Showing 78001 words to 81000 words out of 82472 words

Chapter 27 - Goran Duma by Maimuna Idris Beli

Har Zuwa Yau Ruma Baki Ga Na Cancanci Kar A
Hada Kafadata Data Yushau Ba?
Zuciyarta Ta Nemi Dakatar Da Aiki Amma Wasi Wasi Ya
Hana Hakan Tafara Waige Waige Ko Nazifi Ya
Boye A Wata Kafar Ne Har Yasan Tayi Hirar Sa Da Hafsat
Amma Takasa Gano Amsar Ta Cemasa Nazifi Ina Sonka
Tasake Maimaitawa Kaji Alfaharin Ban Taba Furtawa
Yushau Wannan Kalmar Ba Kai Kuwa Na Sha Furta Maka
Bin Hakki Da Gaskiya Nan Ma Taji Jiran Amsa Cike Da
Fargaba Ta Cemasa Kadaure Karkai Fushi Yace Bazanyi Ba
Amma Ina Sonki Sani
Indai Ruma Ce Ina Sonta Badai Ruma Dai Ruma Sikila Ba?
Ko Mai Amsa Zallar Sunan Ruma Da Mai Amsa Zallar
Sunan Sikila Bazanta Ba Tsana Ba Bareke Ki Dinga Tuna
Haka Ta Ce Na Rike Ya Katse Wayar To Muwuni Lfya A
Wani Bangaren Kuma Farin ciki Yanata Faman Kwatarta
Aminci Da Alfarma A Mahaukacin Masoyi Yaugata Da
Tankasaheshen Gida A Unguwa Mai Daraja Har A Garki
Area I11
**** *******
Lokacinda Cikin Sumoli Yai Wata Takwas Saida Yushau Ya
Gwammace Daya Barta Ta Zubar Saboda Azabar Lissafe
Lissafe Ga Matsaloli Sunyi Masa Yawa Ga Basussuka Sun
Masa Yawa A Wata Juma,a Yana Kasuwa Wajen
Kasuwancinsa Aka Doko Masa Waya Daga Ofishin 'yan
Sanda Na Unguwarsu Wai Ana Son Ganinsa Hankali A
Tashe Ya Tafi Sai Ga Sumayya Tafito Tana Tura Ciki Tun
Kafin A Sanar Dashi Dalilin Kawota Yafara Hargagin Nade
Tabarmar Kunyarsa Da Hauka Meyasa Aka
Kawo Masa Mata Ba Tare Da Saninsa Ba?
Ta Inda Yake Fita Bata Nan Yake Shiga Ba Sam Yaki Yarda
Da Saurari Bayaninda 'yan Sandan Suke Masa Sai Ma Ya
Fice Ya Bar Ofishin Yan Sanda Hargagi Kuje Ku Hadiyeta
Babu Abinda Zanyi Kai Karama Zankai Ku Yawuce Yai
Tafiyar Sa Kwananta Uku A Rufe Wata Daga
Kawayenta Tayi Belinta Ba Dai Wani Abu Ya Kaita Hannun
Hukuma Ba Sai Kudin Matar Nan Data Ci Na
Ankon Sunan Atika Wanda Ta Kasa Biya A Kofar Gida Taga
Motar Yushau Taita Buga Kofar Yaki
Budewa Dole Taja Jiki Taje Gidansu Ta Kwashe Komai
Tasanar Ma Ummanta Haka Taita Mata Hudubar Banza Da
Zagin Yushau Bayan Sallar Magariba Suka Yi Kofa Gidan
Tsinke Yana Masallaci Suka Zauna Zaman Jiransa
Canwajen Karfe Tara Sai Gashi Yadawo Da Take Away
Dinsa A Hannu Yana
Ganinsu Yai Turus Kamar Ya Juya Amma Idan Momi Yai
Masa Katanga Yashiga Yimata Maraba A
Cunkushe Ya Shige Ciki Sunjima A Dakin Sumoli Suna
Jiran Yazo Gaishe Da Suruka Amma Babu Shi BaBu
Alamunsa Momi Ta Ce Lallai Wannan Takadarin Kansane
Tasameshi A Dakinsa Momi Najiranka Fa Tana So Tatafi
Waike Don Allah Zaki Barni Kuwa Na
Karasa Shekarun danazo Yi Duniya Da Sauran Lfya?
