Showing 87001 words to 90000 words out of 99941 words
Chapter 30 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
daga
mazan har matan da yayayensu sunata nannan da ita sai janta sukeyi da nuna mata gata ta
kuwa saki jikinta sosai duk da zuciyarta bata nutse guri daya, kaso mafi rinjaye na sinadarin
tunaninta yana ga Rasheed Wanda kullum saita Kira wayar Mom taji lfyrsa Abu daya take fada
mata jiki ana samun sauqi itakam tanason sanin wanne irin sauqi ake samu gashi Kumbo Hami
ta kasa ta tsare ta hanata wani motsi koda tasamu Baffa Garbu kakanta da mgnr tanason zuwa
Nigeria don ta gano jikin Rasheed hanata yayi gashi shima Kareem yaqi lfy an fada mata ma
Addah ta dawo masa da Zahra Amma don masifa yaqi qyaleta batasan inda yasamu number
data sake ba kusan kullum sai ya kirata da farko Yana bata tausayi idan yana fada mata halin
da yake ciki so batason yasa mata kokwanto akan qudurinta ta qudurce ko zatasha wuya zata
rayu da Baffa'am dinta shi kadai a mind dinta domin yafi kowa cancanta da ragamar zuciyarta.
Bata cikason takura ba hakan yasa sometimes tana ganin kiransa takeqin dagawa musamman
data fahimci sosai Kumbo Hami ke fushi da ita duk ranar data fahimci sunyi waya da Kareem,
Muneefah nata girmanta kwanci tashi har taci wata biyar da haihuwa lkcn tuni Juhud ta hada
iddarta hankalinta ya kwanta tayi wani matsiyacin kyau mai rikita isassun mazaje duk inda ta
juya ido akanta yake a daidai lkcn ne Kuma kawai Baffa Garbu ya shirya musu tafiya shaqatawa
qasashe biyar don sangarta harda wani bata zabi su hudu zasuyi tafiyar shi Kumbo Hami Naila
daya cikin jikokinsa sai ita Meenah da yarta Muneefah.
Yanayin yanda suka tsara tafiyar ne yasasu dole Saida suka bi ta Nigeria Kuma ma ba yini
zasuyi su tashi ba sai sun kwana biyu qusqus taji sunayi wai zasu barsu a masauki suje Katsina
su duba Rasheed daya dawo gida shekaran jiya, ai tanajin haka ta tubure musu kuka baji ba
gani dole don basusan bacin ranta suka aminta suka shirya tafiyar da ita tanata murna zataje
taganshi tare da addu'ar Allah yasa ya warke sosai tunda suka shigo gdan a mota taji gabanta
na faduwa sunayin parking ta daga kanta ta ganshi tsaye saman benen part dinsa corridor din
daya zame masa tamkar gurin shaqatawa yanajin nishadin tsayawa a wannan guri musamman
idan wani abu na damun zuciyarsa.
Suna tsayawa ta zame batare da ta jira sun fito ba ta saba Muneefah a kafadarta ta nufi hanyar
shiga part din nasa cikin saa a bude yake ta shiga ta nufi inda zai sadata da corridor din ta
haura da sauri fadi takeyi “Baffa'am wayyoh Baffa'am dina miss you too....." Tsayawa tayi a
bayansa ta dafa kafadarsa tace “ayyah dai ubana yafi na kowa alfaharina a duniya bama haka
dakai fah" juyowa yayi ya kafeta da idanunsa dake cikin glass baqi ya cije lebensa har Saida
suka fashi ya kama hannunta ya cire daga kafadarsa ya furzar da iska ya juya yabar gurin,
binsa tayi cikin muguwar kidima tana Kiran sunansa baiko juyo ba Saida ya dangana da
dakinsa
[8/21, 8:19 PM] Oum Hairan: Yana shiga tabisa dakin ya tsaya idanunsa na kanta yace “kije
kawai banson hayaniya" dubansa takeyi da yanayin rashin fahimta tace “Ya Rasheed nice fah
Meenanka" sake daure fuska yayi ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa yayi murmushinsa
na isa da indai yayishi tasan ya shiryawa rashin mutunci yace “eh na ganeki fah Juhud Meenah
Aminatuh Mom Sarki junior kinsan nasanki nasan wace ke fiye da sanin da kikayiwa kanki?
