka bazai miki amfani ba kamata yayi kije ki zauna kiyi nazari sosai ki