Showing 18001 words to 21000 words out of 24909 words

Chapter 7 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

28 May 2026

17

yayi ya fashe har ya yanke masa tafin hannu,tsura masu ido yayi yanajin kamar ya tashi ya shak'e Aiban,mik'ewa Muslim yayi yace"brother lafiya?,me yake samunta ne"zaro ido Aiban yayi yace"Muslim yaushe ka shigo gari ne?,ko Hajiya bata sani ba bare ni"dariya Muslim yayi yace"ba jimawa na shigo zamuyi wani aekine da Captain,bata da lafiya ne".kallonsa Najma tayi tace"lafiya ta qlau kawai inajin jiri ne,Kuma yanzu kamai yayi daidaima"dariya Muslim yayi yace"bata ko dai kina tsoron allura ne?"murmushi kawai tayi ta juyo tace"na gode friend Allah yabar tare zaka iya tafiya"da Ameen ya ansa sannan suka k'arasa wurin Ahaad ,hannu Aiban ya bashi ,hannu Shima ya mik'a masa sukayi musabaha Aiban yace"barka dai Captain Ashe Kaine abokin Brother din nawa"Gyad'a Kai kawai Ahaad yayi .kallonsa Muslim yayi yace"wannan shine Aiban yaron Yayar Ummana da nake gaya maka muna da y'an uwa a nan garin"murmushi Ahaad ya k'ak'aro yace"nice to meet u bro"."zanje gida yanzu anjima zamu had'u"Muslim ya fada yana bin bayan Aiban ,a motar Muslim suka tafi dan Aiban yabar tasa a company.
"Wallahi Mama Kinga yanzu Najma ba lafiya ya isheta ba,ya kamata ta bawa y'an uwanta wata dama su taimaka mata akan wannan company din ,balle ga Ahaad yazo gida Kuma zai jima dan wani aeki yazoyi"Mummy ta fad'a."Nima nayi tunanin hakan tunda yanzu jikin sai a hankali Kuma ta kafe taki bari likita ya dubata,zan mata magana idan ta warke inma so takeyi saita koma wani kawai "wani sanyin dad'i ya ziyarci Mummy.shigowar Najma d'akin yasa ta hadiye sauran maganarta,zama tayi a chair bata tankawa kowa ba taumshe ido hannunta rike a kanta.


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe
Stylish star
Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Na
*Maryam ismail Majidadi*


