Showing 18001 words to 21000 words out of 82472 words

Chapter 7 - Goran Duma by Maimuna Idris Beli

yadda rayuwa zata
kasance musu a gaba, zai rabu da ita ne,
idan ya san ita sickler ce, ko kuwa zai yi
shahadar aurenta? Za6i na 'karshe ne
fatanta, sai dai zuciyarta na wuyatantar da
yiyuwarsa.
A yanzu sun fice watanni uku tare, duk wani
laulayi da alayin cututtukanta babu wanda
Auwal bai gani ba. Yau 'kafa ciwo, gobe ciki,
jibi zazza6i, gata mura... Kai shi bai ta6a
ganin mutum mai laulayi kamarta ba, sai ma
'kari saboda tsabar tausayin da ta ke ba shi.
Kuma laulaye-laulaye nta ne ya koya masa
tarin hanyoyin da zai nuna mata kulawa.
Dan haka ya zama dan gida, dan gidan
gaske a zuciyarta da zuciyar kowa ma a
gidan in aka yi gefe da daya da murd'ad'd'e
Yusha'u.
Sai dai duk wannan sha'kuwar tasu ya rasa
dalilin da yasa Rumasa'u ta 'ki amince masa
manya su shigo maganar. Ya bata lokaci ya
'kara mata, amma har yanzu ta kasa gabatar
masa da uziri, sai dai hakan ya 'ki ya dame
shi dan yana da ya'kinin ya kai matsayin da
ya fi 'karfin yaudara a zuciyar Rumasa'u, sai
kawai ya zuba mata idon ganin gudun
ruwa, musamman da yake karatun nata ya
zo 'karshe.
Wata rana sun fice goma na dare suna hira
a zahiri daurewa kawai ta ke saboda cikinta
da ke ta faman murd'awa. Ta daure din har
suka yi sallama ta shiga gidan a birkice, zta
wuce ciki Hajiya ta yi kiranta.
"Zo nan Rumaisa'u, me yake faruwa na ga
kina yamutse fuska?"
Ta 'karaso ta zauna a gajiye.
"Wallahi cikina ke min ciwo".
Hajiya ta dubeta cikin tausayawa, ta ce.
"Sannu, sai ki yi 'kokari ki sha magani, Hafsat
taimaka ki murza mata tafarnuwar ki ta ce ki
kaw mata".
Hafsat ta tashi ta 6arin jiki tana yiwa
Rumasa'u sannu ta wuce kicin ta d'ebo
tafarnuwa masu kyau ta 6are, ta dandaka
sannan ta zuba ruwa kofi daya ta tace da
rariya ta kawowa Rumasa'u ta shanye.
An fi awa daya kafin a samu ciwon cikin ya
lafa, wannan ne kuma ya sa Hajiya ta
tsokano maganar da ta ke jin yyinta ya zama
dole dan ta fahimci Rumasa'u, so ya rufe
mata ido tana shirin yin abin da za a ga
laifinta.
"Rumasa'u kun ta6a maganar ciwonki da
Auwalu kuwa?"
Alamun damuwa da nadama ya bayyana a
fuskar Rumaisa'u, kwalla har ta cika mata
ido, ta girgiza kai ta ce.
"Ba mu ta6a ba Hajiya".
Cikin zura mata ido, Hajiya ta ce.
"Tyn farkon ne kika rasa hanyar sanar da shi
Rumasa'u?"
"Ban san za mu dore tare ba Hajiya".
Hajiya ta yi shiru alamar nazari, sannan ta
nisa ta ce.
"Ni har na fara zargin ko ganin yawan
laulayinki ya hana shi turo manyansa. Ga su
Hafsa suna ta faman jiranki".
Ta matse kwallar idonta tana amsawa.
"Ni ce na ke dakatar da shi Hajiya, kuma na
kasa sanar da shi dalili".
Hajiya ta girgiza kai ta ce.
"Wannan kuma ba dabara ba ce kika yi, za ki
ta zama haka ne Rumaisa'u? Ai a rashin kira
karen bebe yake 6ata, ki kokarta ku tattauna
lamarin".
Cikin sanyin jiki Rumaisa'u ta ce.
"Shikenan zan kokarta Hajiya".
