Showing 6001 words to 9000 words out of 24909 words
kawai",wanka yayi ya shirya kafin suka fito dining din,fitowar Najma kenan daga d'aki sai cika takeyi tana batsewa tsabar masifa kawai ke cinta ,fuskarnan kamar an sauko mata da mutuwa,d'agowa tayi danjin kamshin turaren Abbu aeko da gudu ta ruga ta rungumesa ,shima rik'eta yayi sosai a jikinsa a kunnenta ya rad'a mata"Ina kika b'oye Lilly na",turo baki tayi tanawa Ahaad kallon k'asa Wanda bema nuna yasan da shigowarta ba a shag'wab'e tace"Yaya ne",murmushi kawai Abbu yayi yaja hannunta suka k'arasa dining,a fakaice Mummy ta zabga masu harara tana magana da zuciyarta,duka suka hallara dining ,Daddy yana gaishe da Abbu ba yabo babu fallasa,Mummy da kanta ta zubawa kowa kafin suka zauna suka fara ci a nutse,banda Ahaad dake ta faman latsa waya,Abbu ne ya kashe shirun da fad'in" nikan ina Amaan ne?tun da na shigo gidan nan banji ko motsinshi ba","Ina fa zakaji motsinshi yana can yana fama da shashanci sai faman shegen yawo"Mama ta fad'a tana tab'e baki tare da kai loma a baki(honi Mama tamu ta mutunci bata bar kowa ba🤣😂),shigowa parlon yayi yace"dama ke kullun saka ido kika saka a gaba)cewar Amaan dake shigowa parlon,sosai ya daure zuciyarsa ya samu ya saisaita kanshi ya duk'a dan harga Allah yana matuk'ar kiyayyar Abbu a gidan ganin yafi Daddynshi komai,kanshi a k'asa yace"Abbu barka da dawowa",cike da sakin fuska Abbu yace"lafiya qlau Amaan,sannu ya kok'ari?","lafiya qlau"ya fad'a yana Jan kujera kusa da Najma yana zama,kamo hannunta yayi cike da kulawa yace"sweet sis,barka da hutawa",wani irin bugawa gaban Ahaad yayi,yana maimaita sunan da Amaan ya Kira Najma dashi,ga hannunsu da yake gani rik'e da juna,ta k'asan table ya saka k'afarsa dake cikin b'ak'aken takalmanshi ya danne k'afarta da k'arfi harda murzawa yakeyi,wani irin k'ara Najma ta saki tana kallon k'asa,hankalin kowa ya dawo kanta,kowa yana tambayarta lafiya,shikam ko motsawa beyi ba bare kasa ran shi yayi muguntar,wani irin bakin ciki da kishi ya turnike Fadila tana jin tsanar Najma Wanda ta zarta da komai a rayuwa,saurin had'e kukanta tayi tace"ji nayi kamar wani abu yana bina fa"ta k'are maganar a shag'wab'e,"shine kuma dan iskanci zaki wa mutane ihu,wallahi Najma saina sab'a maki a gidan nan"Ummu ta fad'a,"ni dai wallahi da ba'a hannuna aka haifi yarinyar nan ba da sai ince canzota akayi,duk wani iyar shege yana wurin falwayar yarinyar nan uwar tsawo ,ko kad'an bata da hankali".harara Najma ta zubawa Mama,sai dai ta kasa cewa komai tasan tsab zata sha fad'a wuin Abbu komai zatayi yana dauka amma banda takurawa Mama,a k'a'idar Ahaad komai zaici sai yasha tea,kallon tea din dake kusa dashi Najma tayi sai tiririn zafi yakeyi,a hankali ta dunga matsar da hannunta har ta tankad'o cup din ya zub'e a hannunsa da yake latsa waya dashi,da sauri ya d'ago jin azabar zafin dake ratsa shi,sai dai ko motsi beyi ba,tana kallon idonshi wani irin tsoro ya ziyarceta tayi saurin duk'ar da kai,"innalillahi Najma anya kina da hankali kuwa"gani Ummu ta yunk'ura yasa tabar wurin da gudun tsiya,bowl me ruwan sanyi Ummu ta dauko tana saka hannun Ahaad ciki,sai jera masa sannu takeyi,kowa ya mai da hankalinsa a kansa,rike hannun Ummu yayi bayabo ba fallasa yace"Ummu am owk,zanje jirginmu ya kusa tashi",sai lokacin suka San zai tafi,bankwana yayi masu ya wuce part dinshi,jikkar labtop dinsa da phones ya dauka yabi ta k'ofar baya ,ta window ya hangota tana lek'enshi,yi yayi kamar be ganta ba,da sauri Ema ya rugo ya k'arb'i jakkarsa yaransa sai saluting nashi sukeyi,hannu kawai ya d'aga masu ya shige mota,kamar ko yaushe mota ukku suka cika suka nufi airport,"mutun sai shegen mishkilanci da gadara"Najma ta fad'a tana turo baki.