Telegram
Maryam majidadi


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*
Page 46-50


"Wai ke me yake damunki ne?,tarbiyar da aka baki kenan?,yaushe kike k'ok'arin ki zama haka?"Ahaad yayi tambayar a hassale."yau naga abunda ya isheni Sule meyake faruwane ka shigo kana wani bubbudemun hanci kana jaraba Kai da ubanwa Kuma?"Mama ta fad'a tana mik'ewa tsaye,wata uwar harara ya banka mata yace"ae wacce nake da ita ta San kanta"sai lokacin Najma ta bud'e lumsassun idanuwanta ta budesu a kanshi ta tsura masa ido"ki janye mun wannan idon naki kwalakwala Mai kama dana mayu".murmushi Najma tayi sannan tace"wani abun ya faru ne?",da k'arfi ya fizgota daga zaunen da take ya murd'e mata hannu zuwa baya cikin haushi yace"wannan ya zama last warning da zan ganki wani yayi k'ok'arin tab'a jikinki,idan Kuma hakan ta sake faruwa to kinsan me zan iyayi ae",a galabaice take danba k'aramin riko yayi mata ba, numfashi taja itama cikin muryar rad'a tace"toka saurara kaji,ni ba budurwarka bace so baka da damar yin kishi a kain..."jin ya Kuma murd'a hannun yasa ta saki y'ar k'ara tare da hadiye sauran maganarta,bankad'ata yayi ta fad'a a k'asa,"la'ilahaillah Bilki kin haifo annoba a gidannan,kina zaune yana k'ok'arin kashe y'ar uwarsa amma kin kasa katab'us,Allah ya isanta mugu,Allah ya saka mata,mugu labcecen banza bayahude"k'wafa yayi yabar d'akin rainshi a matuk'ar jagule,sai lokacin Mummy ta kamata ta tayata ta zauna tace"sannu Najma kinsan halin Yayan naku ku rik'a kiyayewa muma ba d'aga mana yayi ba,sannu bara na baki ruwa"gyad'awa Mummy Kai kawai tayi karb'ar Mug din ruwan tayi tasha ta mik'e zata fita,da sauri Mama tace"ina zakije inaso muyi magana dake",wayar hannunta ta duba tace"zamuyi magana anjima yanzu anmun Kiran gaggawa"bata jira cewar Mama ba ta d'aga wayar ta fita,gama sauraran sakatariyar tata tayi sanan tace"owk I will be on my way back"part dinsu ta shiga ,cikin sauri ta shirya cikin dogon riga mai rover kalarta ja bakin dogon takalmi ta saka ,tubke kashin kanta tayi sannan ta dauki siririn bakin gyale ta daure kanta,hand bag ta dauka da key din mota,sosai tayi kyau sai azabar kamshi takeyi rumgumar Nani tayi ,kiss ta mata a kumatu tace"Nani ina dawowa yanzu"da Fadila ta had'u tana k'ok'arin fita daga gate din gidan,cikin takun Isa ta k'araso gareta tace"Najma fita zakiyi ne?",ba tare data kalleta ba ta d'aga mata Kai,"to ki ajiyeni gidansu Islam motana tana wurin wanki kuma har yanzu wannan d'an rainin hankalin Idi bai dawo da ita ba",da sauri Najma ta d'ago ta kalleta tace"Baba idi dinne kike fad'awa haka?".tsuka Fadila taja tace"aekin banza to shidin ubanki ne?,ko Kuma kalar dangin naki har takai gareshi,ni wallahi shiyasa ba ko wacce magana nakeso nayi a gabanki ba"ko kulata Najma batayi ba ta shige mota,ganin bata da niyar