Koda yake ba abin mamaki bane canzawar mutum cikin qaramin taqi Meenah kiyiwa Allah ki
ficemin a daki kada kisa ruwa na ya hau wlh banson ganinki...."
Idanunta sosai ya ciko da hawaye ya fara tsiyaya a fili tace “meye nayi maka?" Zaburowa yayi
kamar Wanda ta bugawa wani abu yace “zanc...." Sai Kuma yayi shiru jikinsa na Bari yace “ki
fice nace da gaske ban qaunar ganinki Meenah kinci amanata kin ha'inceni kin yaudareni kin
nunamin Babu wanda kikeso samana ashe qarya kikeyi dama ce kika kasa samu lkcn da kikaga
Babu idona kika dauko zabinki kika maye gurbina dashi Abu mafi ciwo wai qanina Meenah Ina
raye ki auri Kareem Kuma ki dawo ki fadamin me nace meye zaki fadamin....."
Ya qarasa mgnr da ihu ta dago idanunta da tun kafin ya fara mgnr suke tsiyayar da hawaye tace
“wlh ba laif....." Dauketa yayi da Mari yace “idan na qara cewa ki fita kikaqi Tabbas gangar jikinki
zata riga Rana faduwa Meenah a yanda nakejin tsanarki tsaf ko zaa kasheni zan iya kasheki"
juyawa tayi jikinta a mace bata taba tunanin haka daga gareshi ba tayi tunanin kamar yanda
take a baya yafi kowa fahimtarta da bata lkc yaji damuwarta ashe yanzun ta canza zani ba haka
abin yake ba “to kodai bai gama warkewa ba?" Abinda ta tambayi kanta kenan lkcn da take tafe
kamar mahaukaciya zuciyarta na tafasa gabadaya duhu take gani a idanunta batasan inda take
jefa qafarta ba.
Qara ta saki lkcn data buga kanta jikin bishiya batare data sani ba tayi baya zata Fadi Kareem
dayaketa mata mgn tun dazun ya tareta ta fada hannunsa tafi minti biyar komai Yana juya mata
kafin duhun ya yaye ta bude idanunta ta zubasu akansa ta janye dasauri tare da gyara riqon
yarta tace “tnks" daga haka ta juya taci gaba da tafiya yabita yace “Meenah Ina gurin Aiki
akacemin kinzo nazo dominki ki tsaya Mana mu gaisa" hawayenta ta dauke ta juyo ta dubesa
kamar zatayi mgn sai yaga ta dago Muneefah ta miqa masa yasa hannu ya karbi yarinyar ya
cillata sama yanajin muguwar qaunarta na zaga ruhinsa Wanda ya tabbatar da tasamo asali ne
daga qaunar da yakewa mahaifiyarta.
