Showing 21001 words to 24000 words out of 24909 words
tace"muje muga meye ".a tare suka fito nan suka iske Mama,Mummy ,Daddy da Amaan kowa yayi tsaye kamar ruwa yaci shi.wani wawan maruka ya zubawa Fadila Wanda ya haddasa mata daukewar wuta na tsawan mintuna kafin razananniyar tsawarshi ta dawo da ita cikin hayyacinsa yace"Dan uwarki waye yayi maki ciki?"tambayarsa ta girgiza kowa a wurin a matuk'ar mamaki Mummy tace"Ahaad bansan iskanci ya zaks rik'a had'a y'ata da wannan alkaba'in?"."to ko result zai mata karyane"ya fad'a tare da bawa Mummy takardar.kuka Fadila ta saka,wani kukan kura yayi ya damk'ota yahau jibga kamar zai cire mata rai,kanta ne ya bugu da table ta saki wani muguwan k'ara,da gudu Najma da Nani suka fito.ganin yana k'ok'arin takata yasa Najma saurin duk'awa gabansa ta rike k'afar tace"Yaya dan Allah kayi hakuri karka kasheta",lumshe idonsa yayi sannan ya bud'e da sauri Najma ta sakeshi tayi baya saboda yadda ta razana da ganin kwayar idonshi yau Sulaiman Ahaad dinshi yake sak,cikin kakkausar murya yace"koki fad'amun waye ko Kuma yau banga me rabani dake ba wallahi,y'ar iska kawai"ganin da gaske Ahaad hallakata zaiyi cikin kuka tace"wallahi Yaya ba result dina bane,na Najma ne,itace tayi fitsarin bani ba"zaro ido yayi ya maido kallonsa ga Najma yace"da gaske take?,I mean kece akayiwa awo da sunanta"shiru Najma tayi ta kasa fahimtar komai,cikin tsawa wacce ta haddasa mata juyawar ciki yace"answer me".bata iya magana ba Kai kawai take gyad'awa alamar eh,wani irin sanyi jikinsa yayi kan chair ya fad'a tare da dafe kansa dake barazanar tarwatsewa,"cikin shege a jikinki Najma"Mummy ta fad'a da k'arfi.a matuk'ar firgice Najma ta d'aga tana bin Mummy da kallon tambaya juyowar da zatayi sukayi ido biyu da Aiban,ji tayi ta k'ara shiga firgici da k'yar ta harhad'o kalmar"ciki...ku..ma,Mummy ni"
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe.
For comments ko shawara 07033636337
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Telegram
Maryam majidadi
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 56-60
"To ko baki yarda da me takardan ya k'unsa bane?,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,haba Najma ina ganinki me hankali ashe abun kunyar da zaki ibo mana kenan,kaf zuri'armu babu mai cikin shege sai ke"Mommy ta k'are maganar tana sharar hawayen k'arya.d'ago Najma tayi cikin rud'ewa tace"haba Mummy ya zaki rik'a had'ani da irin wannan ?,ni banyi zina ba,ni banyi komai "ta fad'a da k'arfi.cikin zafin zuciya Ahaad ya taso yayo kanta wata irin shak'a yayi mata tare da zuba mata kyawawan maruka har guda biyu,jibgarta ya shigayi ta ko ina bayaji baya gani,Najma kam banda ihu babu abunda takeyi,da gudu Nani ta iso gareshi ta rike masa hannuwa duk biyu tace"ka barta haka,y'allabai kayi hakuri komai ya faru bada saninta b....."had'iye sauran maganarta tayi lokacin daya ingijeta ta fad'a k'asa.cikin wani irin zafin