Showing 99001 words to 102000 words out of 133788 words

Chapter 34 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA

dama Aunty Murjah ta san za su zo ita da Sameer su kawo Ikkin shi ya sa ta fad'awa Auwal shi kuma ya fad'awa Mukhtar zai zo su gaisa duk da Zainab ba ta sani ba sai da su ka je, su na zaune a parlor bayanta sun gaisa Zainab ta ce "to Aunty Murjah gashi na cika alkawari na dama kyan alkawari cikawa kamar yadda na d'auka na dawo miki da Ikki ki har gida" murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tace "ai kuwa tun d'azu Mukhtar ya zo gidan nan saboda na fad'a masa yau zaki dawo da ita yace za ku yi magana suna ta jira ganin baki zo ba basu dad'e da fita ba shi da Sweet" da mamaki Sameer ya kalli Zainab wacce ta had'e rai ya na cewa.

"Waye wani Mukhtar kuma" dariya Aunty Murjah ta yi ganin yadda Zainab ta ke dad'a cika ta ce "Mukhtar abokin Sweet ne ranar da mu ka je duba ta tare da shi ne dan dai ya na cikin mota ne a lokacin da ka je gurin na mu amma da za ka gan shi" kai Sameer ya jinjina ya na cewa.

"Son Zainab d'in ya ke ko kuma yaya ban gane ba"?.

"Eh man son ta yake sosai da gaske kusan shekara guda tun da ya gan ta tazo gidan nan da ace ta bashi fuska da yanzu an jima da yin bikin su domin tun a lokacin ya nuna min shi da gaske ya ke yi matsalar daga ita ne" ta'be baki Sameer ya yi yana cewa "ai kuwa ya had'a kan sa da wahala Zainab akwai wanda za ta aura ba rabon sa bace gara ki fad'a masa tun wuri ya nemi matar aure kafin lokacin ya 'kure masa" bud'e baki Aunty Murjah ta yi da mamaki ta zaro ido ta kalli Zainab wacce ta yi shiru kamar ba ita a gurin mai da hankalin ta kan Sameer ta yi ta na cewa.

"Dan Allah Sameer da gaske ka ke kodan ka dakatar da Mukhtar ne"?.

"A'a ba dan na dakatar da shi bane gaskiya na ke fad'a miki akwai wanda za ta aura" cikin matsuwa Aunty Murjah ta ce "to Masha Allah haka ake so ai waye wanda za ta aura dama kin tsayar da miji amma ba ki fad'a min ba da sai lokaci ya 'kure ko kuma ya"? Dad'a 6ata fuska Zainab ta yi tana juyawa musu baya ta'ki magana kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ni za ki tambaya domin ni ne na san shi ba Zainab ba" dariya Aunty Murjah ta yi tana cewa.

"Ah ah ban gane kai zan tambaya ba ita ba kenan ka fita sanin sa"?.

"K'warai domin ita wacce ki ke tambayar ita ma ba ta san waye ba".

"Ji Kayan tashin hankali ba ta san shi ba me akai kenan waye zaiyi irin wannan auren ka bar ta kawai ta auri Mukhtar d'in ya fi".

"A'a an riga shi".

"To in dai haka ne sai ka fad'i wanda ya riga shi mu ji waye"?.

"Wani 6oyayyan masoyi ne ba yanzu za ki san shi ba sai ya bayyana" kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "kai dan Allah Sameer please ka barta ta auri Mukhtar ka ji" saurin girgiza mata kai shima ya yi yana cewa "a'a akwai wanda zata aura ki fad'a masa kar ma ya ji cewar ya na da rabo an riga shi" ha6a Aunty Murjah ta ri'ke ganin yadda su ka d'aure mata kai ita Zainab ta juya musu baya shi kuma Sameer ya dage akwai wanda za ta aura, huuuuuhhh ta sauke ajiyar zuciya ta na cewa.

"To fa babba magana ni da aka ban sa'ko ya zan yi wannan al'amarin da nauyi" Zainab ta kalla ta na cewa "yanzu dai abin da za'ai idan ya dawo sai ki fad'a masa da kan ki domin ni ba zan iya ba ina jin kunyar sa" ta na rufe baki Sameer ya mi'ke ya na cewa "wallahi bai isa ba tashi mu tafi tun bai dawo ya same ki ba balle zuciyar sa ta ji dad'i idan ya gan ki" dariya Aunty Murjah ta yi tana kallon sa tace "kaii Sameer wannan har ka fi mai son Zainab d'in kishi irin wannan fad'a daga na fad'i haka ka tashi a zabure kamar an watsa maka ruwan wuta dan Allah ku tsaya man mu na hirar mu".