Ta gama shin bacci ke nan ya mmako mata
waya, ta dauka da kasalar rashin 'karfin jiki.
"Auwal ba ka jin bacci?"
Muryarsa a d'ashe ya amsa.
"Na kwanta ya 'ki zuwa Rumasa'u, abubuwa
barkatai sun cushe a 'kwa'kwalwata. Ga
kadaici ga matsaloli".
Ta dan yi dariya ta ce.
"Me ya dami ranka haka Auwal?"
Ya sauke numfashi.....GORAN DUMA ****12
"Kafin mu rabu na fahimci kamar ba kya jin
dad'i, na taho da tauayinki da neman
hanyoyin da zan samar miki waraka ko da
na dauke kewa da 'karfafa gwiwa ne, amma
duk kin bi hanyoyin da hakan za ta afku kin
toshe. Na fara sarewa Rumasa'u dan na
fahimci kamar kin raba zuciyarki biyu ne kin
bar min daya na sani, dayar kuma kike
wahalar dani da ita.
Wata irin 'kaunarsa ta dingo bijiro mata,
tana nemansa ta 'kwalla, tana kokawar
daurewa yana gagara.
"Auwal wannan ne zai hanaka bacci? To in
dai ni ce ba za a haifi matsalolin da za su
6ata ranka da ni ba. Za mu sami lokaci nan
kusa mu tattauna... Amma ina son ka a jiye a
ranka soyayyarka ce ke hana ni yin abin da
kake hasashe ina jinka da matsayin wani
6angare na jikina, wanda rashinsa zai
gutsire rayuwata, amma na 'kure fatan
hakan zai gaza faruwa".
A raunane ya ce "Saboda me? Rumaisa'u
duk yadda nake da matsayi a zuciyarki da
sha'kar numfashinki d'igo ne na matsayinki
a wata zuciyar, na kuma dami raina da son
kai 'karshen buri a kanki kafin mutuwa ta
runtse ganina, ke kuma kin kasa gane
hakan..."
Ta yi saurin tare shi.
"Haba me ya kawo zancen mutuwa Auwal?"
Shi ma ya tareta da nasa batun.
"Ai ya zama dole, 'karuwar burika, cika wasu
da su6ucewar wasu alamu ne na kusantar
kabari sai raina yake ciwo da hasashen
mutuwa zata iya riksta ba tare da na cika
burin samunki ba."
Ta fara hawaye sosai, dan haka ta jima ba ta
tanka ba, har ta fitar da sautin kukanta
kadan, sannan a cikinsa ta ce masa.
"Ba na fatan dai-dai da kwayar zarra in cutar
da kai Auwal, kuma bana son rabuwa da
kai.."
Ya tare ta a dan 'kuntace.
"Shikenan sai ki bar mu muyi ta bulayi a
soyayyar da ba ta da rana, wadda ta ki ta
zuciya ta saba da ta fatar bakinki, kina sona
amma kin kasa ba ni damar mu kasance
'karkashin sunna... wannan makahon so
ne..."
Ta yi kokarin tare kukanta, ta ce.
"Akwai matsala ne Auwal, ni ke nan yau
lafiya, gobe babu. Zan zame maka dawainiya
in gundure ka, shi yasa ba na son cin karo
da kukanka Auwal".
Ya yi dariyar da ta fad'ad'a masa 'kirji ya ce.
"Wa ya ke dorawa wani lalura Rumaisa? In
Allah Ya so sai Ya yaye miki, ai babu cutar da
ba ta da magani. Ita kanta cutar ma wani
maganin ce, domin tana kankare zunubai...
Ni ma da nake son daukar dawainiyarki
ladan zan samu idan na kula da ke, duk
sanda aka ce ba ki da lafiya sai na ji da tare
muke sai na fi samun nutsuwa..."
Ta 'kara fashewa da kukan da ya tsorata shi.
A rikice ya ce.
"Wai don Allah me yake faruwa ne? Rumaisa
na kaa canko dalilan wannan kukan naki".
Cikin kukan ta ce "Na gode da niyya da
fatanka, amma ciwo na mutuwa ce kadai
zata raba... Saoda haka aurena da kai yana
nufin ka yi ta danniya da hakuri a kaina har
'karshen rayuwata, domin haka Allah Ya
halicce ni, haka kuma Ya so ya ganni..."