Juyowar da zaiyi yaga gurin wayam Meenah har takai qofar falon gdan ya bita da sauri yana
kiranta Amma ko juyowa batayi ba ta fada dakin Mom ta zube a jikin Kumbo Hami ta rushe da
kuka tace “dama saboda irin wannan ranar nace abarni na rayu ni kadai bazan aure ba aka
kasa fahimtata yanzu ga irinta nan Ya Rasheed yaqi saurarona tuhuma yakeyi da naci
amanarsa Kumbo wlh banci amanarsa ba ki fahimtar dashi ki zai gane....." Gabadaya hankalin
Kumbo Hami ya tashi ta qufula an taba mata zuciyar cikarta daidai lkcn Kareem ya shigo suka
kalleshi Meenah ta kawar dakai ya zauna Yana share gumi yace “meye ya faru Kumbo?" Qwafa
tayi tace “yo Wagga sakarar yarinya damuwarta tana wucce ta Abdulrasheedu ne komai
Rasheed Komai Rasheed aiga irinta nan ga wulaqancin da kika jama kanki nan da kinyi
zamanki a Kanon gdan Barrister Kabir aida baisamu damar cin mutumcinki ba"
Jinjina kai Kareem yayi yace “ayi hqr Kumbo kinsan halinsa shi dama fahimtarsa ba daidai take
data mutane ba ni kaina gaba yakeyi dani a gdannan akan abinda bamu Isa mu canzashi ba
Kumbo ya zanyi da rabon Muneefah ne dake tsakanina da Meenah itanma da taqini take
kallona a matsayin maci amanar dan'uwa ya zatayi da ita wlh na tabbata inda Mai Martaba bai
hada auren nan ba ko ta wacce hanya sai Muneefah ta fita ajikina ta shiga nata Kuma saita
haifamin ita tunda haka qaddarar take a rubuce"
Shiru ta ratsa ta dogon lkc Kareem ya dago ya dubi Juhud da har yanzu take kwance jikin
Kumbo tanata matsar hawaye ya miqe yace “kiyi hqr komai zaizo qarshe Allah shine yasan
abinda ke cikin qasa a binne" daga haka ya fice a dakin dauke da Muneefah ya nufi gidansa da
ita Zahrah tana ganinsa da yarinyar ta zabura ta miqe ya dubeta ya kawar dakai itama saita
waske ya shiga kitchen ya daukowa yarinyar biscuits da yourghut ya zauna Yana bata yana
murmushi dadi yakeji a ransa rabonsa da ita tun tana jaririya gata har ta tafi shekara guda ji
yake dama ace mahaifiyarta ce a gefensa.
Share hawayen daya tsiyayo masa yayi Zahrah na kallonsa tana kada qafa takaici yana qara
kamata tace “waikai yar wace ka dauko?" Murmushi yayi yace bakisanta ba ko?" Tabe baki tayi
tace “ya zaayi nasanta tunda baa cikin ahlinmu ta fito ba" sake kallon Muneefah yayi yace
“qwarai kuwa baa cikin ahlinku take ba tunda kinada ikon canzata daga jinina Zahrah na dade
da fahimtar Ina kika dosa koma dai meye a ranki kibi a sannu domin Aisha itace ya babba a
gurina Kuma ko zaki haifi duniya bayanta zasu biyo abu na qarshe da nakeso ki sani a aurenki
ma arziqin Meenah kikeci saboda haka ki taka a sannu"
Tashi yayi ya dauki yarsa ya nufi hanyar ficewa daga gdan tayi dariya tace “iska kuwa na wahal
dame kayan kara wahalalle Meenah dai tafi qarfinka saidai kaganta ka hanga kayi sake dan
zaki ya girma me ita ya dawo son maso wani qoshin wahala"
Bai saurareta ya tsaya bata Amsa ba ya fice ya nufi wani shop yayima yarsa siyayya ya juya ya
koma gdan sarautar har sun shirya suna zaman jiran dawowarsa domin Alh Garbu yace ba
kwana zasuyi ba a ranar zasu koma Kano Meenah bataso haka ba taso ta samu cikakken lkcn
fahimtar da Baffa'am dinta gskyr lamari Amma batada wannan damar, tana kallonsa Yana
kallonta ya dawo daga yawonsa a mota sukayi sallama da Kumbo Hami da Alh Garbu itakam ko
kallo bata isheshi ba wani takaici ya cika mata zuciya abin nasa harda wulaqanci juyawa yayi
yayi tafiyarsa tabisa da kallo ta girgiza kai ta shiga motar suka tafi tana waiwayensa hankalinta
baimakai ga Kareem da yaketa daga mata hannu ba.
Suna tafe tana furzar da iska a haka suka Isa Kano goma na dare suna Isa gdan da suka sauka
ta shige daki ta kwantar da Muneefah dake bacci ta zauna zaman karatun wasiqar jaki batada
mafita ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta bacci ya gagareta sai juyi
kawai da takeyi cikin dare ta lalubi wayarta ta fara neman layinsa ta kasa jurewa Kira biyar tayi
baa dagaba ta rubuta masa gajeran saqo na ban haquri, tana qara Kira taji wayar a kashe taja
fasali ta kashe tata wayar ta zubawa Muneefah idanu tana sharar kwallah Tabbas duk abinda
yasa Rasheed daukan wannan matakin akanta ba qarami bane, da wannan tunanin bacci ya
dauketa da asuba ta tashi suka fara shirye²nsu domin tashi zuwa Dubai, Tara suka tashi itadai
badon tanajin dadin komai ba donma Naila tana dauke mata hankali da dan karen surutunta.