"Kin san Allah tafiya za mu yi da gaske fa nake miki ba zai dawo ya same mu ba Zainab akwai wanda za ta aura idan ma kin fad'a masa ya'ki yarda shikenan shi ya sani dabara ta rage ta shi ko ya ha'kura ko kuma ya ci gaba da wahala idan yaga ta yi aure ya yarda tashi mu tafi Zainab ko dai ke ma ki na son sa ne kar na bada kai na"? Kai Zainab ta girgiza ta na mi'kewa ita ma Aunty Murjan tashi ta yi ta rako su har harabar gida suka hau mashin suka fita daga gidan suka barta ta na ta dariya..........

ZUCIYAR ALIYU CE

J♣W♠A🤙

Story.Written.Editing
“‰YUSRAH MUSA ABUBAKAR

@YMA DUTSE JIGAWA
PAGE 63
Su na cikin tafiya Zainab da ta sauke daddad'an numfashi ta ce "na gode Yaya Sameer gara da ka fad'a mata haka nima na huta Allah da gaske ko kadan mutumin nan bai yi mun ba" jinjina kai Sameer ya yi yana cewa "balle kuma ni gara da bai yi miki din ba ai da ko yayi miki dole ki bar shi" murmushi Zainab ta yi tana cewa.

"Saboda me"?.

"Saboda Aboki na man yaushe ina kallo zan bari wani Tom ko Jerry d'in zai zo ya na hira da ke bayan shi ya na so".

"Ni fa Yaya Sameer abokin nan na ka bana saka shi a layin mutane da ace da gaske mutum ne da yanzu shi ma ya bayyana kan sa shekara kusan nawa ka na fad'a sai dai kullum ka ce zai bayyana har yanzu ya'ki bayyana d'in watakil ido ya bud'e maka kake ganin kamar mutum ne shi, ni dai ba ruwa na ba gara Mukhtar d'in ba tun da shi na gan shi da ido na kuma nasan mutum ne iri na da nayi soyayya da aljani fa"? Dariyar da ba shiri ta saka Sameer ya yi yana jinjina kai yace "da kyau kaiii da kyau tambaya me armashi, albishirin ki? To ki kwantar da hankalin ki ya kusa zuwa kwanan nan za ki gan shi in sha Allahu kun kusa had'uwa sai ki shirya tarbar sa" ya na rufe baki Zainab ta ja dogon numfashi ta na cewa.

"Uhmmmmm!!"

"Uhmm! kamar ya me ya faru"? Kai ta girgiza tana cewa "a'a babu komai" ta fad'a daidai sun 'karasa wani guri ya yi parking sau'ka ta yi shi ma ya sau'ka da mamaki ta kalli gurin ta na cewa "Yaya Sameer me za ka yi anan" key d'in mashin d'in ya cire ya na mi'ka mata ya ce "ri'ke min wannan ki jira ni yanzu ina zuwa" juyawa ya yi ya shiga cikin gurin ta na tsaye ya d'an jima kafin ta gan shi ya fito da plasma a hannun sa da mamaki ta kalle shi ta na cewa.

"Yaya Sameer me za ka yi da plasma kuma ko a d'akin ka za ka saka"? Kai ya girgiza yana kar6ar key d'in ya tada mashin d'in ya na cewa "a'a ba tawa ba ce sa'ko ne dama yau zan zo na kar6a shiyasa na ce idan za ki dawo da Ikram ki yi min magana sai mu taho tare hau mu je" kai Zainab ta d'aga ta na hawa ya saka plasma d'in a gaban sa su ka d'auki hanyar gida.
A 'kofar gidan ya aje ta, ta shiga sannan ya yi parking da mashin d'in shi ma ya shiga ya fara aje TV din ya dawo waje ya shigar mashin d'in ciki a lokacin an kusa kiran sallar magriba ya yi alwala ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan sallar isha su ka shigo tare da wani mutum sannan Zainab ta na d'aki ta ga Sameer ta yi ya shigo ya aje plasma d'in ya na cewa "ki fito daga nan ki shiga d'akin Umma wanda zai had'a miki TV ya zo" zaro ido ta yi a firgice ta nuna kan ta ta na cewa.

"Wai ka na nufin dama na wa ne"? Kai ya d'aga ya na cewa "eh man in ji aboki na ba" dafe kai ta yi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ni dai ina cikin matsala wai Yaya Sameer wanne irin mutun.................

