Showing 9001 words to 12000 words out of 24909 words

Chapter 4 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

28 May 2026

18

waje daure da towel tana nuna hanyar toilet cikin firgici,kamata Nani tayi tana girgizata tace"kina lafiya?,meye a ciki?,me kika gani?"ta jero mata wad'an nan tambayoyin.hannunta na k'yarma take nuna toilet din tana cewa"Nani Najwa ce,na ganta a ciki".lek'a toilet din Nani tayi amma babu komai,juyowa tayi tace "inaga kin tsorata ne babu komai a ciki".ajiyar zuciya Najma ta sauke tace"wallahi Nani na ganta a ciki,kuma ba k'arya nayi ba","ok naji kin ganta yanzu kije ki shirya, Driver zai kaiku duba exams dinku na JSCE ,Yayanku nasan Monday ku koka SS 1".turo d'an k'aramin bakinta tayi,addu'a tayi sannan ta shiga toilet din.
Alhmdllh jarabawa tayi kyau,har sun gama komai Monday zasu koma SS1,sosai Najma tayi kuka ganin number din Najwa kuma itama taci,wani tuk'uk'un haushi ya isheta a hankali tace"zama ba nawa bane ba,dole RUHIna ya zama me cike da buri da zummar San daukar FANSA,na yi alkawari sai sun biya abunda suka yimun nan da bada jimawa ba"ta k'are maganar tana share hawayen idonta.
Tunda ta shigo ta hango shi zaune yayi crossing legs dinsa idanuwansa a lumshe da ganinsa kasan ya zurma duniyar tunani,harta wuce ko motsawa beyi ba,sai da ya dad'e a haka kafin ya mik'e ya shiga parlon,maganar da Mummy ta masa yasa ya tsaya cak yana sauraranta,sai da ta gama sannan ya juyo yace"ni na ce suke su dibo,itama ae ya kamata ta koma scul din"juyawa yayi yaci gaba da tafiyarsa.k'wafa Mummy tayi tana aeyana ranta yadda zatayi maganin Ahaad.
Shirin bacci tayi ta kwanta a d'akinta,lumshe idanuwanta tayi kamar meson yin bacci amma kuma hakan ya gagara,ji tayi kamar motsi a gefanta,a hankali ta soma bude kyawawan idanuwanta,sosai ta zarosu tare da mikewa tana fad'an "kece ,kece da gaske?"
"Kada ki tsorata banzo danna cutar da y'ar uwata kuma jini na ba,mafi soyuwa a gareni ba,a'a sai kawai dan taimako, RUHINA bazai tab'a kwanciya ba ,inhar ba mun dauki fansa ba,fad'an yafi k'arfinki,sai dai ni ina cike da burin daukar FANSA,dole su sadaukar dole su ruhin d'ayansu ya zama RUHIN FANSA ga abunda suka aekata mana.
Luuuu Najma tayi tana shirin somewa,da sauri Nani ta shigo tana kiran sunanta,ganin zata fad'i yasa tayi k'ok'arin tarota sai dai kafin ta tareta taga ta mik'e lafiya qlau kamar ba ita wani abun ya sama ba,sai dai idonta kawai daya canza ya zama ja."Nani kije ki kwanta ina lafiya ni"."y'ata ki kuka da kanki naji komai Ruhin y'ar uwarki ya fad'a haka ki zama a ankare,duk da yanzu na tabbatar Ruhin Najwa yana jikinki",kai kawai ta gyad'a mata sannan ta kwanta,tun daga wannan ranar Najma bata kuma jin d'uriyar Ruhin Najwa ba.