Wane Irin Bala'i Ne Tunda Kika Shigo Rayuwata Kin
Dagula Ta Gaba Daya Har Nafara Manta wani Abu Waishi
Farinciki To Yanzu Dai Kayi Hakuri Kazo Ka Fara Gamawa
Da Mominka Ga Dare Yafarayi Kaji
Yushau Ya Hayayyako Da Bala'i Toko Abincin Ma Bazanci
Bane?
Allah Ya Baka Hakuri Bayan Yakammala Ya Karasa Ya
Zauna Dab Da Kofa Ko Gaisuwa Ba Bu Ya Ce Gani Ita
Kanta Baki Na Rawa Ta Ce Masa Saikuma Kasamu
Wanman Mummunan Labari Yai Banza Da Ita Ta Bige Da
Bashi Hakuri Saboda Ta Lura Baida Niyyar Amsawa
Tagama
Surutanta Ta Wuce Tana Fita Yadubi Sumoli Ya Ce Kinsan
Allah Sisi Bazan Biya Ba Idan Sungadama Suzo Su Kara
Damkeki Ai Bani Na Aikeki Ba Yafice Haka Suka Ci Gaba Da
Zaman Doya Da Manja Yushau
Fishi Sumoli Kuma Tana Dannewa Tana Ladabi Har Yafara
Saukowa Kwatsam Ranannan Yasami Kiran
Gaggawa Daga Mahaifinsa Ta Hannun Mubarak Wanda
Yazo Har Gida Ya Ce Yatafi Dashi Tunda Yaje Mahaifinnasa
Kemasa Wani Irin Kallo Me Alaka Da Tausayi Har Dai
Yakare Da Cewa Wai Kai Baka Da
Lfyane?
Ramarka Fa Tai Yawa Saika Ce Maifama Da Cutar Cida
Lfya Lau Alhji Yanayin Rayuwane Kawai To Allah Ya Gyara
Dama Nakiraka Ne Naji Inda Aka Haihu A Ragaya Harka
Lalace Wajen Cinyewa Mutane Kudadensu Ni Danazaci
Nawa Kawai Kakeci Amma Kusan Mutane
Biyar Nakawo Min Kararka Akanka Hakadai Yushau
Yadinga Kamekame Tsakani Da Allah Yushau Ka Fada Min
Gaskiyar Abinda Ke Faruwa Da Rayuwarka Dan Da Dai Ba
Haka Kakeba Kokafara Shaye Shayene?
Ku Yafemin Alhji Nasan Tabbas Fishinku Na Tasiri A
Rayuwata Kuma Sakayyar Abinda Nayi Muku Ne Yasanya
Aka Jarrabeni A
Cikin Abinda Na Zaba Na Barku Wai Matarka?
Alhji Ya Ce Cikin Mamaki To Meye Nata A Kudin Da
Mutane Ke Binka?
Nandai Ya Kwashe Halin Zamansu Da Ita Yafada Masu
Alhji Ya Ce Har Yanzu Banji Hannunta A Kudin Mutane Ba
Yushau Inbaka
Dauka Ka Bata Ba Aiba Daureka Zata Yi Ta Ce Saika Bayar
Zata Sakeka Ba Nandai Yushau Yaimasa Karin Bayani
Akanka Alhji Ya Cemasa Yanzu Kenan Kaga Shaidar Cewa
Ba Zurfin Ilimi Ne Ke Hana Tarbiyaba?
