Showing 3001 words to 6000 words out of 24909 words

Chapter 2 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

28 May 2026

27

tarin haushin da takeji ya fara zuwa wurin UMMU haka ta daure ta kirkiri murmushin k'arya tace"nima nayi kewarka Son,sannu da hanya,muje ciki ka huta",cikin d'ari d'ari NAJMA tace"sannu da dawowa"beko kalleta ba,tunda yaji yanayin maganar sai kawai ya share,duka suka dunguma zuwa cikin gidan,wani haushin yakaici ya k'ule NAJMA cikin ranta tace"kambu wallahi da sakal inna k'ara kulaka kamun wannan shariyar ae"sosai ranta ya sosu dan NAJMA ta tsani wulak'anci.
A parlo suka samu AMAAN yana ta faman latse latse a waya,da sauri ya sauke k'afarsa daya daura d'aya kan d'aya yace"your welcome back brother",gyad'a masa kai kawai AHAAD yayi dan harga Allah ya gaji da magana,a parlo suka zauna ,shikan necewa kowa komai ba ya wuce part dinsu dan ya samu ya watsa ruwa,Idi ne ya shigo da jikkar laptop dinsa da phones nasa har k'asa ya duka ya bawa Daddy yace"Y'allabai k'aramin Alhaji yabar jakkar sa a mota ",karb'a Daddy"yayi yace sannu da kokari Idi".kallonsa ga NAJMA ya mayar yace "tashi ki bawa Yayanku kila a iya kiransa".wani fad'uwar gaba NAJMA taji daurewa tayi ta karb'a dan Daddy kam ba zata iya masa gardama ba,mutum na gari da sanin ya kamata duk da ABBU dinsu baya zama k'asar amma baya nuna masu k'yara ko banbanci da yaran nasu,mikewa tayi ta karb'a jikinta na rawa tana tsoron had'uwa da AHAAD,a hanya sukaci karo da FADILA wani banzan kallo ta watsawa NAJMA tace"halan ke mahaukaciya ce da bakya ganin mutane in uwarkice zaki bangajeta haka."wani uban tsaki NAJMA taja tana bin FADILA da mugun kallo tace"to ae inaga yanzu kinga banbanci balle ki kira uwata a ciki,ke har wata abace da mutun zai san ta taho bare ya kauce,ina ajin balle girman gaskiya kin yaudari kanki ,wannan kuma ya zama na k'arshe in dak'ik'ancinki ya tashi da zaki saka uwata a ciki"bata jira cewar FADILA ba tayi gaba abunta fuska had'e,sake da bak'i haka FADILA ta bita da kallo cikin d'aga murya tace"kan ubancan wallahi yau sai anyi bala'i a gidan nan ,sai kin gayamun uban waye dad'ik'ik'i"da sauri AMAAN ya fizgi hannun FADILA ya toshe mata baki,dak'in MUMMY ya shiga da ita ya saka key,cikin hassala FADILA tace"nifa Yaa Amaan bansan wannan abun wallahi,yarinya ta zageni ka hanani cin ubanta a gidan nan"wata uwar harara ya b'alla mata yace "aeke bansan yaushe zakiyi hankali ba,kwata kwata bakya rabawa,bakiga meta dauko bane?,kayan Yaa Ahaad ne fa,so kikeyi ki jawo mana bala'in da duka gidan zaita cin ubanmu,kike wani kwashe baki ke ga uwar bala'i,to ki sani watan k'aryaki ne ya tsaya a gidan nan,rigima karki fasa wallahi,tsab zan tattara kayana na gudu sai ya yafi na dawo",knocking k'ofar da akayi ne ya k'ara daga hankalinsu,sosai FADILA ta tsorata ,hannu ta daura saman kai tace"shikenan na shiga ukku ni Fadi,na janyowa kaina bala'i"sai hawaye sharr,"kaini bansan tsabar iskanci ,ku bud'emun k'ofa na shigo"MUMMY ta fad'a cikin tsawa dajin haushi,jin muryar MUMMY yasa AMAAN bud'e d'akin,tana shigowa ta ja tunga ta tsaya tana rike kunkumi cikin hassala tace"wallahi ba'a isaba,be yiwuwa in haifi yaron da cikina amma kuma ya fifita wata banza a kaina,ina tsaye amma ko kallo ban isheshi ba sai da yaje ya gaishe da waccan gayyar tsiyar sannan yazo wurina,wallahi na gaji da ganin SHA'AWA a gidan nan".dafata AMAAN yayi yace"cooldown MUMMY ae dama kece kika tsaya b'ata mana lokaci,kawai ki bani dama nayiwa yarinyar nan wayau ta fad'amun komai kawai sai mu aekasu",murmushin takaici MUMMY tayi tace"tabbas lokaci yayi da zamu kawar da abunda ya tsaya amana a hanya,lokaci