Showing 57001 words to 60000 words out of 99941 words
Chapter 20 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
rayuwarta nata taba ganin kamar tsagin
Kara irin wannan ba kama haske da jiki inda kasan innatun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya
tace “mom wannan fah?"
Dadine ya cika mom ganin ta fara warewa tace “Wannan Kharimatu kenan qanwata ce
babanmu daya daga Mali suke ita da Mamanta Hamida kinganta can" juyawa tayi ta kalli
dattijuwar matar da tayi tsufan jin dadi fatar nan kamar a matsa a tatsi jini tana sanye ds farin
tabarau tayi mata murmushi ta bude mata hannu ta fada jikin matar hakanan takejin wata
nutsuwa na ratsata da kwanciya a jikin Kumbo Hami Kumbo Hami ta shafa kanta tace “kiyi hqr
jikata zakiga ribatai a gaba munci wannan baqin cikin nida babbar yata Aysho tana jaririya a
tsumman goyo aka koremu daga gdan babansu Aishatu surukarki......" Kuka ne ya qwacewa
Kumbo Hami ta share qwallarta tace “saboda qin jini da yanayin qabila wannan abu yake
bibiyarmu kamar garin Bodde wani babban garine da yake cikin Qasar Mali So garin yazamo
kamar Biddah a Nigeria sunyi qaurin sunan asiri da maita Wanda ba dukkan garinne suke da
wannan hali ba su masu yinma sune kaso mafi qanqanta.
Baffana attajiri ne a garinmu a zahiri bama maita bama tsafi Amma saboda dukiyarsa yasa ake
cewa shine shugaban mayun garinmu Baffa Garbu wato babansu Aishatu surukarki yaron
babana ne hakan yasa yabashi aurena tunda nazo garin lkcn baa auro uwayen su Aishatu ba
matan gidan suka tsangwamin Kuma Allah dabawa mugu dama haka akayita rashe rashe a
gabar tun baa yarda har suka amince da gaske ni mayyace hakanan na haifi Aysho ranar dana
haifeta Garbu bayanan uwarsa tasa aka daukemu akaje bayan gari aka yasar damu daqyar na
iya komawa Mali daga Senegal naci gaba da rainon Aysho Garbu nasona Amma bashida ikon
dawo dani domin babana ya fusata hakan yasa Aysho nada shekara goma ya karbeta a gurina
sai labari naji ya auradda ita ga dan qanwarsa ya taho da ita Nigeria tun daga wannan Rana
nakebi akaini inganta nakasa samun dama dakaina nazo Nigeria neman Ayshatu na ban dace
ba a qarshe dai nama hqr domin jikina na bani Ayshatu bata raye don da tana raye inni ban
nemeta ba ita zata nemeni, bayan na rasa Ayshatu ne qulafucina da son naganta yasa na
komawa Alh Garbu shine har na sake haihuwar Kharimatu, Aminatuh yanzun komai ya wucce
bayan ansha wuya kema idan kikayi hqr watarana zai wucce"...........
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/2, 6:36 PM] Oum Hairan: *0026* Jinjina kai Juhud takeyi da jin wannan rikitaccen al'amari
tabbas duniya ta cika da mutane marasa tsoron Allah saidai kayi fatan Allah ya dada maka
Imani kawai, dubanta Mom tayi tace “Kumbo Hami itace ta riqeni tun bayan rasuwar mahaifiyata
banida uwar data fita a duniya Meenah" sosai Meenah taji dadi da ganin dangin surukar tata
hakanan taji tanayi musu wata qauna me game jini suma sosai suke nuna mata qauna da
kulawa sun jima sosai a sashin nata sunata hirarsu gabadaya su anan suka qarashe bikinsu
basajin Hausa sosai hatta Rasheed fullanci yakeyi musu wannan tasa Juhud sajewa dasu.
