Showing 69001 words to 72000 words out of 99941 words

Chapter 24 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1380

rawa Ya'isha tace “mun shigai Aunty Hamida ku Kira mijinta zata tayar
mana da aljanu" yanda jikinta ke tsuma ne yasa Hamida yarda ta Kira wayar Rasheed ya daga
muryarsa can qasa shima rawar tasa muryar takeyi yace “ya aunty Hamida ya akayi?" Cikin
zaquwa tace “Meenah ke neman rikice Mana mun kasa gane kanta don Allah kazo idan kana
kusa" kashe wayar yayi dake dama Yana gdan duk motsinsu yanaji ya dauki doguwar riga ya
saka ya bude qofar ya fito idanunsa kamar garwashi saboda ja dake duk yafisu Rasheed haske

shi fari ne sosai daka kalleshi zaka gane kukan shima yakeyi.
Kuka Fadila ta saka da ganin yanda yayan nata ya zama wani kalar tausayi tace “tunda yarinyar
nan ta shigo zuri'armu muka daina cikakken farin ciki Ya Kareem kaima duk ta susutaka yanzu
kukannan don ita kakeyinsa....."
Hanya ya saita mata cikin zafin zuciya yace “kowa yaje na gde" binsa sukayi da kallo ya dubi
Hajiya Kulsum yace “Mama wlh idan akaci gaba da hayaniya a gdannan tsaf zan haukace brain
dina tana neman daina aiki" sumsum suka rinqa ficewa daga gdan saida suka fice gabadaya ya
tsaya yana jin tashin motocinsu gabansa faduwa yake daqyar ya tura qofar da sallama ya shiga
dakin ya tsaya tsakiyarsa Yana qarenta kallo tana zaune ta dora kanta jikin gado sai tsumar jiki
takeyi a sanyaye ya isa gareta ya tsugunna gabanta yakai hannunsa zai dago kanta gabansa
ya fadi ya janye ya sake saita idanunsa akanta yace “meye yake damunki?" Kamar me jiran
yayi mgn ta dago kumburarrun idanunta suka shiga cikin nasa ya kawar da kansa ya dake
zuciyarsa yakai hannunsa jikinta yajishi zafi zau yaja numfashi ya miqe ya dauki wayarsa Yana
zagaya dakin can yace “Inada petiant a gdana kazo da wuri don Allah" da haka ya kashe wayar
yaci gaba da zagaya dakin can yaji ana qwanqwasa qofar ya sauka ya bude suka shigo tare Dr
Razaq ya fara tambayarta yanayin da takeji tayi masa shiru shikam Kareem ido ya kafeta dashi
can da tambayar ta isheta tace “Kaje Dr Razaq bakada maganin matsalata Allah ne kawai
zaimin magani" wata iska Kareem ya furzar ya juya ya fice Dr Razaq ya biyosa yaganshi tsaye
ya hade kai da garu ya dafashi yace “ka daina Sanya wannan damuwar a ranka Ranka shi dade
kanada heart problem idan komai zaike damunka to rayuwarka tana cikin kwale²"
Juyowa yayi ya dubi Dr Razaq yace “kana nufin Meenah zata soni nima?" Dariya tambayar
tabawa Razaq yace “kama qaddara a ranka tasoka fiye da kowa ta gama karfa ka manta kaine
ta fara so a rayuwarta ko ka manta Karin mgnr hausawa da suke cewa so baya tsufa saidai
masoyan su tsufa bature kuma yace true love never end" wani murmushi yayi yace “na gde Dr
Razaq zan jira lkcn da zan gasqata hakan".............




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....