Ya rasa fassarar da zai wa maganganunta,
rashin yanke shawarar ya sa shi yi mata
tambaya a gajarce.
"Wai wanne irin ciwo ne?" Kai tsaye cikin
dakewa ta yi karfin halin amsa masa.
"Sickle cell" Ya ji kamar ta doka masa
guduma a 'kirji, cikin 'yan sakanni wasu
miliyoyin tausayinta da fargabar yadda
lamuransu zai kasance ya mamaye masa
'kirji, dan ya san ciwon sickle cell ba da wasa
ba kasancewar wani abokinsa sikila ne ya
dad'e da sanin yadda masu ita suke shan
kashi sai dai wannan 'karamar matsala ce
idan aka kwatanta da neman makomar
'ya'yan da za su haifa.
Duk da a rikice yake bai kasa 'ko'karin
tattara kalaman da zai 'karfafa mata gwiwa
ba.
"Mene ne matsala a kasancewar sickle
Rumaisa, ko ke kika yi kanki dan me za ki
raba kanki da ni ballatana Ubangijin da Ya yi
ni Ya yi ki, ba domin na fiki ba? Ki zama mai
tawakkali da ha'kuri da rayuwa sai
matsalolinki su zame miki kaffara. In kuma
domin wannan kike gina katanga tsakanin
da kasancewa tare, to ni ban fahimci gatan
da kike son yi min ko kike son son yi
wakanki ba".
Yanzu ta rage kukan da ta ke, dan a zahiri
hankalinta ya soma kwanciya, duk da ta san
bai kamata ya kwanta din ba.
Ta nisa ta ce.
"Kar ka yi gaggawar yanke hukunci Auwal,
ka zauna ka yi tunani da kyaun duk matsaloli
a kaina ka lissafo suka ga yadda zaka iya
tarbarsu, yadda zaka dinga dawainiya da ni,
dawainiyar aljihu da ta KWANJI, ha'kuri da ni
wajen kukan ciwo da hakurin wasu kulawa
daga gare ni lokacin ciwo in duk wadannan
sun zama sau'ki a gareka Auwal makomar
'ya'yanmu ba zata zama sau'ki ba matu'kar
ba ka kasance wanda ba zai bayar da
gudunmowar da ba zaka haifi sickler ba".
Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin
cewa, amma dole ya nemo shi.
Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin
cewa, amma dole ya nemo shi.
"Yin daainiya da ke, da kuma hakuri da
laulayinki ni ba zan ta6a kiransu matsala ba
Rumaisa, ina son ki soyayyar da nake jin ko
mugun hali ne a jininki ba zata gaza ba, bare
wannan jarrabawar ta Ubangiji da idan kika
haye ta da tawakkali, na haye ta da jurewa
dawainiya da ke zamu iya samun aljanna da
ita.
Batun 'ya'yanmu shi ne hanzari, amma
wannan zai hana ki aure har abada ke nan
Rumasa'u? Kafin haduwa da ni wanne
tanadi kika yiwa kanki a fannin aure, me
yasa kike ganin zan bayar da gudunmowar
da zamu haifi sickler?"
Ta amsa masa a raunane.
"Ban ta6a fitar da rai zan yi aure ba, sickle
cell kuma ba ciwo ne da za a ce ka auri mai
shi ya zama waraka ba, domin za ku samar
da iyali irinku ne gaba daya, amma dai ban
ta6a hasaso aurena da rayuwar auren wani
abu ne mai sau'ki ba. Ina sonka Auwal
wallahi ba na fatan duk wani abu da zai
cutar da kai, na san kuma ko yaya ne aure
na zai iya zame maka matsala ko ta fannin
'ya'yanmu..."
Ya tare ta da sauri.
"Shi yasa na tambaye ki, wacce irin
gudunmowa zan bayar da kike ala'kanta ta
da haihuwar sickler?"
Ta jima cikin shiru, sannan ta ce.
"Idan ka ji a ranka zaka iya aurena, kuma a
gidanku za a barka, shi ne zamu tuntu6i
likitoci dan samun shawarwari, a iya maka
gwaji kuma a gano kai waye, ta nan zamu
iya sanin makomar 'ya'yan namu".
Yanzu ya fara samun nutsuwa, saboda haka
cikin doki ya ce.
