Showing 81001 words to 84000 words out of 99941 words
Chapter 28 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
da hankalinta ga Mom
sukaci gaba da hirarsu tanata dariya abinta shirmen da Rasheed yake buga musu ko Sarki
bazaiyi ba suna haka Fadila ta fito ta debesu ta watsar Meenah tayi murmushi tace “Allah
Sarki wannan fah Mom?" Girgiza kai tayi tace “au Fadila auren ne yaqi dadi mijin neman mata
har ksn gadonsu na sunnah shine tayo yaji ya aiko mata da takarda saki daya" dafe qirji tayi
tace “ya salam Abin tausayi Allah ya daidaitasu" murmushi Mom tayi tace “kayyah dai itama
Amrah jiya ta koma aure mijin ya qara shine zatayi masa haukanta ya korota uwar mijin tace ita
dama batason wannan auren daidai ya nace ne daqyar dai aka sasanta ta koma kayy Meenah
munga jarabawa dan ritsin nan " jinjina kai tayi tace Allah yasa ta zamo kaffara amsawa tayi da
Amin sunata hirarsu ta yaushe gamo Kareem ya shigo suka gaisa da Mom ya dubi Juhud yace
“bansan kin fito ba fah Saida na leqa dakinki naga bakinan" murmushi tayi tace “nazo mu gaisa
dasu Mom ne"
Miqewa yayi ya nufi part din uwarsa yace “ok ku gaisa sosai Amma ki nemamin abinci yau
girkinki nakeson ci....." Rasheed dake tura motar wasan yara shida Sarki ya dago yace “lahhh
zaka sammin?" Tsayawa Kareem yayi ya juyo ya dubeshi da tausayawa yace “in kanaso ma
kullum ka rinqa zuwa kana karba Aminah ta iya girki sosai" tsalle yayi ya dafesa yace “itama
sunanta Meenah nima tawa Meenan ta iya girki nifa tunda Meenah ta mutu ban qara cin abinci
me dadin nata ba"
Tsayawa yayi kamar zai juyo sai Kuma yasakai ya shige ciki sama² suka rinqa jiyo hargowar
Addah Abulle basajin dai abinda suke cewa Meenah ta miqe tace “bari na koma Mom duhun
magrib ya fara shiga saida safe" ta juya ga Rasheed daya zuba mata ido tace “Baffa'am Saida
safe" daga mata hannu yayi yace “zanzo na karbi abincin naki ai" murmushi tayi ta juya ta fice
ta nufi sashinta taji an bangajeta taja baya da sauri tare da cewa A'uzubillahi....." Tana duban
Wanda ya bangajeta din Fadila ce qanwar mijinta tayi murmushi kawai ta juya taci gaba da
tafiyarta a bayanta taji tana cewa “gayyar na ayyah gayyar tsiya an dawo zaaci gaba da dorawa
uwarmu ciwon zuciya jarababbiya qalatacciya da wani shegen cikinki a gaba irin masifa irin
maita......"
Kalamin sun daketa ta cije lebe tare da tsayawa batare data juyo ba tace “hakane saidai kin
manta abu daya bani na liqe mawa dan'uwanku ma shine qalatacce jarababben daya liqemin
wlh da zaku bashi shawarar ya rabu dani ma ya dauka da dadi nikaji domin zan yar da qwallon
mangwaro na huta da qudaje"
Tana fadin haka ta shige tabar Fadila sake da baki lallai yarinyar ta riqa wato sune qudaje
Kareem ne mangwaro tab yau da tashin hankali a gdannan, fuuuu ta shige ciki ta nufi sashin
uwar tasu tana shiga ta fara karanta mata qarya da gaskiya aikuwa ta hau ta zauna ta dauki
waya ta Kira Dada Hanne ta zayyane mata abinda ke faruwa Dada Hanne tace “ai Ni wannan
jaraba na rasa dame tayi kama yarinya ta zamewa mutane qarfen qafa an kasa kwanceta a yar
shima Mahfuz din kwanaki kamar abin arziqi aikin da mukayi ya fara cinsa yanzu Kuma yaqi
kullum abubuwa lalacewa sukeyi"
Takaici ya cika zuciyar Addah Abulle tace “ni takaicina ma cikin nan da yake jikinta ashe bai
fadaman lissafin daidai ba boyemin yayi yanzu kawai Ina ganinta naganta da tsohon ciki
haihuwa kusa" wata uwar ashar Dada Hanne ta qunduma tace “au ke yanzu kina zaune sakarai
kika bari tayi ciki kema zaa jorner miki tsiyar?" Da muryar takaici tace “to ya zanyi kefa kika sani
na rinqa rabar da kudi tsakanin gurin malamanki dana Hajiya Bilki nidai banga wata nasara ba
saita dawowa ta gdannan"
Qwafa Dada Hanne tayi tace “ai shegiyar gantalalliyar yarinyar ce masifar taurin kaine da ita
bansan wanne irin shiri ne a jikinta ba Amma bari intasan wata batasan wata ba" sun jima suna
saqarsu a mugun zare sannan sukayi sallama da shirinsu na cimma matsaya.
