Showing 24001 words to 24909 words out of 24909 words

Chapter 9 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

28 May 2026

21

shima ku lura yana yawan fad'a da kowa a kanta,Najwa kam ko yarda dasu batayi data gansu da ta soma kuka wannan shawara ce".da wad'annan bayanan kowa ya gamsu Jafar ya duba jikin Ahaad dan ganin meye zai bada a matsayin sadaki,agogon hannunsa ya kallah wacce ak'allah a wannan lokacin zatayi dubu d'ari biyu ya dafashi yace " "Babana ka bada sadakin k'anwarka,zamuyi maku aure yanzu"kasancewar Ahaad yarone me wayau da basira da saurin fahimtar abu Kuma ya gane kome suke nufi yasa ya warwaro agogon hannunshi da kanshi yace"Abbuna wannan zaiyi?"murmushi dukansu sukayi suka k'arb'a tare da saka masa albarka sannan aka daura auren wannan shine dalilin auren Ahaad da Najma".turo baki Mummy tayi tare da sakin shewa tace"to Alhmdllh Allah ya rabamu da bakin iri,ada ae Ahaad a mallake hake amma yanzu da matsafiyar ta mutu ae gashi ya dawo gareni"murmushi mai kuna Najma tayi sannan ta mik'e tsaye tace"waya gaya maku Mamana ta mutu?,ko da yake dama ae pretending aekinku ne,ina so ku sani ina nan zuwa gareku,zaku biya kome kuka aekata"wata irin zuface ta kuma karyowa Amaan da Mummy suka kalli juna,cikin zuciya Mummy tace badai yarinyar nan ta gano sirrinmu ba,dole musan abunyi,Amaan kam suman zaune yayi yana tunanin meye hujjarta ta kirasu Makasa Kuma yanzu tace Mamanta na da rai Kuma zasu biya,dawowa hayyacinsa yayi sanadiyar tafin da Najma tayi a saitin fuskarsa ta sakar masa murmushi,sannan ta juya ta fice.mikewa Ahaad yayi yabar masu parlon yana zuwa d'akinshi ya Kuma dafe kanshi akwati ya dauko ya soma zuba duk kayan daya shiga gabansa ,dan ko gani sosai bayayi,abubuwanshi ya kwasa ya fito parlon ,tararsa Najma tayi kowa yana kallonta tace"badai wannan shike had'a rigimar ba?,badai su suka sanya kowa namu cikin tashin hankali ba?meye dukiyar gado?wanda kunsan ba naku bane ba amma kuka saka San zuciya a kai ba?"ta k'are maganar tana d'aga files din ,duka wani dunbin dukiyarsu yana wurin sannan taci gaba da cewa zan tafi nabar maku har gidan bazan Kuma ci daga wannan dukiyar ko sha ba,bazan k'aru da komai da ita ba dukda hakkina ne"hannun Ahaad ta kama ta saka files din ,sannan tayi waya banji me aka ce mata ba naji tace"shikenan ka shigo kawai".cire sims dinta tayi ta karya ta ajiye masu wayar taja hannun Nani tayi hanyar fita.kuka Mama ta saki tana kiranta amma Najma ko waiwayowa batayi ba,Mummy da Amaan murmushi kawai sukeyi,a hankali Amaan yace"Mummy yanzu zata fad'i,Dr Jamil ya gayamun allurar yauce ranarta ta k'arshe a jikinta"wani irin sanyi ne ya ratsa Mummy dajin batun Amaan.tana fitowa cikin gate din sukayi karo da Fadila,wani murmushi Fadila ta saki tace"Najma Jafar Bindawa my beloved sis,am going to miss u,zanga yarda zaku kasance tare zanga abunda zai kallah harya birgesa kyau shine abunda kike tak'ama dashi da dukiya kuma,yanzu ba dukiyar kyan ma zaki rasashi,da sauri Najma ta tura Nani gefe hakan yayi daidai da shigowar Aiban kuma,dariya Fadila ta kwashe dashi kafin Najma tayi magana ta fito da kwalbar Acid din dake bayanta ta watsashi a fuskar Najma a gefen dama,wata irin gigitacciyar k'ara Najma ta saki,Nani ma ihun ta saki ,Fadila kam ta saki kwalbar a k'asa ta shek'a a guje Islam ta dauketa a mota,da wani irin gudu Aiban ya k'araso Najma ta fad'o a hannunsa,k'ok'arin saka hannu takeyi ta shafa fuskar amma ya rike hannayenta hawaye nabin kuncinshi.jin ihu yayi yawa yasa y'an cikin gidan suka fito da gudu saidai har Aiban ya fice daga gate din Nani na biye dashi,wani irin nishi Najma tayi ta fara zubar da bakin abu kawai jikinta ya sake duk wata abu da zata nuna tana da rai ya daina aeki,"no no no it's can't be possible,Najma karki tafi ki barmu,da gudu Ahaad da Amaan suka fito gate din,amma sai dai sukaga k'urar tashin mota."waye yazo ya fita yanzu"Amaan ya tambayi me gadi,share k'wallah yayi yace "bansanshi ba,amma ya fita yana kuka Hajiya Najma ta rasu"wani irin bugawa gaban Ahaad yayi take jinsa da ganinsa suka dauke ya fad'i a wurin sumamme.kuka Mummy da Mama suka saka Daddy kam rasa ina zai saka kanshi yayi .daukar Ahaad sukayi zuwa cikin gida sannan suka fara Kiran Dr.kafin kace me cikin y'an mintoci labari ya bazu an zubawa Najma Acid ,sannan an kasheta kuma an gudu da gawarta,wannan labarin ya fita ne ta hanyar Islam ,tuni gani ya karad'e kowa da abunda yake fad'a ,masu muka nayi masu addu'a nayi abun takaicin shine Kuma ba'asan wa yayi mata wannan abun ba.a labarai Shuhada ta gani wata irin k'ara ta k'wallah tayo waje ba mayafi tana rusa kuka dan harga Allah tanajin soyayyar Najma kamar y'ar uwarta ta jini.ba shiri Hajiya Sadiya ta riketa amma taki natsuwa har sai da suka tafi gidan .da k'yar suka samu hanyar shiga gidan,ko ina y'an sanda ne zagaye da wurin sai sojoji yaran Ahaad sun hana y'an jarida shiga gidan.


*Tofa ya wannan abun zai kasance,lallai akwai rudarwa da sarkakiya kudai ku biyoni a part 2 danjin ya wannan labarin zai kasance,shin Najma zatayi nasara kuwa?ina Fadila ta tafi?me yake damun Ahaad?ina Aiban zai kai gawar Najma da Nani?ina makomar Mummy da Dr Jamil da Kuma Amaan?ya Shuhada zata kasance,meye rawar da Hajiya Sadiya zata Kuma takawa?ina labarin Barrister Abbas mai kula da harkokin Abbi?,shin da gaske Ummu bata mutu ba?wannan tambayoyin dukku nemi ansoshinku a part 2*


*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe*
Stylish star
Jorderh majidadi
07033636337 for shawara or comments

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login