Na Tabbatar Idan Na Rantse Bazanyi Kaffara Ba Duk Cikin
'ya'yan Gidan Nan Ba Bu Wace Zata Iya Haka Agidan
Mijinta Sannan Duk Wahalar Dawainiyar Da
Zata Duk Dawainiyar Da Zaka Yida Ruma Sikila Ina Da
Tabbacin Bazata Wahalar Dakai Kamar Wannan Matar Ba
Tun Daga Kunan Zuciya Zuwa Aljihu
Duk Na Fahimci Kurena Ina Mai Neman Gafararka Kaida
Hajiya Ba Bu Komai Ya Wuce Abu Biyu Ya Burgeni A
Alamarinka Hakurinda Kayi Na Kaucewa Yimata Saki Uku
Bare Inkayi Sakin Taki Tafiya Ku Fada Halaka Dakuma
Yadda Ka Iya Rike Babunka Ba Tare Da Ka Zubarda
Kimarka Wajen Roke Roke Ba Yushau Kam Yakara
Natsuwa Kuma Kaima Ka Tsarkake Zuciyarka Kayimata
Rikon Gaskiya Sannan In Allah Ya Sauketa Lfya Karkai Wa
Danta Ko Diyarta Rikon Dakaiwa Hamida Bana
Tsammanin Zuciyar Yushau Na Dukan Uku Uku Wallahi
Duk Zan Gyara In Allah Yaso Cikin Satinnan Zanje Abuja
To yayi Kyau Alhji Yafada A Gajarce Kuma Yatashi
Yadauko Cek Ya Hau Signing Yushau Na Kallo Yana Hadiye
Yawu Ga Wannan Kadan Toshe Wata Kofar Sauran
Basussukan Kuma Ka Barni Zanji Dasu Inji Alhji Farat
Daya Yushau Ya Kirga Kudin Dake Cek Din Naira Dubu
Dari Biyar Ne Nanfa Yafara Godiya Kuma Na Yafemaka
Kanemi Gafara Wajen Mahaifiyarka.
.
Iyaye kenan, duk wanda ya sabawa umurnin su bazai ga
da kyau ba, dunia ma kadai ta isheshi.
Allah Ya sa mu gama da iyayen mu lafiya Ya sa albarka a
rayuwar mu baki daya.
Aamiin,
Dan Aunty...
GORAN DUMA (P 65)
.
.
Dubu Dari Uku Ya Zaunar A Asusunsa Ya Kwashe Dubu
Dari Biyu Ya Doshi Gida Dasu Cike Da Cin
Alwashin Indai Kudi Na Siyo Soyayya Da Zaman Lfyar
Sumoli Abin Takaici Bai Sameta A Gida Ba Yadinga Tsaki
Ya Bude Drwer Ya Watsa Kudi Yafice Ya Bar Gidan
Hartadawo Tamai Sannu Da Zuwa
Kwana Hudu Suna 'yar Gaba Da Ita Sumoli Tai Halinnata
Na Rashin Riko Dake Shima Yaso Hakan Sai Ya Bada Kai
Bori Ya Hau Cikin Wannan Satin Sukaje Asibiti Awo Likita
Ya Tabbatar Musu Sufara Shirin Amsar Bako A Hanyar Su
Ta Dawowa Yayi Mamakin Da Batafara Yimasa Lissafin
Abinda Za A Kashe Ba Yafara Hamdala Shiriya Tazo Mata
Kamar Yanda Shima Yazo Mata Kwamfa! Cike Da Tsananin
Mamaki Da Sanyin Jiki Yagama Hargitse Dukkan Maajiyar
Kudinsa Bai Tarar Da Dubu Dari Biyun Daya Ajiye Ba
Yanemi Guri Dirshan A Falo Ya Zauna Yana Faman Hada
Gumi Yana Tunanin Yadda Kudinnan Suka Yi Tsuntsuwa
Suka Tashi Dole ya Kira Sumoli Ya Tambayeta Kudindana
Ajiye A Drawer Dakina Nake Nema Sumoli Ta Yatsina
Fuska Wanne Irin Kudi Ya Cemata Banason Tambayar
Raini, Naira Dubu Dari Biyu Ne Kudin Eye!Amma Dai Da
Mamaki Yushau Ko Mafarki Kake?
A,a A Sume Nake Haka Sukadinga
Casa Bala'i Har Na Kwana Biyar Cur Kamar Su Kashe
Kansu Ranar Kwana Na Biyar Dinne Yana Shirin Fita Sallar
Azahar Aka Dinga Murza Kararrawar Gidan Can Sai Ga
Sumoli Tana Takawa Da Kyar Fuskarta Akumbure Saboda
Kuka Ta Cemasa Don Allah Ka Bude Momina Ceta Zo Meta
zoyi?