"Mummy just kawai ki bari nayi me nayi niyyah"Amaan ya fad'a yana fita waje,kai tsaye wurin Najma ya nufa tana zaune tana ta faman rubuce rubuce,dafata yayi yace"lil sannu da aeki",ba tare data dagoba tace yauwa Yaya",tattara books din tayi ta maido hankalinta a kanshi ,a hankali yace"waini sis har ina Abbu yake b'oyon takardunku na filaye da campanies dinku,na dai San k'anwar tawa babbar yarinyace akwai tarin dukiya"washe baki Najma tayi tace"wallahi ko Yaya ,kaga Campany dina ukku sai filaye da tarin kudad'e,kullun Abbu cikin saka mana kud'i a accounts dinmu yake,gana Ummu data raba mana kudad'enta ni da sister,ga Wanda Grandpa ya bamu akace tun haihuwarmu"."ah ah kice dai da Hajiya nake zaune ban sani ba,ranki ya dad'e,uwar gidana"ya k'are maganar yana risinawa,dariya Najma keyi harda k'yalk'alawa tace"wallahi fa duka Documents din suna d'akinshi a k'asan gado cikin wani akwatin k'arfe yace sai mun gama scul zai bamu".wani irin sanyin dad'i ya ratsa Amaan dajin yasan inda kayan suke,haka yaita janta da fira har lokaci ya tafi.
Wani irin k'ara Najma ta saki tare da isawa inda Najwa ke kwance malemale cikin jini duk an soketa da wuk'a,ga k'asanta na zubar jini anyi mata faca faca almar fad'e ,saurin riketa tayi tana kuka dukta gigice tace"wa yayi maki haka,wallahi bazan barshi ba".cikin wahalar numfashi Najwa take magana a hankali tace"yanzu ba wannan lokacin bane ba,duka dukiyata na baki,na tura duk wani kudina a account dinki,kowa yayi wannan akan dukiya yayi shi,ki zama jaruma ,ki dauki fansa akan koma waye,kada kiyi kuka kada ki karaya"wata magana ta k'ara gaya mata a kunne a hankali tace"kiyi komai ta sirri"takardu ta mika mata a wata jakka ,take komai nata ya saki,rai yayi hakinsa,cikin ihu Najma tayi d'akin su Ummu tana kwalla masu Kira,abun da ta ganine yasa komai nata tsayawa dukda k'ananun shekarunta hakan sai da ya girgizata,Abbu ne kwance cikin jini,sai Ummu dake kwance itama jikinta duk jini,jin motsin mutane a gaban part din ya sakata lekawa da sauri,dukansu fuskarsu a rufe da bakin abu,ganin suna zubawa ko ina fetir yasa tayi d'akinsu da sauri,jikkar da Najwa ta bata ta dauka bata jira komai ba tayo part din su Ummu,a bakin mamaki a lokacin gawar Abbu kawai ta iske,kuma babu alamun an fita dan babu sawun jini,ji tayi an fizgota da k'arfi zuwa waje,juyawa tayi ta boye jakkar saboda kashedin da Najwa tayi mata,sauri takeyi taga masu zuba fetir din kafin a kunna wutan,baya tayo da sauri ganin part din ya kama da wuta bal bal,wani irin ihu ta saki tana kiran sunan su Abbu,da sauri Amaan ya k'araso ya janye ta ,kallonshi tayi kamar mesan gano abu sai kuma ta k'ank'amesa tana kuma sakin kuka mai k'unar zuciya,nunfashinta ne ya dauke gaba d'aya ta sume a jikinshi,shafa bayanta yayi ga fuskarsa dauke da murmushi mai wuyar fassaruwa,daukarta yayi ya shiga part dinsu da ita,kuka riris Mama keyi tayi zaune a k'asa tana fad'an innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,wannan gobara ta cutar damu"kuka sosai Mummy da Fadila keyi kamar ransu zai fita,Daddy kam ya rasa ta cewa ya goya hannuwa a baya ga masu kashe wuta sunzo ,a kujera Amaan ya ajiye Najma kanta Mama tayi tana girgizata"Allahu akbar,ashe Najma tana raye ita,rashin jinki yayi amfani nasan fita kikayi har wutar ta kama baki ciki"sai kuma ta fashe da kuka,ruwa Mummy ta shafawa Najma ,wani irin yunk'urowa tayi da sauri sai dai idonta kyam hawaye kawai ke zarya a kan fuskarta,bata ida daskarewa ba sai da taji ana sanarwa Daddy sai dai suyi hak'uri ga tokar su Abbu nan da Ummu an kwaso harda ta Najwa,girgiza kai Najma tayi dan tabbas tasan lokacin da wutar ta kama Ummu hata d'akin,sai dai bata ce komai ba,dafe kanta tayi dake barazanar tarwatsewa tabbas ita kanta tasan shekarunta sunyi k'anana da daukar wannan tashin hankalin.kuka ya koma sabo gida ya kuma rud'ewa tuni ko ina ya dauka da rasuwar Alhaji Jafar Sulaiman Bindawa da iyalansa.