shigowa yasa ta fara k'ok'arin tayar da motar da sauri ta zaga ta bud'e motar,murmushi kawai Najma tayi taja motar.Ahaad Kam kallonsu kawai yakeyi ta window ya rasa meke masa dadi,yanzu baya da makama ya zai b'ullowa Najma d wannan rayuwar data dauka bazai yiwu ya zuba mata ido ba tayi shigar da take so ba ta Kuma fita lokacin da take so ba,duk da bawai zarginta yakeyi ba,sai dai yana ganin hakan Sam be kamata ba,balle yadda take yarinya mai k'ananun shekaru irin haka,dole yasan abunyi kafin lokacin komawarsa.kai tsaye k'ofar gidansu Islam tayi parking ,kallonta Fadila tayi tace"Najma ya kamata ki shiga kinsan yau Islam ta had'a paty ne na dawowar y'ar uwarta k'asarnan da Kuma k'anwar mamanta"Najma kallon tsadaddiyar agogon hannunta tayi tace"Fadi ina da meeting ,Kuma lokaci na neman k'ure mani","aeba saikin zauna ba pls ,dan Allah"bud'e motar kawai Najma tayi ta fito Dan babu amfanin musun wani lokacinne zata kuma cinyewa,murmushin mugunta Fadila tayi tace"naga da k'afar da zakije meeting din,keda dogon takalmin naki k'asa zaku tsinci kanku,shegiya kawai".a tare suka shiga gidan kamar abun arziki, decorations ta gani ta ko ina,gidan yayi kyau sosai ciki suka k'arasa can bayan lambun gidan aka shirya dan gabatar da patyn,tunda ta shigo wurin mazan wurin da matan wurin suke kallonta kowa da abunda yake ayyana a ransa,ji tayi dukta tsargu ta rasa sukuni dan ita ba ma'abociyar zuwa irin wad'annan wuraren bane,bata son yawan hayaniya yanzu kam,Jan hannunta Fadila tayi zuwa inda taga Islam,tab'ota tayi cikin jin dadi Islam ta juyo tare da rungumar Fadila tace"gaskiya nayi fushi daga bari naje na dawo shine sai yanzu kike dawowa,Kuma abun harda gayyar sodi?"dariya suka saka tare da tafawa sannan Fadila tace"gaskiya ba haka ya kamata ta samu tarba ba,itace ta kawoni motata na wurin wanki"far da ido Islam tayi sannan ta mikawa Najma hannu alamun su gaisa,basarwa Najma tayi ta bata hannu itama,kallonsu tayi tace"na tayaki murnar dawowar y'ar uwarki sai dai ina rok'on Allah yasa hali ba d'aya ba,magiya da taimako ya kawoni nan dan taron naga baikai armashin ace kamata Billionaire nazo wurin ba,fatan alkhairi"sakin hannun Islam tayi ta juya zata tafi,"kan uban can,wannan ae gaba d'ayanmu ta had'a ta wulak'ance,lallai wallahi zanyi maganinki"Islam ta fad'a a fusace bin bayan Najma tayi da sauri Fadila ta rikota tace "come down ,zakiga mezai faru yanzu"bata k'arasa magana ba sukaga santsi ya ibeta ta tafi zata sulale runtse idonta tayi da k'arfi ta sadakas ta jita a k'asa,dama gashi ba k'arfin jiki takeji ba dauriyace kawai,ji tayi ta fad'a akan jikin mutun ya rungumota da k'arfi zuwa faffad'an kirjinshi,hakan yayi daidai da sakin sanyayyar wak'ar soyayyah mai dadin gaske ,a hankali ta soma bud'e idonta ta saukesu akan kyakyawar fuskarshi sanye