"A'a ba sai kin ce komai ba na gane ki kwantar da hankalin ki ai na fad'a miki ya kusa zuwa ba za'a dad'e ba za ku had'u" ya na fad'in haka ya fita shiru Zainab ta yi zuciyar ta na bugawa da 'karfin gaske har Sameer ya shigo da mutumin ba ta iya tashi ba sai da ya sake le'kawa ya mata magana sannan ta mi'ke da'kyar ta na jan 'kafa ta fita ta shiga d'akin Umma, ita ma Umman ta na kallon ta kuma ta ga a yadda ta shigo sai dai ba ta da bakin magana akan wannan al'amari tun abun ya na damun idan ta gani ko tsoron a je a fad'awa Hajiya yanzu har ta watsar ko fargaba ba ta ji.
Har mutumin ya gama aikin sa Sameer ya biya shi ba wanda ya fito sai dai su na jin maganar su dad'in abun ma Asabe ba ta gidan ta yi tafiya ana biki a dangin su da ace ta nan da yanzu ta had'a musu kururuwa ta kirawo mutanen gidan nan, jin da Zainab ta yi shirun ya yi yawa yasa ta fahimci sun fita har Sameer d'in mi'kewa ta yi jikin ta a mace ta fice ta koma d'akin ta kawai kallon iya TV d'aga mata hankali ya ke rasa inda za ta saka kan ta, ta ji dad'i ta yi ta na jin lokacin da Sameer ya shigo ya na tambayar Umma abincin sa ta fito ta saka masa.

Ta na kwance idanun ta a rufe sai haske ta gani d'auu da sauri ta bud'e ido ta ga nefa aka kawo ga shi harda sabuwar 'yar yawo ta gani a gurin Sameer ya cire wancan tsohuwar ya saka mata sabuwa numfashi ta sauke tare da mayar da idon ta ji tayi Sameer yace.

"Yauwa an kawo nefa Zainab ki na d'aki ne"? Sake bud'e ido ta yi a hankali ta ce "eh ina nan".

"Ok" ya ce tare da yin shiru can kuma ta ji sallamar sa ya shigo ya na cewa "amma ba ki gwada kunnawa kin gani ko da akwai matsala ba"? Ya fad'a ya na kunnawa ya d'auki remote ya jawo kujerar da take d'inki ya zauna akai ita dai ta na gefen katifar ta da waya a hannun ta ba ta ce komai ba Sameer kam fita yayi ya koma d'akin sa ya d'auko abincin sa ya dawo d'akin domin so ya ke ya gani idan da matsala gari na wayewa zai kira mutumin ya zo ya sake saitawa sai kuma ya ga komai normal".
ZUCIYAR ALIYU CE

WRITTEN BY
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨

@YUSRAH MUSA DUTSE
PAGE 64
Duk abin da ya ke faruwa Bilki ta na daga d'aki ta na jin su kai ta jinjina cike da takaici ta fito daga d'akin tare da takowa cikin sand'a a hankali ta le'ka window ta ga yadda TV take walwalin sabuntaka ji ta yi sabon ba'kin ciki ya rufe ta kamar ta d'auko katon dutsi ta jefa TV ya fashe tsaki taja ta na fita daga 'kofar tasu ta shiga gurin Hajiya ta yi sa'a ita kad'ai ce kuwa babu kowa ganin ta tayi ta baje naman kazar da Aminu ya siyo mata sai dagwargwaza ta ke zama Bilki ta yi tana cewa.

"Tabd'ijan Hajiya ban ba ki labari ba kin san...................

Tun kafin ta fad'i abin da take son fad'a Hajiya ta tare mata numfashi da fad'in "wani abu ne ya faru a gidan nan"? .

"K'warai kuwa Hajiya gagarumi ma".

"A ina su waye"? Cizon yatsa Bilki ta yi tana cewa"a 'kofar mu man d'azun nan Yaya Sameer ya shigo da wata 'katuwar TV na d'auka shi ya siyo wai ashe ta Zainab ce mai sakawa har yazo ya saka mata a d'akin ta ya saita mata tashoshi yanzun nan da aka kawo nefa Yaya Sameer d'in ya shiga d'akin ya kunna ba ki ji yadda 'kara ta ke tashi ba a 'kofar mu kamar gidan DJ" zaro ido Hajiya ta yi ta na daina cin naman ta ce.