yayi da zamu wataya,amma sam in har NAJMA na gidan can ba zaka iya aekata komai ba,kabar ganinta da k'ananun shekaru amma akwai wata baiwa da Allah ya bata,ni zanyi maganin ta,daga baya sai kayi sauran aekin,sanan kuma ka bari sai waccan gayyar tsiyar ABBUN naku ya dawo dan shima ya kamata ya tafi ko dan mu gaje dukiya,dama ta haramce ya tara"(kujimun MUMMY da k'arfin hali faπŸ˜„πŸ˜‚),wata sanyayyar ajiyar zuciya FADILA ta sauke tace "wallahi gara ku hanzarta,danni zan iya shak'e waccan matsiyaciyar yarinyar wata rana,shegiya me kalar aljannu,haka akwai koma ace mune baya,kullun sune gabanmu,to gara komai ya canza na gaji da zama baya","karku damu in dai ni BALKISU diyace ga JAMILA kuma nononta na sha to zanyi maganin abun cikin ruwan sanyi ba tare da samun matsala ba,amma ya zama dole ku kawar da k'iyayyar da kukewa NAJMA dole mu jata jikinmu har zuwa lokacin da burinmu zai cika"haka sukaita k'ullawa da sak'awa,nikan nace hmm muje dai zuwa .
tsaye tayi bak'in d'akin gabata na fad'uwa ta rasa me zatayi,knocking ta yi har sau ukku amma shiru ba ansa,hakan yasa tayi shahada ta tura k'ofar ta shiga,wani sanyayyan kamshin dad'i ya bigi hancinta sai da ta lumshe ido,kafin ta daura k'afarta akan lallausan carpet din dake malale tsakar d'akin,komai na d'akin blue ne sai golding kad'an babu wani yawan tarkace a dakin sai dai yayi masifar had'uwa,gani takeyi kamar yaune ta fara shigowa d'akin,zaune yake a d'aya daga cikin chairs na d'akin ya daura k'afarsa d'aya kan d'aya ya lumshe idanuwansa kamar mai barci,a hankali yake taunar pink lips dinsa wanda hakan ya zame masa jiki,wandon sojinne jikinsa sai vest kawai,shagala tayi da kallonsa,kamar daga sama taji muryarsa yace"meye?"dukda k'ananun shekarunta sai da taji daban cikin in ina tace"Daddy yace na kawo maka wannan"be ko motsa ba bare tasa ran zai mata magana,kusan minti biyar sannan ya mike ya iso gabanta ya kama hannunta ya had'e wuri d'aya,zaro idanuwa tayi harta fara hawaye tace "dan Allah Yaya kayi hakuri wallahi na daina"kallo ya k'ara binta dashi cikin hassala yace"tun yaushe na hanaki saka kaya haka"kallon jikinta tayi wando ne iya gwaiwa sai farar vest sai net data sakawa kanta,cikin kuka tace"Yaa barci na tashi ,shine kuma MUMMY ta fito dani haka"ta k'are maganar tana turo baki,k'ara had'e fuska yayi yasa hannu ya murd'e bakin da k'arfi,wani azabar zagi taji da zugi sun ziyarci ballanta ,tuni suka koma kalar ja,ihu take san yi amma ba dama,sai hawaye kawai dake zarya a kumatunta,cikin kausasshiyar murya yace"next time zan cire bakin ne,in ance ki fita haka kuma ki kara fita haka pls"ya k'arashe maganar yana ingizar da ita,k'asa ta fad'i ta bige kai da bango wani ihun azaba ta saki,ganin ya nufota yasa ta arce ana kare tana kuka,kwafa yayi ya juya sam ya tsani shigar banza,dukda ba wani girma NAJMA din tayi ba,kuma bata da kiba ko kadan,yawan masifarta da surutunta yasa ko kad'an basa zama inuwa d'aya,haushi take bashi ,shiyasa baya d'aga mata k'afa ko kad'an.
Da gudu ta shige parta dinsu kai tsaye jikin UMMU ta sauka tana kara fasa k'ara,"nikau iskancin yarinyar nan yawa gareshi,yo in banda sakalci meye na haye uwarki da girmanki haka,ki wani ishi mutane da bakinki kamar na tsuntu"MAMA ta fad'a wacce ke zaune tana dama fura,wata harara NAJMA ta balla mata tace"anje anyi to","kimun iskanci wallahi insa wancan mishkilin bayahuden ya maki shegen duka,nama nasan shiya sakaki kuka yanzu"wani kukan NAJMA ta kuma sakawa,dariya NAJWA ta saka aeko fad'an ya juye kanta,da k'yar UMMU ta rabasu ta zauna rungume da NAJMA tana aekin lallashi dan NAJMA badai bak'ar zuciya ba,abu kad'an zai hassalata.