3years later


Abubuwa da yawa sun faru na dad'i da marar dad'i,naci gaba da kuma fad'uwa dama rayuwa haka take dole akwai k'alubale akwai kuma nasara duk bawan dayayi imani da Allah to dole a jarabashi,hakan ta faru ga wannan family mai cike da abubuwan al'ajabi,ciki harda kammala secondary school dasu Najma sukayi.yanzu suna gida basa zuwa ko ina.
Zaune take tsakiyar parlon,ta k'ara girma sosai duk da ko kad'an Najma bata da alamar k'iba a jikinta ,sai dai ba kuma zaka kirata wacce bata da shape ba,komai alamun girma sun bayyana a jikinta,daka ganta kaga cikakkiyar mace mai aji daji da kanta da kuma isa da mulki.kanta duk'e k'asa ta harde hannuwanta tana murd'a kamar tana wasa dasu,wani daddan k'amshin turare ya doshi hancinta sai dai ko k'an bata motsa ba bare ta d'ago sallama yayi amma shiru sai da ya k'ara sannan ta d'ago manyan adanuwanta ta zubasu garesa cikin dad'in murya da sai ka natsu zakaji me tace ta ansa sallamar,wani irin fad'uwa gabansa yayi yasan ko shekara d'ari zaiyi bazai tab'a manta me wannan fuskar ba,yana tare da ita,fuskar da kullun sai idanuwansa sun tariyo masa ita,ya makance akan nemanta,tsawan shekara hud'u be k'ara ganinta ba sai yau.maganar Mummy ce ta dawo dashi hayyacinshi tace"a'a Aiban ka k'araso kenan,sannu shigo mana kamar ba d'an gida ba zaka wani toge bak'in k'ofa"murmushi Aiban yayi tare da shigowa cikin tank'ameman parlon,amma idonsa k'yar akan Najma wacce tayi kamarma bata San wani ya shigo ba dan tunda ta mayar da kanta bata kuma d'agowa ba,"kije ki kawo masa abunsha kafin inzo"Mummy ta fad'a tana kallon Najma,ta d'an jima kamar ba zata tashi ba sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar kitchen,kayan jikinta yabi da kallo sanye take cikin wando iya gwaywa fari sai t-shirt ash colour kanta yana cikin net,sai silifas ga wata agogo bak'a mai shegen kyau daure a tsintsiyar hannunta,har ta b'acewa ganinsa idonshi na kanta,ruwa da lemu ta dauro a k'aramin tray ta dauko,a ransa yace bata da k'iba sai dai akwai shape ba laifi komai ya dace da jikinta,a rayuwar Najma ta tsani kallo hakan yasa ta b'allawa Aiban harara tare da ajiye tray din,jin da tayi an fizgota ta mik'e tsaye yasa ta juyo a masifance taga wanne isasshen ne,Fadila ce ,cikin tsawa take fad'in"uban meye had'inki da Wanda zan aura?,wallahi Najma bazan tab'a barinki kiyi hasara a kaina ba wannan karon,kin jibge a gida babu mai so shine abun har yakai kin fara bin mazan mu".kamanta na k'arshe ji Najma tayi kamar ta watsa mata ruwan zafi ,da k'yar ta had'a harrufan bakinta tace"sake ni"y'an gidan har kowa ya fito wata irin yanayin murya Najma tace"sake ni"ba shiri Fadila ta saketa.tuni idanuwanta sun canza cala cikin kausasshiyar murya tace"ya zama na k'arshe da zaki shake yin wannan shashancin a kaina,in ba haka ba"k'wafa kawai tayi ta nemi hanyar fita,bin bayanta Amaan yayi yana bata hak'uri dan awai abunda yake buk'ata wurinta,cikin gajiya da ganinsa a tare da ita tace"please wai lafiya?",daurewa yayi yace"dama zan tambayeki ne,wai dan Allah ko kinsan ina Abbu ya ajiye wata agogo tashi?"ji Najma tayi kamar ta shak'esa sai kuma ta daure tace"ban sani ba"tayi gaba abunta,kwantaccen gashin sajenshi ya shafa yace"zakizo hannu ne,ni na wuce ajinki balle ki rik'a wani shan murr,lokacin dana saninki yazo ne"
Kuka Fadila tasa tace"wallahi Mummy bazan tab'a barin Najma tayi nasarar kwacemun Aiban ba,ya kamata kiyi wani abu inba haka ba tabbas akwai gagarumin tashin hankalin dake doso gidan nan,Dan itama zan aeka da ita"saurin rufe mata baki Mummy tayi tace"ke baki da hankali kike irin wannan maganar idan wani yaji fa,kamar dai bani na haifeki ba,zanyi maganin komai kima fara daukar kanki a matsayin matar Aiban kawai"dariyar jin dad'i Fadila tayi ta mik'e tace"da kinmun haka kin gamamun komai"sannan ta fita,kallon Amaan takeyi hannunsa rik'e da Karan sigari yana busawa,"har yanzu dai baka rabu da sigari ba ko Amaan?,baka San lafiyarka?,to aeko ya zama dole ka barta yanzu.murmushin takaici yayi yace"babu kuma Wanda ya isa ya hani sha,idan kuma kina musu to ki kwatanta hanani,ni yanzu bana zaman kowa,so kisan akan me zamu rik'ayin magana".