zuciya Najma da maganarta ke fita da k'yar tace"karka Kuma wannan kuskuren a rayuwarka,zan iyayin komai akan Nani na,ita ta zame min uwa madadin mahaifiyata duk abunda uwa kewa yaranta ita keyimun,shin tsawon lokutan nan kasan ta yarda na rayu?,ni ako yaushe ina girmama mahaifiyarka,babu dadi ka wulak'anta wacce take matsayin uwa a gareni tayimun abunda dukanku jinina kuka kasa yimun"k'ara sha'areta yayi da k'arfi,wani ihu Mama ta saka tace"na shiga ukku abun naka bana hankali bane,labcecen banza,wallahi ka bigi Bilki gata nan tsaye a gabanka munafiki,komai ya faru ae laifinka ne,yarinya ta kai minzalin aure aeya kamata ka kula da ita amma saboda bak'in hali irin naka kaki saurarena wallahi ka sakarmun jika kafin hukuma ta shiga tsakanina da kai da wannan uwar taka me lak'awa jikata cikin shege"ganin ko sauraren Mama bayayi yasa Aiban shigowa da sauri shida Shuhada ,cikin zafin rai Aiban yace"haba Ahaad kayi hauka ne?,tashin hankali baya warware tashin hankali,in rai ya b'aci hankali yabar gushewa,tana da juna biyu saika janyo wata matsalar kuma?,ka saketa yanzu",dafa Ahaad Shuhada tayi tace"Dan girman ubangijinmu Allah kayi hak'uri ka sassautawa zuciyarka ka saki Najma,karka kasheta "kuka ta fashe dashi,wani irin muguwan harara ya wurga mata da rinannun idanuwansa Wanda yasa Shuhada matsawa baya da sauri tana silalewa k'asa,Ahaad kam sakin Najma yayi ya dafe kanshi yanajin zuciyarsa na barazanar tarwatsewa a kausashiyar murya yace tare da nunata da yatsa"kin bani mamaki,ashe dama zaki iya aekata mumunan abu irin haka?,b'allagaza dabba,ko a cikin dabbobi babbancin naki dabanne,sai ki gaya mana karuwanci kike fitayi ba aeki ba,dama can wannan aekin ba kwanta mun yayi a raiba,ke abun kyamace Najma ke fasik'ace,mazinaciya mazinaciya,da igiyar aurenki amma kije ki aekata zina?,na tsaneki na tsaneki,na tsaneki bana kosan sake ganin wannan k'azamar fuskar taki a rayuwata,bazan tab'a yafe maki abunda kika aekata mun ba"ya k'are maganar hawaye na fitowa daga idanuwansa,numfashin kowa tsayawa yayi bama na Najma ba, a matuk'ar firgice Mummy tazo ta dafashi tace"son me naji kana fad'a Najma tana da aure?"cikin k'unar zuciya yace"kwarai kuwa Mummy Najma tana da igiyoyin aurena a kanta,kuma aure na yarda addinin musulunci ya tanada,na biya sadakinta da abu mafi daraja kafin aka daura aurena da ita tun tana y'ar shekara d'aya"fad'awa yayi jikin Mummy ya rungumota sosai yace"Mummy ta cuceni ta yaudareni,matata ta Sunnah da aekata zina,na tsaneta dan Allah kice ta tafi tabar nan wurin",juya ido kawai Najma takeyi gaba d'aya ta rasa meke mata dad'i ta kasa gane duniya take ko lahira yau itace a matsayin matar Ahaad na tsawon shekaru ba tare data sani ba,wata uwar k'ara ta saki ta sulale k'asa sumammiya,kuka Mama ta saki gab'a d'aya wurin ya k'arasa rud'ewa Daddy kam ya kasa aewatar da komai illah zama da yayi tare dayin k'asa da kanshi.babu zama dirshen Shuhada