Ni Nai Mata Waya Na Sanar Da Ita Komai In Ma Biyan
Kudin Ne Nasan
Zata Biyaka Tunda Kace Ni Na Dauka Tsinanniya Kawai A
Firgice Sumoli Ta Ce Wa!
Niko Ita?
Yakawar Dakai Rai A Bace Oho Miki Yamike Yazari Key
Yana Budewa Momi Kofar Ko Kallonta Baiyi Ba Yajuya Ciki
Abinsa Can Sumoli Tazo Waikazo Inji Momi,babu
Indazani Ku Gama Kintsa Gulmarku In Ma Miko Min
Kudina Zatayi Sannan Tatafi Dake Inajira Har Sumoli
Zata Tanka Da Tsiwa Tana Tuna Marin daya Zabga Mata
Shekaran Jiya Saita Hadiye Can jimawa Yai Alwala Kamar
Mai Zuwa Masallaci Yafita Amma Saiyadawo Ya Labe
Musu Muryar Momi Yafara Jiyowa Ai Duk Laifinkine
Ummi Tunda Kin San Wutar Cikin Mijinki.
Ni Dakinyi Shawara Dani Tun Lokacinda Kika Dau Kudin
Dakinzo Munje Wajen Malam Ya Kulle Bakin Ja"iri
Naje Fa Tun Kwana Daya Da Daukar Kudin Malam Ya
Cemin Indai Yushau Zai Iya Tunawa Da Kudin Nan Tozai
Tuna Ranar Da Aka Haifeshi Kema Momi Kin Manta Taurin
Kan Mugun
Mutumin Nan Ne Kawai Asirin Muke Kamar A Bayan
Farcensa Yake Makalewa Mts!
Aikin Banza Yo Dole Saita Hanyar Asiri Za Aci Kudinsa?
Banda Ma Dai Ke Sokuwace Doluwa Kawai In Nice Ina
Ganin Wura Wura Zai Gane Na Taba Kudin Ba Sai In
Kunna Masa Gobara Ba Ya Isa Ya Ce Kudin Wutar Bazata
Kone Suba,wallahi Danasani Hakan Nai Masa Akalla Da
Baitashi Hankalina Yanzuba Yushau Yadinga Hirji A Zuci
Ciki Tashin Hankali A Iyakar Zace Zacensa Baita Ba Zaton
Taurin Kan Sumoli Yakai Haka Ba
**** *****
Doctor Aiki Yasha Kaina Ban Sami Rako Matata Ganinka
Ba Nazifi Ke Fadawa Likita A Waya Hakane Batafi Minti
Goma Sha Biyar Da Barin Asibitinnanba Ya Cemasa
Ammafa Kusan Sati Biyar Kenan Tanafama Da Yawan
Laulayi Ai Satindaya Wuce Da Mukazo Ma Na Sanar Daka,
To Gaskiya Har Yanzu Ba Bu Sauki Jiya Cikin Darema Saida
Ta Kwara Amai Shima Likitan Cike Da Doki Ya Amsa Waida
Bari Nayi Tafara Baka Albishir Naga Kamar
Taso Haka Wane Albishir?
Tana Dauke Da Juna Biyu Na Sama Da Sati Shidda A
Firgice Nazifi Ya Ce Kace Me?
Da Gaske?
Dariya Kawai Likita Yake Yana Jin
Nazifi Na Sumbatu Har Daga Karshe Wayar Ta Katse
Kwana Biyu Nazifi Na Hadiye Murna Da Farin cikinsa
Yanajiran Ruma Ta Bashi Albishir Dinda Kanta Kamar
Yadda Likita Ya Gayamasa Amma Ta Share A Kwana Na
Uku Yakasa Daurewa Yadawo Da Wuri Ya Ce Mata Na Fiye
Sonkifa Da Kalmominda Yajanyo Bakin Zarenta Kenan Ni
Mahaka Tare Da Tsura Masa Ido Ban Yarda Ta Zarce Da
Dariya BaBu Kyau
Rainuwa Fa Babu Kyau Nazifi Ya Kauda Kai Tasha Jinin
Jikinta Tajuyo Da Kafadarsa Meyai Zafi Ido Zaici
Wuta?