Meenah kam tana shiga part dinta idanunta ya sauka qasan tiles din taga wani garin magani
duk an barbadar dashi kiyayewar Allah ce kawai tasa taga maganin saboda shima arsh ne kalar
tiles din, taja baya da sauri tana a'uziyya a fili ta fara dube dube bataga Wanda zata Kira ba ta
koma gefe ta tsaya tsam jikinta na tsuma tsoro ya cikata tana nan tsaye Allah ya jefo mata
Kareem taja ajiyar zuciya, qarasowa yayi da sauri yace “meye kikeyi anan Kuma?" Dubansa
tayi jikinta na tsuma tace “naje zan shiga naga wannan abun" idanunsa ya zuba a tiles din ya na
kallon abin ya girgiza kai yace “ki shigo da Bismillah babu abinda zai sameki sai abinda Allah ya
hukunta kiji haka aranki"..........
Kama hannunta yayi suka shiga cikin gdan ya janyota jikinsa yana sunsunar qamshin gashinta
yace “kin wahalar da zuciyata yau" dagowa tayi ta kalleshi yayi mata murmushi yace “kiyi komai
ba komai ya lfyr babyna" ajiyar zuciya tayi tace “nima nasani" dariya yayi yace “kuma kina tare
dashi?" Kautar da kanta tayi sukaji ana buga qofar suka kalli qofar tare ji sukayi anyi sallama
gabanta ya Fadi ta janye yace “ina zaki?" Kallonsa tayi tace “Baffa'am ne ke buga qofar nan
fah...." Janyota yayi yace “to me zaki bashi?" Tsayawa tayi tayi sororo sai Kuma ta juya da sauri
tace “zan bashi hqr ne yace yau bazaici abincin kowa ba sai nawa"
Zama yayi ta bude qofar tana budewa ya shigo yace “ina abincin nawa?" Yana mgnr yana kalle
kalle ta kalli Kareem tace “yanzu zan girka maka me kakeson ci?" Kallon kitchen din yayi yace
“nima fah na iya girki muje na tayaki nawa ma sai yafi naki dadi" zaro ido tayi tayi dariya tace
“habadai aiko Ya Kareem bazan sa girki ba balle kai da girmanka da matsayinka" nuna mata
hanya yayi yace “ok aje abani abincina naci na kwanta sallar ma yau bazanyi ba" kitchen din ta
nufa Kareem ya tashi yabi bayanta taliya ta dauka ta girkata fara ta tace ta dauko kayan miya
ta soya ta zuba kifinta bushasshe data gyara ta dauki hantarta ta zuba ta soya sannan ta zuba
kayan dandano ta juye taliyarta ta cakuda a cikin man nan da kayan miya ta barsu suka dahu
daidai buqatarta ta sauke.
