Showing 102001 words to 105000 words out of 133788 words
Chapter 35 - KOWACCE `KWARYA Ƙaddarar Zama Matarsa By YUSRAH MUSA
nan an mayar da ni gawa wacce babu ita a duniya" tsayawa ta yi tana kallon Sameer ta ce "Samar uban waye yake aiko ka, ka fad'a min tun mu na mu biyu kafin na tara maka jama'a kasan Allah daga shi ba wani idan ba ka fad'a min ba sai nasa dukkan samarin gidan nan sun ri'ke min kai na ba su igiya su d'aure ka nasa Habibu da Aminu su yi maka dukan tsiya idan ba ka fad'a min ba" ta na rufe baki Sameer ya she'ke da dariya ya na dafe goshin sa tare da ri'ke ciki kai Hajiya ta jinjina ganin yadda ya ke dariyar ko tsayawa ba ya yi yasha numfashi ta ce.
"Hummm! dole ka yi dariya tun da ga mahauciya ta na maka magana ka mayar da ni ban san abin da na ke ba" tsagaitawa ya yi yana zama a kusa da ita ya ce "Hajiya kin sani dole na zauna" ya fad'a tare da gyara zaman sa ya ci gaba "ni fa dariyar ce tazo min lokaci guda sakamakon nishad'in da nake ciki amma ba abun da ki ka fad'a ne ya sa ni dariya ba sannan maganar kayan da ake kawowa Zainab wannan gaskiya ne haka yake wanda ya ke son ta ne yake siya mata kuma auren ta zaiyi ya kusa zuwa kwanan nan za ku gan shi in sha Allahu".
"Wanene shi"?.
"Ki yi ha'kuri Hajiya ba zan iya fad'a miki ba za ki san shi amma ba yanzu ba sai lokacin da ya zo" ido Hajiya ta zuba masa ganin haka yasa yayi murmushi ya na cewa "ki yarda da ni gaskiya na ke fad'a miki" kai ta girgiza ta na cewa.
"Ka ga Samar ba na son munafirci ka fad'a min waye"?.
"Kaiii Subhanallahi Hajiya ki na da son ayi ta maimaita magana nace ba zan yi iya fad'a miki ba idan na yi haka ban ri'ke amanar da na dauka ba".
"Har wacce amanar ce wannan kuma idan ba mutum ba ne ya za ka biya bashin aljani da ka ke d'auka irin wad'annan dukiyoyi"?.
"Mutum ne man".
"A ina ya ke d'an waye a garin nan"?.
"Dan Allah Hajiya ki bar yi min tambaya a kan sa domin ko kashe ni za ki yi ba zan fad'i waye ba duk ranar da ya bayyana kwa gan shi" ya fad'a ya na mi'kewa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "kar ka fad'a d'in d'an me ba'kin hali wata uwar zan ce idan ka fad'a min ko kana tunanin zan cinye shi mayya ce ni"?.
"A'a ni fa Hajiya ba ki ji haka daga baki na ba, duk abin da zan ce miki ba za ki ta'ba fahimta ta ba kawai sai da safe" ya na fad'in haka ya juya ya fita ya bar Hajiya ta na fad'a kamar ba za ta daina ba daga baya kuma tayi shiru tun da wanda ta ke fad'an dan shi ya tafi ba jin ta ya ke ba.
** ** YUSRAH MUSA ** **
Chat with me.
+234 8160983083
WhatsApp number
YMA DUTSE JIGAWA STATE.
