Showing 81001 words to 82472 words out of 82472 words

Chapter 28 - Goran Duma by Maimuna Idris Beli

Na Farko Halayyar Dan Adam Na
Karanta Babu Laifi Ina Iya Karantar Mutane A Yayin
Furucinsu Ko Kallonsu Lokacinda Suke Wani Aiki Kamar
Dai Yadda Na Kalli Fuskarki Akan Dutse Sanin Kankine
Duk Wanda Zai Nufi Daji Ya Kurawa
Horizon Ido Cikin Aihini Tabbas Sai An Tarar Yana
Jinjinawa Makagin Sammai Da Kassai In Kuma Zai
Zurfafa Tunaninsa Sai Ya Dangana Da Mutuwa
Ruma Ta Sake Rafka Tagumi Tana Kallonsa Cikin
Murmushi Can Ta Sauke Wata Wawuyar Ajiyar Zuciya
Wato Abinda Kaimin Kenan,?
Kwarai Da Gaske Kyautatawa Nayi Ko Laifi?
.
Idan an samu isashshen commnts zamuyi post din
karshe anjima....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA
KARSHE...
NA MAIMUNA BELI
TARE DA ABBAS ABDULKADIR HADA HADA
.
.
Eh To Uhum Ka Kyauta Din Kenan Kila Ba Dan Kayi Haka
Bada Yanzu Bansami Maijin Kaina Nida 'ya'yana Ba Cike
Dajin Dadi Yace Ko Banyi Haka Ba Dole Zamu Hadu Allah
Ya Hukunto Tuni Cewa Sai Mun Auri Juna Saboda Haka
Dole Mu Hadu In Baki Wannan Bebin Tare Da Kannensa
Masu Zuwa Ya Shafi Mararta Ko?
Tafada Cikin Kunya Da Dariya Toke Yaya Kika Gani?
Yatareta Cikin Dole Dan Karta Ci Gaba Da Sharewa Takada
Kai Hakane Yadanyi Shuru Zuwa Wani Lokaci Sannan Ya
Ce Idan Nasami Lokaci Mai Kyau Zan, Samu In Wargaza
Saitin. Ya ShiGa Duban Agogo Sannan Yasake Dubanta
Lokacinkine Yanzu Kin Kuma Cinye Shi Da Tuhume-
Tuhume Karka Damu Duk A Ni Din Ne Yakura Mata
Ido Har Saidata Tsargu Tanemi Baasi Da Ido Ya Ce Wai Da
Gaske Zaki Haifo Min Ya'yan Dazasu Janyo Na Kara Sonki?
Kuma Nima Idan Na Haifo 'ya'yan Nasan Tawa Zuciyar
Zata Iya Tarar Da taka Zuciyar Wadda Ta Shahara A Sona
Ya Kame Kafadarta Da
Sauri Tokice In Kara Murna Haihuwarki
Nafada Ka Kara Murnar Suka Tuntsire Da Dariya Su Duka
********* ***
Duk Da Yushau Ya Yanke Kaunar Kawai Sumoli Ta Mutu
Bai Kasa Kwasarta Cikin Tashin Hankali Yanufi Asibiti Ba
Ananne Aka Tabbatar Masa Da Bukatar Jini Bayan Ta
Farko Daga Dogon Sumanta Lokacin Dake Gwada Jininsa
Dan Neman Dacewa Da Nata Saida Ya Kawar Dakai Cikin
Hawaye Ga Ruma Can Wadda Ta Cancanci A Bata Abinda
Yafijini Tana Can Tana Rayuwa Da Jininsa Amma Ba A
Matsayinsa Ba Wannan Asarar Da Kyar Zai Iya Mayar Da
Gurbinta Jinin Sumoline Ya Hau Abinda Ya Sabbaba Mata
Barin Jini Kenan Ta Galabaita sosai,
Aka Fara Yimata Karin Jini Da Jiran Cikar Waadi Da Idan
Bata Haihu Ba Sai Ayimata Aiki Cikin Ikon Allah Kafin Sfya
Ta Haifi Santalelen Danta Namiji Bayan Yai Waya Gidansu
Ya Sanar Da Hajiyar Su Haihuwar Saiya Mikawa Sumoli
Wayar Wadda Ke Kashangare Tana Kallansa Bakin Cikin
Sakin Dayai Mata Ya Hanata Farin Cikin Karuwar Data
Samu
Ungo Ki Kira Mutanen Gidanku Ki Sanar Dasu Kin Haihu
Kai Bazaka Sanar Dasuba?