Kumbo Hami ta fahimci abinda yake damun jikar tata koda suka isa dinma bata wani saki jiki ba
har suka Isa masauki sukayi sallah sukaci abinci sukayi wanka kowa ya nemi makwanci sai
dare suka fice daga masaukinsu, suka shiga gari itadai Meenah yaqe kawai takeyi lkc zuwa lkc
tana gwada layin Rasheed Amma har yanzu yaqi dagawa har dole tasa ta saduda ta qyaleshi. Sai asuba suka koma gda sukayi sallar asuba suka kwanta rayuwar taci gaba da gudana a
haka baqin naci ya hana Juhud daina kiransa shikuma yaqi dagawa kamar yanda Kareem yake
nacin kiranta itama tana jizgashi idan abin ya dameta saidai ta Kira Ya'isha tasa mata kuka tace
ta tayata bawa Baffa'am dinta hqr saidai Ya'isha tayi murmushi tace “wlh Meenah baqin kishine
yake damun Ya Rasheed Amma Ni shaida ce bai daina sonki ba" da haka take dan kwantar
mata da hankali take samun nutsuwa.
Satinsu biyu suka daga zuwa Malay daga Malay sukayi India daga can sukayi Saudi sukayi
Umarah daga nan sukayi Turkey daga Istanbul suka gangaro Nigeria daga Nigeria suka zarce
Mali, watanni hudu suka kwashe a yawon nasu suna dawowa suka shiga bikin Naila da
Hameen dake abin duka na family ne yayi armashi sosai.
Mom ita da Ya'isha da Aunty Hamida duka sunzo tunda sukazo take maqale da Mom tanata
zubanta shaqwaba washegari suna gurin dinner Rasheed ya dira a qasar Basu dawo gida ba
sai wajen 12:30am suna kowa baccine akansa tana shigowa tana cewa “ni Allah Mom badon
kin takura ba bazanje wannan dinner ba gara na kwanta nayi chat....." Mgnr ce ta maqale mata
lkcn da idanunsu ya sarqe ana juna ya wani maze tunaninsa zatayi masa mgn ga mamakinsa
sai yaga taba banza ajiyarsa ta Kara wayarta a kunne tana cewa “double sorry na shiga
yanayine wayar na jakka bansa ka kiraba sai yanz...." Iyakar nan Rasheed yaji ta shige daki yaji
gabansa na mugun faduwa ya dubi su Mom da suketa faman dariya ita da yan'uwanta ya miqe
zuciyarsa na tafasa yace.
“Gobe da wuri zan wucce Ghana ba lallai mu samu haduwa ba" bai jira amsar Mom ba ya fita
ya ishe Alh Garbu da fadawansa sunata hira gda kamar kasuwa ya lura suma dabi'ar qasar
kamar basa bacci sosai da dare, daquwa Alh Garbu yayi masa yace “dan boko dan qaniyarka
shine ka shige cikin mata ga qannenka da yayyaenka da iyayenka duka bazakazo cikinsu ba"
yaqe kawai Rasheed yakeyi ya isa garesu ya gaishesu wasunsu da yawa yasansu qannen
Mom ne wasu Kuma jikokin gdanne nan aka baje sabuwar hira Nan Alh Sulaiman babban
yayan su Mom ya kaikaice yace “Alh dama tun kusan sati uku nakeson yi maka mgn wai ya
mgnr yaran nan Najeeb da Ameenah....." Tunda ya Fadi haka Rasheed ya zubansa ido duk da
baisan wacce Aminan ake nufi ba Amma yaji saukar saqon faduwar gaba.