*yanzu aka fara,salon na dabanne kudai ku bani comments nima na dage da faranta maku rai,kamar yadda na fada labari ne na daban salonsa daban da ko wanne,pls share*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.


STYLISH STAR⭐
Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
NA
*MARYAM ISMAIL MAJIDADI*


Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa


wattpad MARYAMMAJIDADI123
*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*




page 3-5


"kinga ki daina wannan kukan kinji Yarinyata,kuma ABBU dinki zai dawo anjima fa"UMMU ta fad'a a cikin kunnen NAJMA,saurin d'ago idanuwanta tayi tace"la da gaske Ummu?"ta k'arashe tambayar cike da yarinta."da gaske mana,amma in kika b'ata fuskanki ae kinsan bazaiji dad'i ba",rungume UMMU NAJMA tayi tana wani dariyan farin ciki da gudu tabar cinyar UMMU tayo main parlo na gidan gaba d'aya.tsayawa tayi tana k'arewa HAJIYA SADIYA kallo wacce keta kwad'a sallama,wani haushi ya ziyarci NAJMA ita bata san me wannan matar ta mata ba,ko kad'an jininsu bai had'uba,ganin ISLAM a bayanta yasa ta k'are had'e fuska tamkar an aeko mata da mutuwa,remote ta dauka ta zauna tare da fara canza tasha"ikon Allah ke baki ganin manyanki ,anata sallama kinyi wani shiru,wannan aeba tarbiyavbaceba,ita SHA'AWAN haka ta koya maki?"ta k'are maganar tana wani yatsina fuska,ita ga babbar HAJIYA,wani irin banzan kallo NAJMA ta jefa mata tace"karki kuskura,abun naki ya tsaya iya kaina,dan wallahi yanzu zan tata rashin kunya ga tsohuwa ahto"da sauri MUMMY ta fito dan taji maganar NAJMA kuma tasan k'aramin aekinta ne tayi abunda yafi wannan ma,"dan Allah AMINIYA kiyi hakuri,kinsan halin yaran yanzu,yanzu dai zo muje daga ciki ma tattauna"kallon mamaki HAJIYA SADIYA tabi MUMMY dashi cikin ranta tace anya lafiyar BILKISU kuwa qlau bari dai naje naji,jan hannun ISLAM tayi wanda tun d'azu take cika tana batsewa tana hararar NAJMA ,tana samu su MUMMY sukayi gaba aeko ta maza ta gayyato FADILA tare da fad'a mata abunda ya faru,jikinsu har rawa yakeyi su fito sai dai parlon wayam hakan yasa suka nufi wurin sha'k'atawar gidan sunsan iyakar yawanta kenan,aeko anan suka sameta ,harda gudu suka had'a suna zuwa FADILA ta dag'a hannu zata kaiwa NAJMA mari,da sauri ta duk'e ta mari iska tana d'agowa tace"kan ubancan,yo wallahi da kin mareni yau gidannan da kinga tashin hankalin da baki tab'a gamo dashi ba,ko uwata bata tab'a tamarina ba sai ke kutt",carab ISLAM tace"ae uwarki daban mu dabankuma da kinsan darajan uwar taki da bakiyiwa ta wasu wulak'anci ba"ji kake tas tas tas NAJMA ta dauke ISLAM da mari har ukku ta nunata da yatsa tace"yarinya ki kiyayi bakinki,uwata tafi gaban shiga irin wannan k'azamin bakin naki in kuma wani dukan kikeso to ki maimaita banza kawai"kuka ISLAM ta fashe dashi tace"wallahi Allah saina rama"tuni dambe ya kacame a tsakaninsu NAJMA ta yarda ISLAM k'asa tahau jibga kamar Allah ya aeko ta,ita kam FADILA sai faman janye NAJMA takeyi tanaso itama ta daketa,duk su biyun sun rasa yadda zasuyi da ita,da gudu NAJWA ta k'araso wurin tana cewa"innalillahi dan Allah kuyi hakuri ,ku daina mana"kuka ta sanya tana k'ok'arin rabasu.