Inji ruwan comments pls share


Stylish star
Jorderh majidadi
Page 21-25
"Nani inaji a jikina mamana tana raye,bata mutu ha"."meye haka kike fad'a anya Najma bakin fara zaucewa kwana biyun nan ba?".dafe kai Najma tayi cikin k'osawa da magana tace"ba wani zaucewa feelings din da nakeji yanzu ya banbanta dana ko yaushe".gyad'a kai Nani Fammah tayi tace"to ina rok'on hakan ya zama gaskiya ,da zanfi kowa farin ciki idan y'ata ta kuma kasancewa da Mamanta na asali"ta k'are maganar tana shafa fuskar Najma,murmushi sukayi tare da rungumar juna,saurin kallon agogon hannunta tayi Wanda a b'oye tasa aka canzawa cala ta danna tana k'are mata kallo,da sauri tace"Nani zanje baya",bata jira cewar Nani ba ta fice ta k'ofar baya kai tsaye bayan window din Amaan ta lab'e tana hango me akeyi a ciki,"Barrister ka fad'amun gaskiya kawai ".murmushi Bar Abbas yayi yace"Alhaji yabar wasiyyah da kada a bawa kowa dukiyarsa sai yaransa to kuma sun rasu da d'aya,yanzu bana da ikon fiddo kudin harsai ta cika wannan shekarun daya iba,amma kada ka damu lokacin nayi zan mallaka maku komai".murmushin jin dad'i Mummy tayi tace"inko harka rik'e amana ka zama daga cikinmu ta tabbas zaka samu kaso me tsoka,kuma ba zaka samu matsala ba kaga mijina shine Governor na katsina ,kaga ka samu y'anci"dariya yayi sosai ,sannan suka dauki cups da lemu a ciki suka sha cike da farin ciki. Ganin Bar Abbas zai fito yasa tayi baya da sauri ,ganin babu kowa a bayansa yasa ta fito ,da ido ya mata signal sannan ya jefa mata takarda , gyad'a kanta tayi ta dauki paper din ta tura a cikin rigarta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa ganin sun had'a ido da Amaan tana zatan koya ganta, murmushin mugunta yayi yace"a'a yanzu kika zo ko kin dad'e a nan?",kawar da tsoron tayi tace"yanzu nazo"bata jira cewarsa ba tayi gaba abunta zuwa part din Mama,nuna ta da hannu yayi ta baya alamun ya gama da ita sannan ya koma d'aki,safa da marwa yaci gaba da yi kafin ya kalli Mummy yace"ya kamata Najma ta mutu".zaro ido Hajiya sadiya tayi tace"meyasa zata mutu,meye wannan yarinyar ta sani balle kuma a ce za'a kasheta?"kalllonsa ya maido garesu zama yayi ya daura k'afa d'aya kan d'aya yace"tsinken daka raina shi yake tsone maka ido,yanzu na ganta a wurin nan kuma ina da yak'inin taji komai amma sai ta wayance,yarinyar na lura tana da masifar wayau da fahimta,kuma dai kunsan tana da ilimi dukda mun hanata damar wucewa gaba karatu"."amma Amaan mace face,ina taga jarumtar daukar Fansa?,mace ba zata tab'a yin abunda namiji yayi ba,sai dai kuma bank'i shawararka ba,amma ina son abi hanyar da waccan mayatacciyar tsohuwar ba zata zargi komai ba,kun dai sai komai nata yanzu ya ta'allaka ne akan Najma".shiru duka sukayi alamar tunani can Amaan yace"zamu samu Dr ne d'an hannu ya bamu magani mu bata ta fara ciwo,idan kuma ta kwanta sai yayi mata allurar da zata kasheta ta ruwan sanyi"."yes hakan yayi ,shawara mai kyau sai dai waye likitan da zai mana wannan aekin?"Hajiya Sadiya ta fad'a,"Aiban,Aiban shi ya kamata ya mana wannan aekin saboda shine na jikinmu"Mummy ta fad'a,zaro ido Hajiya sadiya tayi tace"na shiga ukku ni sadiya,anya Bilkisu kina da hankali kuwa?,gaskiya kina buk'atar aekin k'walwa Aiban din zaiyi wannan aekin?,ko da wasa karku tab'a barin Aiban ya gane abunda mukeyi inko haka ta faru to ina tabbatar maku koni dana haifesa bazan tsira ba,saboda halina nak'in talakka Aiban be cika San zama Nigeria ba yafi zama can Canada wurin Auntynshi Maryam,dama dai ace Islam ce a matsayinshi da bana haufi,dan da tasha nono na bata zub'ar ba"."shikenan ku barmun aekin zan samu Wanda zaiyi mun komai"Amaan ya fad'a a haka suka baro part din kowa da tunanin dake ransa.