*Oum Hairan*
[8/8, 9:07 PM] Oum Hairan: *0032* Sallama sukayi ya rakashi ya hau motarsa tare da karbar
magunguna bai koma gdan ba shima ya shiga tasa motar Yana duba agogo 8:30pm ya jinjina
kai ya fice a gdan kai tsaye wani restaurant ya nufa yayi musu siyayyar abinda zasuci ya juya
ya koma gdan ya kulle ko Ina ya nufi saman Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya sanya kayan
baccinsa ya fito ya bude nata dakin tana zaune inda ya barta har yanzu kukan takeyi gabadaya
lamarinta ya tsinka masa lakar jiki da gaske take jin damuwar a cikin ruhinta.
Aje ledar dake hannunsa yayi ya tsugunna a gabanta ya kamo hannunta ta fuzge ya zauna
sosai a gabanta ya dafe kuncinsa da hannayensa biyu ya zuba mata manyan idanunsa da a
baya suke firgitata da sanyata shiga taitayinta baiji a ransa ko yace ta tashi suyi nafila zatayi ba
shiyasa ya janyo ledar yace “Ya'isha tace tun shekaran jiya bakici abinci ba ko meye dalili?"
Shiru tayi masa yaja fasali ya furzar da iska ya bude ledar ya fara yaga mata Naman yanda
zataji dadin ci ya dauko yakai mata bakinta ta kawar dakai yayi murmushi yace.
“Lamarinki abun mamaki ne Meenah sai naga kamar kina jayayya da hukuncin ubangiji ne ya
kamata ace rayuwarki kadai ta ishenki darasin da duk wani abu da Allah yayi zaki tarbeshi
hannu biyu wlh duk da nakasance me qulafuci da addu'ar idan kedin Alkhairi ce gareni ki zama
gatana ki zama mallakina bantaba furtawa wani burina a kanki ba na fawwalawa ubangiji na
yarda duk abinda yayi daidai ne so Kuma sama taka cikin lkcn da ban tsammata ba kiran Mai
Martaba ya shigomin yana fadamin na tanadi sadaki a hannuna daga dubu hamsin zuwa abinda
Allah ya horemin nazo masallacin Fada yana nemana bansan meye zai faru ba hakanan na tafi
Ina zuwa naga dogare sun budamin na shiga kamar yanda baa nemi izininki ba nima baa nemi
nawa ba wlh kudin aljihuna kawai Mai Martaba ya karba dubu tamanin yabada umarnin a daura
nidai na nemi guri na zauna Ina jiran naji auren waye zaa daura kawai naji ance yace shi a
matsayin waliyinki ya bada aurenki gareni akan sadaki naira dubu tamanin bisa sharadin zanyi
miki lefe kamar yanda al'ada ta tsara"



Shiru yayi yana mayar da numfashi sannan yaci gaba da cewa to meye laifina cikin lamarin nan
Meenah?" A qufule ta dago tace “meyesa bakace bakaso ba?" Murmushi yayi yace “ko bake
bace zan karba balle Kuma ya kasance dadaddiyar addu'ata ce ubangiji ya amsamin tare da
tabbatarmin da ita kamar mafarki so ni a tsarina bana jayayya da duk abinda nasan ba ikona
bane, Meenah a baya kema haka kike saboda kedin dalubata ce bansan meye ya sauyaki ba
kinga inada maganganu da yawa da nakeso mu tattauna da zasu zame mana mafita Amma
farko don girman Allah badon halin Abdulkareem kici abinci muyi sallah wlh ko Isha banyi ba
saimu zauna"
Yanayin magiyar tasa tasata dole ta dauki Naman takai bakinta yaji dadin hakan sosai ya miqe
ya shiga bathroom ya dauro alwala lkcn daya fito ta gama ya tattare ya fita da kayan ya dawo
ya isheta a bayi tana brush da alwala, abin sallar ya shimfida yajasu sukayi Isha sukayi nafila
raka'a biyu ya sanya hannunsa ya dafa kanta ta zame zata miqe ya miqe ya riqeta tare da
matseta a jikin bango ya fara karanto addu'o'insa cikin larabcinsa me Sanyaya jiki sunkai 10
minutes a haka sannan ya saketa yana binta da kallo har zuwa lkcn bata daina dauke hawaye a
idonta ba miqewa yayi ya dagata ya zare mata alqyabbar jikinta ya sake ware lafayar jikinta

tana tureshi tana komai ta durqushe da sauri yayi dariya wai kunyarsa takeji Meenah da lkcn
data fara period shine mutum na farko daya fara sani shima a lambu ya isheta tanata kuka wai
taji ciwo daqyar ta fada masa yayi mata bayani.
Sautin dariyarsa ce tasata dagowa ya zauna tare da daganta gira yace “ashe kinajin kunyata
Meenah yaushe kika farajin kunyana?" Harara ta galla masa yace “ko a jikina ki kwana kinayi
yanzun dai Bari na barki ki kwanta ki huta abinki Saida safe" ficewa yayi yaja mata qofa tabisa
da kallo tare da miqewa tayiwa dakin key ta haye gadon tayi kwanciyarta badon tayi bacci ba
saidon tabawa zuciyarta damar tunanin abinda yake damunta.