Fadamin Laifi Nayiko?
Nasani Baka Cancanci Laifiba,ina Neman Afuwa tun Kafin
Katuna Min Laifin Yai Murmushi Ainazaci Ninai Laifin Ake
Hukuntani Da Boyemin Abinda Yakamata Nasani
Tashi Ga Cikin Dimuwa Menake Boyemaka?
Ko Menene Banyi Da Gayya вa,a,
"Da Gaske?"
Aiko Da Mamaki Ace Bakida Dalilin Sanar Dani Kina Da
Ciki Har Sai Likita Daga Waje Yafadamin Nandanan Tai
Fuska Oh!Wallahi
Nazaci Kasani
Nasani?
A Ina Zansani?
Ta Dubeshi Ido Cikin Ido Aina Kake Sanin Abubuwan
Danake Yi Lokacinda Bamatare?
Yadanyi Kasake Saikuma Yamike Cikin Kuzari Yana Kai
Komo A Falon
Itakuma Tai Tagumi Kawai Tana Kallonsa Da Sauri Ya
Nunata Da Yatsa Wannane Dalilinda Yasa Kika
Boyemin Kina Da Ciki?
Bare Har Na Rubanya Miki Tattalina Kukasance Cikin
Koshin Lfya Keda Bebin?
Cikin Dakewa Ta Kada Masa Kai Yajima Yana Kallanta
Fuskarsa Ba Yabo Ba Fallasa Yanufi Daki Yana Cewa Ina
Zuwa Ta Bishi Da Kallo Cikin Fargaba Tana Hasashen
Abinda Zaiyi
*** **** ***
Yana Dogare Da Kofar Dakin Yawatsa Wa Somoli Takarda
Yana Huci Idonsa Akan Mominta Ya Ce Ina Fata Zaku
Hada Kare Yanzu Kubarmin Gida A Tafi A Babbakamin
Gidan Wani Nidai Allah Ya Kubutar
Danawa Dan haka Kudin Da Kuka Dauka Saiku Yi Hidimar
Haihuwar Dasu Dama Abinda Zanyi Dasu
Kenan Ya Fice Abinsa Cikin razana Musamman Da Suka
Ga Saki Uku Momi Ta Dora Mayafi Aka Jikinta
Sai Karkarwa Yake Kinga Kwantar Da Hankalinki Kiyi
Zamanki Zanje In Sami Boka Tafice A Gaggauce Tabar
Sumoli Cikin Mawuyacin Hali Da Nadama Kaitsaye Yushau
Gidansu Ya Zarce Ya Kwashe Komai Yagayawa Hajiyarsa
Dukda Cewa Ta Razana Dajin Hakan Ta Ce Kaikuma Haka
Allah Ya Jarrabeka
Da Sakin Mata Kuma Da Ciki Musamman Ma Wadda Take
Gargarar Haihuwa ?
Cike Damamaki Yake Kallonta Kodayake Mai Daki
Shiyasan Inda Yakemasa Yoyo Amma Sumayya Ko Cikin
'yan Dari Take Dashi Ya Cancanta Yaimata Saki Uku
Karfe Sha Biyun Dare Yakoma Gidansa Idonsa Akan Dakin
Sumoli Yaga Alamar Tanan Cikin Tafasar Zuciya Yanufi
Dakin Yakwankwasa Babu Jimawa Ta Zo Ta Bude Kofar
Yajima Yanamata Kallon Mamaki Ke Kinsan Allah?