Tana shiga d'akin Mama Fadila ta gani kwance tana ta faman danne danne a waya hankalinta kwance,k'afa ta saka mata tayi taga taga zata fad'i,amma tayi k'ok'arin dafa bango ta juyo tana kallonta kallon tuhuma,mikewa Fadila tayi tace"ae wallahi baki ba zaman jin dad'i a gidan nan,banza me kwacen saurayi kawai,ke ba namiji ba amma bakya da shiga sai k'ananun kaya da wando sai kace d'iyar kafurai?,a hakan zai soki,to ina fad'a maki sama tayiwa yaro nisa sai dai ya tada kai yai kallo,yadda kika baro cikin uwarki kisa a ranki haka ba zaki tab'a samun Aiban ba,banza karuwar gid...."had'iye sauran maganarta tayi danjin wasu irin zafafan maruka daga ko wanne kuncinta wani ihu ta saki hakan yasa Mama fitowa da gudu tana cewa"shikenan tashin duniyar yazo,kowa yayi ta kansa masu bak'in hali karsu rab'oni"turus ta tsaya tana kallon su Najma tace"ku kuma daga ina?,wannan wanne irin iskanci ne zaku cikamun kunne da ihu".a kausashe Najma ta muna Fadila da yatsa tace"wannan ya zama na k'arshe da zaki kuma ambaton iyayena a shirmenki,kuma ina so ki sani zan iya daukar komai daga gareki amma banda ki kirani karuwa ,waye kuma wani Aiban wai da mutun ne?,sai faman shishigi kikeyi amma baki k'arb'u ba ,shi Aiban din yaa nuna yana sanki ne bake kika kai kanki ba,to bari kiji ni ba soyayya zanyi da Aiban ba amma zan jawoshi jikina na kwaceshi daga gareki tunda haka kikeso,kuka inga duk fad'in gidan nan Wanda ya isa ya hanani abunda nayi niyyah","wallahi baki isaba ke k'aramar y'ar iska ce,zan nuna maki baki kaaiba,ni ni kadai ce wacce ta isa ta kula Aiban,ke har kin kai matsayin da kika mareni ,yau akwai tashin hankali a gidan nan wallahi"Fadila ta fad'a,"ke bansan iskancin banza da wofi,k'atuwar banza ki isheni da ihu a d'aki ni ku hita can waje ku k'araci iskancin naku,Dan kunga labcecen bayahude baya nan shine zaku tada hankalin kowa a gidan".uwar harara Fadila ta aekawa Mama tayi kan Najma dake shirin fita,da sauri ta damk'o gashin kan Najma dake cikin net ta janyo da k'arfi,had'e fuska Najma tayi tana jin zafin tab'a gashin na ratsa ta,a hassale ta juyo ta ingiza Fadila ta fad'a k'asa kanta ya bugu da table na tsakar d'akin ,wani uban dukan ta kuma yi mata a baki kan kace me dambe ya kaure a tsakaninsu,ihu Mama keyi tana neman ceto ta koma can bakin k'ofar d'aki tana cewa"wayyo jama'a na annabi Bilkisu kuzo kada suyi kisan kai,wayyo Sale(kana ina)na shiga ukku sun haifamun jaraba"sai kuma ta sake fashewa da kuka,shak'e Fadila Najma tayi kafin kace me ta canza mata kamanni dan sukanta takeyi kamar Allah ya aekota ko ganin gabanta bata yi,jin ihun Mama yasa duka sukayo part dinta harda Nani dake nufo wurin ga y'an aeki duksun fito,duk k'arfi Amaan kasa k'wace Fadila yayi,dan ba k'aramin shak'a Najma tayi mata ba,har idanuwanta sun zazzago ta fara hango mutuwa tana wani kuka,Mummy da Nani kam kuka suka saka,shigowarsa kenan daga wani aeki daya fita yau kwanansa biyu baya gidan a matuk'ar gajiye yake sai faman lumshe ido yakeyi,da gudu Mama data fito neman taimako tayo kansa tace"ka duba girman Allah Sule kaje kayi ceton rai,tunda uwata ta haifi ban tab'a ganin Najma a wannan yanayin ba kace karta kashe y'ar uwarta ita ta kashe kanta sai surutai takeyi mararsa kan gado"kamar bazai jeba kuma sai ya fara takawa cikin jarumta yayi part din,yana shiga yaga abunda ke faruwa ae da sauri ya k'arasa yana k'ok'arin k'watar Fadila dake dab da kabari(πŸ€£πŸ˜‚honi Najma),ganin Najma tak'i saketa hakan ya tilasta masa saka duka k'arfinsa ya ingijeta