Batasan lkcn da bacci ya dauketa ba a sama ta rinqajin ana taba qofar ta miqe tana miqa tare
da yin salati tace “wayene?" Cikin sanyin yanayinsa na dabi'a yace “kinyi sallah ne?" Bata bashi
Amsa ba ta nufi bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga ta tayar
da sallar bayan ta idar tayi azkhar ta sake zubewa a gurin duk da ba wata hidima tayi a bikin ba
tanajin gajiya a jikinta sosai, bacci ne ya sake dauketa bata farka ba sai 10:30pm shima din
wayarta ce taji tana ring baqon layine ta Kara a kunnenta yace “barka da safiya ki fito kinyi baqi"
Miqewa tayi tasa rigarta ta bude qofar ta fito Sarki ya rugo da mugun gudu ya rungumeta ta
dagashi daqyar tana dariya yaron yace “Mom jiya nayita kuka daban ganki ba ashe gdan Uncle
kika dawo nima na dawo nan" murmushi tayi tace “surutu dai kazo ka dameni ko" tsuke fuska
yayi zaiyi kuka Kareem ya matso ya karbeshi yace “ba tun jiyan nace kazo mu taho ba kace kai
bazaka tafi kabar Mom dinka ba to yanzun fah zaka taho ko shima aa?" Da sauri ya daga kai
yace “eh" Mom dake tsaye tayi dariya tace “aikam baka isaba yaro muna tare aurena dakai
mutu ka raba" kuka ya saka Yana cewa “nin...Ni Mom banasonki kinmin tsufa ni gurin Mom dina
da uncle zan dawo"




Dariya sukayi dukkansu ta nemi guri ta zauna Hamida tace “jikin yayi sauqi kenan tunda na tafi
nakasa sukuni dake na kwana a raina" sunkuyar dakai tayi ya miqe yace Mom me zaa kawo
muku gdan namu bai gama tsaruwa ba Hajiyan sai yanzu ta fito" kiransa Mom tayi tace “kazo
kayi zamanka bama buqatar komai tun jiya da sukaje suka sanar dani halin da ake ciki na kasa
sukuni shiyasa nazo naganku yanayin Alhmdllh komai zai wucce insha Allahu Meenah hqr
zakiyi da abinda Allah ya hukunta, Aminatuh nice na haifi Rasheed Amma bazanyi shaidarsa
kamar yanda zanbada shaida akan Kareem ba kin samu miji na nunawa saa daya tamkar da
dubu idan kin kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo qarshe ita rayuwa kowa da irin
tasa jarrabawar Babu me taya wani dakon kayan da ubangiji ya qulla masa dole shine zaiyi
dakon kayansa rabon dake tsakaninku me qarfine Allah ne kawai yasan adadinsa saboda haka
kuyi hqr da jarrabawarku"
Kallon kallo sukeyi kowa da abinda keyi masa yawo a ransa Mom ta miqe tace “Inason mgn
dake Meenah miqewa tayi tabita suka haura saman dakin baccinta suka shiga Mom ta zauna a

gefen gadon ta kama kunnenta tace “ki kiyayi shiga haqqin Kareem kawaicinsa da kararsa ta
game kowa zai iya zubanki ido akan duk abinda yaga baki da raayi koda kuwa shi zai cutu
hqrnsa abin jinjinawa ne shiyasa yake wahala idan ciwo ya ganshi don Allah kada ki zama silar
wargatsa masa rayuwa kinji"