Bata tsaya hada lemo ba ta dauko na kwali ta dora akai ta zuba mawa Baffa'am dinta nasa
sannan ta zuba nasu ta fita yana zaune har yanzu Yana karkada qafa ta ajiye masa a gabansa
ya dauka ya miqe yace “yawwa na gde" ficewa yayi ta girgiza kai ta dauko nasu ta jera a
dinning ta nufi dakinta tayi wanka ta fito ba kwalliya take ba ita dama doguwar riga kawai tasa ta
fito ta qwanqwasa dakin na Kareem tajishi yana karatun qur'ani ta bude ta shiga, Saida yakai
simuni sannan ya juyo ya dubeta yaja ajiyar zuciya tace “barka da hutawa" jinjina mata kai yayi
tace “na kammala" murmushi yayi yace “kin bawa Ya Rasheed din?" Dagansa kai tayi yace “ya
tafi?" Ta qara daga masa kai yace “ok sannu da qoqari"
Tashi yayi suka fita suka zauna a dinning din ta hada masa abincin ta miqa masa itama ta zuba
yaja yayi Bismillah ya faraci itakam juya cokalin kawai takeyi gabadaya zuciyarta kwanakin nan
a karye take akan lamarin rayuwarta ta dago tace “Ya Kareem" dagowa yayi ya zubanta ido tayi
qasa da nata yace “fadi Mana" zuciya taja tace “ina tunanin wani abu fah zuciyata tana saqamin
abubuwa da yawa nikam don Allah Ina neman alfarmar kabani damar kula da Baffa'am dina
kamar yanda ya kula dani a baya" zubanta idanunsa yayi da suka fara canza kala ya aje cokalin
hannunsa ya furzar da iska ya miqe ya juya zaibar gurin, yakai bakin qofar dakinsa tace “itace
alfarma ta farko dana fara nema a gurinka idan kaqi yimin ita to tabbas zanci gaba da ji a Raina
na rasa damata na rasa yancina tun shekara goma baya lkcn da Ina matsayin ya a gurin
Baffa'am dina da shekaru shidda shudaddu da na kasance mata a gurinsa Kareem meye kake
zargi don nace zan kula da Abu mafi muhimmaci a sashina?"..............
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/13, 9:07 PM] Oum Hairan: Juyowa yayi ya zubanta idanunsa da suka jima da canza launi
yanayi mata kallon sakarya ya sake juyawa zai shige ciki tace “idan kaqi aminta hakan ba Yana
nufin zan barshi ya wofinta bane gareni shine qarshen....." Daganta hannu yayi yace “ya isa
dalla kada ki tarwatsamin zuciya da wadannan shashashun kalaman naki da bazasu taba
yuwuwa ba ke a qaramar qwaqwalwarki kin taba ganin inda wani sashi ya kula da sashi a halin
wancan sashin ya kasance abin farautar dayan to ki nutsu ki dawo hayyacinki wannan shirmen
bazaa yisa Dani ba Ni nasan kaina Kuma nasan ciwon iyalina"
Zabga masa harara tayi tamai da hankalinta kan flat din gabanta zuciyarta na angizota ta fada
masa ba sugar shima wata na hanata tana cewa da ita tayi hqr ta qyaleshi hakanan ta miqe a
gajiye ta shige dakinta tayi sallar magrib ta zauna tana addu'arta har Isha tayi ta aikata sannan
ta miqe tayi Shirin kwanciya tayi hayewarta gado taja bargo tana me miqa lamuranta ga Allah
baccin me dadi kuwa ya dauketa Wanda ta jima bata samu irinsa ba cikin baccin taji an bude
qofar an shigo tanaji ya mayar da qofar ya rufe yazo ya kwanta kusa da ita ya janyota jikinsa ta
janye tace “ko likita yace ake dagamin qafa don Allah ya Kareem ka rabu dani..." Rufe mata
baki yayi da qirjinsa yaci gaba da luguiguitata bataso dole don Babu yacce zatayi dashi ta hqr ta
gyaleshi itakam zuwa yanzun bajin dadin komi takeyi ba saboda cikinta ya tsufa sosai.