Zaune yake daga gefansu idonshi lumshe kamar mai bacci ,sanye yake da 3quater ja sai farar t-shirt,cup din lemun dake hannunsa ya ajiye ya d'ago idanuwansa yana kallonsu gaba d'aya hayaniyarsu ta dameshi tun da suka fara fad'an duk yana jin me sukeyi,tabbas yasan basu lura dashi ba da basuyi gigin wannan fad'an ba,yunk'urawa yayi ya mike ,takalmansa farare y'an soke ya sanya tare da zura duka hannayensa a aljihu,cikin takun izza da cikarsa na namiji ya k'araso wurin wata tsawa ya daka masu,tuni suka saki juna kowa ta kama kanta,da sauri NAJWA ta had'iye kukan da takeyi,kallonsu kawai yayi cikin sanyi murya yace"ku sameni d'aki"yana zuwa nan ya juya ya wuce,wani saban kukan NAJWA ta saki tace"shi kenan kun janyo mana,wayyo Allah dama banzo nan ba","dallah malama ki rufe mana baki,to da waya gayyatoki matsoraciya kawai,ni in kinga ina fad'ana ki daina wani zomun rabo tunda zuwanki baya da amfani"NAJMA ta fad'a tana bin hanyar d'akin AHAAD dukda a tsorace take sosai sai dai bata san raini ,bata so su ISLAM su fahimci halin da take ciki na tsoronsa,sukam duk hawaye sukeyi a haka suka shiga d'akin,zaune suka sameshi a chair yayi d'aya kan d'aya,rage tsawansu sukayi d'an nesa dashi ,a hankali FADILA tace "Yaa AHAAD gamu","idan na sake jin bakinki sai kin raina kanki"ya fad'a amma ko motsi beyi ba,bazaka tab'a cewa shi yayi maganan ba,can kusan minti biyar ya d'ago yana k'are masu kallo duksun jikgata da rage tsawon,NAJMA ce kawai ta daure amma shi yaga gajiyanta sai dai sanin halinta da yayi na nuna jarumta ga abu,"NAJWA tashi ki tafi"sai da gaban NAJMA ya fad'i dukda kanta k'asa yake tasa ita zai kira,aeko har had'a step takeyi garin barin d'akin,cikin kausasshiyar murya yace"meyasa bakwajin magana?"cikin san kuka ISLAM da FADILA sukace "Yaa AHAAD dan Allah kayi hakuri,wallahi itace da tsokana tun farko"wani wawan kallo ya bisu dashi sora kad'an su saki fitsari yace"na tambaya ne",har lokacin kuma NAJMA bata d'agoba ko ta motsa ba,saboda tsabar zuciya"magana ta k'arshe wannan ya zama fad'a na karshe da zan kamaku kunayi,wallahi idan kuma kuka dab'a kunsan sauran,kuna manya amma rashin kunya baya barinku zama lafiya a gida,ku tashi kuje ke kuma NAJMA ki tsaya"wani zuciyanne ya k'ara ciwota,tana jin gudu gudun su FADILA suka wuce a d'akin,k'arasowa yayi gabanta ,ji tayi zuciyarta na neman fad'owa saboda azabar tsoro,amma ta dake still bata d'ago ba,"a gidan nan ina kuma kika sabo tarbiyar yiwa manya fitsara?"ya fad'a murya a tsawace, bakinta na rawa tace"ba ko