Showing 12001 words to 15000 words out of 24909 words

Chapter 5 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

28 May 2026

19

tureta,tsare shi tayi da ido kamar mai tunanin abu sai kawai ta had'e fuskarta kamar an mata mutuwa ta kawar da kanta ta mik'e tabar d'akin,kai tsaye part dinsu ta nufa ,da sauri Nani ta rungumeta tace"kin tsorata ni y'ata ,meyasa kika yi haka?,na damu a kanki bana son wani abu ya sameki"ta k'are maganar tana hawaye tare da shafa fuskar.hannuwan Nani ta rik'e tace"karki damu dani ina lafiya ae,yanzu ba lokacin tsoro bane ba,lokaci ne yayi da nima zan nuna ina da daraja"bata jira cewar Nani ba tayi d'akinta Toilet ta shiga tayi wanka,tea tasha a tsai tsaye ta fito babban parlo na gidan Wanda rabon data zauna harta manta,zama tayi tare da d'aura d'aya kan d'aya ga Mug din lemu a hannunta,TV ta kunna ta mai da hankalinta gaba d'aya a kallon.
Tsaye Mummy tayi daga stairs sai cika takeyi tana batsewa a hassale tace"kan uban nan,wallahi y'ar cikina bata isa ta juya gidan nan ba"da sassarfa ta k'araso parlon remote ta dauka ta kashe TV din tana k'arewa Najma kallo ,sanye take da purple siket yad'an wuce gwaywa mai tsaga a baya sai farar T-shirt anyi rubutu da Purple colour,gashin kanta ta saki tare da dauresa da rivom shima purple,sosai tayi kyau duk da ba wani tarkace a fuskarta,da hannu take nunata sama da k'asa tace"dube ki,kalleki saboda Allah kuma kullun kina Kiran kanki a matsayin musulma ,shigarki bata da banbanci data kafirai,ko wanne namiji haka yake kallonki "wani murmushin mai rikitarwa Najma tayi cikin kwantar da kai tace"Mummy ae a shiga kawai na tsaya,wannan kuma tsakanina da ubangijina ne ke baki da hurumin yanke hukunci akan shigata,and kuma ae Allah da abunda ke zuciya yake amfani bakya ganin in aka tona zuciya wasu ba zasu fito ba balle suyi yawo?,ki saka wannan a rai dama can yanayin shigata kenan kuma zanci gaba da yinta har lokacin da Allah yayi zan daina,kuma zanyi abunda ko wanne Namiji zai iya aekatawa ,zamana mace bazai tab'a zama gazawa ba".kallonta ta maida ga Iro sarkin mota daya shigo tace"iro a fiddo mun motar Abbu ina so zan fita"jiki na rawa ya ansa da "to ranki ya dad'e ,wannen Driver ne zai kaiki?"sai da ta d'an nisa sannan tace"ba bak'ata"da sauri ya gyad'a kai ya fita dan cika umarnin Hajiyar tasa,itakam d'aki ta koma hills ta sanyo masu masifar kyau da tsini sai handbang duka cakarsu white colour eyeglasses ta daura bak'i tayi kyau sosai mukulin hannun Iro ta k'arb'a tayi waje tana taku dai dai,Mummy kam tsaye tayi kamar statue ko motsi ta kasa yi,ta kasa yarda wai Najma ce ta zama haka lallai sun sakar mata da yawa,da sauri ta k'arasa ta window tana lek'enta,Najma kam wata dalleliyar Ranz rover ta shiga ba'a y'ar yayi ta fice gidan da gudu.hannu Mummy ta daura saman kai tana cike da matuk'ar mamaki yaushe ma Najma ta iya mota?da sauri tayi hanyar d'akin Amaan.