tayi taga taga zata fad'i yayi saurin rik'o hannunta ,fizge fizge ta farayi tana kiran"wallahi yau saina yi maganinki duk wani iskanci da kikemun kawai saka maki ido nakeyi,banza jahila"Fadila kam jikin Mummy ta fad'a fuska duk jini sai neman sik'ewa takeyi."ki natsu mana,meye haka?"cikin sanyin murya yake maganar ganin bata sauraransa yasa ya zabga mata mari cikin tsawa yace"nace kima mutane shiru,bana san hayaniyar nan"sai lokacin Najma ta samu damar kuka wani irin zafi takeji a zuciyarta ji takeyi kamar anan watsa mata garwashin wuta,murya bata fita ta fashe da kuka,kafin Nani ta kamata yai saurin janyota yabar d'akin da ita,ranga ranga Amaan ya dauki Fadila suka nufi part din Mummy a gado ya ajiyeta tare da Kira likita,Mummy kam ta cika tayi fal sai sauke ajiyar zuciya takeyi da k'arfi tace"kai ina wallahi Sam bazai yiwu ba ba'a haifi yarinyar ba,ta maidamun jini na haka,wallahi sai yanzu na tabbatar da lokacin mutuwarki yayi shegiya mai siffar aljannu"."ohni Allah ya ceceni ba'a kashe kowa ba anan,yanzu da Kabiru saiya k'ullaceni ,Allah ya tsareni labcece yazo kan lokaci"sai kuma ta kwashe xa dariya tace"maganin y'ar banza kenan,nasan ita ta tsokaneta gobema ta k'ara in wahala bata isheta ba"haka Mama keta faman surutu ita kad'ai.
A chair ya zauna yana kallon yadda take huci kamar taci babu,tabbas sai yau ya tabbatar tana nan a matsayinta na Najma sauyi ne kawai ta samu saboda halina rayuwa,girziga hannunta yayi amma Sam taki d'agowa saima hawaye dake bin kuncinta ga idanuwanta da suka rik'ide zuwa ja,ruwa mai sanyin gaske ya zuba a Mug bece komai ba ya kai a bakinta,bata ce komai ba ta fara shan ruwan dan dama tana buk'a ba zata iya magana bane ba,sai da ta shanye tas sannan ta koma tana ajiyar zuciya ,ta dad'e a haka kafin ya d'ago kanta gani yayi ta lanhwab'e a jikinsa alamun bacci yayi awan gaba da ita sai sauke numfashi takeyi tare da ajiyar zuciya,murmushi yayi yaja lips dinta a hankali yace"sarkin rigima kawai",a bed ya mai data yaja mata duvet kafin ya wuce d'ayan d'akin dan yayi wanka ya samu ya huta.soi da likita yabawa Fadila allurai sannan ta samu sukunin ciwan da jikinta yake mata tea tasha mai zafi sannan tasha magani daga nan bacci yayi awan gaba da ita. "Naji bayanan ku amma ina baku shawara ku bari wannan satin ya fita kudun kada a zargi Fadila,indai zaku biyani ba abunda zai hanani yi maku aekinku"murmushi Amaan yayi yace"kada ka damu ko nawa ne zan baka ae shiyasa na nemoka dan nasan zaka iya"sosai Dr Jameelu yayi dariya yace"zan wuce sai ka jini"misabaha sukayi kafin ya tafi.datiyar jin dad'i Mummy tayi tace"komai yazo k'arshe Najma".

Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe,pls share.
Stylish star
Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Na


*MARYAM ISMAIL MAJIDADI*
______________________
__________*
*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*




*RUHIN FANSA Fans yau page din naku ne,ina jin dad'in yadda kuke nuna k'auna a novel din nan kuma kuke comments yadda ya kamata,I luv u guy,son so fisabilillah*


Page 26-30


Tsaye yake yana kallon yadda ta jik'e da zufa sai jujjuya kanta takeyi alamun firgici da tsoro,wani ihu ta saki ta mik'e tana neman guduwa,cikin zafin nama ya rungumota zuwa jikinshi bubbuga bayanta yakeyi ,a hankali yake tofa mata addu'a,k'ank'amesa tayi kamar za'a k'wace mata shi,sun dad'e a haka kafin ta nutsu,d'agowa tayi a hankali tana kallonsa,wata uwar harara ya jefa mata yace"dallah malama barmun d'aki,kuma kici gaba da wasa da addu'a kinji ko?"ya k'are maganar yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login