Showing 54001 words to 57000 words out of 99941 words

Chapter 19 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1256

yasa batada wuyar bacci nandanan bacci ya dauketa sai asuba ta farka
shima tashinta yayi a waya tayi sallah ta shiga harkokin gyaran gdanta duk da akwai masu
gyarawa tafiji a ranta tayi abinta domin ta fahimci mijinta ba Maison a rinqa dafdala a sashinsa
bane.





Goma ta gama tayi karinta ta sako hijjab dinta har qas ta fito tare da kulle sashin ta nufi cikin
gdan domin gaishe da surukanta abin mamaki yau dinma duk inda tabi sai taga jama'ar gurin
sun miqe zunbur sun watse wani sanyin jiki ya kamata itan da a baya idan ta fito kowa yakeson
yaga tayi masa mgn yanzu itace wai bayin gidan ma suke gudarwa hawaye ya ciko idanunta
tayi qarfin halin shanyewa taci gaba da tafiyarta harta Isa qofar shiga bangaren matan gidan ta
murda qofar ta shiga falon tare da sallama Mom Addah Amrah sai Urwat sune kadai a falon sai
Mai Martaba dake duba jarida a gefe.
Ta nemi guri a qasa nesa da Mom cikin ladabinta da alkunya ta fara gaishe da Mai Martaba ya
amsa da sakin fuska yace “Aminatuh baiwar Allah an fito to ya nauyin jikin?" Kunyace ta kamata
yayi murmushi yace “kunyar nanan dai to madallah Allah yayi albarka" amsawa Mom tayi da
Amin suka gaisa da Mom itama cikin kulawa take amsawa ta juya ga Addah Abulle ta gaisheta
ta amsa mata Babu yabo Babu fallasa bata damu ba domin tayi alqawarin jure komai domin
mijinta ta dubi Amrah dake kwance tana latsa waya tace “sister ba mgn...." Da sauri tayi jifa da
wayar tace “wace sister taki ta ina muka hadu Allah ya kiyaye irin gidannan Babu yanlasan wlh
saidai a kwasosu a kwashe² kamar yanda aka kwaso Mana ke ak......"

Wata qara ta saki tare da dagowa ga mamakinta sai taga Kareem ne ya sake kai mata duka
Addah ta janyeta yace “na dade Ina fada miki ki rinqa saita kalamanki banason ku rinqa shigar
da kanku abinda babu ruwanku kunqi ko to waima Ina ruwanku da lamarin Aminah ne kuke
neman hana masa mata sakat a gidannan nine dai zakuce kuna tayawa jin haushi Kuma bada
ita kuke ba da ubangiji kuke domin shine yayi alqawarin bazai taba bayar da rabon wani ga
wani ba Aminatuh bata yaudareni ba tasoni tabani kulawa ta shirya rayuwarta dani qaddarar
baa kaina take ba akan Ya Rasheed take matarsa ce rabonsa ce da iya wuya saita isa gareshi
ni na yarda waman qaddarallahu haqqan qadarihi Babu wani ruwa dazai kwaranye zanen
qaddararmu ta son Abu daya nida dan uwana Kuma dama duk inda mutum biyu sukayi tarayya
akan son Abu day to dolene daya yayi nasara daya ya fadi"




Yana fadin haka ya juya ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa har yakai bakin qofar fita ya tsaya
ya juyo idanunsa taf da hawaye yace “Meenah!" Yanda ya Kira sunanta hatta Mai Martaba
Saida ya dago idanunsa suna tsiyayar da hawaye yace “kada komai ya dameki bakiyimin komai
ba qaddarar so ce a haka har gaban abada ke nakeso Amma bazan taba goyon bayan ki
bijirewa mijinki ba domin nasan kema kinasona Meenah (Fa Inna maal usri yusra) ba zance na
bane zancen Allah ne kiji haka a ranki"
Da sauri ya fice fit daga falon yabarsu zaune da sanyin jiki itakam Meenah gabadaya
kalamansa tsinka mata jijiyoyin jikinta sukayi ta kasa koda miqa wuyanta miqewa Amrah tayi
tana taunar dabino tace “aikin banza Harbin daurarre dama tunda an cinye maka zuciya Ina
zakaga laifinta baqar munafuka wlh bantaba tsanarta irin wannan lkcn ba" daquwa Mai Martaba
ya watsa mata yace “dake da tsanar na hada na dakaku a turmi naci kan uwarku ja'ira me qirar
yar tsana" sumsum tabar gurin tana haarar Meenah Mom ce tace da ita Aminatuh tashi ki shiga
ciki ki kwanta naga kamar sanyi kikeji ko?" Miqewa tayi ta nufi sashin Mom ta bude ta shiga ta
ishe Ya'isha na guga ta karba tana tayata suna hirarsu itadai qarfin hali kawai takeyi da taji ma
bazata iyaba sake mata gugarta tayi ta koma ta kwanta nandanan zazzabi ya rufeta wasa
kamar wasa Abu ya rinqa qarfi hardai a qarshe Saida aka Kira likita ya daura mata ruwa da
magunguna.