tayi tabbas sai yau tasan kuka rahama ne,wai yau Ahaad ne da aure?,Wanda duk duniya babu Wanda takeso sama dashi,zata iya hak'ura da kamai amma banda zama da kishiya ,sai dai Kuma yarda yakejin son Ahaad a ranta batajin zata iya hak'ura tabar ma wata shi.Aiban kam da sauri yayi kan Najma yana girgizata tare da kiran sunanta,wata uwar tsawa Ahaad ya daka mashi yace"ka saketa ,dama ae Kaine kwaraton nata ba kowa ba,babu Wanda take kulawa a sanina sai kai,ina so in fad'a maka inhar kana da saka hannu akan wannan wallahi Allah anzan tab'a d'aga maka ba,da duk Wanda na gano yana da saka hannu a wannan".ware ido Fadila tayi dukta raina kanta dukda tana cike da matsanancin tsoro haka ta daure tare da wayincewa,ruwa Nani ta mikowa Aiban da yak'i sauraren kowa ,ya k'arb'a tare da zubawa Najma,wata irin ajiyar zuciya ta saki ta mik'e da k'arfi tare da sakin kuka mai cin rai cikin dakiyar murya tace"bazai tab'a yiwuwa ba,bazan tab'a k'arb'ar wannan auren ba,nafi tsanarka fiye da yacce ka tsaneni,kayi gaskiya inhar da gaske kake ni dabbace Kuma karuwa naji dukna k'arb'a wannan aeba kaina farau ba,ka sakeni bazan tab'a iya zama inuwa d'aya da kai ba"takowa yayi har zuwa gabanta ya Kuma daure fuska ya fito a aenahin Ahaad dinshi yace"dama illar karuwanci kenan,ae kinsan inda kika kai mutuncin naki dole ki k'arb'a,Kuma kedin kin kasance me fuska biyu,Kuma baki da maraba da jahila ilimi beyi amfani ba,da iyayenmu na nan da wannan abun kunyar zai k'arasa mana su amma sai yau nake godewa Allah da suka mutu bs tare dasun riski wannan abun kunyar ba".murmushi Amaan yayi yace"wai meye na tashin hankalin yarinyar da bayau ta fara bin maza ba,so nawa na ganta kawai rufa mata asiri nakeyi,amma babu kalar namijin da batabi".lumshe ido Najma tayi tanajin kalaman Amaan kamar yana watsa mata garwashin wuta,hawayene sukaci gaba da zarya akan kumatunta bakinta ya soma rawa ta rasa kalmar furtawa illah innalillahi wa'inna ilaihir raju'un da taketa fad'a a zuciyarta dake barazanar tarwatsewa,matsowa Aiban yayi gabanta hannu yasa ya share mata hawayen yace"ki daina wannan kukan Najma ganin hawayenki yana tab'amun zuciya,ki daure ki k'arb'i kaddararki,sannan ki daure ki sanar mana da mahaifin yaran nan,nayi maki alk'awari kina haihuwa zan aureki,ba karuwa suke kiranki ba koda a gidan karuwai kike zan tabbatar na cika alk'awarina a kanki,bazan tab'a k'asa a guiwa ba,balle har yanzu ni ban zargeki ba,na dauki hakan a matsayin tsautsayi,indai har zaki soni to tabbas zan aureki a haka Kuma na rike abunda Allah ya baki tamkar nawa,ba zasu tab'a kukan maraici ba ,kuma zasu k'arb'a sunan Aiban a matsayin mahaifi"wani wawan duka Ahaad ya kaiwa Aiban a baki take jini ya b'alle bakinsa ya fashe ,dafe wurin yayi da sauri Mummy ta shiga tsakaninsu tace"Sulaiman kayi hauka ne?,akan karuwa zaka daki d'an aminiyata,ae babu batun aure yanzu basai anjima ba zaka datse igiyar dake tsakaninku sannan