Ko Kwalam Ta Koki Ce Ta Kawoki Duniya Saikin Bar
Gidannan!Wallahi Sai Kinbar Shi Zama Dakena
Haramtawa Kai Har Abada Saboda
Haka Nayi Miki Alfarmar Safiya Ki Hada Tsiyarki Kifita
Daga Rayuwata Jafa'inki Yafi Karfina Sumoli Ta Daga Kafa
Da Kyar A Kokarinta Na Komawa Dakι Sakamakon Wani
Matsanancin Ciwon Ciki Dataji Ya Soketa Lokacinda
Yushau Ya Bar Gurin Wasa Wasa Ya Zarce Ciwon Mara
Batasan Sanda Ta Rarrafa Kofar Dakin Yushau Ba Tana
Bugawa Yushau Yadinga Tsaki Yana Juyi A Gado Yanajin
Nishin Sumoli Har Na Tsawon Fiye Da Minti Ashirin Yana
Kwance Sai Nasihar Mahaifinsa Ta Fado Masa Ka
Kyautatawa Kanka Ta Hanyar Bin Umarnin Ubangijinka
Bisa Kyautata Mu,amala Tsakaninka Da Matan Daka saki
Hakanyasa Ya Fito Kilama Haihuwa Ce Amma Me?
Yana Bude Kofar Yaci Karo Da Ita Kwance Cikin Jini Da
Alama Ta Mutu!
*** *****
Idon Ruma Nakan Hanya Nazifi Yafito Dakin Hannunsa
Dauke Da Wayoyi Biyu Yazauna Kusa Da
Ita Ta Fahimci Wayartace Da Tasa Wayar Cikin Dukan
Zuciya Daitake Binsa Da Kallo Tana Canki Cankar Meyake
Nufi Iyakar Zamanta Dashi Bata Taba Ganin Wayarta A
Hannunsa Ba Yadago Wayarta Yana Karemata Kallo A
Hankali Ya Ce BB PORSCHE Ya Dago Ya Dubeta A Ina Kika
Sai Wayar Nan?
A Rude Take Ta Ce Milkyway Mana Ai Tunda Kuka Tsafeni
Ko katin Waya In ba na Can ba Sai Inga Bashi Da Auki...
ᴬˢᴹᵞᴳᵞᴳᴳ
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 66)
.
.
Nawa Kika Siya Ina Tsammanin Ko Dubu Tamanin Ne Ko
Saba'in Ne Mts Na Manta Dai Zaki Iya Tuna Ranar Dakika
Sai Wayar?
Ban Mance Ranar Dana Siya Ba Ranar Sha Biyar Ga Watan
Nuwambar Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyune Na Rike
Ranarne Lokacindana Shiga Tarkonka Na Bincika Kuma
Na Tarar Kaine Nazifin Dana Fara Haduwa Dakai Ranar
Danaje Siyen Wayar Kinsan Gaskiyar Kudin Wayarnan?
Ta Zuramasa Ido Tana Dawani Farashine Bayan Wanda
Na Siya? Kudin Wannan Wayar Yana Kamawa Daga Dubu
Dari Uku Zuwa Sama,ruma Ta Saki Baki Kawai Tana
Kallonsa Har Tsawon Dayagama Danne Dannensa A
Wayar Ya Dago Suka Hada Ido Yasakar Mata Murmushi
Itakuma Ta Basar Ta Kawar Dakai Amma Yasanya Ta
Dawo Dakan Ta Dubeshi Lokacinda Ya Cemata Inasonki
Rumasai Muryarta Na Sarkewa Ta Ce Game Din Bai Kare
Ba Kenan?
Yadan Kai Mata Dukan Wasa Cikin Raha Wato Game ne?
Kai Ka Kirashi Da Haka Ta Fada Yanisa Hakane Ubangiji
Mai Cewa Kasance Kuma Ya Kasance Shi Yajefamin
Kaunarki Farat Daya
A Ganin Farko Danayi Miki A Harabar Milkyway Ranar Sha
Biyar Ga Watan, Nasan Zaki Tuna Yadda Naso Nuna Kaina
A Wajenki Kika Ki Bani Hadinkai Inda Har Na Kai Ga Yimiki
Karya Na Karanta Jarida A
Jami'ar Bayero Na Kuma Dace Na Fada Daidai Alhalin Ban
Taba Karatu A Kanoba Ta Daga Masa
Hannu Alamar Jinjina Tana Murmushi Daga Nan Saime?