Da safe data tashi ta gama abinda takeyi tayi wanka ta nufi sashin su Mom a lilo ta tarar da
Rasheed kamar wani cikakken mutum yaci wanka harda su agogo su glass yana duba wata
magazine tayi masa sallama ya dago ya zubanta idanunsa Yana wani lumshesu tace “barka da
sfy Baffa'am" daga mata hannu yayi tayi murmushi tace “dama kacemin duk ranar death date
din Meenah kana azumin mgn so yau ma azumin mgnr kakeyi kenan" zare glass dinsa yayi
yace “kuma ma tace na gaisheki tace tanasonki kadan" murmushi tayi tace “amma kam na gde
duk kishin Meenah da kake bani lbr harta soni nikam inada saa" bai kulata ba yaci gaba da
karatunsa ta juya tace “shikenan tunda kaqi kulani na daina qawancen" tafiya tayi batasan ya
biyota ba tana shiga ta zauna sun fara gaisawa da Mom kenan ya shigo Yana sharar hawaye
kamar yaro qarami Mom tace “subhana meye yayi zafi?" Nuna Meenah yayi yace “ba itace tace
ta daina qawancen ba" murmushi Mom tayi tace “to Banda abinka Rasheed qawance da matar
aure ta Ina zai yuwu?"
Saurin katseta Juhud tayi da cewa “tsokanarsa ma nakeyi ni ban daina qawancen ba" tsalle yayi
zai rungumeta Mom tayi saurin tareshi tace “kayy kada ka illatata Mana bakaga yanda take
bane" guri ya samu ya zauna Meenah ta miqe ta nufi dakin Addah Abulle ta tura qofar ta shiga
da sallama Addah nakan sallaya da alama walaha ta idar ta samu guri ta zauna tace “ina kwana
Addah" dibanta tayi ta watsar sukayi shiru na tsayin lkc kafin tace “EDD dinki yaushe ne?" Shiru
tayi tana tunani can tace “17 January" qwafa tayi tace “nasa malam Musa da yake yima yaran
gdannan rubutu ya rinqa yo miki qila ki samu sauqin naqudar"
Gabanta ne ya fadi hakana taji zuciyarta batayi na'am ba a fili Kuma sai tayi murmushi tace “na
gde Allah ya dada girma" daga haka sukaci gaba da shiru har Fadila tazo ta ishesu a haka ta
kallesu ta watsar itakam aikin da Addah ta bata batajin zata iya da fari ma ta yaya zata shiga
jikin Meenah bayan tun farko basa jituwa balle har tayi nasarar bata gubar da zatasha ta kashe
dan dake cikinta? Wannan tunanin ne ya Hana zuciyar Fadila sakat har Juhud ta miqe tana
cewa dasu sai anjima dukka suka bita da kallo kowa da saqarsa a zucci.
Sashin Mom ta koma ta zauna tayi tagumi tana tunanin wannan al'amari Mom ce ta fahimci da
matsala tace mata “yadai Aminatuh?" Dagowa tayi tace “mom Addah ce tace wai kullum zata
rinqa karbar rubutu gurin Malam Musa tana kawomin inasha" da sauri Mom ta kalleta tace “akan
me?" Sunkuyar da kanta tayi tace “wai zan samu sauqin naquda" shiru Mom tayi can tace “miqon
wayar nan" miqa mata tayi ta Kira lambar Malam Musa bugu biyu ya daga suka gaisa tace
masa “Hajiya Abu tayi maka mgnr rubutun naquda ne?" Shiru yayi can yace “gsky ban tuna ba
Ina tunanin ta sha'afene?" Murmushi Mom tayi tace “shikenan Meenah ta ce takeda ciki wata
takwas ka fara yo mata rubutun kana kawomin" gdy yayi sukayi sallama ta kalli Meenah tace “to
kinji dai sai kiyi takatsantsan koda wasa kada ki yarda su baki kisha wadannan mutanen babu
Allah a ransu.
Jinjina kai tayi sukayi sallama ta tafi sashinta ta kwantaTunaninta Yana bata to da me Addah
Abulle ta shiryawa cikinta da Mom ta ganota?" Tabe baki tayi ta juya baya suna chat da Ya'isha
taji an turo qofar da sallama ta tashi ta zauna tare da amsawa Amrah ce ta shigo tayi mata
murmushi itakam tsayawa tayi sororo tana kallonta ta nemi guri ta zauna tare da cewa Aunty
Meenah Ina yini" fuzgo numfashi tayi tare sauke ajiyar zuciya tanajin abin wani bambarakwai
wai namiji da suna Fatsum bata gama wannan tunanin ba taji Amrah tace.