Kwana uku aka dauka ana bikin qofar falo Rasheed hana Juhud zuwa yayi da sunan biki to
itama bata matsa ba ganin Mom ta goya masa baya a gdanta tayi nata bikin saidai tasa ta cire
kawai idan yaga garara mutane sunwa bangaren sauqi yasata a corner yayita hadanta aiki ta
rasa a wanne bigire zata aje Rasheed irin mazan nan ne masu jarabar nacin masifa shi indai
zaki dagansa qafa to bakida matsala dashi idan har kaga Yana ciccin mazu to ya nema anyi
masa rowa ne.
Tunda ta fahimci haka itakuma taci alwashin kozata wahala indai ya nemi haqqinsa zata bashi
domin shima Babu ta inda ya tauyeta ya tsarenta mutumcinta fiye da yanda ma ya tsare nasa,
ranar da biki ya watse aka kai amare gdajensu washegari su Kumbo Hami suka shirya tafiya
Juhud har tafi Mom shiga damuwa da tafiyar tasu da anyi mata mgn sai hawaye lkcn da taga
sun kusan gama shiryawa sulalewa tayi tabar gidan ta koma sashinta tasa Rasheed a gaba da
kuka wai ita bataso su tafi.
Murmushi yayi ya shafa kanta yace “ke har yanzu yarinya ce Meenah to yanzu Kuma kawai
saboda bakison su tafi sai su zauna? Kiyi hqr idan kika haihu zan dauki dogon hutu zan kaiki
garinsu nima rabona da Mali nafi shekara ashirin" da haka ya samu ta sake har sun shiga mota
Kumbo Hami ta fito ta kama hannunta hakanan takejin yarinyar a jininta tace “kici gaba da hqr
mijinki Yana sonki Ni shaida ce Meenah idan Allah yasa watan hsihuwarki ya kama da rai da
rayuwa zan dawo ni zanyi miki biqi kinji jikata" dariya tayi itama tayi dariya suka tafi suna
dagawa juna hannu tana kwance bisa kafadar mijinta.
Taso rakasu airport fir yaqi saboda yasan idan taga tashinsu tsaf zata rikice masa, suna
komawa kuwa ya fara hadansu kaya ta dubesa tace “yada hada kaya?" Dubanta yayi yaja
numfashi yace “tafiya muma zamuyi" komawa tayi ta kwanta yaci gaba da aikinsa bayan ya
gama yazo shima ya kwanta sukaci gaba da soyayyarsu sai biyar na yamma sannan sukabar
gidan Muntaz ne yakaisu airport suka daga zuwa Enugu.
Sun sauka da dare suka samu motar taxi takaisu masauki suna zuwa ta kwanta zazzabi ya
rufeta Saida ta kwana uku tana kwance yana jinyarta har ta samu ta samu sauqi sukaci gaba da
rayuwarsu gwanin dadi.
Aikam tana ganin qauna da soyayya ririta cikin nan yakeyi kamar me, lkc ya rinqa turawa cikin
nata Yana qara girma komai yanayi mata wuya shine yake yi mata komai kafin ya fita hatta
abinci daya barta ta girka gara yaje ya siyo musu, October watan haihuwarta ya kama
tsakiyarsa suka dungumo suka dawo Daura kwanansu uku kuwa da dawowa Kumbo Hami ta
dira a Daura sunyi murna sosai sunata farin ciki kwanansu uku ya tafi ranar daya tafi kuwa cikin
dare ciwon naqudar na gaske ya tashi.
Wayyoh anci wuya matuqa kwana tayi ta wuni tana naquda har Saida suka yanke shawarar ayi
mata aiki sun gama komai sun shiga da ita ubangiji ya kawo mata sauqi cikin taimakon Allah ta
sunkuto qaton danta namiji wayyoh farin ciki gurin Mom da Mai Martaba da Ya'isha hatta
Muntaz yayi murna da wannan haihuwa kwananta daya a asibitin aka sallameta suka dawo gda
Kumbo Hami na kulawa da ita shikam gogan saboda farin ciki har kuka yayi gashi bayada
damar dawowa bama ya qasar Yana sauka aka turashi Africa ta kudu.