Yakama Hannunta Yahada Da Nasa Shirine Ni Da Masud
Wato Manajana A Karbi Wayarki Da Zummar Za A Sanya
Miki Credit Anan Muka Dauki Lambobin Wayarki Ta Zaro
Ido Cikin Mamaki Eye!Ai Tukunna Ya Fada Yana Dariya Ta
Sauke Ajiyar Zuciya Sannan Ta Zame Hannunta Daga Nasa
Ta Mayar Da Tagumi To Cigaba Yakarbi Wayarta Yana
Dubawa Wannan Wayartaki Ko Sati Daya Banyi Da
Mallakarta Ba Na Siye Ta A Japan Sannan Wani
Abokin Karatuna Kuma Kwararre A Fannin Kerekere Yayi
Aikin Sanya Mata Wata Software Mai Suna "droid Air Ya
Ajiye Wayar Tata Sannan Ya Dauko Tasa Ya Shiga Matso
Hotuna Kana Ya Ci Gaba Kinsan Ko Wacce BB Tana Da
Blackberry Id Wannan Ne Yake Bayar Da Damarko
Ansace Ta Ake Iya Ganota Ta Wannan Hanyar Kuma Ana
Iya Ganin Abinda Ke Gudana A Wayar Kamar Aikawa Da
Sakonni Kira Da Shiga Internet a Sannan Kuma Ana Iya
Gane Inda Take Ruma Tadinga Kallon Wayar
Cike Da Doki Bayan Haka Ita Wannan BB Porsche Din
Tana Iya Daukar Hoto Mai Ita Ta Tura Wani Guri Daban
Idan An Saita Ta Yamika Mata Daftarin Wasu Hotuna Daya
Budo A Wayar Sa Hannunta Na
Karkarwa Ta Karba Cikin Baza Ido Dantun Kafin Wayar
Tazo Hannunta Ta Gane Hotunanta Ne Cikin Rawar Ido Da
Jiki Tafara Duban Hotunan Daya Bayan Daya A Abujane A
Kano Ne A Motane A Rano Ne A Kan Dutsene Gasunandai
Dayawa Yamiko Hannu Ta Bashi Wayar Amma Takasa
Kawai Sai Ta Dago Ta Zuba Masa Ido Numfashinta Na
Bugawa Da Sauri Da Sauri Ya Boye Damuwar Rikitar Yaci
Gaba Dayimata Bayani Waccan Software Da Abokina
Yasanya Min Ana Samunta Ne A Irin Wannan Android Din
Yanuna Mata Wayar Sa Dake Hannunta Idan Aka Saita
Wayoyi Biyu Masu Wannan Software
Duk Nisan Dake Tsakaninmu Ko Da Inanan Nigeria Kina
China Zaniya Sarrafa Wayarki Yaddanaso,zaniy
a Gano Indakike Zaniya Daukar Hoto Zaniya Nado Sauti
Zan iya Shiga Mesgs Dinki Hakadai Ya Ci Gaba Da
Nunamata Ita Kuma Taita
Godiya Ga Allah Dayasanya Bawani Abin Asshan Take
Aikatawa Ba A Boye Lokacin da Kike Tsaye A Harabar
Milkyway Muna Tsaye Nida Masud Muna Kallonki Tare Da
Kulla Yadda Zamu Bullowa Lamarinki Har Lokacinda
Kawarki Ta Shigo Kuka
Shigo Tare Kawai Sai Ga Sani Ya Rugo Fadamana Ai Ipad
Kikazo Siya To Anan Ne Ba Tare Da Dogon
Nazari Ba Masud Ya Kawo Shawarar A Siyar Miki Da
Wannan Wayar Ruma Ta Rasa Bakin Magana Sai Kallonsa
Kawai Take Babu Kiftawa Cikin dariya Ya Hura Mata Iska
Ta Wadannan Hanyoyin Nai
Tracking Din Ayyukanki Ta Haka Nasan Ke 'yar Jarida Ce
Har Nagano Jaridardakike Da Wa Aiki Wanda Hakan Ya
Saukakamin Gano Muhallinki Ta Haka Nasanke Sikila Ce