yake cikin T-SHIRT red colour wai wando jeans bak'i,gashin kan nan yasha gyara sai salki yakeyi ga wani shu'umin k'amshin turaren da takeyi,gira d'aya ya d'aga mata tare da kanne ido yace"kallon fa y'an mata?"lumshe idonta tayi ta sake waresu a kanshi tace"Yaa Ahaad mezan kallah a nan?"ta k'are maganar tana turo d'an k'aramin bakinta,hannu yasa ya murd'e baki saida ta saki k'ara sannan ya saki yace"kinamun rashin kunya saina cire bakin,Kuma na sakeki ki fad'i a nan".mik'ewa yayi tare da sakinta,dafe Kai Fadila tayi tace"wallahi Yaa Ahaad be tab'a b'atamun rai irin yau ba,wai wama ya gayyato shi"."ae kinfi kowa sani,Yaa Muslim fa Shima yazo ba dole ki gansa ba"Islam ta k'are maganar tana Jan siririn tsaki,"amma wallahi ya bada mu"Fadila ta fad'a cikin haushi.ido suka had'a da Aiban murmushi kawai yayi mata ya juya zai bar wurin,yunkurin binsa tayi Ahaad ya rike hannunta ya matse sosai yace"karki kuskura,inba so kikeyi na b'allaki a wajen nan ba"sahagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka,cikin shiga ta alfarma ta k'araso wurin duk abunda akeyi akan idonta ,kallon tuhuma takebin Ahaad dashi ,idanuwansu na haduwa gaban Shuhada yayi mugun fad'uwa,kallonta takeyi tana son tasan ina ta taba ganin me kama da ita amma ta kasa tunowa,cikin sanyayyar murya tace"Yaa Ahaad wacece wannan?"sai lokacin yasan da isowar Shuhada a wurin,yi yayi kamar ya share sai Kuma yaga rashin dacewar hakan yace"Najma"sake fuska Shuhada tayi tace"wow kace lil sis dinmu,sai yau Allah yayi zanga Najma ,ina samun labarinki a wurin Yaa Ahaad"harara ya watsa mata ,da sauri Shuhada tayi shiru tare da sunkuyar da Kai,balle sai da tasha matuk'ar wahala kafin ya yarda yazo wurin,wayen cewa Najma tayi tace"sannu Auntyn mu,ashe ina da rabon ganinki a yau"ta k'arashe maganar tana k'unshe dariyar dake cinta tana kallon yadda Ahaad ya had'e fuska.riko hannnunta Shuhada tayi tace"nayi farin ciki da ganinki ,ina fatan kema patyn yazomun da ke?",k'ara sakewa Najma tayi saboda lokaci d'aya taji tana matuk'ar son Shuhada tace"a'a Auntyna hanyace ta biyo dani,ina da meeting,amma insha Allah zan maki zuwan kanki,sai dai ko sunan Auntyn ban sani ba"murmushi Shuhada tayi tace"haba yanzu aeke k'awata ce,tunda Kinga zamuyi sa'annin juna kinga mun zama k'awaye kenan sunana Shuhada"."wow nice name,amma zan wuce yanzu kada inyi latti"har Najma ta juya zata wuce Shuhada ta riketa ,wani irin bugawa gabansu yayi su duka biyun suka d'ago a tare,basarwa Shuhada tayi tace"kimun alk'awari zaki dawo",gyad'a kai Najma tayi tare da murmushi,matsawa tayi kusa da Ahaad a hankali tace"ba laifi akwai kyau sosai,sai dai k'aramar yarinyace kamarmu,Kai da baka son kowa sai babbar mace?",dungure mata Kai yayi ta wuce tana dariya abunta.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.