Tuk'i takeyi hankali kwance sai lokacin nasan Najma dana phone ,wayarta ta fiddo Samsung Galaxy S7 ta turawa wata number sak'o ,kai tsaye wani pack ta nufa na y'ay'an manya ,parking tayi ta dad'e bata fitoba kafin ta zuro kyakyawan k'arta ,cikin Jan hankali take tafiyan babu Wanda ya damu da shigarta kasancewar lagos ba daga baya ba wurin k'abilu sai dai kyan da tayi yasa maza da yawa raja'a garin kallonta.a can private wuri ta zauna tana duba agogon hannunta ,abun sha aka kawo mata ,kad'an ta kurb'a lemu,zare glass din idonta tayi cike da k'osawa tace"Barrister ka dad'e fa",zama Barrister Abbas yayi yace "sorry ranki ya dad'e na tsaya duba wasu muhimman files dinne"ya k'are maganar yana ajiyesu a gabanta.d'auka tayi ta fara duddubawa ta d'an jima kafin ta saki murmushi tace"thank u,na gode kwarai da gaske ".cike da tausayinta yace"kada ki damu,munyi zaman amana da mahaifinki ya zama dole garemu mu rik'e amanarsa,duk kud'ad'en daya kamata su shiga account din ki sabo an tura,ga ATM nan da duk abunda ya dace".murmushi tayi ta k'ara godiya ta k'arb'a y'ar jakkar daya mik'o mata,sallama sukayi sannan ta juyo da niyar wucewa,ji tayi ta bige da mutun da sauri tayi baya ta d'ago dan taga wanene, murmushi dauke fuskar Aiban yace"malama Najma ashe ana ganinku a irin wannan wurin?",murmushin ta mayar masa tace"mezai hana idan mutun yana da wani uziri"kai ya jinjina yace"haka ne,ya kike?"a takaice ta ansa"da lafiya zan wuce"saurin Shan gabanta yayi ,gani tayi yayi mata wani irin k'warjini ga kyau sosai da batayi zaton yana dashi ba sai yau data k'are masa kallo,katse mata tunani yayi da fad'in"kamar kina jira nazo sai kice zaki tafi?,ya kamata ko a matsayin aboki a bani matsugunni please".juya manya manyan idanuwanta tayi,Wanda Sora kad'an ya shid'e saboda yadda suka dauki hankalinshi ,ji tayi ba zata iya musu dashi ba a sanyaye tace"tohm barka da zuwa aboki"bata jira cewarsa ba tayi gaba abunta.juyawa yayi yana k'are mata kallo yadda tayi masifar kyau ko kad'an Najma bata da k'iba sai dai tana da hips ba laifi ,gemunsa ya shafa a hankali ya furta"Masha Allah bata da banbancin da indiyawan usul"kanshi ya d'an buga sannan yayi gaba.cikin natsuwa take driving harta iso gida,gabanta ne yayi mumunar fad'uwa ganin Ahaad ya tare k'ofar shiga parts din gidan gaba d'aya ya zuba hannuwansa cikin aljihu,daurewa tayi ta fito tana tafiya cikin natsuwa,ganin irin mugun kallon da yake mata yasa ta tsaya gabansa ba tare da tace komai ba"ke wacce irin dabbar yarinya ce?,harkin isa just look at ur dressing"ya k'are maganar cikin tsantsar b'acin rai.sosai ta tsorata da yanayinsa tace"ni banga me shigana yayi ba ae"marin daya dauketa da shine ya sakata suma na y'an mintuna yace"har kina da wannan bakin?,ki fad'amun daga gidan ubanwa kike kafin na karyaki a nan".dafe kunci tayi tabi ta gefensa zata wuce fizgota yayi harta kusa fad'uwa ,"na gaji na gaji,me kake nema wurina Yaa Ahaad in baka iya ganina haka toka tafi,ka dai San bazan tab'a aekata abunda zai zubarmun da mutunci na ba a matsayina na wacce bata da kowa sai Nani d'ina,wannan shigar wani abunne daban tsakanina da ubangijina ina da abubuwan daya kamata na nuna zan iya,dan Allah na rok'eka ka barni na zauna lafiya naji da maraicina,na kumayi abunda zan iya,is barni na cika burina and kuma ina so ka sani I want to be a Soldier"ta k'are maganar tare da had'a hannuwa biyu alamar rok'o,File dinta da suka zube taga an mik'o mata ,k'arb'a tayi tare da kallon Wanda ya mik'o mata wani irin mumunar fad'uwa gabansu yayi su duka biyun,kauda hakan tayi ta k'arb'i files din ta shiga parlon,a table ta ajiye abunda ta shigo dashi cikin d'aga murya tace"Yaa Amaan,Yaa Amaan"cike da firgici Amaan ,Mummy da Fadila suka fito Wanda fuskarta ke a kumbure,kallo d'aya ta masu ta kauda kai tace"ka k'araso mana",murmushi kawai yayi ya k'araso yana kallonta."ina lissafin kayan da aka shigo dasu wancan satin?"wani kallon raini yayi mata yace "na rik'esu akai ae,me zakiyi dasu"."ka natsu nan a matsayin shugabarka ta aeki nake ,ba a matsayin k'anwarka ba,Dan haka ka fad'amun meye lissafin?",wani irin firgici da tsoro ya bayyana garesu,murmushi Ahaad yayi da suke shigowa da Muslim ya tsaya kallon ikon Allah,"a Campanyn ashana an siyar da kaya na million 25,sai na kayan masarufi na million 30"ya k'are maganar yana kallonta,murmushi tayi cikin haushi tace"lissafi yafi haka,a Campanyn ashana an sayar da kaya na million 30 ne,na kayan masarufi kuma na million 50 ne,dan haka duk inda million 30 yake to kaje ka nemosa nan da sati d'aya,kafin nazo akan sauran,ina mai sanar da kai daga gobe zan fara fita aeki kuma a matsayin shugabar ko wanne company da yake mallakin Babana,ka kula"kayanta ta kwashe tabar wurin tana tafiya cikin izza da k'asaita ,Mummy kallo takeyi tsab kamar Abbu ne ya dawo saboda har yanayin tafiyarsu iri d'aya,da kuma yadda yake harkokinsa "ragab ta fad'a a chair tana mai da numfashi hankali a yashe tace"shi kenan bansan meye abunyi ba kuma".gyad'a kai Ahaad yayi yaja hannun Muslim sukayi part dinsa,ruwan sanyi Amaan yasha yace"mun kashe maciji amma bamu sare kansa ba".