Bayan sati biyu
*Yanzu muka shiga labarin,ku dai ku bani ruwan comments nikan n saki alkalamina*
*Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu wayana ne ya lalace,amma yanzu na canza zaku rika jina*
Stylish star 🌟
Jorderh majidadi
*RUHIN FANSA*
page 11-15
Abubuwa sun faru dana dad'i da akasin haka,gaba d'aya yanayin gidan ya canza yanzu,kullun cikin farin ciki suke da jin dad'i kasancewar yanzu suna da yak'inin babu Wanda zai iya tarar masu gaba,Mama kam komai sukeyi tana saka ido dan lamarin Bilkisu sai dai addu' hakan yasa bata kula ta ko kad'an kullun tana part dinta,ba k'aramin abu bane ke fiddota ba.
Kwance take tana bacci sai zufa takeyi kamar wacce wani abu ke faruwa da ita a cikin bacci,a wani irin firgice ta farka bakinta dauke da addu'a,hawaye suka zubo a idanunta da gudu tayi waje ga ganin gabanta batayi,babu kowa a bakin gate hakan yasa ta fice abunta,dukda hanata fita da Mama keyi,kiyy kiyyy motar ta bada k'ara tare da tsayawa ,Driver din motar ya fito a hassale yace"ke wacce irin dabbar yarinya ce?,baki ganin gabanki salan ki jawa mutane sheri ko?".fitowar mai asalin motar yasa yayi saurin had'iye sauran maganarsa mussamman da yaga irin kallon da take binsa dashi matace da ba zata gazawa shekaru 40 ba kyakyawa da ita ta sha wankanta na alfarma,cikin dad'in murya da mutunta dan adam tace"Bala meye haka,so nawa nake gaya maka ka daina irin wannan halin?","kiyi hak'uri Hajiya naga da yanzu ta janyo mana wani tashin hankalin ".wani banzan kallo Najma ta bisa dashi kafin ta maido hankalinta ga Hajiya Maryam dake tambayarta "yarinya lafiya kuwa?,me kike so?".hawaye wasu na korar wasu da k'arfi tace"adalci nake buk'ata zaku bani?,i want justice"ganin kamar bata cikin hayyacinta yasa Aiban dake bayan Hajiya Maryam fitowa ,kyakyawan namiji ajin farko San kowa kin wanda ya rasa Aiban ba fari bane ba sai dai yana da haske mai kyau Wanda kallo d'aya zaka masa kasan hutu ya ratsa shi,dogo ne me faffad'an kirji gashin kanshi mai sheki irin me gazar gazar dinnan,kallonta yayi cikin dad'in murya yace"ayyah Mr kyakyawa ki daina b'ata fuskanki haka da kuka please,me akayi maki?",takai tsawan minti biyu tana kallonsa ,tana k'arewa halittar Allah kallo,manyan idanuwanta da suka fara canza cala ta lumshe tare da taune lips kawai sai ta juya tana share hawayen dake k'ok'arin zubo mata,har Aiban ya d'aga k'afa zai bita Hajiya Maryam (Ammi) ta rik'e hannunsa suka koma mota.
A hankali take tafiya harta iso gidan kai tsaye baya ta wuce ,dan bata buk'atar hayaniya ko wani magana yanzu,tunda abun nan ya faru Najma tayi wani irin sanyi bata magana ko kad'an ,zakayi abunka kaci ka tsire ko kallo baka isheta ba,magana ta zama abu mafi tsada a wurinta,ga rashin san hayaniya ,gaba d'aya ta canza wani irin mishkilanci ya shigeta.