1_💓Mai alfaharin jiha ta ce
2_🚗Ko'ina na ke inda zan zarce
3_🇳🇬A cikin Nigeria mu ke da gada mun taka kan Dutse
4_🌃Birnin daraja daya batse
5_🏜️Ga haske
6_🏞️🏔️Ga adon Dutse👍💙💃💚
💛JIGAWA TARON ALLAH💛
@YUSRAH MUSA
PAGE 65
Baby ba ta ta'ba tunanin da gaske Shareef zai iya auren wata mace bayan ita ba saboda ganin irin sha'kuwar su ta d'auka idan yaga ta nutsu ta kame kan ta zai tausaya mata amma ta ga ba canji jiya iyau,
Kamar kullum yadda ta saba yau ma lokacin da ta zo hospital ta ga motar sa amma kuma ta yi iya neman ta bata gan shi ba har ta ha'kura ta samu guri ta zauna tana zaune tayi tagumi 'kawarta Badiyah ta karaso gurin tana zama tace "ke Baby ina ta neman ki ashe ki na nan ban sani ba"? Kallon ta Baby ta yi cikin yanayi na rashin jin dad'i za ta yi magana Badiyah ta ce "tsaya ma na tambaye ki wai dama Shareef aure zai yi ne"? Sake d'agowa Baby tai jikin ta yayi mugun sanyi da'kyar tace "taya kika sani waye ya fad'a miki"? Wani d'an littafi ta d'auko daga jakar ta wanda bangon sa yake d'auke da sunan su alamar an yi mu su engagement mi'ka mata ta yi tana cewa "waye ya fad'a min kuwa bayan ga sheda nan na gani da ido na kalli man" kar'ba Baby tai hannunta na kakkarwa ta fara dubawa wani irin zaro ido waje tayi tana zabura a rud'e tace.
"Mene wacece Nihal Alhaji Mustapha kuma"? Kai Badiyah ta girgiza tana cewa "oho duniya da fad'i taya zamu santa tunda ba a hospital d'in nan take ba amma dai kamar naji ance 'kanwar Doctor Ammar ce fa" kamar idon Baby zai fito waje ta ce.
"Kanwar Ammar kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa tare da komawa da sauri ta zauna tana ri'ke kan da hannu biyu ta runtse ido sakamakon wani irin ciwo daya sara mata lokaci guda dafa ta Badiyah tai tana cewa.
"Baby kina lafiya kuwa meya faru"? D'agowa Baby tai tana kallon Badiyah maimakon ta bata amsar data tambaye ta sai kawai ta fashe da kuka mamaki ne 'karara ya bayyana a fuskar Badiyah harta kasa gane me hakan yake nufi karshe tunani ya bata kodai son Shareef take shine dalilin wannan kukan nata shiru tayi ta zuba mata ido harta gaji ta share hawaye tana sau'ke ajiyar zuciya.
"Wai Baby me ya ke faruwa ne kukan me ki ke yi"?.
"Dole na yi kuka Badiyah 'kanwar Ammar fa me saka glass d'in nan wacce kwanan baya muka ganta tare da kanwarta harta buge mata glass d'in ya fad'i Shareef ya fito ya d'auka ya ba ta" kai Badiyah ta jinjina ta na cewa "kenan dama son ta ya ke" zazzafan huci Baby ta fitar tana sake kallon littafin memo d'in ta cije lips cike da takaici ta ce.
"Taya zan sani bayan ba fad'a min yayi ba amma sai dai daga baya yake sonta domin ranar haduwar su ta farko bai santa ba a kanta har fad'a mu kai da shi ban manta ba" d'an murmushi Badiyah ta yi ta na cewa "abun mamaki zuciya kenan mai son abinda take muradi daga had'uwar su shikenan nan ya kamu da son ta irin haka ake so wallahi ka so mutum dan Allah" jin abinda Badiyah tace yasa Baby sake cije lips d'in ta har ta fara huda shi da ha'kori amma ko zafin ba ta ji rad'ad'in da ya ke cin zuciyar ta yafi wanda ta ke ji akan lips d'in na ta kallon Badiyah kawai take cikin takaici tace "na rasa me yasa Shareef yayi min haka meye bana dashi meye zanyi ya burge shi ya rasa a inda gayun nasa zai 'kare sai a kan nakasasshiya me ciwon ido ki na kallo fa a ranar da 'kanwar ta ta, ta buge mata glass d'in bata gani fa saida shi in ta cire kamar dare haka take ba ta ganin komai" jinjina kai Badiyah ta yi tana cewa.