Ta Tambaya Ya Kawar Dakai Yana Kara Bata Rai Idan Kina
So Su Sani Kawai Ki Sanar Dasu Kaitsaye Ta Amsa Cikin
Kuramasa Ido To Banaso Su Sani Dan Allah Ka Daukeni
Mu Koma Gida Na Rantse Zan Rayu Dakai Kai Kadai
Batare Da Kowa Ba Kuma Nai Alkawari Zanzame Maka
Zallar Farinciki Har Mutuwa Ya Gwasaleta Ya Ce Allah
Sarki Bakin Alkalami Aiya Bushe Sukai Shuru Har Tsawon
Wani Lokaci Saida Sumoli Ta Ga Babu Sarki Sai Allah
Sannan Taiwa
Mominta Waya Ta Sanarmata Yushau Na Harabar Asibitin
Mahaifan Sumoli Sukazo Tare Dawasu Yayyenta Yana
Sane Ya Boye Musu Suka Shige Har Saida Yagano Nasa
Mahaifin Sannan Yataro Su,
Tunkafin Su Shiga Dakin Suke Jiyo Bambamin Fadan
Mahaifin Sumayya Wanda Ya Saci Jin Hirar
Anyiwa Sumayya Saki Uku A Dalilin Satar Kudi Tsakanin
Momin Da Yayyenta Masifar Dayake Batawasa Ba Ce Yana
Nuna Tsananin Bakincikinsa Da Auren Momi Wadda Ta
Tarwatsa Masa Rayuwar 'ya'ya Yanzu Zawarawanta Hudu
A Gaba Allah Ya Kubutardani Abinda Yushau Ke
Maimaitawa Cikin Ransa Kenan Ganin Su Yasanya
Mahaifin Sumoli Yin Shuru Saida Aka Gaggaisa Tare
Dayiwa Juna Barka Sannan Mahaifin Sumoli Yanemi
Komawa Fadansa Alhjin Yushau Yatareshi Ai Alhji Duk
Hakuri Za Ai Kai Yushau Daure Ka Mayar Da Matarka Cike
Da
Karsashi Yushau Ya Ce Ai Saki Uku Ne Alhji Kayi Wauta
Yushau Alhji Yadinga Maimaita Cikin Alhini
Yushau Kuma Yai Sagare Yana Kallan Alhji Sannan Ya Dubi
Sumoli Wannan Kadai Yaisa Tabbatar Da
Nufinsa Na Sumoli Tafi Karfin Hakuri Duniya Mahada
Duniya Maraba Inji Wani Mawaki Anan Dangi Biyu Suka
Hakurkurtar Da Juna Tare Da Alkawarin Kin
Yasar Da Zumunci Daganan Kowa Ya Kwashi Nasa Iyalin
Akai Gida Dukda Yushau Yadinga yi yana Ta Satar Kallon
Dansa A Goye Bayan Sumoli Zuciyar Sa Cike Da Dokin Ya
Cika Shekaru Biyu Ya Dauko
Abinsa Ba Tare Daya Tashi Gidan Da Ake Rowar Tarbiya
Ba.
Wani Lokaci Ciwon Ruma Yatashi Yadda Take
Murkususun Ciwo Cikin Kuka Haka Nazifi Ke Murkususun
Ciwon Zuciyar Tausayinta Cikin Hawaye Sai Bayan Allura
Tafara Ratsa Ta Harta Sami Bacci Sannan Ya Kwashi
Sanyayyar Gwiwarsa Ya
Bar Dakin Da Aka Kwantar Da Ita Ya Cimma Likita A
Ofishinsa Likita Wane Aikine Ka Ce Ana Yiwa Sikila A
Rabasu Da Ciwon?
Likita Wane Aikine Kace Anayiwa Sikila A Rabasu Da
Ciwon?
Likita Yadan Dubeshi A Razane Baki Na Rawa Ya Amsa
"'Bone Marrow
Transplant""
Wato Dashen Bargo Kasancewar Ciwon A Ainihin
Jininsune Kuma Bargo Ke Samar Dajini Dan Haka Saidai A
Canja Shi Da Wanda Zai
Samar Dajini Mara Wannan Kantararrun Sel Din To Ina So
Ayi Wa Matata Likita Ya Dubi Nazifi Da Kyau Saiya gane
Sam Ba Cikin Hayyacinsa Ma Yakeba Saboda Haka Ya Bar
Kujerarsa Yadawo Kusa Dashi Yadinga Rarrashinsa
Tsawon Lokaci Har Ya Fahimta,
" Ka Manta Ne?"