Cikin tak'un k'asaita yake fitowa daga mota dawowarsa k'asar kenan tun bayar tafiyarsa,sauri kawai yakeyi yaje yaga Ummu ya tambayeta meyasa kullun wayarsu ita da Abbu a kashe,in ya tambayi y'an gida kuma suita masa b'oyeb'oye wanda sarai yasan dole akwai abunda ake b'oye masa,wannan dalilin yasa ya dawo k'asarma badan ya gama abunda yakeyi ba(Allah sarki Ahaad besan meke faruwa ba😭).sanye yake cikin kak'in uniform na soji yayi wani masifar kyau sosai kayan suka masa kyau ga wani sihirtaccen kamshi da yake fitarwa,so yakeyi sai ya fara yin wanka kafin ya shiga cikin gidan,kayansa ya karb'a a hannun Ema ya wuce ta k'ofar baya,tun daga nesa take jiyo k'amshin turarensa ga wani irin fad'uwar gaba amma ko motsawa batayi ba,kallon bayanta yakeyi harya iso kusa da ita,hakan yayi daidai da iskar me dad'in gaske na yanayin damana yake kad'awa tare da k'amshin k'asa gashin kanta dukya tashi,hannu tasa da niyar mayar da gashin bayan kunnenta taji an sakar mata wani azababben rank'washi,mai makon yaga ta juyo da masifa kamar yarda ta saba balle batasan waye ba sai yaga ta taune lips dinta kamar zata huda tare da yamutse fuska a hankali ta juyo kallo d'aya tayi masa ta kauda kanta,wani irin fad'uwa gabansa yayi ganin halin da take ciki,daure fuska ya kuma yi yace"wuce ki rufe kanki",bata ce komai ba ta Mike ta nufi cikin gida,tsaye kawai yayi yana kallon wani irin sauyin da be tab'a zato ba,anya wannan Najma ce kuwa,sosai abun ya bashi mamaki,d'age kafad'a yayi alamun ina ruwansa yayi ciki abunsa,yana shiga d'aki tun a parlo ya fara cire kayansa,duk da baya nan d'akin ba laifi and'an gara amma kallo d'aya yayi mashi ya gane wannan ba gyaran Ummu bane ba kuma bana Najwa bane ba ko Najma dan yasan suma takan sakasu gyaran d'akinshi, toilet ya shiga yayi wanka daure da towel ya fito ga k'arami yana goge sumar kanshi,phone dinshi ya dauka ya Kira waya banji meye fad'a ba sai naga ya ci gaba da abunda yakeyi kuma.
"Najma nace ki gayamun haka zakici gaba da rayuwa bacin abinci ba walwala ,Najma magana ma gagararki takeyi,dan Allah kiyi hak'uri mu dauki kaddara kinsan ko wanne bawa da tashi kaddara nasan abun dole ya tab'aki amma banyi tunanin zaikai haka ba,ace gobara ta cinye naka tas ba Wanda ta rage ae akwai tashin hankali wallahi".hular dake hannunta ta net ta saka tare da cukuicuye tulin gashin kanta Wanda yake safkowa har tsakiyar baya,ta sakashi cikin net din cikin sanyin murya Wanda muryarta ta dad'e da komawa haka tace"dan Allah Mama kibar hayaniya haka,ni ba abunda ke damuna,kawai dai nasan yanzu babu zafin da bazan iya jurewa ba,zuciyata ta daskare bana k'arayin kuka dan ciwon cin amanar da akamun kuma zan iya jure komai yanzu,kuma....."saurin rufe bakinta tayi gudun kada Mama ta gane inda ta dosa,yasa ta juya zata kwanta,shigowa Fadila tayi tace"Yaa Ahaad yace kizo Najma"."lailahaillah yauni Dije naga abunda ya isheni,waini Fadila yaushe zakiyi hankali haka kawai yarin haihuwa bana haihuwa bad'i ki ringa shigomun wurin ba sallama kamar tsohuwar b'arauniya?".turo haki Fadila tayi tace"bayan wacce nayi baki ansa ba"ta juya ta fice abunta.bin bayanta Najma tayi ta wuce part din Ahaad duk surutun da Fadila keyi ko kad'an bata kulata ba,tana zuwa bakin k'ofa ta d'an tsaya kafin ta kwankwasa k'ofar,sai da tayi kusan sau ukku sannan can cikin mak'oshi yace "shigo"tunda ta shigo ya kafeta da ido har tazo gabansa ta d'uk'a amma batace komai ba,kusan minti ukku suna haka sannan yace"zaki gyaramun d'akin nan ne",kai kawai ta gyad'a ta mik'e cikin sanyi,d'akin baya buk'atar wani gyara amma haka ta dage tana gyara ko ina kamar yadda Ummu ke koya masu,ji