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi


*RUHIN FANSA*
*MARYAM ISMAIL MAJIDADI*
*_________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*
*inawa masoyana fatan alkhairi,na dawo zamuci gaba da gashi,na sadaukar da page din kyauta gareku na gode da soyayyarku ,masu Kira da masu text a chart ko a phone na gode kwarai Wanda ban samu amsamawa ba yayi hakuri kunsan abubuwan da yawa majidadinku na nan cikin koshin lafiya Kuma ta dawo dan faranta making*


PAGE 31-35


Dafe kai Amaan yayi yace"tab wallahi akwai babbar matsala dole musan abunyi","kwarai kuwa karka damu zan shirya wani abun,yo me akai akayi Najma Allah na tuba yarinyar da aka haifa akan tafin hannuna"Mummy ta fad'a tana mik'ewa tare da wucewa d'akinta,Najma Kam tana shiga part dinsu taga babu kowa Kai tsaye d'akinta ta shiga ta adana files din da tazo dasu,sannan ta saka kayan training ta fito,bayan gidan ta zagaya kallon k'ofar tayi an dad'e ba'a bud'e wurin ba da sunan a shiga sai dai duk week masu aeki sukan shiga su gyara wurin,bud'ewa tayi ta shiga ko ina fes abubuwa da yawa suke dawo mata akan wurin ,gani takeyi kamar zataga Abbu ya fito dan motsa jiki duk safiya,goge guntun hawayen dake idonta tayi ta soma motsa jikinta kamar zata shid'e training kala kala takeyi tana Kuma koyon abubuwa da dama,tuni tayi zufa sharkab ,fitowa tayi babban filin wurin Wanda yake k'awace da filawowi da Kuma glasses masu matukar k'yau filin an tana deshi ne saboda buk'atar gudu,gudu ta fara tana zagaye filin.Muslim dake kallonta ta window ya juyo ya kalli Ahaad yace"wacece waccan yarinyar?),shiru kamar beji saba sai Kuma yaje"Najma".da sauri Muslim ya juyo yace"what Najma kana nufin itace ta zama haka?,Amma nayi mamaki meye Kuma tsakaninta da Ahaad?".d'ago daradaran idanuwansa yayi a lokacin da yake k'arasowa gaban window din kallonsa yakai gareta,yaga yadda duka halittar jikinta ke motsawa wani irin kishi yaji ya turnik'eshi,janyo hannun Muslim yayi suka zauna amma be kuma cewa komai ba.a matuk'ar gajiye ta zauna a chairs din wurin da sauri cikin masu kula da wurin ta kawo mata glass cup dauke da ruwan sanyi,hannu tasa tare da janye gashin kanta daya rufe mata ido,sannan ta k'arbi ruwan tana tana mai da numfashi a hankali a hankali,sai da ta huta sosai sannan ta dauki k'aramin towel tana Kuma goge fuskarta tayo hanyar fitowa,ji tayi ta buge da mutun tayi baya zata fad'i,hannunta ya riko yana kallonta Sora kad'an takai k'asa Kuma yaki d'agota ya Kuma ki barinta ta k'arasa k'asa ,turo d'an k'aramin bakinta tayi tace"ae dama da gangan zaka tureni,ni ka sakeni"waro ido Ahaad yayi yace"what"sakinta yayi ta fad'a akan stairs din wurin ta bige k'ugu rintse ido tayi da k'arfi zata saki k'ara yace"shihhhhh a hakan zaki zama sojan?",had'e fuska tayi ta shanye hawayenta ta mik'e tana murgud'a masa baki tabi ta gefan sa ta wuce tana rike k'ugu murmushi yayi ya juya"wallahi har yanzu baka bar mugunta ba mugun banza "Muslim ya fad'a yana tangare k'eyar Ahaad,be dai ce komai ba har suka bar gidan.