Ba Shiba ita kanta taso ace yana kusa yaga dansa yasa masa albarka hakanan dai akaci gaba
da hidindumun haihuwar wani abin mamaki babu wani daga bangaren Addah Abulle daya leqo
barkar wannan haihuwa lamarin ya bawa kowa mamaki itako Meenah batasa a ranta ba balle
abin ya dameta domin ba iyakar su kadai bane duk Wanda ke gdan sarautar Babu Wanda ya
leqo musu barka tasan saboda itane Kuma tariga tayi forget na komai dazai sanyata damuwa
dane dai ta haifi abinta Kuma ubansa da shaqiqan danginsa suna murna da zuwansa duniya.
Duk wani gata da maijego yar gata take samu Meenah ta samu samansa Babu abinda
zatacewa surukarta da Mai Martaba sai gdy domin shima ya taka rawar gani gaya a wannan
haihuwa, duk abinda uba yakeyi shine ya dauki nauyi donma komai na buqata Rasheed ya
tanadi abinsa sai dan abinda baa rasa ba Kuma ya zuba mata kudi masu kauri a account dinta
ko zata buqaci wani abu.
Ranar kwanaki uku ne suna zaune da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida a falo Juhud na
feeding din babynta ya kafeta da ido qurr yana qare mata kallo suna dariya Kumbo Hami tana
cewa “wannan ja'irin yaron quiya zaiyi tun yanzun Yana qarewa uwarshi kallo da shegen
wayonsa aka haifesa" itadai saidai tayi dariya kawai. Sallama akayi a bakin qofar suka daga kai suka kalli me shigowar Hajiya Bilki ce ta shigo ita da
Dada Hanne babbar yayarsu Mai Martaba Mom ta taresu fuska a washe tana musu sannu da
zuwa ta basu gurin zama Dada Hanne ta tabe baki tace “ashe an haihu?" Da yanayin rashin jin
dadin tambayar Mom tace “eh wlh yau kwana uku" tabe baki sukayi Dada Hanne tace “eh tun
ranar aka fadamin shine dai yau na daure nace Bari nazo Ke Bilki bani ruwan qanzon nan"
dukkansu kallonta sukayi ta miqa hannu ta dauki yaron a cinyar Juhud tana harararta kawai ta
bude bakin yaron ta dauki ruwan zata dura masa Meenah ta miqe da sauri tayi kukan kura ta
warce danta Dada Hanne ta kuwa dauketa da mari tace “kutmar ubancen ke dan uwarki ni zaki
qwacewa yaro a hannu koda yake ba banza ba dama anfada ance indai da abar a jikinki bazaki
Bari a karyawa danki ba gashi kuwa munga alama to wlh baki Isa ki bata Mana zuri'a ba dolene
abawa yaron nan ruwan qanzon nan Kuma daga yau an daina bashi wannan baqin nonon na
tsiya a nema masa Madara ko abawa Fadila ta shayar dashi shidai Rasheedun da kwadayin
farar fata da kyauwun banza yakaishi ya dauko to ta qare masa akansa...."
Tana qoqarin fusgar jaririn Juhud ta qara qanqame abinta ta saki wani kuka me sauti tace “wlh
bazaku kashemin daba duk abinda zakuyi saidai kuyi....." Mom ce ta karbe da cewa “Dada Ina
ganin mutumcinki ki fita daga lamarin halwata kafin na hada dake na tsince muku zarafi yaran
nan daga ita har mijinta basu damu da lamarin kowa ba ku kun damu dasu to waima Ina
ruwanku da abinda ta Haifa ne ince dai nasu ne su suka Samar da abinsu ke yanzu bakiji kunya
ba gotai gotai dake kizo kina yada girma gaban jikarki"
Hayayyaqo mata Dada Hanne tayi tana cewa eh dama Mana dole kice haka Aisha ai kinci kin
qoshi mun kaiki matsayin da baki takaba a baya to dake da Mahfuz da Rasheedu da duk wani
Wanda yake yaruwa a gidannan a qarqashin darajata yake balle wannan yar galaulawar da
kuka kwaso kuka manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga
tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki
har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai
bala'i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba" Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa
“yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da
gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban
bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a
samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya
ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya
debemin albarka ta sama data qasa har Yana cewa indai halwata ce to har abada bayaso......"