"TV kuma uban wa ye ya siya mata"? Kafad'a Bilki ta d'aga ta na cewa "taya zan sani Hajiya mafita d'aya ce kawai ki kira shi Yaya Sameer d'in ki takura masa ya fad'a miki wanda ya bashi ya kawo mata duk tsiya ai shi ya sani dashi ake had'a baki ana duk wata barna ta 'kofar mu domin duk wani abu da za ki gani a gurin Zainab shi zai kawo ya ce in ji abokin sa gashi har gobe abokin na sa ya'ki ya bayyana a san waye ai ko ta nan Hajiya ya kamata ki san 'karya su ke kawai raina ma na hankali za su yi dan kin ga misali kwanan bayan nan lokacin da ba ta da lafiyar d'in nan da ace ciki ne da ita wallahi Yaya Sameer za ku ritsa ya fad'a muku gaskiyar komai tun da duk wani abu da za'a kawo shi ne manaja da hannun sa komai zai zo gurin ta a hakan dan ma ba'a 'kofar ki ke ba da takaici ne zai kashe ki idan ki ka ga irin bushashar da ya ke kawo mata kala-kala naman kaji da na shanu kayan 'karfi zaki gan shi ya kawo mata ko chocolates da biscuits sai kace yarinya balle kuma su Faro da yogurts wadannan ai idan ana sallah ba'a magana Hajiya ku da ba ku sani ba shi ya sa hankalin ku ya ke kwance amma mu da muke 'kofar za'a kawo komai a gaban mu ba'kin cikin da mu ke sha'ka ya yi yawa ga masifar rowa ko zaka mutu ba za ta baka ba" ko kad'an bakin Hajiya ya'ki rufuwa tun da Bilki ta fara magana har ta kai 'karshen kai kawai take jinjinawa ta ce.

"Kan bala'i dama irin abubuwan da suke faruwa kenan a 'kofar ta ku ban sani ba ko shi yasa na ga kwanan nan Abdullahi ya yi 'kiba har da naman wuya ashe dad'i ya ke ci ni ina nan a 'kai'kashe wato ga tsohuwar banza wacce ba ta da daraja sai a idanunsa bare humm ya yi kyau koda na ji shiyasa idan na tambaye shi kud'i ba musu yanzu zai d'auka ya bani ashe sabuwar rayuwa ya canza? Ai kuwa zan ci mutuncin sa zai zo ya same ni tashi ki je ki kira min Samar d'in shi ma wani munafikin ya zo na ji uban waye ya ke aiko shi da kaya gurin Zainab d'in yau sai na ci uban sa tashi ki kira min shi na ce".

Zaro ido Bilki tayi tana cewa "tab ni ce zan kira shi so ki ke ya karya a gidan nan gashi Umman mu ba ta nan Baban mu kuma ba laifin sa ya ke gani ba gaskiya indai nice na kira shi cewa zaiyi ni na fad'a miki ki bari d'an wata 'kofar ya shigo sai ki aika masa".

"To shikenan Allah ya kawo wani d'in yau ba zan yi barci ba sai na yi magana da Samar a gidan nan ko da ace zan samu nutsuwa" tashi Bilki ta yi ta na cewa "bari na nemo miki wani yaron sai ya kira miki shi" to Hajiya ta ce Bilki kuma ta fita ganin babu kowa ya sa ta le'ka 'kofar su Zakiyyah 'kanin Rasheedat ta gani a zaune ta ce.

"Yauwa kai Adam ka je Hajiya ta na kiran ka yanzu" ta na fad'in haka ta juya 'kofar su ta koma da sauri ta fad'a d'aki a lokacin Sameer kam ya dad'e da fita a gidan Zainab kuma barci ma ya d'auke ta, sallama Adam ya yi shigo ba wanda ya amsa tun da duk sun yi barci shi kuma Sameer ya na waje le'kowa Bilki ta yi ta na cewa "Adamu ka tafi chemist d'in sa ya na can baya gida" ta na fad'in haka ta saki labulen ta koma fita ya yi daga gidan ya tafi chemist d'in ya fad'awa Sameer Hajiya ta na neman sa bai yi mamaki ba kuma ya na ji yasan dalilin kiran ba zai wuce wani ne yaje ya fad'a mata ya kawowa Zainab TV ba, humm mutanen gidan nan su na da abun haushi bari ya je yaji me za ta ce masa tun da dama dare ya fara yi goma har 'yan mintuna rufe chemist d'in ya yi ya tafi gida gabadaya idan ya fito daga gurin Hajiya kawai sai yayi kofar su.
Ya na shiga kuwa abun da ya ke tunani ko sallama da yai ba ta amsa masa ba ta fara magana "kai Samar 'karshen alewa 'kasa yau sai ka fad'a min uban waye abokin ka wanda ya ke aiko da abubuwa ka ke baiwa Zainab haukan ya yi yawa abun ya wuce inda hankali zai d'auka alhali ku na da nagaba da ku amma ba mai tambayar ku saboda ba sa son su 6ata muku rai tun da zilamammu ne ku na d'an ba su wani abu ko kwanan baya ka shigo da firiza yau kuma har da kayan kallo duk waye ya ke aiko ka"? Kallon ta ya yi yana jinjina kai ya ce "tsinannan munafikin da ya ke zuwa ya fad'a miki gulmar ya zo kenan ya yi kyau amma ya manta bai fad'a miki har da katifa ba da yadin gado da fanka duka na kawo mata"? Zaro ido Hajiya ta yi tana cewa "au har da katifa da fanka kuma wai har da yadin gado kamar wacce ta kama d'akin mijin ta? na shiga uku ina raye a gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login