Kwantar da kanta tayi a cinyar Mom tana shassheqar kuka ta dauko wasu turaruka masu
qamshin gaske na humra da na wuta tace muje a jerasu a show glass din fita sukayi suka jera
ta fito da wani garin magani ta dauko danyen nonon raqumi ta barbada a ciki ta miqa mata tace
“shine yayi saura da jiya kikaqi sha duk yanda kike tunanin fitinar Rasheed Kareem yafisa
saboda akan hakan har so akayi a raba aurensa da Zahrah kwanakinsa bai qare ba yanzu
Kuma gashi zaki zauna ke daya da sunyi hqr ma sun barta ta dawo da kin samu sauqin wani
abun don Allah banda rowa Meenah shidai abinnan in kin hanashi ma ba ado zakiyi dashi ba
Kuma ba kwanaki zaa qara masa ba idan wa'adinki yayi shima nasa yayi please a kula don
Allah" sosai Mom ta rinqa bata shawari a fakaice saida taga ta dan sake sannan sukayi musu
sallama suka tafi shima ya fice a gdan ta shiga bathroom tana wanka ta jiyo wayarta tana ring
batabi takanta ba Saida ta gama shirinta tsaf sannan ta dauka number Ya'isha ce tabi suka
gaisa tace “ya amarci jiya tsohuwar zuma ta motsa Ya Kareem an kwana ana zikiri" dariya mgnr
tabata tace “waiku don Allah meye yasa kuka bawa abinnan muhimmaci ne haka"
Dariya Ya'isha tayi tace “mahadin rayuwa kenan gulma nazo yi miki" gyara zama tayi tace “aike
dama indai anga kiranki to gulma ke cinki meye zaki fadamin" gwauron numfashi ta sauke tace
“wato bantaba sanin Addah Abulle jahila bace sai jiya iliminta baya mata jagora kamar yanda
yakeyiwa danta jiya Mai Martaba Yana zagaye bayan an taho kawoki ya nufi bayan gda ya
isheta ita da Dada Hanne suna qusqus Dada Hanne nabata shawarar kawai tunda duk bugunsu
yaqi tasiri akanki to su dora miki jinya yanda shi Kareem din zai gaji ya koreki sannan su
sanyawa kowa qiyayyar ki a zuciyarsa ta yanda ko kin dawo gdannan Babu me karbarki Ina
kaiki sun gama tattaunawar nan suna daga ido sukaga Mai Martaba da Ya Muntaz shine Mai
Martaba yayi musu wani warning mai kama da daukar rai har yana fada musu daganan zuwa
shekara goma idan kikayi ciwon kai saiya hanasu kwanciyar hankali ke sosai fah akayi rikici
qarshe dai Addah Abulle tace da Mai Martaba tunda har ya nuna mata ita ba kowa bace akan
danta to saidai ya zaba ko ita ko ke shikuma yace ya zabi zabin dansa aikuwa tace saiya saketa
anso hanashi yaqi ji qarshe yayi mata daya me kyau sannan yace da Kareem yabashi damar
rabuwa da Zahrah tunda abin nasu iskanci ne aikuwa tuni ya yankawa Zahrah ticket itama
Kinga sai tafi samun sukunin zaman gida"




Zuciyar Imani ta Meenah duk sai jikinta yayi sanyi tace “Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Ya'isha
wannan ba labarin badawa bane Allah fa shine ya halatta saki Amma bayasonsa nikam banji
dadi ba idan Addah bataci arziqin komai ba yakamata taci na yayanta wlh wannan sakin bala'i

Mai Martaba ya qara jefani sannan ita Zahrah meye laifinta a ciki najifa ance iyayenta ne suka
dauketa bataso tanason mijinta Kuma ko jiya da yazo dakina naga ta kikkirashi bai dagaba
haba don girman Allah wannan ba adalci bane bai kamata ba"
Tabe baki Ya'isha tayi tace “saiki fada mawa Mai Martaban tunda kinfishi hangen nesa nikam
naji dadin hakan ko banza sayi hankali susan ba ko Ina ake shimfida a zauna ba" kashe wayar
tayi ta zabga tagumi wannan wacce irin masifa ce daga wannan sai wannan?
Bataji tsayuwar motarsa ba saiji tayi ya zare hannunta a kuncinta ya tsugunna a gabanta ya
shafa habarta ya dago kanta taja numfashi tace “Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Babu alamun
bacin rai a tattare dashi yace “meye kuma?" Kafin ya rufe bakinsa yaga ta balle da kuka tayo
qasa ta dora hannunta a cinyarsa gwiwarta na gugar nasa tace “kayimin wannan alfarmar ko ita
daya ce a rayuwa don Allah Ya Kareem" da rashin fahimta ya dubeta tayi qasa da kanta tace
“ka dawo da matarka dakinta domin Allah.