Stylish star
Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Na
*Maryam ismail Majidadi*


Telegram
Maryam majidadi


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*
*Godiya gareku masoyana marar adadi,hakika kuna sakani farin ciki marar misaltuwa,ku d'in na dabanne son so fisabilillah,ina jin dad'in comments dinku,haka zalika masu Kira ma na gode*


*Wannan page din sadaukarwa ne ga*
Shugabata *Aunty Fauza y'ar amana*
*Yayata Momyn Ahlan*
*Sai sister Ummu Nasmah*


Page 51-55


Kai tsaye Najma motarta ta shiga,wasu hawayene suka zubo mata,duk'ar da kanta tayi tana jin sautin bugun zuciyarta na tsananta,tabbas tasan tana cikin garari da mugun tashin hankali,wai yau itace ba a matsayin cikakkiyar budurwa ba,abun takaici shine bata ma san waye ya k'arb'i budurcin nata ba,"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,nasan na gama rayuwa me dad'i waye zai aureni haka a wulak'ance?,waye zai yarda dani?lallai dole na daina shagala nayi abunda ya kamata,tunda nake ban tab'a ganin y'an uwa irin nawa ba"ta k'are maganar cikij muryar kuka,tada motar tayi tabar wurin Kai tsaye inda zasuyi meeting taje,shiga tayi tare da basu hak'uri akan makaran da tayi,Mai gabatarwa gabatar sannan aka fara taron ,cikin manyan jami'anta d'aya ya mik'e yace"ranki ya dad'e babban abunda ya taramu shine mun mik'o kokenmu akan ayyukan da kika sabayi na alkhairi,duk sabbin islamiyyun da masalatan da kikace a gina y'allab'ai Amaan ya hana k'arass ginin ya rufe duk wani account da muke cirar kud'i dan gabatar da aekin,Kuma be bamu wata sahihiyar hujja akai ba"jinjina kai tayi cike da tunanuka iri iri sannan ta mik'e tsaye tazo tsakiyar wurin tayiwa kowa sallama da fatan alkhairi sannan tace"naji k'orafinku,ina so ku sani babu abunda za'a fasa,inaso gobe ayyukan suci gaba ,sannan ga kud'in gidajen marayu da kudin sauran magunguna na NNJ special Hospital,da kudin da ake rabawa nakasasassu"kallonta ta mayar ga ma'ajin dake kula da wannan harkokin tace "zan tura maka kudi yanzu"wayarta ta dauka ta tura masa million 20 ,sannan taci gaba da cewa"ku fara da wannan in ana buk'atar k'ari k'ofa a bud'e take".haka sukaita saka mata albarka taron ya tashi cikin kwanciyar hankali kowa fuskarsa da fara'a, a hankali take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ji takeyi tamkar ana yankar naman jikinta wani irin zafi da ciwo yake mata,dafe Kai tayi tanajin zufa na keto mata a wahalce tace"ya Allah,nikam na rasa wannan wanne irin ciwo ne"Driving ta fara ba shiri ta tsaida motar ta fito da sauri dan bazata iya tukinba Kuma ga wani fitinanniyan ciwon da takeji,ganin mutane sunata kallonta yasa dukta fara tsarguwa da kanta daga nesa taji wasu suna cewa"kuji waccen ba itace y'ar gidan marigayi Alhaji Jafar mai K'wal ba,ae babu Wanda nesan Family dinba,amma kuma ae ta mutu tare da iyayenta"."ke Hanna me kike fad'a haka,ancefa y'an biyu ne,wannan ae batayi kama da wacce ta mutu ba,wallahi dukiya rahma ce"Jamila ta fad'a.girgiza Kai Najma tayi ta saki murmushi Mai k'una tace"dukiya babban tashin hankali ne,inama ni Allah ya bari kamarku da nayi rayuwar farin ciki dajin Dadi"ji tayi tana buk'atar ruwa,duka motarta ta duba babu ruwa,Kuma babu shago a ciki,k'arasa tayi wurinsu Hanna tayi masu sallama.washe baki sukayi tare da ansa sallamar ,cikin cool voice tace"Dan Allah ko zaku sayarmun da ruwa nasha?"haba Aunty ae ba'a sayar da ruwan nan,zamu baki kisha dai"."la la,jama'a kuzo kuga y'ar indiya ko ince y'ar indiya,irin wad'an nan da muke gani a film,wallahi itace cikin Wanda muka kalla a TV jiya"k'aramar yarinya y'ar shekara 7 ke fad'a"dariya ta kama Najma ,sosai takeyin dariyar nan ma suka k'ara shagala da kallonta sosai dariyan yayi mats kyau,k'arb'ar ruwan da Jamila ke bata tayi ,Bismillah tayi tare da kai ruwan baki,yana hawa kan harshenta ta maidoshi da sauri,tambayarta suka shigayi amma batace komai,duk yarda taso tasha ruwan kasawa tayi ,wani irin tausayinsu ya kamata tayi alk'awarin taimaka masu ,kafin tabar wurin ta saba da mutane sosai dukda dauriya kawai takeyi saboda tsabar ciwan