"In Allah Ya so cikin satin nan sai mu je
asibitin, amma ki sani duk yadda bincike zai
nuna ba na ji zai iya yi min katanga da
aurenki. Ki cire shakku daga ranki Rumasa'u,
ina yi miki soyayyar d aban san matsaloli a
tare da ke".
Ta yi shiru tsawon wasu sakanni sannan ta
ce.
"Abin da na fi so da kai Auwal ka fara
tuntu6ar magabanka shawara a kaina, kar
ka biyewa soyayyar zuciyarka ka yi abin da
ransu ba zai ji dad'insa ba...q
Ya tare ta kamar a 'kufule
"Rumaisa'u sickle cell ne yakai girman da ba
za a auri mai shi ba? Haba! Wannan
maganar banza ki ke..."
GORAN DUMA *****13
Ita ma ta tare shi a tausashe "Auwal babu
yadda za a yi ni da kaina in 'kir'kiro
abubuwan da zai nesanta mu da juna,
amma duk abin da yake matsala ina guje
mana shi kasancewara sickler na san da
yawanmu irin matsalolin da suke fuskanta a
rayuwa, ciki har da tsangamar da dangin
miji ke masu matsaloli (sicklers) da za yi ta
faman dawainiya da nauyi akan mijinsu ko
kuma haihuwar dawainiya da su. Auwal
wani lokacin ma mazajen ke tsangwamar
matan akan sun zame musu nauyi... Kai wata
ba sikilar ba ce idan suka taru ita da dangin
mijin suka haifi sikila sai ya tattara laifin ya
dora mata, wata mahaifiyar sikila da na sani
ta ta6a bani labarin yadda mijinta ya fito kai
tsaye yake 'kalubantarta akan cewa matansa
hudu, amma ita kadai ta ishe da haihuwar
sickler duk da cewa tare da mijin suka
haifeta. Amma ka fahimta ba gudu nake a
tsangwame ni ba ko ko kuma a 'kalubalance
ni, na rantse maka babu wata wuya da ba
zan iya jurewa ba, kawai dai bana sn ka yi
abin da magabatanka za su yi kuka da kai.
Idan aure zai shiga tsakaninmu ya kamata
mu kori duk wani abu da muka san
'kalubale ne a rayuwarmu ta gaba dan a
gaban ba mu da lokacinsa abin da ke
gabanmu ma ya ishe mu".
A sanyaye ya nisa, ya ce.
"Na fahimce ki, in Allah Ya so zan yi abin da
kika ce, amma dai dole mu hanzarta zuwa
gwajin, ina son yin tanadin dukkanin wata
juriya a kanki".
Ta yi murmushin karfin hali cikin saduda ta
ce.
"To shikenan, Allah Ya za6a mana abin da fi
alkhairi Auwal".
Ya amsa cike da farin ciki.
"Amin Rumaisa'u, Allah Ya sa mutuwa ce
zata raba mu".
Ta yi dariya ta ce.
"Kuma ya zama ni zan rigaka mutuwa, na
tabbatar rayuwa zata yi min 'kunci idan
babu kai".
Shima ya yi dariyar, ya ce.
"To kin ga gara ni na riga ki mutuwar,
saboda ni ba zan iya jure rayuwar da babu
ke din ba".
Da dad'i ya cikata kawai sai ta amsa masa da
cewa.
"Ina sonka Auwal!"
Ya nisa cikin wani irin shauki ya ce.
"Ni na san ina yi miki abin da ya fi So
Rumaisa'u".
Babu abin da ya motsa dan jua baya akan
soyayyar da Auwal ke mata, sai ma wani
'karin tattali da tausayi da yake mata. Ya
daura d'amarar sanin duk wani abu da ake
gudunsa ga sickler, nisali ko a ina yake idan
iska ta taso a wajen sai ya nemi Rumasa'u a
waya, idan ta shiga motarsa sai ya zuge
gilasai tsab, sannan duk wata sabga ta aljihu
da zai mata ya juyar su kaf akan abubuwan
da zai taimaki lafiyarta, dangin kayan sawa
masu kauri da rufe jiki, dogayen riguna,
hijabai, ni'kab har da safar 'kafa da hannu.