Bayan wani lokaci
Tun daga lokacin da Najma ta koma office komai yayi daidai ga ma'aikatanta ,tana matuk'ar k'ok'ari tanayin duk abunda ya dace sai dai ta zama busy bata da lokacin kanta balle na wani,dukiya Kam Alhmdllh sai habbaka takeyi sai dai Sam ba haka Amaan da Mummy suka so ba dan ta tare masu ko ina ,duk da suna cutarta ta k'asan k'asa amma sam sai ta nuna bata damuba,b'angaren Fadila Kam tunda sukayi fad'a da Najma har yanzu takeyi ciwo tsaitsaye har yakai ga ya kwantar da ita dukta bi ta k'are sai wahala takeyi tsabar taurin kai ya hanata zuwa asibiti a dubata Kuma taki yarda ko wanne likita ya dubata.Zaune suke kowa ya zurfafa cikin tunani "yes yes"Amaan ya fad'a yace ku kwantar da hankalinku komai yazo k'arshe,kubarmun komai nan da kwana kad'an zakuga sakamako."to Alhmdllh hakan yayi kyau dama sanyarka ce ta saka muke shan wahala ya kamata ayi komai da tsari gaskiya"Hajiya Sadiya ta fad'a.fad'ad'a murmushi Mummy tayi tace"karki damu,Amaan mun baka wuk'a da nama in dai nina haifeka yarinyar nan karta kuma sati biyu a duniya koma meye kayi,sai dai kayi a hankali dan yayanku yau zai shigo gari"."Baku da matsala Mummy zanyi komai yadda ya dace".fitowarta kenan daga meeting tayi matuk'ar gajiya sanye take da suit bak'a sai rigar cikin fara tasha zanzaro daura suit din saman tayi a k'ugunta kanta sanye cikin wata k'aramar farar himar ta idonta sanye cikin farin eye glasses ,shoe dinta bak'ak'e hill dasu tayi matuk'ar kyau sosai sai zuba kamshi takeyi duba tsadaddiyar agogon hannunta tayi kafin taja siririn tsaki ta nufi office dinta,tsaye tayi ganin Aiban zaune yana zama jiranta , mataimakiyar ta taso da sauri ta k'arfi files din hannunta tayi cikin office din dasu ,zama Najma tayi akan bench din da yake zaune sai dai d'an nesa dashi tace "ae ban san ka k'araso ba".murmushi me kyan kallo ya mata yace "ya za'ae ki sani bayan gimbiyar tawa tana can tana fama da harkar kasuwanci".y'ar dariya tayi tace"wannan suna yana mun nauyi ina laifin k'anwa ko kuma k'awa"."zaki gane nan gaba dukkin wuce wannan matsayin a tare dani"d'agowar da sukayi sukayi ido hudu da Fadila wanda shigowarta kenan tayi kyau cikin shigar bak'in dogin riga saidai tayi rama ba laifi ga wani haske da tayi,fuskarnan tata murtuke kamar an aeko mata da mutuwa tayo kansu tace"kutumar uba,yanzu Aiban cin amanar da kakeyimun kenan?,to wallahi bazan tab'a y'arda ba Kuma wannan zai zama na k'arshe,ganin tayo kan Najma yasa ya Mike da sauri ya shiga tsakaninsu yace"Fadila meye haka?,sai kin tara mana mutane?,karki kuskura kiyi k'ok'arin kaiwa gareta".wasu hawayen bak'in ciki suka zubowa Fadila tace"lallai Namiji ,Namiji ba d'an goyo ba ,akan wancan sakaryar kake wani tareni karna tab'ata ?,ina hankalinka yaje ?ko ka manya ita din k'anwatace shine cin amanar ya wuce kan kowa sai k'anwata zakaso ?,wallahi wallahi indai ina numfashi hakan bazai tab'a faruwa ba"tureshi tayi cikin huci da zafin zuciya ta nuna Najma da d'an yatsa tace"ke Kuma butulu maciyiya amana,macijiya wacce bata ramin kanta wallahi saina saka kinyi kukan wuya,wallahi saina zama Dana sani a rayuwarki bazan tab'a raga maki ba,Kuma ina gargad'inki ki rabu da Aiban,stay away from him"jikkarta ta dauka data fad'i k'asa ta fasa k'arasawa ciki ta fita da gudu tana kuka Kai tsaye inda tasan zata samu Islam ta nufa.