Amma Tun Zaman Farko Damukayi Na Sanar Dakai Cewa
A Nigeria Ba A Taba Wannan Aikinba Sai A Kasashen Turai
Acandin Ma Saiwane Da Wane Akewa Saboda Yana Lasar
Miliyoyin Kudi Nazifi Ya Katsi Numfashinsa Nawane Kudin
Farashin Yana Canzawa Daga Wannan Kasa Zuwa Wannan
Amma Dai Yana Lasar Makudan Daloli Likita Ya Amsa
Nazifi Yamike Dafe Dakai Yana Ambatan Innalillahi Wa
Inna Ilaihirajiun Sannan Yanuna
Alamun Fadawa Tunani Mai Nuna Kwantar Da Hankali
Yadinga Safa Da Marwa A Ofishin Cikin Dukan Zuciya
Likita Na Kallansa Cike Da Tausayi Sai Can Yaga Nazifi Ya
Daga Hannaye Sama Cikin Hawaye Fuskar Sa A Sakeya Ce
Ya Ubangiji Ina Rokonka Da Iliminka Nashaida Kaine
Ubangiji BaBu Wani Bayan Kai Makadaici Wanda Bai Haifa
Ba
Kuma Ba A Haifeshi Ba Ubangiji Kaika Ce Duk Wanda
Yarokeka Zaka Amsa Masa Ina Rokonka Ka Hore Min
Halak Dinda Zan Biya Kudaden Daza Aiwa Matata Ruma
Da 'yarta Hamida Aiki Sannan Ka Saukaka Musu Su Da
Sauran Sikila Irinsu Tare Da Dukkan Marasa Lfya Allah Ka
Sanya Wannan Ciwon Yaimusu sauki, Kasa Yai Sanadin Shi
Ga Aljanna In Har Sun Bayar Da Gaskiya Dakai Kuma Ka
Bawa Jagororinsu Juriyar Kula Dasu
Amin Likitaketa Faman Amsa Masa Cike Da Jintausayi
Yana Kallan Nazifi Wanda Ya Goge Kwalla Sannan Ya Juyo
Yai Masa Murmushi Yana Daga Masa Hannu Har Yafice
Likita Yakoma Mazauninsa Jiki A Sanyaye Cike Dajin Wani
Irin Kaye A Zuci Dama Dai Duk Sikila Suna Samun Irin
Wannan Gatan Daga Mazaje Ko Iyayensu Dama Hakan
Takasance Rayuwa Yacigaba Da Wanzuwa
Cike Dajin Dadi Da Kulawar Nazifi Har Allah Ya Sauki
Ruma Lfya Tasamu Danta Kyakyawa Maikama Da Ubansa
Cike Da Koshin Lfya Batare Da Sikila Ajikinsaba Inda Suka
samasa Sunan Mahaifin Yushau Sunakiransa Da Irfan Dan
Ruma Tana Alfahari Da Alhji Yajajirce Kwarai Akanta Da
Lfyarta Wanda Tai Amanna Koda Mahaifantane Iyakar
Abinda Zasui Matakenan.
.
ALHAMDULILLAH
KARSHE
Marubucia MAIMUNA IDRIS SANI BELI.
.
Naso ace an iso wajen da Ruma zata samu lapia , ace
koda a cikin dangi ne an hada kudin da za a mata aiki da
erta Hamida,
ciwon bashi da dadi ko kadan, nasan ciwon, shine
sanadin tafiyar kanwata mai bina, yanzu haka karamin
kani na yana dauke da kwayan ciwon.
Likitoci sun tabbatar ba cuta bace, halittace abun kamar
yadda kuka ji a cikin littapin, mace da na miji su suke
haipar da irin kwayar cutar a jikin d'an da zasu haipa.
Shi yasa yanzu likitoci suke bada shawaran kowa yasan
Genotype din sa, tun kapin soyayyar ku tayi nisa kusan
makomar ku, ammana kuskure ne sai ana saura kwana 3
aure aje gwajin genotype, da dama basa barin auren su
koda an same su da duka A.S , suna duba soyayyar dake
tsakanin su alhali basu san illar ciwon ba,
a cikin littapin nan kadan aka ambata muku game da illar
ciwon , ga wanda suka sani sun sani,
ciwon kaman iska, yanzu-yanzu zaku zauna da mutun
lapia anjima kadan ya birkice babu lapia.
A binciken da akayi a dunia a Nigeria tapi yawan masu
dauke da ciwon sikila,
kuma arewacin Nigeria ne, saboda ba'a gwaji yayin aure
shi yasa muka pi kowa dauke da masu shi ciwon,
kwanaki nagani a jarida wasu en mata da aka musu
dashen bargo tun suna yara, a lokacin an musu dashen
bargon ne ko wacce kimanin 26m a Austrilia,
A yanzu kuma kudin ya kama kimanin 100m (Miliyon
dari,)
a kudancin Nigeria ma wai an para, anyiwa mutun 6 an
samu nasaran mutun biyu,
lititocin sunce idan ana son abun ya daure dole sai
gwamnati ta shiga ciki ta bada nata gudumowar da tura
likitoci kara ilimi da kayan aiki.
.
dan Allah ina kira ga samarin gidan nan da en mata da ku
ziyarci asibiti domin a muku gwajin wannan GENOTYPE
din saboda koma yasan makomar sa.
Ina ganin yadda mahaipiya ta take pama da ciwon, tayi
jinyar kanwata, ta rasu 2015, tun tana wata 8 ake pama
da jinyarta, san da takai shekara 15 ta rasu,
yanzu ma haka ga kanina ana pama da jinyar sa shima
tun aihuwar sa,
shi da zapin ciwo yana kuka mahaipiya da hawaye....
Kusan kullun haka suke shi da ita idan ciwon ya tashi
babu bacci a idon su, haka zasu ini haka zasu kwana.
Mahaipiyata kullun tana hanyar asibiti tare dashi....
Ciwon babu dadi ko kadan.
Ina mai Addu'ar Allah ya sawaka wa masu pama da cuta
komin kankantarta Ya basu lapia Ya yaye musu,
mu kuma da muke da lapia Allah Ya kara mana lapia mai
albarka.
Aamiin
.
Dan Aunty... Angon Hamida.. Ehem..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login