ka gayamun a yaushe akayimun wannan cin amanar da bak'in zalincin ba tare Dana sani ba".cikin dakiyar murya Najma tace"ko baki fad'a ba bazan k'ara awa d'aya a matsayin matar d'anki ba,never no way,dole ka sakeni yanzu".ji yayi k'afafuwansa na neman gaza daukarsa ,cikin kuka Mama tace"shege munafiki ka sakarmun jika yanzu basai anjima ba,kaga ta samu d'an mutuncu zai aureta ba irinku ba gadon Bilki"ihu Fadila ta saka tace"wallahi bazai yiwuba indai ina da rai Aiban baya da wata matar data wuce ni,wannan ae zalinci ne,jikanki yace neso shine za'a lik'awa mijina wallahi Aiban bazai auri jaruwaba wacce ta bayar da mutuncinta ga k'artan banza"runtse ido Najma tayi da k'arfi Amma ta kasa cewa komai,"tsaiwar uban meye kakeyi ka saketa yanzun nan,ko in tsine maka ba zan tab'a iya had'a jini da Sha'awa ba"cikin k'arfin dauriya ya furta "ni Ahaad Kabir Bindawa na saki matata Najma Jafar Bindawa saki d'aya"."uban meye yaci sauran biyun?"Mummy ta fad'a,girgiza kai ya shigayi yayi saurin ficewa daga d'akin yana goge guntun hawayen da yake k'ok'arin fitowa a idonshi.wani murmushin takaici Najma ta saki da k'yar take had'a yawu tana jin jiri na nemen kwasarta bango ta dafe tare da fara karanto duk addu'ar da tazo kanta.da gudu Fadila tayi hanyar fita tana sambatu tana kiran "yau k'arshen komai zaizo,yau zakiga abunda Ni Fadila zan it's aekatawa wallahi saina ajiye maki tabon da yafi wannan muni a rayuwarki,bazan tab'a barin kiyi nasara a kaina ba".Nani ta kama Najma sukayi part dinsu kuka tashin hankalinsu a lokacin ba'a misaltashi,jikin Nani Najma ta fad'a ta fara rusa kuka Wanda bata San dalilinsa ba.Aiban kam da k'yar ya lallab'a Shuhada ya tafi da ita gida,Wanda Shima ya gama fita hayyacinsa dauriya kawai yakeyi.
*Tofa kunji yarda tashin hankali ya b'arke a wannan ahalin shin koya zata kaya ?kudai ku biyoni danjin k'arashen labarin*
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan k'arshe
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Telegram
Maryam majidadi
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 61-70
*End of part one*
Zaune kawai Najma amma ta rasa gane duniya take ko lahira,gani takeyi kamar mafarki takeyi,rungume k'aton hotonta da Ummu da Abbi da Najwa tayi,wani irin marayan kuka ta saki mai ban tausayi,shafa pic din takeyi a hankali ta furta"nayi kewarku,a tunanina na saba da zama babu ku,amma gashi yanzu ne lokaci mafi mahimmanci da nake buk'atarku,ina buk'atar mai taimakona ,meyasa kuka tafi kuka barni?"shafa cikinta takeyi tayi zumbur ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,nice da cikin da ba'a san ubanshi ba,ni Kaina bazan iya nuna waye ubansu ba,Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni khairan minha,ya Allah ka bani mafita"dafe kanta tayi tanajin yana barazanar tarwatsewa gashi lokaci d'aya ta soma jin jiri na ibarta,Nani kam kuka takeyi tana kuma lallashin Najma amma abun yaci tura.