Kwananta biyu tanajin jiki sannan taji dama sabon laulayi yasata a gaba batada aiki sai cin gurji
shi dayane abincinta aikuwa nandanan ta zuqe kowa yazo ya dubata a gidan Amma Banda
Aliya da Nana matan yayyen mijinta itakam Addah cewa tayi haqqin dantane da tun ranar daya
zabgawa Amrah Mari yake kwance ciwon zuciyarsa ya tashi yanata Aman jini duk ya fice daga
hayyaci sunan matar yayan nasa kawai yake kira a qarshe dai dole Mai Martaba ya daukeshi
yabar qasar dashi.
Itakam tama manta da babinsa ta kanta takeyi da lfyrta gabadaya ta zuqe ta rame saboda
tsangwamar da take fuskanta a gidan batada wani sauqi a gidan saina bangaren surukarta da

kullum take rarrashinta da bata baki shikam Rasheed baisan meye akeyi ba kasancewar daga
Dalta Enugu aka turasa wayarsa ma ba samuwa takeyi sosai ba a haka dai har bikinsu Ya'isha
ya qaraso aka shiga hidimar biki ka'in da na'in dake bikin yazo mata a wani yanayi batama fiye
shiga mutane ba warin jikinsu amai yake sanyata.




Ana jibi daurin auren yan uwan Mom sukazo daga Mali ranar Juhud yini tayi a daka Babu lau
tana kwance taji an shigo part din batada qarfin miqewa ma shiyasa ta sake bin katifa ta lafe ya
bude dakin ya shigo cikin dokin ganinta da shauqi ya tsaya jikin qofar dakin yace “Uhmmm
qaddarar so! Kenake so!! So habo ya zabaran yayi naso!!! Yadda nakeyin nazarin so habone!!
Ni inajinsa arai tuntubene!!! Dan Adam shikuwa Mai kuskurene!!! Afuwa ki agaran nayi zaune!!!
Ban iyawa da rabon qaddarar so!!!!!
Wani tsalle tayi ta saki ihun murna ta rungumeshi tana kissing dinsa ta ko Ina shima kissing
dinta yakeyi suka zube a gurin ta hade bakinsu cike da shauqin qaunarsa sun jima a haka ta
janye ta shafa kansa zuwa qirjinsa tace “miss ur My life...." Miqewa tayi da sauri hawaye suka
zubo mata ya miqe ya riqota yasa harshensa ya lashe hawayen yace “ina tsananin buqatar
matata wlh nasha wahala a wata ukun bantaba gwadawa ba......" Hannun takai ta shafo
mararsa zuwa qasa ta dago tayi masa murmushi tace “burina kenan Abba Aanam ya kasance
me kiyaye kansa hakan shine farin cikina" harararta yayi ya riqe kunnenta yace “bakijin tausayin
babynki?" Tasan meye yake nufi ta riqe hannunsa tace “asalin tausayi ma kuwa duk da ajiyarta
ya hanani sakat Amma zan bata kulawa bakin gwargwado da haka ta samu ya tashi ta hadamai
ruwan wanka yaqi Wai saidai tayi masa batason qamshin sabulum hakanan ta daure ta tayashi
suna gamawa ya kulle dakin ya janyota jikinsa ya fara lalubeta ta sakensa jiki sosai sukayi
qara'in watanni sun gurji juna kuwa son ransu ita kanta ta yarda sunyi missing junansu bayan
komai ya nutsa ne ya dubeta itama shi take kallo ya lumshe ido yace “da kewarki da qaunarki
zan mutu Meenah kowanne motsina kene na yarda so Yana canza mutum wlh tunda na tafi naji
bana sha'awar kowacce mace bayan ke ko nayi qoqarin nema idan na tuna dake sai naji na
qoshi nake nakeson ci.........