Haka nan 6angaren abinci mawuyacin abu
ne ya je mata ba tare da wani abinci da zai
amfaneta ba, ko da mafi 'kan'katarsu ne
wato rake.
Tun daga nan hankalin Rumaisa da na
iyayenta ya kwanta, suke ganin lallai ta sami
mijin marainiya, Auwal ya zama dan gida a
nan Kano, Rogo har ma da Abuja kowa a
dangin Rumaisa'u.
A nasa dangin ma Rumaisa'u, saboda haka
na'am da girman gidan su Rumasa'u,
saboda haka har sun amince da aurensu.
Auwal ya kasa tarar mahaifansa ya sanar da
su Rumasa'u sickler ce, saboda ta tsorata shi
da yadda iyaye ke kar6ar lamarin dansu ya
auri sickler, sai ya ke shakkar goyan baya
daga nasa iyayen, musamman da yake shi
kadai suka haifa, yadda suke zumudin
aurensa ya fahimci yadda suka dora masa
burin tara 'ya'ya saboda haka ya yi kirmisisi
ya 'ki sanar da su, haka ma zuwa gwajin ya
share shi saboda fargabar da ta cika ransa,
alhalin ko me ma suka samo ba zai iya karya
masa gwiwar auren Rumaisa'u ba.
A haka manyansa suka je nemar masa auren
Ruma aka yi duk yan hidimomi bisa
al'adunsu aka sanya musu rana, in ta
kammala karatu za'ayi.
*BAYAN SHEKARU BIYU*
Wata biyu ya rage aurensu, wanda za a
had'a da na Hafsat da angonta Sani. Zancen
duniya da ba ya 6uya, sai ga batun cewa,
Rumaisa'u sikila ce a kunnen mahaifan
Auwal.
Kwatsam wani dare ya bar wajenta ya koma
gida, ya shiga wajen Innarsa neman ruwan
zafi, mahaifinsa ya yi kiransa fuska babu
walwala a fuskarsa ko kad'an.
Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin jiki,
mahaifin nasa ya ce.
"Daga ina haka?"
Sai ya ji tambayar ba wai, saboda babu irinta
tsakaninsa da mahaifin nasa ko da can ma
da ba shi da gurin zuwa ba a fiye tambayar
ina ya je da dare ba ko dan yanayin aikinsa.
Amma yau shi ne ake tuhumarsa inda ya je.
Kawai sai ya yi 'kasa da kai, dan bai san abin
fad'a ba, yana ji a cikin ransa nan da wata
biyu Baban nasa ba zai ganshi a wannan
lokacin ba ma bare ya tambate shi.
Mahaifiyarsa ta shigo da fulas har da
farantin kayan shayi ta dire a gabansa, zata
fara hada masa ya yi sauri ya kar6e ta yana
godiya. Ta nemi guri ta zauna, shi kuma jiki
a sanyaye ya fara bude gwangwani yana
sauraron mahaifinsa da ya dora.
"Yaya me jikin?"
Ya dago da sauri ya dubi mahaifinsa
hankalinsa a tashe, amma fuskarsa ta kasa
nunawa. Ya tattare 'kululun da ya taso masa
a ma'kogwaro ya kora shi ta hanyar
hamud'ar madarar ya hadiye sannan ya ce
wa mahaifin nasa.
"Abbba ina ka san ba ta da lafiya?"
"Zancen duniya ai ba ya 6uya".
Abban ya fada cikin rashin kulawa tun daga
nan Auwal ya sha jinin jikinsa, kawai sai ya
ci gaba da hidimar gabansa. Abban ya gyara
zama ya ce.
"Wato Auwal ka san yarinyar nan sikila ce ba
ka sanar da mu ba, dan kawai ka na son
abin da zaka sanya mu 'karanta?"
Auwal ya dago cikin bugun zuciya ya dubi
mahaifinsa bakinsa na rawa ya ce.
"Abba... Mene ne 'karantar a auren sickler?"
Cikin 6acin rai Abba ya ce.
"Auren sickler ba 'karanta ba ne, kantafi ne
kawai da rayuwar 'ya'ya da ta aljihu... In da
'karantar ta fito shi ne zuwan da zamu yi mu
ce mun janye..."