Mama ta buga uban tagumi sai hawaye takeyi,kiris take jira ta fashe sallamar Daddy yasa ta saki kukan da take nemanyi cikin masifa tace"Haba Kabiru yanzu a gabanka akai wannan d'ayan aeki,kanaji kana gani wancan bayahuden banzar ya sakarmun jika ba laifin tsaye bana zaune,kai ace iyalenka sunfi k'arfinka?,kaine babba a gidan nan fa,Kaine zaka iya daidaita komai daya lalace,amma ka zama hoto Bilki ta gama shanyeka,duk da tana y'ar y'ar'uwata amma ko kad'an basu da halin kirki,ya zama dole a gareka ka had'a taro na gaggawa ta warware abunda ke faruwa,ya zama dole kowa yasan dalilin aure Najma da Ahaad tunda magana ta fito fili,ka duba girman Allah ka zama namiji haba Kabiru"sai da ya tabbatar Mama ta gama sannan yace "kiyi hak'uri ki daina kuka insha Allah zansan abunyi,ni Kaina bana jin dadin abunda yake faruwa sai dai kuma bana so na yanke hukuncin da bai dace ba,ban sanin me yake zuwa kaina Mama amma aeta addu'a insha Allah komai zaiyi daidai"sallama yayiwa Mama ya fita yanajin wani nauyi a zuciyarsa sai dai besan kuma me zai iya aekatawa ba.Daddy yana zuwa ya iske Mummy da Amaan tsaye suna jiran shigowarsa"basai ka zauna bafa dama shigowarka nake jira,yau saika gayamun wanne macucinne ya had'a auren d'ana da waccen karuwar?,wallahi bazai yiwuba sam wannan ae munafirci ne"Mummy ta fad'a,kafin Daddy ya bada ansa sukaji muryar Mama tace"munenan muka munafirceki ae,a kanmu ya dace ki huce marar kunya"k'asa Mummy tayi da kai tace kowa ya sameni a parlo yanzu,juyawa tayi ta fita,uwar harara Mummy ta b'allawa Daddy sannan taja hannun Amaan suka fito parlo ,zaune suka samu Mama a kujera ga Ahaad zaune k'asa kusa da ita ya daura kanshi akan cinyarta idanuwansa a lumshe kamar meyin barci,duka jijiyoyin kanshi sun tashi radau radau kamar zanasu akayi.yatsina fuska Mummy tayi sannan suka zauna,Daddy ma ya zauan.a hankali take takowa zuwa wurin Nani na rik'e da hannunta danji takeyi kamar zata fad'i k'afuwanta basa daukarta,bakinta kam ya bushe yayi fari ko miyo da zata had'a babu saboda tsananin tashin hankali,can gefe suka zauna ita da Nani kamar marayu,Mamace ta bud'e taro da addu'a sannan tace tambaya ta farko anan shine "Hadiza ki fad'a mana wa yayi maki ciki?,waye uban d'an dake cikinki?".wani fad'uwar gaba ya dirarwa Najma ta lashi busassun lab'anta ta sunkuyar da kanta k'asa hawaye suna bin kuncinta cikin dishewar murya tace"ki tambayi Fadila ita tasan abunda ni ban sani ba"."wannan wanne irin sakarcu ne?Fadila ita keda ciki ko ke?,kiyi magana da kikasan kowa zai kama a matsayin ansa mana"Mummy ta fad'a .daure fuska Najma tayi tamau kamar an mata mutuwa tace"ban sani ba,nice uwa Kuma nice uba"gyad'a kai Mama tayi tace "dalilin taraku anan badan komai bane sai don mu samu mafita ga matsalar da ta kunno ga ahalin nan mai dunbin tarihi,yanzu idan muka yarda magana ta fita cikin minti kad'an zata zage duniya,musassaman gareki zaifi illah Najma keta mutane ce,Kuma mai taimakonsu ce Kuma y'a ga Jafar to tabbas cikin mintoci abun zai bazu,sannan abu na biyu shine sanin dalilin auren Najma da Ahaad"."Mama kiyi magana kai tsaye ki bada dalilin aurensu amma magana kam ae ta fita ta gama,tunda ciki dole ya fito,Kuma ae fita takeyi Kuma bazata iya hak'ura da zuwa wurin kwartonta