Ta Haka Nasankin Taba Aure Har Nasanwa Kika Aura
Nasan Kintaba Son Wani Auwal Amma Ya Rasu Nasan
Ranar Birthday Dinki Saidai Nasan Ki Da Kyau Daga
Nanan Gidanku Abuja Har Mazauninki Na Kano Kafin Nan
Tunda Nasan Ke Sikila Ce Na Shiga Neman Sani Akan Sikle
Cell Naziyarci Kwararren Likitan Da Ya Shawarceni Tare
Da Gwaje Gwajen Har Na Dace Da
Cewa Zan Iya Aurenki 'ya'yanmu Su Tsira Saida Duk Na
Gama Danan Sannan Na Dauki Hanyar Kano Dan
Haduwa Dake Nana Kum Nayi Katarin Haduwa Da Sani A
Matsayinsa Na Abokin Abokina Shi Kenan Yaimin Tsanin
Haduwa Da Alhji Wadda Nan Ma Na Sake Katarin Ashe
Yasan Mahaifina Wannan Katarin Ma Yakara Saukaka Min
Samin Aurenki Musamman Ta Bangaren Mahaifiyata
Waddata Kyamaci In Auri Bazawara Amma Mahaifina Na
Jero Mata Lissafin Daga Gidan Dakika Fito Saita Saki Ya
Tayar Da Kallo Akanta Cikin Dage Gira Wannan A Takaice
Kenan Kin Gamsu?
Jiki A Sanyaye Da Kuzarin Karfin Hali Ta Girgiza Kai
Sannan Ta Shiga Cikin Wayarta Ranar Sha Daya Ga Watan
Sha Biyune Naje Abuja Dan Tsira Daga Basajarka Ta Kano
Nakuma Zarce Milkyway Da Zummar Tura Wasu Ayyuka
Ta Yanar Gizo Tunda Na Sauka Abuja Na Fahimci Mutane
Na Binada Kallo
Haka Ma A Milkyway Din Kowa Yasamin Ido Miyasa?
Mutanen Gari Dake Kallonki Tsarguwa Kawai Kikayi
Jama,ar Milkyway Kuwa Duk Sunsan Da Zamanki A
Zuciyata Harma Masud Ya Basu Umarni Duk Lokacinda
Suka Ganki Su Sanar Masa Ta Kada Kai Alamar Nuna
Gamsuwa Sannan Tajefo Wata Tambayar Yaya Akai Kasan
Zanyi Rubutu Akan 'yan
Maye Ko Zuwana Gidan Hafsa?
Na Nadi Sautinku Lokacinda Kuke Hira A Mota Da
Mubarak Tare Da
Abokinsa Haka Zalika Na Nadi Sautin Farkon Hirarku Da
Hafsat Ruma Tajima Cikin Kada Kai Da Tunani Sannan Ta
Furzar Anji Amma Tayaya Kake Gane Abubuwan Da Nake
Rayawa A Zuciyata?
Cikin Zaro Ido Ya Ce Kai Haba!Saika Ce Wani Maye?
Sukayi Dariya Su Duka Sannan Tazarce Da Magana Misali
Ranar 16th Ga Watan Biyu Dubu Biyu Da Sha Uku
16-2-2013 Ranar Naje Rogo Kuma Na Hau Dutse
Sakonka Na Daidai Lokacin Tamkar Kalubalanta Ne Ga
Radadin Da Zuciyata Take Dalilin Hasashen Da
Kaicon Daya cikata Tana Sauke Numfashi Ya Amsa Mata
Idan Ina Son Abu Ko Wane Irine Ina Da Juriyar Nunawa
Allah Shi Na Tsananta Addua Akanki Fiye Da Yadda Kike
Tsammani A Tsawon Dararena Dan Haka Karkiyi Mamaki
Idan Na Dinga Aikin Da Zai Dinga Dacewa Da Abinda Uwar
Dakin Zuciyarki Ke Kimsawa Abuna Gaba Kuma Daya
Kamata Kituna Digirina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login