"Eh a hakan yaji zai iya zama da ita baki san dalilin sa ba akwai abinda yasa ya za6i ya aure ta kuma ya kamu da son ta".
"Ba wani dalili Badiyah dan ya wula'kanta ni yayi haka nasan shine dalilin sa ba komai ba yana so ya nuna min idan ni bansan ciwon kaina ba ga wacce ta cancanta zamowa abokiyar rayuwarsa ne".
"To ke meye ruwan ki a ciki ko son sa ki ke"?.
"Ke za'a yi wa wannan tambayar idan ina son sa ma kin sani idan ba na son sa nan ma kin sani shekarar mu nawa tare da ke a hospital d'in nan ina da wata 'kawar bayan ke"?.
"A'a ba ki da ita amma Baby a tunani na sirrin zuciya sai me ita taya ba ki ta'ba fad'a min ba kawai zan san ki na son sa? Amma yanzun na fahimta sai dai zan baki shawara dan Allah ki cire damuwar dake damun ran ki wai tsaya ma na tambaye ki kina kallon fuskar ki a mirror kuwa kin ga yadda ki ka koma kamar skeleton".
"Hummmm!!" Kawai shi ne abin da Baby ta ce domin a halin yanzu yadda take ji ba ta san da yadda zata kwatantawa Badiyah ta fahimta ba ita kuma da take jin zafin da ciwon ba ta san ya zatai ba sake sau'ke ajiyar zuciya ta yi ta na mi'kewa ta ce "ina zuwa yanzu zan dawo".
"Ok" Badiyah ta ce Baby kuma ta bar gurin cikin hospital d'in ta shiga sosai ta ri'ka tambayar doctor's da nurses ta na neman sa har sai da ta samo shi ya na can yaje wajen wani abokin sa a 6angaren 'yan surgery tuni zuciyar ta ta fara tashi ta na yun'kurin amai sakamakon kallon mutanen da su ke gurin gabadaya abun ba kyan gani da'kyar ta wuce ta shiga ciki su na office tare su na magana ta shiga da sallama tare da tsayawa daga jikin kofar ta na kallon Shareef wanda shi ma yake kallon ta tace.
"Shareef dan Allah ina so za mu yi magana".
"Ok nan ma maganar mu ke ki jira ni a waje ina zuwa".
"Wai a gurin wad'annan 'yan surgery masu 'konannan jiki zan jira ka"?.
"Eh idan ba za ki iya ba ki tafi can wajen office d'ina ina zuwa".
"Gaskiya sai dai na tafi can d'in na jira ka amma wa zai iya kallon wannan kayan 'kyan'kyami haka" kai ya jinjina yana d'agowa ya kalle ta ita kuma ta juya ta fita ta bar sashin a wani guri inda wasu kafafun kujeru su ke ta zauna ta na jiran sa kafin ya fito jin ana kiran wayar ta yasa ta fito da ita daga cikin jakar ta ganin Badiyah ce ya sa ta ja tsaki ta na maida wayar ta d'auko ruwa ta bud'e robar shi ma kur6a kad'ai ta yi ta mayar ta d'aure ta d'auki karamin towel ta goge bakin ta tare da kallon agogon da yake hannun ta taga lokacin tashi ma ya yi dafe goshi ta yi tana buso iska daga bakin ta tare da mi'kewa ta fara zaga gurin kafin ya fito ta d'an jima amma har lokacin shiru tunani ta fara yi kodai ba zai fito bane shanya ta ya yi ta na cikin haka ta hango shi sun fito tare da wancan doctor d'in ya mi'ka masa hannu sun gaisa ya koma Shareef kuma ya taho wajen inda ya gano ta numfashi ta sau'ke ta na d'aukar jakar ta, ta nufe shi fara tafiya su kai akan doguwar verandah irin ta asibiti.
"Uhum fatan dai lafiya ina jin ki me ya faru"? Dakatawa da tafiyar da take ta yi ta na fuskantar sa sosai ta zuba mi shi ido kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce.