ba"Amaan ya fad'a duk abunnan sai yanzu Ahaad ya d'ago yana aekawa Amaan da wata muguwar kallo mai cike da ka shiga taitayinka,ji yayi da Amaan na maganar kamar ana yankar naman jikinsa da addane zuciyarsa kam suya kawai takeyi kamar ana soyen gy'ada,kallo d'aya zakawa Ahaad ka kawar da fuska saboda yanda ya canza kammanci saboda tsabar b'acin rai,ya koma sojan nashi na asali babu alamun Wasa tare dashi,da sauri Amaan yayi shiru ganin irin badak'alar dake dososhi idan harya kuskura yaci gaba da magana,nisa Mama tayi tace a shekarun baya lokacin Najma tana da shekara d'aya a duniya ita da y'ar uwarta Najwa Kuma cikin shekararne kakanku wato mijina ya rasu saidai kafin ya rasu yayi abunda ya dace ,abun ya fara ne daga lokacin da kika dauki hassada da Karan tsana kika daurawa Sha'awa,Kuma a lokacin kina zarginta da janye hankalin d'anki Ahaad wanda bakiga d'awainiyar da tasha dashi ba,haihuwar Ahaad kawai kikayi amma ke kanki kinsan ita ta masa wahala ta uwa kuma Ahaad tarbiyar Sha'awa ne shiyasa ya banbanta da wannan shashashun yaran naki"wani Kallo Amaan yabi Mama dashi,dakuwa tayi masa tace"ungo wannan ja'irin yaro,kai meka sani ,ita uwar taka ae tasan komai,Kuma batayi la'akari da cewa Allah shike azirta bayinsa ba,dan Sha'awa ta fita komai bashi ke nufin ta fita wurin Allah ba,wannan jin zafin shiya kawo rarrabuwa tsakanin iyalinmu,Wanda hakan ba k'aramin d'aga mana hankali yayi ba,babu jituwa tsakanin Kabir da Jafar Wanda a da ba haka suke ba,sune mafi soyuwar y'an uwa Wanda na gani Wanda d'ayansu zai iya sadaukar da rayuwarsa danya ceci ta d'an uwansa wanda nayi kukan hakan ,nayi bak'in cikin rarrabuwa kan Yarana,Kuma har Allah ya k'arb'i ran d'an uwansa basu dawo kamar da ba,wannan dalilin ne yasa Alhaji Sulaiman kakanku ya yanke shawarar had'a yaransu aure tun suna k'anana Wanda muna ganin hakan zai kawo mana mafita,lokacin daya kawomun maganar banyi tantama ba na amince amma ya zomun da niyar had'a aure Amaan da Najwa ne"."tabdi lallai da anyi babban kuskure kuwa,ni za'a aurawa wad'annan jinin karuwan?".kallon rainin wayau Najma tayiwa Amaan cikin hassala da dasasshiyar murya da bata fita sosai tace"da ita zata fi kowa bak'in ciki saboda ta auri dangin bunch of murders,gaba dayanku haka kuke makisa ,azzalumai kawai"wani wawan mari taji an dauketa dashi ba tare da tayi aune ba,Ahaad ne ya mareta ya nuna ta da yatsa amma ya kasa furta komai,cikin sanyin murya tace"kayi komai kaso,amma wannan ya zama rana ta k'arshe da zakayi k'ok'arin daura hannunka akan jikina,dan bazan tab'a iya jurewa ba,karka yarda sauran girman da nake ganinka dashi ya idasa zubewa kamar nasu"."ya isa haka kada na k'ara jin wannan shashancin a tattare daku,ba kamar ke da yake Ahaad wanki ne to kome yayi maki dole ki girmamashi"Mama ta fad'a sannan taci gaba da cewa ana zuwa wurin daurin auren a parlon Baban Sha'awa wato Alhaji Aminu ,Ahaad ya shigo rike da hannun Najma zama yayi yanajin me ake fad'a a lokacin yana shekara goma sha biyu,kallonsu Alhaji Aminu yayi yace"wannan aure akan Ahaad da Najma ya dace ba Amaan da Najwa ba,dalilina shine Najma tun tana k'arama kuna ganin yarda take shiga wurinsu Kuma kome zasu mata zatayi kuka anjima ta koma saboda yarda ta shak'u da Ahaad,kuma