Najma Kam har yanzu bata motsa daga inda takeba sai da ya juyo yace"madam dan Allah kiyi hakuri"hannu ta d'aga masa tace"karka damu kasan nasan komai,Amma aeni ina tare da Kaine a matsayin aboki kuma Yaya bawai bawani abun ba,itace take kasa fahimta nasan tana sanka ae tasan bazan tab'a sanka da aure ba ,sai dai muyi rayuwa mu mutunta juna,ni zan wuce gida"bata jira cewarsa ba ta shiga office dinta hand bag da key din motarta da jikkar laptop dinta ta dauko ta fito,bata samesa a wurinba dama tayi zaton hakan,mota ta shiga tayi hanyar gidan zuciyarta da tunani kalakala harta k'arasa gidan zuciyarta bata samu sukuni ba,me gadi ya bud'e mata gate ta shiga ta dad'e a ciki kafin ta kwaso kayanta ta fito zuwa cikin gidan,a parlo ta yada zango zama tayi tare da fad'in washh,ta soma rage aninayen gaban rigarta tana k'ok'arin zare rigarne ta d'ago idonta sukayi ido hudu da Ahaad da Mama dake zaune parlon, saurin mayar da rigar tayi,"rasa kunya aeda kin k'arasa cire rigan,ni wallahi Hadiza na gaji da halinki yarinya kin koma d'iyar arna,innalillahi,yanzu Sule ka jimun yarinyar nan wai y'ar musulmi kullun yana zarya kan titi da fita k'asashe ,ae duk laifinka ne,hakkinka ne itadin amana ce a wurinka ka Kuma sani,amma kayi burus da hakan"had'e fuska Najma tayi tace"zaki fara ko?,ae nasan me kikeyiwa nifa aure yanzu baya gabana bare kice zan rasa mijin aure,Kuma ae ina da hankali bazanyi abunda zai cutar dani ba,to kisa ido ki kallo"."ka gani ko ka gani da idonka tsab yarinyar nan ta canza"d'agowa tayi da niyar magana karab suka had'a ido da Ahaad had'e maganar tayi ya duka tare da zare shoe dinta ta kwashi kayanta zata wuce,wani kallon tsana Fadila kebinta dashi wanda shigowarta kenan ,kauda Kai Najma tayi yabar parlon gaba d'aya,da murna Nani ta tareta tare da rungumeta tace"sannu da dawowa y'ata,bari na baki ruwa"kafin tayi magana Nani tasa mata Cup a baki ruwan tasha sannan tace "na gode Nani ,ya zaman gidan?"dariya Nani tayi tace a'a komai lafiya lau gaki yanzu kin dawo gidan yamun haske sosai "dariya sukayi duka kafin Nani ta Kuma cewa"kije kiyi wanka ki huta kafin kizo kici abinci"ta k'are maganar tana shafa mata Kai,rike hannun Nani tayi cike da tsantsar Sonta da kularta tace"Nani ina sanki sosai,ke din ta dabance".dariya itama tayi tace"ina sanki y'ata sosai"kayanta ta dauka tayi d'akinta.
"Ina fad'a maku idan kuka kuskura aka samu matsala to kunsan sauran,ayi komai yadda ya dace"Islam ta fad'a tana kallon Maza su hud'u dake gabanta."warning na k'arshe ne wannan kuyi duk yadda za'ayi kuyi komai yadda ya dace"Fadila ta fad'a.dariya babban cikinsu yayi cikin murya marar dadin sauti yace "an gama baku da matsala ,bayau na fara irin haka ba,kudai da komai yayi daidai ku biya kudi kawai"rafar kud'i Islam ta mik'a masa tace"inkun gama zan baku sauran"basuce komai ba suka wuce.
"Zaman me kikeyi anan wurin?,ya naga baki da k'arfin jiki Kuma?"rike hannun Nani tayi tace"inajin zazzafi da ciwan Kai ne Nani"subhanallah tun yaushe?,Kuma kike zaune da ciwo baki fad'awa kowa ba?"Amaan ya fad'a yana k'arasa shigowa d'akin."ah karka damu ba wani case bane ba"."a'a bazai yiwuba zama da ciwo K'aramin alhaji dole zamu kaita asibiti yanzu"."Nani Zan Kira likita ya dubata a gida kawai"ya fad'a yana zaro waya a aljihu Dr Jamilu ya kira yace yazo gida zai duba Najma,bayan ya kashe wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login