*JH013 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare
na yafe miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba
94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*

*Oum Hairan*
[8/1, 8:43 PM] Oum Hairan: *0025* Sake shigewa tayi jikinsa tana sunsunar qamshin turarensa
cikin wata murya me kashe jiki tace “inasonka My world" matseta yayi Yana shafa cikinta na
watanni hudu yace “inasonki fiye da yanda nakeson komai a duniyata ki zama amanata tawa Ni
kadai kinji" murmushi tayi masa ya sake mirginawa kanta ta lumshe ido ya dora bakinsa saman
idanun nata Yana lasar eyeslashers dinta tare da matse nononta a qirjinsa yana matsata yanda
yaga dama wannan Rana an kurbi zumar qauna yanda ya kamata.
Sunaji ana buga musu qofar sukayi likimo abinsu fir ya hanata fita wai yau lkcnsa ne bazaa
yimasa ojoro ba hatta abinci Saida dare ya fita yaje ya siyo musu ya dawo suka qara bajewa
suna tsinkar furensu da dare aka kwanta akaci gaba da bawa qauna haqqinta tun Juhud na
jurewa har ta fara gajiyawa abinka dame yaron ciki shikuma dadinta ya hanashi qyaleta, da safe
Mom da kanta tayo tattaki tazo barayin nasu domin babu wanda yasan ya dawo sai Muntaz
daya daukoshi a airport.
Ta jima tana bugu daqyar ya saki Juhud daya maqale ya fito parlourn yana tambayar waye? Jin
muryarsa yasa Mom cewa ”haba nidai naji shirun tayi yawa Rasheedu ashe ka dawo?" Bude
mata qofar yayi ya kwantar da kansa a kafadarta wannan tsohuwar al'adarsu ce yace “wlh tun
jiya da yamma na dawo" murmushi tayi tace “babu Kuma ko nemanmu saima hanamin yata
fitowa anata hada² a cikin gida tun jiya wayarta a kashe" sosa qeyarsa yayi ya zauna lkcn da
Juhud din take fitowa ganin mom yasa taji kamar ta nutse ta rusuna a kunyace ta gaisheta tayi
dariya tace “yar jaka ba ko sisi waike dadi miji mijinki ya dawo kin manta dani ko zai tafi yabarni
dake ai muga qaryar rashin kunya"




Dariya sukayi dukkansu Ya'isha da Amrah suka shigo da Khadija da Zahrah matar da zaa
aurawa Kareem Ya'isha ce kawai ta kalli Juhud tace “ai dama Saida na kawo haka a Raina
nace duk yanda akayi Babban ogane ya dawo kika manta damu" murmushi tayi tace “yo mi
zanyi muku duniyata ta dawo gareni" dukkansu kallonta sukayi ta matsa jikinsa lkcn da Mom
take fita tana cewa “aifa baki ya bude da alamun shima unborn din babansa yake buqata naga
yau jiki ya wartsake ya samu abinda yakeso"
Gaisheshi sukayi ya Amsa hankalinsa nakan Meenah ya miqa mata hannu ta kama ya dagota
jikinsa ya zaunar da ita suka kalli juna Ya'isha tace “baba Aminu ne yace mu kawo maka Aunty
Khadija ku gaisa Wai kun dade baku hadu ba" shafa qirjinsa yayi yace “wlh fah tun rasuwar
mijinki halan kin gama idda ne?" Wani farr tayi da idanu tace “kayyy soja ai tun lkcn mutuwar
Aunty Zulaihat ma nayi iddah" tabe baki yayi yace “ok to ai saiki fidda miji kiyi aure kada kice
zakici gaba da shashancin da kika rinqayi a baya yaja miki aure da qananun shekaru" murmushi