"Shareef da gaske ne"?.
"Da gaske ne me"?.
"Da gaske ne aure za ka yi"? Zaro ido ta yi farko da ta ga ya girgiza masa kai ta d'auka ko bai san da zaman wancan littafin ba har ta fara jin sanyi a ran ta sai kuma ta ji ya ce.
"Ana aure da wasa ne"?.
"Kenan abin da na gani d'azu ba 'karya ba ne"?.
"Me ki ka gani"?.
"Memo na engagement d'in auren ka da wannan yarinyar".
"Wacce yarinya kenan"?.
"Kai zan yiwa wannan tambayar tun da ka fi ni sanin ta ai" kai ya jinjina su na ci gaba da tafiya ya ce "ya yi kyau" daga haka bai sake magana ba ita ma shiru ta yi tunani iri-iri sun cika mata zuciya har su ka 'karasa ya rufe office d'in sa sannan su ka je wajen aje motoci tana tsaye ya shiga ya tafi ba maganar da ta sake had'a su kamar ta had'iyi zuciya ta mutu haka take wani irin takaici da d'aci ya na ma ta yawo a ma'kogoro da'kyar ta tafi gurin motar ta ita ma ta shiga ta nufi gida tu'kin ma ba sosai take kula da titi ba hankalin ta duk nema ya ke ya fita daga jikin ta kafin ta je gida zazza'bi ya rufe ta, ta na parking kuwa ko key ba ta zare ba balle ta tsaya d'aukar handbag kawai kofar parlon su ta bud'e ta shiga Mom d'in ta tana zaune ganin a yadda ta shigo tana layi kamar wacce tasha abun maye yasa tasowa da sauri ta na cewa "Subanallahi Baby ke Baby lafiya"? Ba ta iya ba ta amsa ba sakamakon idonta ya gama rufewa ba'ki kawai take gani luuuu hajijiya ta d'ebe ta tayi baya zata fad'i da sauri Hajiya Fatima ta tare ta tana ri'ke ta a jikinta tare da 'kwalla kiran........🖋️ Typing sai gobe in sha Allahu.
ZUCIYAR ALIYU CE.
................PAGE 66
"Aminah Aminah ki na ina sauri ki zo" da sauri wata mace ta fito daga wata kofa da kayan aiki a jikinta da alama kitchener ce karasowa tayi tana cewa "gani ranki ya dad'e" a rud'e Hajiya Fatima tace "d'auko min ruwa a fridge yanzu kiyi sauri Baby ce ta ke suma" juyawa tayi ta gudu ta d'auko mata kar6a tayi ta bud'e ta d'an tsiyaya ta shafa mata a fuska ta 'kara shafa mata shiru kamar gawa sai numfashin ta da yake kai komo shi ne kad'ai zai tabbatar maka tana da rai kusan awarsu guda sannan ta sauke nannauyan numfashi amma ba ta bud'e ido ba cikin kulawa Hajiya Fatima ta d'an girgiza ta tana cewa.
"Baby Baby bud'e idon ki" a hankali Baby ta ke jin tashin maganar mahaifiyar tata da'kyar ta bud'e idonta da sukai nauyi suka zama ja tana kallon ta kafin ta yun'kura a hankali ta tashi zaune d'aga ta Hajiya Fatima ta yi ta 'karasa shiga da ita parlon ruwan dake gora na hannun ta, ta mi'ka kur6a d'aya tayi ta aje tana dafe kai ido Hajiya Fatima ta zuba mata tana mamakin meya sameta ta fita lafiya 'kalau ta dawo a haka.
"Baby ki na lafiya"? Kai ta girgiza numfashin ta na fita da zafi ta ce "Mom kai na ciwo ya ke kamar zai fashe jiki na da zazza'bi na dawo zuciya ta zafi ta ke min" ta fad'a ta na dafe saitin zuciyar ta zaro ido Hajiya Fatima ta yi tana kallon ta ta ce "Subanallahi har da zafin zuciya Baby wai me ya same ki ne nasan dai lafiya kalau ki ka fita daga gidan nan ko wa ya 6ata miki rai fad'a min"? Shiru Baby ta yi hawaye ya na zuba mata da ace yadda take samun komai daga gurin mahaifan ta yadda ba ta san rashi ba ina idan ta sanar musu su yi 'ko'kari su taimake ta kar ta rasa Shareef a rayuwa yardar sa da auren sa kawai yanzu shi ne matsalar ta...............
"Wai Baby ba za ki fad'a min abin da ya ke damun ki ba ki na ganin kukan shi ne mafita"? Kai baby ta girgiza ta na cewa "koda na fad'a miki ba ki da maganin matsala ta Mom duk duniya ba wanda zai iya min maganin ta sai Allah".
"To ai ke ki na da matsala kuka ba zai kai ki ba tashi za ki yi kije ki yi alwala sai ki yi sallah ki fad'awa Ubangiji damuwar ki zai yaye miki duk wani ba'kin ciki da ki ka tsinci kan ki haba dan Allah kamar bakya zuwa islamiyya ya kamata ki dawo hayyacin ki mana komai yai zafi maganinsa Allah ne ki share hawayen ki, ki tashi ki je kiyi sallah" kai Baby ta d'aga tare da mi'kewa ta shiga part d'in ta shiru Hajiya Fatima ta yi cike da tunanuka iri-iri a ran ta akan abin da ya ke damun Babyn tun da har ta ga ta'ki fad'a mata to fa ba 'karamin abu bane.
Ta na nan a zaune har Daddy ya shigo shi ya sa ko numfashi bai gama saukewa ba ta fad'a masa komai ya ce ta kira masa Babyn tashi ta yi ta shiga kamar yadda take tunani haka ta tarar ta a zaune ta zuba uban tagumi da hannu biyu ta yi shiru kai ta girgiza ta na cewa.
"Baby".
Shiru ba ta amsa mata ba alamar tunanin da take ta yi zurfi 'karasa shiga Hajiya Fatima ta yi ta na d'an girgiza ta ta ce "Baby" a firgice ta d'ago da jan idon ta tana kallon Hajiya Fatima wacce ta ce "wai ke meye haka ne sai kin kashe kan ki yau d'aya mtwwww ki zo Daddyn ki ya dawo ya na son ganin ki" ta na fad'in haka ta juya ta fita ajiyar zuciya Baby ta sau'ke tare da mi'kewa jiki a sanyaye ta fita tun su ka ganta duk su ka zuba mata ido kowa cike da tsantsan mamakin yadda ta mayar da kan ta abar tausayi lokaci guda, zuwa ta yi ta zauna tare da yin 'kasa da kan ta tace "Daddy ina yini"? Kai ya jinjina ya na cewa "lafiya 'kalau daughter me ya same ki ne yau"? Jin tambayar da ya yi mata yasa ta 'kara 'kasa da kan ta ba ta ba shi amsa ba".
"Ok ba za ki fad'i abin da ya ke damun ki ba sai na kira miki Hakeem ko"? Jin ya ambaci Hakeem yasa ta girgiza kai da sauri ta na cewa "dan Allah Daddy ka yi ha'kuri".
"Na ji amma zan ha'kura ne kawai idan har ki ka fad'a min gaskiyar lamari me ya ke damun ki"? Hawaye ne ya fara zuba mata bakin ta ya'ki bud'uwa balle ta samu damar iya fad'a masa kuka kawai ta fara yi tun ta yin sa a hankali ciki-ciki har ya fito fili daskarar da su ta yi suka saka ta a gaba kamar TV su na kallon ta babu wanda ya ce ta yi shiru a cikin su waya Daddy ya d'aga ta ji zai yi kira cikin kuka ta ce.
"Dan Allah Daddy kar ka kira Yaya Hakeem ka bari zan fad'a maka ba ni da lafiya zazza'bi na ke yi"? Ta na rufe baki cikin fad'a