dake cinta.a haka ta tuk'a motarta zuwa gida,ko da ta shiga bata kula kowa ba,da gudu Fadila ta fad'o jikinta tare da sakin kuka,tace"sister na rok'eki da girman Allah ki taimaka mun,wallahi in gaskiya ta fito Yaa Ahaad zai kashe ni"cikin rashin fahimta Najma ta bita da kallo sannan tace"ki natsu mana ,me yake damunki?,ni ban gane komai bafa".ganin duk Fadila ta rikice yasa ta kama hannunta d'akin Fadilan suka shiga tare da zama gefen bed,wani banzan kallo Islam ta bita dashi wacce ke kwance daga ita sai y'ar k'aramar riga mai hannun vest tana taunar gum,tsaki Islam taja tace"haba Fadila wannan wanne irin iskanci ne zaki sakamu gaba kina rusa ihu daga dawowarmu,kefa kika janyoni Kuma kinsan a buk'ace nake in baki bani abunda nakeso toni zan tashi na nemi wata bazan iya ba"wani irin zaro ido Najma tayi tana k'ok'arin tattaro kalaman Islam ta had'asu akan ma'aunin fahimta girgiza Kai tayi bata San yarda da abunda zuciyarta ke fad'a mata,maganar Fadila ta dawo da ita daga tunanin da ta jefa kanta da taji tana cewa"haba Islam ki tausayamun mana,kefa kinsan komai,kinsan Kuma in hakan ya fito dukanmu mun gama yawo wallahi","a'a kedai kin gama yawo Kam,kinsan ba zaki iyaba kika fara?,kiyi da ita nikan ta fita ta bamu wuri,ko Kuma ni nayi a gabanta dan har ita na soma k'wad'ayinta kam"wani banzan kallo Najma takebin Islam dashi da kuma tsantsar tsana da k'yamar halinsu indai abunda take tunani ne,"sister dan Allah ke kad'ai zaki iyamun wannan taimakon ,kullun inata Zazzab'in dare shine Mummy ta gayawa Yaa Ahaad tace masa Kuma naki zuwa Hospital ,shine ya Kira Dr yace ya dubani,Kinga abunda ya bani yana son yimun awan masu ciki,Kuma ni ina zargin ina dashi "ture Fadila Najma tayi daga jikinta tace"meye kike son fad'a mani?,garin yaya kika bari hakan ta faru,Fadila kinsan girman zunubin da kika aekata kuwa?,wanne mugun ne kika zauna ya rabaki da abu mafi daraja a rayuwarki?"lumshe ido Fadila tayi yace"yanzu ba wannan lokacin bane,ki duba girman Allah ki taimaki y'ar uwarki daga baya mayi magana akan wannan".rok'on Najma tai tayi sannan ta k'arb'a roban taje tayi fitsari ta kawowa Fadila suka fita tare,ita ta wuce part din Mama ita Kuma ta wuce part din Ahaad,kamar wacce ruwa yaci haka Fadila ta shiga tare da mik'a roban,wani mugun kallo Ahaad yayi mata yace"now get out, idiot gal kawai"da gudu tayo waje tana jin zuciyarta kamar zatayi tsalle ta fito.
Da wani irin mamaki Najma ke kallon Mama saidai ta kasa furta koda kalma d'aya,"kinajin mena fad'a maki ko Hadiza?,kinyi shiru baki ko kallona kefa macace,mace mai rauni ce bazaki tab'ayin abinda Namiji zaiyi ba".wani k'ululun bakin ciki ya tsayawa Najma a rai murmushi tayi tace"ba komai Mama za'ayi hakan indai hakan zai zama farin cikinki",mik'ewa tayi zata fita taci karo da Daddy kallonsa ta tsayayi saboda ba zata iya tuna rabon data ganshi ba,duk'awa tayi tace"Daddy barka da wuni".gy'ada kansa yayi yace" yauwa barka sannu"ya karkata ta gefenta ya wuce ciki wurin Mama,wasu hawayen ne masu d'umin gaske suka samu damar gangarowa daga idonta,lumshe zara zaran girar idonta tayi Wanda saika rantse da Allah sakasu tayi ,sannan ta ware ta goge idonta tayi cikin part dinsu abunta."Dr ina son result nan da anjima pls do ur best bana so ya dauki lokaci"Ahaad ya fad'a .gyad'a Kai Dr yayi yace"insha Allah kafin lokacinma zan kawo ranka ya d'ad'e"sannan sukayi sallama ya fita.
Bayan awa d'aya
Cikin wani irin firgici Ahaad yake kallon saka makon yace"wannan bamai yiwuwa bane,ka koyi aekinka da kyau?,yarinyar nan bata da aure fa,a iya sani na ba Kuma yawo taneyi ba"."wannan aekin ni nayishi da kaina,Kuma abunda ya bada kenan kaje ka binciketa zata fad'a maka gaskiya".harda d'an gudu gudu ya had'a zuwa main parlo na gidan,ganin bazai iya k'ara wani takun ba yasa ya tsaya cikin d'aga murya yace"Fadila ,Fadila"wani irin fad'uwa gaban Fadila yayi ta daura hannu a Kai tace"na shiga ukku ni Fadila yanzu Kuma me nayi?".tsaki Islam taja ta tashi ta dauki after dress ta daura akan k'aramar rigarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login