Miqewa yayi yace “ok kinyi sallar Isha?" Girgiza masa kai tayi yace “ki dafamin coffee ki
kawomin dakina" ficewa yayi daga dakin ta bishi da kallo wani takaici ya tokareta waishi miji
gashi babu damar yin musu yau izzar yakeji sosai batada zabi sai nufar kitchen din da tayi ta
fara hada masa coffee din ta gama ta nufi dakinta tayi wanka ta Sanya kayan baccinta ta zura
hijjab ta nufi dakin nasa ta qwanqwasa yabata izinin shiga ta bude ta shiga gabanta na faduwa
ta kawar dakai tunda take bata taba ganinsa a tube ba sai yau cikar zatinsa kawai abin ka tsaya
ka nazarta ne qirarsa ta hutun gaske fatarsa lufluf su ta lura kamar sign na Fam dinsu ne
gargasar jiki daga mazansu har matansu.
Sunkuyawa tayi ta aje masa ta miqe zata fice ya Kira sunanta ya nuna mata guri ta zauna Saida
ya gama abinda yakeyi sannan ya miqe ya nufi wardrobe ya dauki riga yasa yajasu sukayi sallar
ya dauki coffee din yanasha Yana kallonta ita Kuma na kallon qasa ganin yanda duk ta takura
yasashi cewa “jeki Saida safe" kamar me jiran umarni ta miqe tayi zuruf ta fice ya girgiza kai
yana murmushi yace “Meenah kenan"




Ya jima zaune Yana tunanin hanyar da zaibi ya samo kanta bai kwanta ba sai 12:00am koda ya
kwanta din baiyi bacci ba yanason kasancewa da matarsa Yana tsoron takurawa rayuwarta ko
kadan baison shiga rayuwar dan' Adam balle Meenah da take da muhimmaci cikin rayuwarsa
hakanan ya kwana Yana juyi shikam bacci me sunan bacci baiyishi ba da safe ta rigasa fitowa
ta gyara part din nata ta sauka qasa ta gyara ta koma ciki tayi kwanciyarta fitowa yayi cikin
shirinsa na fita yaga ta gyara ko Ina ya girgiza kai ya bude dakin nata tana kwance tana chat ta
kallesa ta kawar dakai yace mata “barka da safiya" aje wayar tayi ta miqe tace “ina kwana"
shafa sumarsa yayi yace “na tashi lfy Visa dinmu zan karbo gobe da safe zamu tafi nayima
Sarki passport Mai Martaba ya hanani shi bansan meye yasa ba" itadai batace masa komai ba
ya miqe yace “kina burgeni salonki yana sanyani nishadi nabarki kiyi iyakar abinda zaki iya kafin

ki shigo hannuna"
Ficewa yayi ta tabe baki ta koma tayi kwance abinta bata tashi ba sai azahar da yunwa ta
fafaketa ta shiga kitchen ta samawa kanta abinci ta dawo ta zauna a falon qasa tana zaune taji
an bude qofar an shigo ta daga kanta suka hada idanu da Amrah da Zahrah ta miqe tana cewa
dasu “Lahh Amrah sannunku da zuwa ku iso mana" wani mugun kallo suka watsa mata Zahrah
tace “tun Ranar dana fara ganinki matsayin tsohuwar budurwar mijina naji zuciyata bata karbeki
ba ashe kedin masifa ce Kuma bala'i cikin rayuwata Aminah kin kashemin Zainab nikuma nayi
alqawarin kashe taki rayuwar sai kinyi nadamar shigo da kanki cikin rayuwar gidana"..........…...





Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login