ina","owk raini ne ?"shiru bata ansa ba sai fashewa da tayi da wani irin azabban kuka,zama kawai tayi ta had'e kanta da gwaiwa taci gaba da rairo kuka,cikin haushi ya mangare mata kai yace"na maki wani abunne sarkin jan sheri",bata kulasa ba taci gaba da kukanta a hankali tace"wallahi duk shegiyar data kuma sakamun Uwa a shirmenta saina illata..."wani wawan bugu ya kaima bakinta da sauri ta had'e maganar ta fad'a jikinshi ta rungumeshi kwarai tana cewa"Yaa kayi hakuri wallahi na daina","inafa zaki daina sai ranar dana cire wannan bakin dake zagi da rashin kunya sakarya kawai",jin kamar zai k'ara dukanta yasa ta kuma nak'aleshi,wani irin yanayi yaji yana shigarshi lokaci d'aya ,boyayyen ajiyar zuciya ya sauke yace"tashi ki barmun d'aki kin wani cikani da ihu kafin ni na karyaki kin"aeko kamar jira takeyi ta runtuma a guje,wani b'oyeyyen murmushi ya saki mai mai wuyar gani a fuskarshi yace"y'ar k'aramar yarinya sai jaraba",sometimes har mamakin jarabar NAJMA yakeyi har tsoro take bashi,bata da hakuri ko kad'an ga bak'ar zuciya,ko ina ta samota oho,dan UMMU da ABBU badai hakuri ba,ko magana ma basu cika yiba.
tana fita ta k'ofar baya ta bi,d'akinsu ta shiga ta kwanta a bed tana rabsar kuka har bacci yayi awan gaba da ita a hakan.tana shan baccinta ABBU ya dawo,sai da ya shigo har d'aki ya ganta sannan ya wuce nasu d'akin danya kimtsa,ko da ya tambaya meya sakata kuka,NAJWA ta fad'a masa murmushi kawai yayi yace"kai MAMANA akwai rigima wallahi",dariya MAMA tayi tace"ni dai bata gadoni ba,dan bani nace a saka mata KHADIJA ba,jarabar yarinyar can tayi yawa wallahi,kamar jira takeyi a tab'ata tahu bala'i can dai tayo gadonta kai wannan yarinyar jarabar JAMILA(GOGGO) ,babu abunda ta baro itace ta tashi da masifa haka"duka dariya suka saka sannan ya wuce abunshi.
B'angaren su MUMMY kam suna shiga d'aki HAJIYA SADIYA tace"AMINIYA me nake gani haka?wace irin tab'ewace ta sameki har kike gogan bayan y'ar SHA'AWA?",dariya MUMMY tayi tace "haba kwantar da hankalinki kinsan bani abu sai da dalili ae,wani abun nake nema a yarinyar kinsan itace garkuwar iyayen nata ae,dana sayeta zata bamu labarin komai kafin mu aeka dasu"dariya HAJIYA SADIYA tasa wacce yara ke kira da AUNTY tace"yauwa AMINIYATA ni dai nasan angulu ce ke bakya jewar banza,ni yanzu ga maganin nan na ansa maki,kiyi kok'ari yaci wallahi yana ci ya gama aeki,zai dawo hannunki duk wannan zafin kan na KABIR{DADDY} wallahi tafiya zaiyi sai yadda kika juya abunki,dama ga takarar SENATOR dinnan da ABBAN ISLAM ke kok'arin ya fito tun da shi na mutane ne tuni zasu tada jam'iyyah mu zama mu ke da gwamnati,ba za'ace suita siyasa ba amma cikinsu a rasa me fitowa takara ba"wani murmushin jin dadi MUMMY tayi sannan ta karbi maganin,sosai suka sha fira kafin HAJIYA SADIYA ta wuce akan cewa kome kenan sai sun sake had'uwa.