tayi tace “ai nama fitar Yaya Soja" bai bawa hirar muhimmaci ba ya kalli Zahrah yace “wannan
itace dayar amaryan ance amaren ukune halan ya jikin Kareem din hope Yana samun sauqi?"
Tabe baki Amrah tayi tana wani yatsina tace “to bama dolenshi ya warke ba wannan auren
gayya da zaayi masa da yar asali me cikakkiyar nasaba" kallonta yayi batare daya fahimci meye
takeso tace ba ya miqe yace “Life help me breakfast kin yasheni jiya fah" Saida taso ta nutse
dan kunyar qannen mijin nata hakana ta miqe Khadija na harararta ta nufi kitchen cikin yan
mintuna ta sama masa abinda zaici ta dauka ta nufi dakinsa ta aje masa zata fita ya riqota yace
saurin na meyene?"




Zama tayi tana hada masa tea din tana cewa “mom tace idan na gama naje mu gaisa da baqin
Mali sunzo tun jiya sunata buga sashin nan ka Hana a budensu" yasan da hakan shiyasa baice
komai ba ya rinqa janta da hira Saida ya gama yayi wanka sannan suka fito tare sunsha kyau
na ban mamaki suna fitowa da ango Kareem suka fara kicibis sukayi musabaha ya tambayesa
aiki shikuma ya tambayesa jiki itadai gaba tayi saboda zuwa lkcn wani haushin Kareem din
takeji yanda yake nacin kallonta.
Ta rigashi shiga tana shiga parlourn Hajiya Bilki da su Nana da sauran mutanen suka fara
watsewa ta tsaya sake da baki kawai sai tajiyo a bayanta wata mata na cewa “ai wannan kina
ganinta kyaun dan maciji baqar annoba kenan yanzu kina cika wargi zaki tsinci kanki a Ramin
kabari ta tsotse bargo ta lashe kurwa" Juyawa tayi ta zubawa me mgnr ido hawaye wani nabin wani shiyasa jiya taqi fitowa saboda
gudun abinda zatayi gamo dashi a wannan taron bikin, ji tayi an saqalo qugunta taja ajiyar
zuciya tare da share hawayenta da gefen mayafinta ya zagayo gabanta yace “dame Kuma kika
gamu daga fitowarki" murmushi tayi tayi gaba ya riqo hannunta yace “wlh bazaki shigaba saikin
fadamin uban waye ya tabaki?" Tana Shirin mgn Ya'isha tace “wato Ya Rasheed yau zaayi
kutmar uba a gidannan....." Fuuuuuu tayi gaba tana zuwa ta dauke Hajiya Bilki da Mari ta kama
qunduma mata ashar abinka da bakatsina yau jini ya motsa bala'i takeyi tana dara nandanan
gurin ya kacame taron biki ya koma taron fada shidai Rasheed baisan meye yake faruwa ba
Saida yaji tana cewa “aikin banza aikin wofi har wasu kune zaku dubi Meenah ku rinqa jifanta
da miyagun kalamai dama ai na dade Ina jiran damar cin bura uban kowannen shege a
gdannan idan kuna taqamar ance muku itan mayya ce to ai gara ita ansan wacece ita ku waye
yasan asalinku yayan bayi kawai Wanda tsiya da munafurci ta Haifa ta goya ta shayar Bilki kibi
a sannu halwa ce dake gaba da baya Kuma mata ba maza ba aure Big Cele yace bayaso bazai
auro irin masifa irin jaraba ba wlh dadai auren halwarki gara auren mayyah so million indai
msita irinta Meenah ce Kuma Meenah ta zame muku ciwon ido a gdannan kowanne dan iska
saidai yaganta yabarta idan da meja Kuma yaja shima ya wullah barzahu kamar yanda Zulaihat
data dage saita shiga tsakanin rabo ta fece, yan iskan banza munafukan wofi"