“Abubuwa da dama sun faru da suka sanyani nadama tabbas ita gsky duk inda take sunanta
gaskiya lkcn da labari ya isheni cewa kedin yar yayar Mom ce jikina yayi mugun sanyi kunya ta
lullubeni a lkcn da Mom ta dawo take sanar da Mai Martaba cewar kece akwai yayarta data
dade tana nema a 9ja tabi rugage ds dama domin gano inda zata sameta hakan ya faskara ta
tabbatar bayan dogon bincike d ruwan da akakai Rana baffaninki da sukazo suka sanar damu
kedin Mayyace sun kwatanta mata inda zata same kakanki harma da bata tsoffin hotunan Kati
guda biyu na kakarki wacce ta haifi mahaifinki Aminatuh wadda kikaci sunanta da Kuma na
mahaifiyarki, a jikin wannan hoton ne ta fara fuskntar wani abu"
Shiru Amrah tayi kana ta dago ta kama hannun Meenah tace “ganin kamanni da yanayi na
jininta jikin wadannan hotuna yasata bin duk wata hanya ta roqi alfarmar wadannan baudaddun
Fulani su rakata inda zata samo miki danginki ke Saida ta hada musu da qaryar cewa kin cinye
mata yayanta biyu ne jin ba abin arziqine zai kaita ba yasasu yarjemata Amma da sharadin zata
biyasu ladan bata lkc hakan kuwa akayi suka dunguma ta biya musu kudin jirgi sai Senegal ga
mamakin Mom sai taga sun nufi gidan sarkin birnin da suka sauka Wanda yake kakane a
gurinta shine ya haifi mahaifinta itadai bata tofa ba har suka isa ciki sunata karbar gaisuwa suka
Isa sashin kakarta wadda itace uwargida a gidan ta tsufa sosai tana ganinta tace “yar qaniya
ashe kina tunawa da mutane" nandanan labarin isowarta ya cika gdan ta sallami Manga ya tafi
masauki bayan anci ansha an huta komai ya lafa mom ta fito da hotunan nan ta miqawa Attajiri
Dodda ya karba Yana ganin dayan ya tashi zaune yace “Aminatuh Aishatu Ina kika samo hoton
babarki Aminatuh?" Hawaye ne ya zubo masa yace “Aminatuh ta mutu tun baa haifeku ba
dama su biyu ns Haifa daga mahaifinki Garbu sai Aminatuh naso riqe dan Aminatuh wato
Haruna Amma Ina sun hanani banason zumunci ya mutu na sake Basu auren Aishatu yayarki
nidai tun daga auren nan ban sake sanin labarinta ba sunbar inda nasansu sun hanata
nemanmu duk da hakan shi Haro yakan kawo mamu ziyara daga baya kuma mukajishi shiru
shima bayan yan watanni na tashi yaje ya ganomin ko qalau Haro shekara uku an tafi hudu
baizo ya ganni ba shima mukaji lbrn mutuwarsa nayi kukan rashin Haro, babban tashin
hankalin sun sake tashi a inda mukasansu Babu Indo Babu dalilinta babu yarsu guda daya tun
daga lkcn na baza koma ta a Nigeria neman wannan yarinya saboda naji lbrn baqin fentin da
akayi masu ta dalilin kakarta data haifi uwarta Hamida sun zama abin tsangwama ababen
kyara wai ana musu kallon mayu"........
Dakatawa tayi ta dago ta zubawa Juhud da jikinta keta rawa ido tace tana Shirin mgn ta miqe
da mugun gudu ta nufi cikin gdan Kareem dake nufo sashin ya rufa mata baya tana shiga ta
fada jikin Mom ta qanqameta ta rushe da kuka me sauti Mom ta dora hannunta akanta tana
Shirin mgn Meenah tace “Ashe kin nemomin asalina Mom kikaqi fadamin kika barni cikin
zullumin tunanin ta Ina zan fara nemansu Mom meyesa kikeson boyemin duk abinda ya kamata
na sani"
Murmushi Mom tayi tace “wato Dana Hana a fada miki Saida aka samu Wanda ya gumtsa miki
Meenah tawa yata ta kaina Ni dama bantaba jinki daban da jinina ba kiyi hqr bawai na boye miki
don banaso ki sani bane aa na boye miki ne don inason idan kin haihu