*inji ruwan comments reader's dan ALLAH ,danshi zan karanun kwarin gwaiwar suburbudo maku labarin,har yanzu bamu shiga sarkakiyar labarin ba ,kudai ku kasance dani majidadi zanjin ya zata kaya*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe


STYLISH STAR⭐
Jorderh majidadi
*RUHIN FANSA*
PAGE 6_10


Mummy da kanta tayi girki a ranar,alkubus tayi da miyar agushi tasha busasshen kifi,fa kaitar idon masu aeki tayi ta zuba maganin daidai inda tasan zata bawa Daddy,saurin juyowa tayi danjin sallamar Abbu bata san zai dawo a lokacin nan ba,fuska ta saki tace "tace a'a barka da dawowa Abbu ashe ana tafe?"tayi tambayar fuskarta sake,shima murmushin yayi yace"wallahi fa ina hanya Mummyn yara,ya hidima da gida kuma?,fatan na sameku lafiya?","lafiya qlau Alhmdllh"ta fad'a da gudu Fadila ta fito tana masa oyoyo fad'awa tayi jikinshi,wani uwar harara Ahaad ya jefa mata yace"sai kin karya mana shi ko","a'a Babana barta ae tayi kewan babanta da yawa ne ,ko Fadilana"ya karashe maganar yaba kallonta,kai ta d'aga alamun eh,fitowar Najwa da Ummu da Mama ya mai da hankalinsu kansu,sai harara Fadila ke zabgawa Najwa ,ko kulata batayi ba saboda bata da rigima kwatakwata,cikin girmamawa Abbu ya duk'a har k'asa yace"ina wuni Mama ,mun sameku lafiya?","lafiya qlau Jafar ,sannu da dawowa","yauwa Mama"rungumesa Najwa tayi tana jin kaunar Baban nata,shima tsam ya riketa a jikinshi,"kaji mun tab'ara in banda tsoron Allah ke Najwa shine zaki mak'alemun y'a in banda daukar alhaki".dariya suka saka banda Ahaad da yake mik'awa Fadila jikkar Abbu yace"zan wuce sama","kaga gantalalle,balcecen banza me halin yahudawa,kai kullun fuska a tamke kuma ba sakewa da y'an uwa,nikan ba haka mariganyi na yake ba gaskiya,daba sani dana hana wannan suna gaskiya",kwafa Ahaad yayi bece komai ba,sai tamke fuska daya kumayi ya wuce part dinsu kai tsaye,kowa b'angarensa ya wuce dan su shirya su dawo dining,suna shiga b'angarensa suka zauna yace"Ummu ina Daughter na ,tunda na taho idanuwana suke mararin ganinta,hankalina yayi kanta,daurewa kawai nayi da ban ganta a parlo ba",murmushi Ummu tayi tana Mika masa cup din ruwa tace"Abban Najwa kana yawan nuna soyayyar Najma,baka tunanin hakan zai iya shafar zumuncin yaranmu?,son yayi yawa ",cup din ruwan yakai bakinsa yasa sannan ya ajiye ya maido da hankalinsa kan Ummu yace"amma Ummu ae kinsan ina b'oyewa ,kuma Ina kwatanta adalci,duk abunda zan mallakawa Najma kinsan ina k'ok'arin mallakashi ga y'an uwanta,saboda haka kici gaba da addu'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login