takeyi kamar ta saka ihu ko zataji sauki a hankali take tuna ranakun da suke taya Ummu aeki,saurin had'iye hawayenta tayi,ta k'arasa mopping din ta wanke toilet tuni d'akin ya dau k'amshi ba kamar yadda akayi gayaran d'azu sama sama ba,duk abunda takeyi yana kallonta,mamakin canzawarta yakeyi sai dai ya hango tsantsar damuwa da tashin hankali a tattare da ita,kallon inda ta tsurawa ido yayi akan bedside drawer dinsa pictures dinsa ne da Ummu da Abbu,sai wani d'aya da yake cikin kak'i,fad'uwa gabansa yayi daurews yayi ya janyo hannunta,wani irin yarr yaji amma ya dake a hankali yana lumshe ido yace"Ina Ummu?"kallon mamaki ta bisa dashi sai dai ta kasa cewa komai,girgiza hannunta yayi da k'arfi yace"please kice wani abu"hawayen data kasa tsaidawa ne suka gangaro akan fuskarta a hankali tace"duka sun rasu",wani irin zaro ido yayi yana mata wani mugun kallo yace"na lura bakya da hankali har yanzu amma ae me 11yrs ya isa ace yana da hankali"silifas dinsa ya zura yayo waje a matuk'ar rikice,a parlo ya samu duka y'an gidan suna kwasar dariya,a k'ufule yace"Mummy me kuke tunanin kunyi?,ace ba Wanda zai iya gayamun abunda ke faruwa a gida?".sai yanzu Mama ta fito tace"saboda basa so hankalinka ya tashi shiyasa har gobara ta cinye wan ubanka da matarsa data reneka da kuma kanwarka Najwa,Najma kadai Allah yasa bata cikin part din"tuni idanuwansa sun canza cala,wani irin harbawa zuciyarsa keyi da k'arfi,dafe kansa yayi dake barazanar tarwatsewa,tuni ya fara k'yarma,cikin tsantsar b'acin rai yace"yanzu idan iyayena suka mutu baza'a gayamun ba,sai su danba haihuwata sukayi ba,wallahi bana kallonku da banbanci hasalima yadda na shaku da Ummu ko kwatan hakan banyi da Mummy ba"ji yayi jiri na neman kwace masa da sauri Daddy ya kamasa ya zaunar da shi,ruwan sanyi Najma ta miko Daddy ya bashi yasha ,a hankali yake sauke ajiyar zuciya,kallon mutanan parlon kawai yakeyi"a wanne station kukayi reporting ?",maganarsa ta dawo da Mummy cikin hayyacinta kallon tsab yake mata yana ganin yadda ta rasa abun fad'a,mikewa kawai yayi yabar parlon be sake cewa komai ba.boyeyen ajiyar zuciya Mummy ta sauke duk da tasan bawai yabar case din bane ba,amma tana tunanin kafin yayi wani yunkurin zata iya gyara kokai.
Shigowar Nani Fammah yasa Najma sakin murmushin da batayi niyyah ba,aeko da gudu taje ta rungumeta tace"Nayi kewarki Nani".Nani babbar macace zata iya kaiwa shekara 36 amma tana da kyan jiki duk da ta kasance ba musulma ba ,ba zaka iya gane shekarunta ba,ita take taya Ummu rainon su Najma har suka girma kuma ita ke kula da komai nasu har yanzu,tayi tafiya zuwa garinsu ne sati biyu daya wuce duk da bata nan komai ya faru,amma ta San komai a waya,shiyasa ta dawo danta kula da Najma,Nani Fammah itace amintacciyar mai aekin Ummu.
*Gaskiya bana jin dadin yadda bakwa comments yarda ya dace ba kamar da farko ba,idan har naga ba comments alamun bakwajin dad'in lavarin kenan to zan daina rubutawa kuwa in ba'a gyara ba*
Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe.
Stylish star ☀️
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 16_20
Cikin dishewar murya Najma tace"nayi kewarki sosai Nani"kanta take shafa cike da tausayinta dan tanajin kamar ita ta haifi Najma,"nima nayi kewarki y'ata"."Ina ga tunda kin dawo zaifi ku koma part din su Ummu da aka gama gyara jiya,komai kuke buk'ata saiku nema"cewar Mummy ta k'arashe maganar tana hayewa sama,gaisa da mutan gidan Nani tayi kafin taja hannun Najma suka tafi part din,babu laifi an gyara,kuma an zuzzuba y'an abubuwan buk'ata sai dai ba masu tsad'a ba.gyara ko ina sukayi tsab kafin Najma ta shiga wanka,da gudu tayo