Fashewa tayi da kukan munafurci nandanan Mom ta zuciya Mom akwai hqr da kawaici Amma
tanada mugun zafi idan aka kaita qarshe ta miqe tace “Hanne ku fice daga bangaren nan tunda
baa ginashi da sunan dayanku ba da sunan Dana Abdulrasheed aka ginashi Kuma iyalinsa ne a
ciki munji ko Meenah zata rinqa sakatarmu da daidai munasonta a haka tunda danmu yanaso
munafiki ya ciji yatsa maqi gani ya rintse ido insha Allahu Meenah saita haifi sarkin gobe a
gdannan muga shegen daya Isa ya Hana Allah ikonsa magani ne bamaso mun gode bazaa
bawa yaron nan ba indai ta jikin dana ya fita muga Wanda ya isa ya gwada ikonsa a gidannan"
Tana fadin haka ta karbe yaron a hannun Meenah data hada kanta da center table taketa kuka
wannan cin mutumci da take jawa uwar mijinta yayi yawa itakam da tana da dama data fita
daga cikinsu ko da samu salama to tunanin halin da Rasheed zai shiga shine yake takanta burki
ya dauki amanar kansa da komansa yabata sun jibanci lamarinta sun yarda da kowanne irin cin
mutumci indai akanta ne idan tace zata gudu tabbas batayi musu adalci ba domin ta kwaranye
musu baya magautansu zasu samu damar yi musu dariya.
Kumbo Hami ce ta matsa jikinta ta riqe kafadunta tana jinjina girman halin da yarinyar take a ciki
bata taba tunanin abun yayi qamarin haka ba dole yarinyar ta kasa sukuni cikin wannan ahli
lamarin rashin kararsu azumin ne basa da mutumci ko kadan sosai kalamin Dada Hanne sun
girgiza Kumbo Hami ta dago Juhud jikinta ta shige jikinta cikin kuka tace “don....don Allah
Kumbo ki taimakeni kice da Rasheed ya hqr da zama dani tunda danginsa basa qaunata wlh
zuciyata zata buga idan naci gaba da zama a cikinsu ya sukeso nayi ne da wanne zanji?
Yaushe zanyi farin cikine yaushe zan samu salamar rayuwa nima kamar kowa, Allah inason
mijina Amma lkc yayi da zan barsa na nemawa kaina yanci ina zangansu??"
Bubbuga bayanta Kumbo Hami takeyi cikin jimami tace “ki daina tuhumar ubangiji akan abinda
bai kawo qarshensa ba Meenah meye laifin mijinki ne da zaki zabi jefashi cikin garari yanasonki
baitaba kallonki da abinda wadannan debabbun ke kallonki dashi ba surukarki ta karbeki ta
yarda da komai daya jibanceki kada ki bata rawarki da tsalle koda bazakiyi hqr domin Allah ba
kiyi don wadannan ahlin mijinki mahaifiyarsa yan'uwansa da suka fito daki daya nasan Allah zai
baki ladan saka Alkhairi da Alkhairi kada ki zama butulu rayuwar butulu bata qarshe me kyau
kinji?"