Tuni har hawaye ya fara zuba a idon Auwal,
wanda ke kallon mahaifinsa garau da
alamun rashin kwanciyar hankali bare
kimtsa maganar da zuciyarsa ya kamata ta
haifa, bakinsa kuma ya furta hakan ne kuma
ya sa Innarsa ta sami sararin shiga maganar.
"Wannan d'an ka yi wauta in dai ka san
cewa yarinyar nan sickler ce, amma ka juya
wa matsalolinta baya zaka aure ta... Muna
zaune 'kalau ka kawo mana sickler dangi..."
A yanzu ya sami ga6ar abin cewa wanda
ra'ayin kansa da na zuciyarsa suka yi tarayya
yana 'kokarin tsayar da hawayen ya tare
mahaifiyarsa.
'Idan dai zan iya haihuwar da Rumasa'u, to
lallai zan iya haihuwar sickler da wata mai
lafiya wadda ba sickler ba ce..."
Shi ma mahaifinsa da yake zazzafan mutum
ne sai ya tare shi.
"Idan Allah Ya hukunto hakan na tabbatar
idan za ka haifi sickler goma da Rumaisa'u
idan wata ce sai Allah Ya ta'kaita ka haifi
hud'u..."
Auwal kawai sai ya yi shiru ya ci gaba da
shan shayin da ya fi kama da shan magani,
'kwalwarsa ta tsaya cak! Da 'kirkirar mafita
ko ta 'kofofin da duk ransa ya raya masa har
ya gama kushe masa aure da Rumasa'u tsab
ya 'karkashe batunda da haramta aurem.
Auwal dai bai tanka ba, har mahaifin nasa ya
diga aya sannan cikin rashin hayyaci ya tashi
ya fice daga falon.
GORAN DUMA
BY M.I.S.B
*****14
Tsawon daren nan ba zai iya dorar da wani
abin kirki da ya yi ko lissafinsa ya yi ba
dangane da yadda zai 6ullowa al'amarin, ya
san dai ya gurji kukan da tsananin 'kauna
da tausayin Rumasa'u ya haifa, kuma su
suka hana shi hasala komai bayan ya 'koshi
da ji a ransa duk tsanani ba zai iya rabuwa
da Rumaisa'u ba.
Sai 'karshen dare ya sami runtsawa saboda
haka bai sami sallatar asubahi ba, 'karfe
shidda dai-dai wayar Rumasa'u ta farkar da
shi.
Yana ganin sunanta kan wayar sai da
'kwalla ta taru a idonsa, ya daga yana
kokarin gyara muryarsa saboda daskarewar
bacci da kuma ta ma'ka'kin tausayinta da ya
ma'kale maasa a ma'kogwaro.
"Rumaisa'u" Muryarta tar ta ce "Duk
wadannan gaibu ne Abba, babu wanda ya
san abin da gaba zata haifa, kamar yadda ba
mu isa za6ar abin da muke so mu 'kyale
wanda tanmu yake hasashen hadari cikinsa
ba. Da dan Adam na da iko akan za6in abin
da yake so na matar da ta zarce Rumaisa
saboda abin da nake mata ya fi so, shi yasa
ban san ko wacce irin matsala ba a kanta,
amma da yake na san ba dukkan abin da
mutum ke so yake samu ba, tun bayan
umarninka na jiya na kwana ina gwajin
yadda zan iya rayuwar da babu Rumaisa'u.
Na yi ta cin karo da gazawa, har ta fara
barazanar keta min zuciya. Ban fitar da rai
zan iya din ko kuma zan kasa ba, na san a
biyu daya ce zata faru, ko in iya d'in in
wanzu bisa tsarin da ka za6a min, ko kuma
in gaza ta dalilin in bijire maka ba, wanda
babu irin haka a tarbiyyar da ka ba ni... Abba
kar ka damu da yadda ka ganni har in mutu
in Allah Ya so ba zaka had'u da abin kuka ta
silata ba..."
Yanzu hawaye ya fara cin 'karfinsa, kuma shi
ne ya tilasta shi diga aya ba don ya rasa abin
cewa ba.
Duk jikin mahaifinsa ya yi sanyi, sai kallon
Auwal yake shi ma kamar ya yi hawayen,
amma wata zuciyar na tuna masa siyasar
Auwal ta dadin baki da sadaukarwa har ka
yi masa abu ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login