Showing 3001 words to 6000 words out of 99941 words
Chapter 2 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
saita tatsi na mijinsu sannan takai kasuwa ta siyar ta samu na cefane ita
kuma Aminatu yawan shanunta yasa bata fita tallen nono yarane da ita da suke dauka mata
suke saidawa su kawo mata kudin.
Wannan abu yana ciwa Gwaggo Lami tuwo aqwarya gashi ta rasa yanda zatayi da Aminatu ga
wata kulawa da Maddibo Wandu ke bawa Aminatu ta musamman kinsan abinka da lamarin
maza idan suka auro yarinya wannan abu ya taru ya hadu ya haifarwa da Aminatu baqin a
gabadaya rugar domin kowa Bayan Lami yakebi sai ya kasance shikuma Moddibo ya koma
bayan Aminatu, kwatsam ana haka sai aminatu ta fara rashin lafiya ana shawara ce basir ne
ashe cikine da Aminatu a haka dai ba tare da kowa ya ankara ba har cikin Aminatu ya isa
haihuwa cikin dare ciwo ya turnuketa gashi Maddibo bayanan a lkcn ya tafi Nigeria sawo wasu
shanaye.
Gwaggo Lami tanajin Aminatu tanata nishin ciwo amma taqi ko leqota saida Buba ya fito fitsari
yajiyo ya nufi dakin da sauri ya isheta cikin mawuyacin hali a lkcn ta gama jigata kan da ya
sawo kai amma yaqi qarasa fitowa aikuwa ya ruga da gudu yaje ya taso wata dattijuwa me suna
Suwai suka taho tare kafin kace wannan dakin Aminatu ya cika da mutane amma ko qeyar
Gwaggo Lami Cikin ikon Allah ana kiran Assalatu aka samu Aka ciro yaron daqyar Amma
Aminatu batasan wake akanta ba gashi jini yaqi tsayawa Suwai tayi iyakar qoqarinta zamani
bana asibiti ba amma ina saida ubangiji yayi ikonsa Aminatu bata ko kalli fuskar danta ba Allah
ya karbi rayuwarta.........
Mutuwar Aminatu ta girgiza duk wani mutum dake rayuwa a wannan ruga hakana aka tashi
Manzo ya tafi Senegal ya sanarwa da iyayenta suka taso suka taho tare, tabbas Baffa Dodah ya
tausayawa Moddibo matuqa da irin halin dimuwar daya riskeshi a ciki daqyar da qarfin Addu'a
ya dawo daidai amma duk da haka daya kalli Jaririn da Aminatu ta tafi tabar masa sai ya kama
hawaye kwana sittin da haihuwar jaririn aka rada masa Suna Haruna su Baffa Doda sunso
tafiya da Haruna amma Moddibo yaqi yasa musu kuka yana roqonsu idan sun barshi zaike
dauke masa kewar Aminatu.
Badon ransu naso ba suka tafi sukabar masa wannan jariri hakanan Wannan yaro yaci gaba da
rayuwa tun yana tsumman goyo cikin rashin kulawa da qyara indai kinga anyiwa Haro wanka to
Dattijuwa Suwai ce ta daukeshi a qarshe ma dole Maddibo barmata shi yayi itake kula dashi da
komansa duk da cewa kwana Saba'in da rasuwar Aminatu Gwaggo Lami ta haihu hakan baisa
taji tausayin maraici ta bawa wannan yaro nono ba watsin da tayi da wannan jariri yasa shikuma
Maddibo ya dauki qaunar duniya ya dora masa komai ya samo na Haro ne Buba dake yarone
me hankali kuma ya dan fara tasawa bai damuwa da wannan fifikon hasali ma tausayin Haro
yakeji inda Bangel ya taso da qiyayyar haro shima Rubado daya tashi qarami da wannan aqida
da uwarsu ta koya musu ya tashi Haro ba mutunne me hayaniya ba wannan tasa ko fita sukayi
kiwo sai su kamashi su zaneshi da zarar sunga Buba ya kauce haka zai dawo gda yanata kuka
Suwai da Moddibo suyita rarrashinsa.
Rayuwa tayita tafiya a haka har suka tasa sukakai munzalin girma Al'adarmu ta fulani yaro yana
kaiwa sha takwas akeyi masa aure suyita tsalle tsallensu da matarsa har hankali ya iso musu
su rungumi junansu wannan ce ta faru da Buba da Bangel buba yanada Sha tara bangel
yanada Sha bakwai akayi musu aure Buba aka aura masa Jumme shikuma Bangel Asubi
Jumme mace ce me kawaici da hqr itakam Asubi irin mijinta ce sai ya kasance Haro ya tare a
gdan Buba komansu tare sukeyi ko shawara buba zaiyi baya shawara da yan uwansa da suke
ciki daya saidai Haro saboda nutsuwarsa tasa tunanin manya yakeyi.
Rayuwar ta farayi mawa Haro dadi ya saki jiki da Jumme sosai duk abinda ya samo daga
Jumme sai Suwai lkcn da shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da
aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga
Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune
suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan'uwana dan
qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka
kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne
Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru
biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya
Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai
da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama
qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan
rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo
halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a
Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu"
Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya
rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani
kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa
kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa
suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da
ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har
kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda burbushinta.
Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta
fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne
Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku
ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu
komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda
kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona
saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa'anninki
ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan
tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin
mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin
wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki,
ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin
kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye, badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to
kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki.............
*THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT
0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241
ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*
*Shares Please*
*Oum Hairan*
[7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD*
*(OUM HAIRAN)*
*( Pure love sex nd romantic)*
*FP THREE*
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
*TUNATARWA*
Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne
sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa
sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko
akasinsa.
*CIGABA*
Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na
sani shine inayi miki addu'a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya
fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun
kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama
cikin Yan'uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a
cikin wannan qangin ne oho.
Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni
nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da
Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har
gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan
nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?"
Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar
masa nono" numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido
akan Aminatu kuwa?" Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro
nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba" sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace
“dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa
shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi
hanyar birni" dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu
inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi" jinjina kai yayi yace “shikenan adai
qara kulawa" ashe wasan baa fara ba.
Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono
gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya
bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki
ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka
aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka
liqa mana.
Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya
nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi
tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu
meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da
yan'uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga
ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka
babanki su kwashe dukiyarki,
Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har
mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba
nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki
yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi
farin ciki ba" jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na
tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin
lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta.
Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin
nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar
juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su
kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin
shanh ne suka kasheshi.
Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda
yan'uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin
abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai" daya dawo bai sanar dani ba
nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa
masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen
Lu'ulu'u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah
ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin
Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda
daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya
mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da
wadannan abubuwan"
Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha
Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su
kubce miki kinji" jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa
Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka
cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata
malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada
dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika
fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe
wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin
tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita
dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa
karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa
dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina
zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba
ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da
zaki fita dashi talle.
A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan
basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da
suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na
Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi
Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan
kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin
Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa.
*ASALIN LABARI*
Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace “yanzun wadannan sune kadai
dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu
wannan wacce irin Al'umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin
hawaye tace “haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu
tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to
Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga
kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka"
Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar
nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya
saceta.
Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo
ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari
koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na
quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk
suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na
dari biyu shiyasa da haka zata koma.
Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama
kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe
hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi
taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi
ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “na
nawa ne?" Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu"
dubanta yayi yace “harke?" Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace “inaso ki
juyemin da sauri" daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana
waige² yace “ko bakiji ne?" Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace
banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran" karba yayi yasa a
bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace “gashinan har kudin qoranki bana shigowa
garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso" karba tayi tayi godiya ta juya da