Kwantar dakai tayi cikin yanayi na nadamar kalami tace “yanzu shikenan ni tawa qaddarar
kenan Kumbo haka zanta rayuwa cikin tsangwama a cikin ahlin da ba nawa ba haka zan qare
rayuwata ni a qunci halwata a qunci?" Murmushi tayi tace “kada ki cire tsammani daga rahamar
ubangiji insha Allahu komai zaizo qarshe" da hikima irin tasu ta dattijan da sukaga jiya sukaga
yau suke sa ran ganin gobe ta kwantar mata da hankali ta kwanta kanta na ciwo Aunty Hamida
ta dauko Sarki junior ta kawo musu Kumbo Hami ta karbeshi ta zubawa yaron ido dan
kyakkyawa dashi kamanninsa na ubansa hasken fatarsa na uwarsa.
Miqa mata shi tayi tasa masa nono ya kama Yana zuqa tana cije lebe zafi takeji sosai idan
yanashan nonon hakanan take daurewa take shayar dashi bata jima da kwanciya ba bacci
barawo ya dauketa cikin baccin taji ana shafa fuskarta tayi miqa tare da tallafe kan yaron ta
zare masa nonon a bakinsa ta daga kai ta sauke idanunta da suka kumbura sukayi luhu² a
kansa shima ita yake kallo yakai hannu ya dauki Mahfuz ya zubawa yaron ido yanajin qaunarsa
data mahaifiyarsa na nunkuwa a ransa ya sake shafa fuskarta yace.
Kin biya Aminatuh Allah yayi miki albarka ya rayani tare dake" ajiyar zuciya taja me qarfi ya
sake zubanta ido yace “naji labarin komai daya faru don Allah ki taimakeni kiyi hqr ki dainasa
damuwar wadannan mutanen a ranki kinji" lumshe idonta tayi tare da lasar lips dinta daya
bushe yace “talk me Mana" kallonsa tayi idanunta na tsiyayar hawaye tace “idan ya kasance
nice matsalarka a duniyar nan Abdulrasheed meye yasa bazaka datseni cikin tarihinka ba ko ka
samu record me kyau?" Sakin baki yayi yana kallonta ta zame daga gadon tace “don girman
Allah mu hqr da zaman nan tunda mun kasa samun farin ciki a cikinsa Abdulrasheed bantaba
zama silar farin cikinka ba saidai na akasinsa tunda ka janyoni ka hadani da rayuwarka taka ta
gurbata ta ahlinka ta gurbace inda kai kadai ne da sauqi tunda kaine kaji ka gani Amma meye
yasa saboda son ranmu da son zuciyarmu mu zamo silar yankewar farin cikin wasu Baffa'am
Munjefa Mom cikin tsaka me wuya mun jefa Mai Martaba mun jefa kanmu mun jefa duk wasu
masoyanmu. Please don Allah don girman Allah mu hqr kabarni na rayu da yanci kaima ka rayu
da salama kaji"......
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/3, 9:13 PM] Oum Hairan: *0027* Tunda Juhud ta durqushe gabansa ta riqe qafafunsa tana
kuka tanayi masa magiyar jikinsa ke rawa ya kafeta da manyan lumsassun idanunsa ya kasa
furta mata ko kalma daya da zata zama salama ga ruhinta saboda gani yake duk furucin da
zauyi yayi kadan wajen goge mata radadin ciwon dake cin zuciyarta wanda harya sanyata
zabar rabuwa dashi fiye da rayuwa dashi. Kwantar da kanta tayi a cinyarsa ta dora hannunta a
fuskar Sarki junior ta sake rushewa da kuka tace “idan ya kasance kalaminka sun qare ni Kuma
Ina kakeso nawa suje Baffa'am kaine duniyata kaima kana neman zamewa daga gareni tabbas
rayuwata babu kai akwai rudani a cikinta Amma zan zabi na rayu da quncin rashinka fiye da
rayuwa da haqqin wasu nikam banajin dadin yanda zamana dakai ya zamo silar rarrabuwar
kawunan ahlinka Baffa'am meyesa Allah bai qadarta zamowata Alkhairi gareku ba?"
Lumshe idonsa yayi ya bude