Tunda yaji dalilin rikicin jikinsa ke tsuma ran maza ya baci idanunsa suka kada sukayi jawur ya
dubi Juhud data durqushe a qasa taketa aikin kuka me cin zuciya ya juya ya dubi mutanen
kowa jikinsa ya hau karkari baice komai ba baiwa kowa mgn ba ya figi hannunta da qarfi suka
fice daga falon gurin Mom din da baajeba kenan ya mayar da ita sashinsu ya kulle ya zauna
yanata huci ya miqe ya zauna yafi sau ashirin sannan Kiran Mai Martaba ya shigo yayi jifa da
wayar ta tarwatse ya tashi ya shiga dakinsa batasan me yayi ba ya fito dauke da jakankuna
manya guda biyu ya fice ya jefa a mota daidai lkcn da yake Sanya kayan a mota Mai Martaba
ya iso gurin yace “ya subhanallah meye Kuma hakan Ina zaka?" Juyowa yayi idanunsa sun
kada sunyi jawur ya dubeshi ya kawar dakai Alh Aminu ne ya matso shima lkcn Rasheed din ya
koma cikin gdan ya figo hannun Meenah ko dankwali Babu akanta Mai Martaba daya fahimci
barin gidan yake niyyar yi yace “wai ba mgn nakeyi maka bane" a fusace ya juyo yace “banaji
Mai Martaba banji abinda kaceba ka kauce kabani guri yau kam ko baku koreni ba na gama
zaman gdan sarautar nan akan matata zan iya hqr da komai....."
Muryarsa ce ta sarqe ya jefata a mota ya kulle har yanzu kuka takeyi yama kasa rarrashinta ya
sake kallon Alh Aminu ya nunasa da yatsa yace “ka sanar da munafukar matarka ni
Abdulrasheed nafi qarfin yayanta a aure kun bani Zulaihat banaso na karba Allah ya dubeni ya
kasheta kun bani Hidaya na sakar muku kayarku shine yanzu zaku liqamin bazawara kwancen
wasu saboda kun Mai dani jani talau waima ni kadaine da namiji ne a gidannan Ina Salman Ina
Arman Ina Kareem Ina Muntaz hatta Urwat kukayiwa aure zama zaiyi da matarsa saini akanme
zaku sanyawa rayuwata idanu ne banaso na fada muku banaso wlh tallahi zanci mutumcin duk
ubanda ya qara tunkarata da mgnr aure auren banza auren wofi da har zaku sanyawa matata
tsura akansa aiba ita ta hanani ba nine naga batada tamka bare mahadi, Abu na qarshe ka
fadawa Bilki ta kiyayi dawowata gdannan Kuma ta shirya Amsa Kira kotu saita fadamin uban wa
matata ta kashe da take fadawa duniya cewa in mutum ya cika rabar Meenah saidai yajishi a
Ramin kabari?....."




Sosai Mai Martaba ya girgiza da yanayin Rasheed din yasan tabbas yau yakai qarshe akwai
gagarumar matsala idan yabarshi yabar gidan dama Meenah ce zatake kawoshi tunda shi
dama asalinsa bayada ra'ayin zaman gdan sarautar to ya dauke abarsa meye Kuma zaisa
suganshi? Mai martaba na Shirin mgn Mom ta iso gurin ita da wasu mata su uku dole tasashi
yin shiru ta kama hannun Rasheed tajashi gefe sun jima suna bugawa kafin ta shawo kan
kayanta Yana kuka kamar wani yaron goye daqyar ta lallabashi ya yarda zaibar Meenah a gidan
sarautar Amma da angama biki da ita zai tafi.
Zuwa tayi ta fito da ita a mota ta janye mata sumar data rufe mata fuska tana ganin Mom din ta
fada jikinta ta sake rushewa da kuka itama hawaye ta share tana tausayawa rayuwar Meenah
Babu uwa Babu uba babu shaqiqin dan'uwan da zata zanta dashi taji dadi ga rayuwar taqi mata
dadi wata murya taji ta bayansu tace “kiyi hqr Aminatuh komai yayi tsanani sauqi na zuwa
hakanan Allah yake jarabta bayinsa zababbu domin ya gwada imaninsu ba sonki ne bayayi ba
qaunace ta kawo miki hakan bantaba ganin Wanda akayiwa irin wannan qazafin ya qare rayuwa

a wulaqance ba ko baizama wani ba zai samu yardar Allah"
Juyawa tayi ta zubawa matar idanu gabanta ya yanke yabada wani rass ta janye jikin Mom da
sauri tana qara kallon matar tare da langwabar dakai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login