Zubansa idanu Alh Garbu yayi Yana nazarinsa can yayi murmushi yace “to ai lamarin Aminah
ne akwai rikitarwa kaga mijinta na farko ko igiya daya bai yanke mata ba nemansa akayi aka
rasa shari'a tabata damar aure ta auri qaninsa shikuma qaddara ta rabasu da saki daya to
mijinta na farko din ya bayyana Kuma tanasonsa shima na shaida yanasonta wani dalili ne ya
hanashi magantuwa saboda haka indai sunason juna to sunfi dacewa da juna wannan dalilin
yasa nace da Najeeb ya hqr wannan abu duk na gidane dashi da Rasheed duk jikokin gdannan
ne rashin zumincinsu yasa basusan juna ba"
Tunda Alh Garbu ya fara mgnr gumi ke karyowa Rasheed baqin kishinsa ya motsa ya dago
idanun nan kamar gauta Yana Shirin yin mgn wayarsa tayi ring ya zaro ya duba aqogo daya na
dare harta gota ganin number Ya Arman yasashi tunanin akwai dai wani abu daya faru daga
wayar yayi ya Kara a kunnensa numfashi ya sauke me nauyi yace “ina Kareem din?" Huci ya
furzar yace “Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?" Sake jan numfashi yayi yace “ok zan
dawo gobe" daga haka ya kashe wayarsa.
Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun
kasheshi shida matarsa? To akanme?" Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a
hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta
qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, “Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a
tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan
ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta
ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba saidon bata
damar kasancewa dakai domin kaine zabinta, dani qaddara ta rubutawa bacewa ka auri matata
idan na dawo gdy zanyi maka badon bana kishinta ba aa saidon nasan ta cancanta ne shiyasa
ta zama matar gado cikin ahlinmu"..........
A daren nan Rasheed bai rintsa ba kwana yayi Yana tuna abubuwa da dama da suka faru
tsakaninsa da Kareem tun daga ranar farko da suka fara qullah soyayya da Meenah kawo lkcn
daya aureta ta qarfi da irin wahalar da Kareem ya rinqa Sha ta ciwon zuciya duk akanta kawo
yanzu yanayin da suke ciki da irin bibiyar da Kareem ya rinqa yi masa akan yayi hqr ya daina
gaba dashi sosai yayi kuka da baitabayin irinsa ba a duniya tabbas ya tafka kurakurai masu
wuyar gyarawa Kareem baya duniya labarinsa ya shude balle yaje ya nemi afuwarsa akan
abinda yayita qoqarin ganar dashi yaqi bashi qofa.
Da asussuba kuwa ya dokawa Mom Kira itanma yanda ya kwana haka ta kwana saboda tun
Daren itama aka fada mata abinda ke faruwa Meenah kam batasan meke faruwa ba Amma
ranar ta kasance cikin wani yanayi domin a daren waya sukeyi da Kareem Yana mata wasu
kalamai data kasa fahimtarsu can taji yace “Meenah kada ki manta wannan wlh tallahi duk
duniya nafi kowa sonki ban barki don biyayya ga umarnin Addah ba nabarki ne don nasan kedin
banine a zuciyarki ba Meenah in son samuna ne Muneefah ta rayu a qarqashin kulawarmu ni
dake nasan hakan bazata samu ba wani abu yana gaf da faruwa dani, Ina kukan rabuwa da
abubuwa biyu da nafi qauna ke Meenah da Kuma yarmu Muneefah Amma a wani sashin Ina
farin cikin kasancewar zata rayu da cancanta madadina wato Rasheed Meenah ki komawa
Rasheed don Allah don taimakon maraicin Aishatuna kinji......" Daga haka ya tsaya da mgnr taji
wata qara can taji yace “ina zuwa zan kiraki kamar Yan fashi sun shigo unguwarmu" daga
wannan tajishi shiru kalamansa sun tsayanta a rai zuciyarta ta karye tabbas lamarin Kareem
akwai taqawa da tsoron Allah baitabayin Abu don jin dadin kansa ba komai zaiyi yanayine don
mafitar Al'umma Kareem yakai masoyi a gurinta.
Miqewa tayi zumbur lkcn da taji Ya'isha ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir
raji'un Allahumma ajirni fih musibati Mom da gaske Ya Kareem sun kasheshi ya mutu shikenan
bazai qara dawowa duniya ba Muneefah ta zama marainiya....."
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta