Showing 42001 words to 45000 words out of 69832 words

Chapter 15 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

833

kallonta Mama take tace “shiyace miki kibiyashi “? Girgizama Mama kai
tayi tace “Mama you’re my responsibility ni kadai don’t others, banson wani ya taimakeni wajen
kula da mahaifiyata, inda bekaiki asibitin masu kudin nan nasu ba dana iya biya amman
yakama kaman an sashi ya kaiki asibitin kudi” tai maganan tana batarai tsayawa kawai Mama
tayi tana kallonta tun Rashida na yarinya tanada wani irin kishi dasai ka san halinta ne zakasan
kishine itafa batason kowa na raban Maman ta, yana daga cikin abinda yasa takejin haushin
Riyad dakuma so tabiyashi kudinshi sabida yanda taga yana nan nan da ita bataso taga Mama
na kula wasu with a smile, maida kudin kawai Mama tayi hannunta ta danne tace “listen to me
umarni nabaki kisai kayan salla inaso nima naga yarinyana tayi kyau takuma fito da salla kinji”
shiru tayi tana kallon Mama taki magana hade fuska Mama tayi tace “bazaki amsaba?” Ahankali
tace “naji toh” dan murmushi tayi tabata 20k tace “wannan sai kiyo su cefene su maggi da nama
da kayan miya tunda mun sami kayan abinci” gyadama Mama kai tayi ahankali ta tashi Mama
tace “adawo lpy ki duba titi kafin ki tsallaka kinji” toh ta amsa tawuce tasa takalminta tafita
abinta Mama tai murmushi.

Kusan 3hrs tabata a kasuwa, tasayo atampa mai kyau da gyale da takalmi tadansai bra da pant
guda biyu sai pad dan tanaji cikinta na ciwo sannan tayo cefene tashigo keke tabar kasuwan.
Abakin titi aka saukesu hakan yasa ta dandaro cikin anguwansu da kafa, tun kafin takai gidansu
ta hango wata arniyan karaman mota baka pake a kofar gidansu motan waye wannan? Hakan
yasa ta kara sauri tana zuwa tabude kofar gidansu da sauri ta shiga saura kadan tayi karo da
Riyad azaure yadan koma baya kadan tsayawa itama tayi gabanta kawai yafadi ta zubamai ido,
yana sanye da wani milk soft yard dake kyalli yabi jikinshi kaman magic, kafanshi kafanshi
sanye da Jordaan leather loafers brown, hannunshi daure da agogon Audemars Piguet, dayan
hannunshi rike da waya samsung galaxy fold, ba hula gashin kanshi ya kwanta yana sheki sai

kamshi yake zubawa, dauke kai tayi da sauri daga kallonshi dan he’s so clean wlh ko datti ko
stain ko tabo guda daya babu ajikin kayanshi, haka kayan a goge babu squeezing ko daya,
shima tundaga kan kafafunta dake sanye dawani black takalmi flat da duk an dinke ya kalla
dudda fararen kafanta are shinning ga long fararen nails na kafanta da babu lalli ko daya akai
zuwa ataman dake jikinta da hijabin da ledoji biyun dake hannunta bakake data rike sannan
yazubama fuskanta idanu she looks tired, she’s even sweating a goshi dan duk gashi ya kwanta
a goshin nata, ga lips dinta sun bushe kaman she’s a bit sick. “Kallon fa”? Tai maganan cikeda
rashin kunya dayasa ya daidaita kwayar idanunshi cikin nata dasauri ta janye idanunta hakanan
taji takasa kallonshi but tsabagen karfin hali tace “kadena zuwa gidanmu banso” cikeda isa
kaman anyi forcing nashi yayi maganan awulakance yace “are you angry ba wajenki nake zuwa
ba”? Wani dum! Taji saukan maganan da sauri ta kalleshi tsaf shima yake kallonta mene
mutumin nan yace? Mema ya dauketa? Taji haushi dan ba wajenta yake zuwa ba on wat
ground? Kokarin hado martanin dazata bashi take dan she was a bit speechless but yarigata
wani kallon raini yamata calmly yace “bakida matsayin dazan zo nemanki” yana maganan yabi
ta gefenta yafice wlh takai 1 good minute fassara maganan shi take akanta taji ranta na kumfa
dasauri tajuyo tafito kofar gida daidai yaja motanshi tabishi da kallo yana wani saka bakin glass
a idanunshi ko inda take bai kallo ba yawuce abinshi kaman zata hadiye zuciya tamutu tace
“nima ka isa kazo wajena ne aka gayamaka? Sai ji dakai kaman wani dan shugaban kasa
sabida yana takama da dan hotel din dayake dashi I will leave your company soon zan nemi
wani hotel din wlh kuwa” tana maganan tajuya tana saisaita bacin ranta takoma cikin gidan kaya
tagani cikin gidansu harda su indomie da kwalin kwai kudan 5 crete gasu manta manyan roban
madara Milo oat, wlh shopping data gani zube a compound yakai na 300k ga bandir na kudi
kuma ijiye kasa na yan 1k guda biyu dasauri ta shiga ta tsaya gaban kayan ranta abace tace
“Mama waya kawo mana abubuwan nan”?

Ahankali Mama tace “Riyad yakawo” kaman zata fashe sabida bacin rai tace “Mama shine zaki
karba?” Kallonta Mama tayi tace “babu yanda banyi dashi ba amman yaki yarda wai ni
mahaifiyar sa ce kodan darajan azumi na amsa, kinga uban kudin daya ijiye dane naki amsa da
kyar na zari yasake daura daya, haka ya ijiye komi anan dan ni naki karba” cikeda bakin ciki
harda abinda yamata a zaure tace “Mama shine baki kira yara kinsa sun maidamai da kayan
mota ba”? Kaman wacce aka daka kawai saita fashe da kuka sosai ta ijiye kayan data shigo
dasu daga kasuwa nan kasa ta tsallaka tashiga daki kawai tahau kuka idanunta sunyi jajir tashi
Mama tayi tabiyota ciki cikeda damuwa tace “Rashida mekuma haka da kuka? Duk mai imani
yadaga ido yaga rayuwanmu dole yaji tausayinmu, na karba badan komi ba saidai naga yaron
kirki ne hakanan zuciyana ya natsu dashi kuma bawai saurayi bane ya gayamin yanada mata
so mutum ne mai hankali ba yaro ba, saikuma dalili nabiyu shine karbansu zai saukaka miki
kema at least daganan zuwa 2month zamu manta da siyan Kayan abinci albashin dazaki samu
saimu hada da wayan nan kudin ki biya kudin school fees ragowan mu rike na asibiti, you think
I’m happy da rayuwan wahalan dakikeyi? Understand me it’s Ramadan kyaututuka haka is
normal ko na yan anguwan man sabida baki karba ne da yanzu an kawo mana, it’s okay ya isa
stop crying” Mama tajawota cikeda lallashi rabon datai kuka haka tun ranan da aka kwantar da
ita a asibiti cikin kuka tace “Mama stop collecting abu daga hannun kowa, I’m enough for you,
Mama bazan taba bari ki kwana da yunwa ba, I will never” hawaye taji yaciko idanunta saikuma

tai murmushi ta danne takai hannunta ta share mata fuska tace “I know y’ata will never allow me
to go hungry, natuba to bazan kara karban komi daga hannun kowa ba, Rashida na is enough
for me, the best daughter aduk duniyan nan, come here” Mama kawai ta rungumeta tana
murmushi she’s lucky Allah ya azurtata da y’a dake sonta haka, sun dade ahaka sannan Mama
ta dagota takai hannu ta yaye hijabin jikinta ta tana taba wuyanta tace “jikinki da zafi baki da
lafiya ne”? Ahankali tace “cikina ke ciwo kadan gobe naje asibiti zan karbi magani” cikeda so
Mama tace “sannu kinji, zauna kihuta ni zan miki girki” dasauri tace “zanyi Mama” tashi zatayi
Mama takama hannunta bawasa kan fuskanta tace “zauna kihuta” zama tayi Mama ta tashi
atampanta tafara dubawa ta yaba sannan tashiga daura musu abinci itakuma anan bacci yayi
awon gaba da ita.


Da kyar Mama ta tadata around 4 na asuba sabida suyi sahur, tariga tasan bata azumi wucewa
tayi tama Mama abincin sahur sannan tawuce bayi yau da hot water tai wanka dan zazzabi
takeji da ciwon mara but she feels she can manage dan is not that serious tana dawowa
takaima Mama itama nata ruwan zafin tashigo daki tace “muje Mama” idanunta Mama ta kalla
tace “dan Allah kina zuwa clinic kisha magana kar zazzabin nan yarufeki da kyau kinji”
gyadamata kai tayi Mama tace “barshi zan iya zuwa bayin da kaina jeki kimtsa” batai musu ba
ciki tawuce tashiga kimtsawa tasa black abaya tahada jakanta na baya saikuma ta kara
kwanciya yawanci a rashin karfi ne kafi gane Rashida is sick dan baka ganewa a baki da fuska
sabida masifa da fada, shigowa Mama tayi ganinta a kwance yasa Mama tace “namiki shayi”?
Girgizama Mama kai tace “idan naje school zanci abinci Mama karki damu” da dan damuwa
Mama tadauko mai tana shafawa hartai salla tana kwance wajen saima lumshe ido data farayi
sai kawai Mama ta barta zuwa 7 ta tabata tace “tashi kitafi school” tashi tayi ganin Mama tafara
damuwa yasa tace “laaaa Mama kinga najini garau maybe dama baccin danake ji yakara
karamin zazzabi” 200k na jiya Mama takawo da 100k nasu tasa asama tabata tace “gashi ki
biya kudin makaranta kisai yan littafan da baza’a rasa ba” kallon kudin tayi zatai magana Mama
tace “ni Maman ki aka bama kudin nan, nikuma nabaki, kaman yanda Hajiyan nan taraba mana
20k a clinic naje na siyamiki crocs consider wannan kudin haka, go and pay school fees naki
and buy textbooks dakike bukata” ayanda fuskanta kadai yayi kasan bataso ba but ganin yanda
Mama tayi yasa tasa hannu ta karba kawai tasa kudin ajaka ta goya, taja black gyale tashiga
rolling tai kyau kaman balarabiya dudda bakomi akan fuskanta sannan tace “Mama natafi” 5k
takara cirowa cikin kudinsu dabaifi 50k ba Mama tabata tace “dan Allah kihau keke yau, kici
abinci mai kyau a school kinji” gyadama Mama kai tayi tace “natafi Mama thank you” “adawo lpy
Allah bada sa’a” fita tayi tana kaiwa junction ta shiga cafe tai printing ramita, sannan tafito
tashiga keke sai bank taje tafara biyan school fees nata sannan tafito tashiga keke again sai
asibitin su, sauka tayi wuraren 9:30 taga student nasu Maimoon na hangota ta taho wajenta
dagudu tace “anyi releasing namu yau, kaman za’ayi manyan baki ne dai ance mu student
mutafi wlh” ahankali tace “really, bari na karbi magani to natafi” dasauri Maimoon tace “meke
damunki”? Dan yatsine fuska tayi tana tafiya tace “I think I’m coming down with Maleria saikuma
cramps” Maimoon tace “oh no sorry” office nasu tashiga tabude locker ana ijiye musu magani
haka tadauki na Maleria da cramps suka fito yawance Maimoon ke hiran, ahankali tace “I want
to buy food da water dazansha magani dashi” dasauri Maimoon tace “muje cafeteria” Jellof rice

tasaya da beef 800, tasai ruwa daya ganin tana bude jaka yasa Maimoon tace “mu zauna anan
kici mana” girgiza kai tayi tace “kema kawai na gayamiki ne only Mama na ke sani idan bana
azumi I don’t want people knowing kunya yake sani” dan murmushi Maimoon tayi tana kallonta
yanda take arranging abincin ajaka tana maganan she looks so cute and adorable maida jakan
bayanta tayi ta goya tace “bari naje to sai gobe” Gyadamata Kai Maimoon tayi suka fito tana
kaiwa titi tashiga keke, is just around 10 yanzu gwara ta tafi hotel tamusu aiki saita sami free
evening har gaban hotel din aka kaita ta sauka tabiya kudi tashiga ciki, direct changing room
nasu taje, saida tafara chanza kaya sannan tadan fito ganin kowa na aikinshi yan morning sun
riga sunzo tun dazu so kafin wani yadawo dakin nan cikinsu kuma probably sai idan yan
afternoon sunzo kuma, hakan yasa tadawo ta maida kofan tarufe batare data saka sakata ba
takoma ta zauna taciro rice daga bag da water dakuma maganinta ta ijiye kan long bench dake
wajen itama ta sauna ahankali sannan ta dauki abincin tabude tasa spoon tafara ci ahankali
bayamata dadi ma abincin sabida zazzabi.


Ahankali yake tafiya da shi da Munir dawasu ma’aikata guda biyu dake biyedashi abaya, akwai
some changes dayakeso ayi abinda ma yakawo shi hotel din kenan this morning, duk ya gama
nuna musu saura changing room na ma’aikatan shi corridor suka shigo suna biyeda shi yasa
hannu yabude kofan yasakai ciki yana magana yace “the lockers nakes…….” Shiru yayi ganin
yanda Rashida tawani yarda takeaway jellof rice din da ruwan yashiga tittila akasa ta tashi tsaye
da sauri daidai su Munir zasu biyoshi su shigo ciki yace “wait!” Duk kallonshi sukayi suna tsaye
bakin kofan batare da sun shigo ba strictly yace “kuje lobby” yanayinshi kawai yasa Munir yace
“okay” yajuya ma’aikatan ma suka bishi yajuyo yazuba mata ido tana kallonshi cikeda fada baki
tabude zatai magana dan akwai abinci abakinta sai kawai tai wani wawan kwarewa sai tari,
maida kofan yayi yarufe ya kalleta ganin yanda take tari kaman zata mutu yasa gently yaduka
yadauki bottle water nata daya fadi yadan zube yamike tsaye yasake kallonta tsabagen tarin
datakeyi tama kasa tsayuwa ta tsugunna idanunta sunyi jajir ga rice guda daya fito daga
hancinta alamun ba karamin kwarewa tayi ba, dasauri yataka zuwa inda take ahankali ya
tsugunna yamika mata bottle water batare dayayi magana ba yana kallon fuskanta, tsabagen
azaba sabida ga yaji a abinci ga kearewa mai kyau batasan lokacin data daura duka
hannayenta biyu saman kan nashi ba takama both hannunshi da goran takai bakinta hakanan
jiyayi jinin jikinshi ya tsaya chak jin saukan hannayenta biyu kan nashi, ahankali yadaura
idanunshi kan hannunta dake saman nashi sannan yakai idanunshi kan fuskanta da yanda
takeshan ruwan kaman yaki, tass ta shanye ruwan sannan tacire bakinta daga goran har
lokacin tana rikeda hannunshi dabatasan tayiba tana sauke ijiyan zuciya kaman wacce tagudo
daga hanyan mutuwa idanunta sunyi jaa, kusan 1min tayi tana sauke ijiyan zuciya sannan
ahankali kaman mara gaskiya tadan dago kanta tadaura idanunta akan nashi yanda yake duke
dab da ita kamshin turarenshi ya bade wajen da sauri ta maida idanunta kasa still bata sakeshi
ba, yana kallon fuskanta baya ko kyafta ido yace “can you let go off my hand now”? Dawani irin
sauri ta kalleshi saikuma ta kalli goran ruwan data rike ganin yanda ta kama hannunshi da duka
hannuwanta biyu saida taji kaman ta kurma ihu sabida kunya dawani irin sauri tasakeshi hakan
yasa ya mike tsaye ya kalli magungunan ta dake kan bench na wajen sannan yawuce kofa
haryasa hannu yabude kofan ya tsaya batare daya juyoba yace “kifito amaidaki gida, kafin ki

mutu in my building” dasauri ta kalleshi kaman wata damusa dan juyo da kanshi yayi but bai
kalleta ba yace “take days off when you feel better you can resume” yasa kafa yafita saikuma ya
tsaya yace “someone will clean the place you don’t have to, kifito akaiki gida!” Yana maganan
yawuce yafita takai almost 2min aduke a inda yabarta saikuma ta daga hannuwanta ta kalla
yanda tarikeshi saikawai taji kunya da haushin kanta sai abin yasa taji mugun zazzabi ya rufeta
tanama jin sanyi, ahankali ta lallaba ta mike tadauki jakanta ta goya abaya batare data chanza
uniform nata ta maida abayanta ba kafin wani ya sake shigowa yaganta tana chanza kaya she
will not take the risk, tadauki magungunanta tarike a hannu tafito tana tafiya ahankali hakanan
kawai sanyi taji tanaji barinma a hannuwanta dasuke abude dan uniform nasu short hands ne,
gashi small farin baby hijab ne jikinta that covers her chest only, ahankali take tafiya is as if
every step datai taking yana kara mata zazzabi harta fito lobby kadan kadan take tafita tana jin
sanyi kaman akwai kankara awajen, hakan yasa bakinta yahau kakkarwa irin na me jin sanyi
din nan kaman an sata a cold room, idanunta na rawa rawa suna kukkullewa kadan kadan take
bude idanunta tasan ta hango mutane zazzaune da suit a lobby daganan kuma batasan meya
sake faruwa ba dipp kaman an dauke wuta ta zube awajen.
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI


✍M SHAKUR


EPISODE 1️⃣8️⃣

JOIN KISSA PRO CLASS DINA WITH JUST 1500 and stand a chance to win 200k


Ahankali take bude idanunta dataji sun mata nauyi sosai kafin tagama budesu da kyar tazubasu
asaman dakin sake lumshe idanun tayi tabudesu taga drip na ruwa hakan yasa tabi dakin da
kallo da kyau, idanunta ne suka sauka kan Riyad dake zaune kan wata kujera mai kyau one
seater, wannan karan babu jacket na suit ajikinshi just white shirt da trouser hannunshi rike da
wani file yabude yana karantawa ga pen a hannunshi, faduwa gabanta yafarayi kadan kadan
hannunta daya ta daga taga anyi fixing drip hakan yasa ta daga dayan hannun takai saman
fuskanta sabida iska dataji yana shiganta da kyau jitayi babu hijabinta kan fusnanta babu dan
kwali asaman kanta, hannunta takai saman wuyanta zuwa saman riganta taji an bude boturan
saman riganta har zuwa wajen bra Allah yasa tasaka singlet sauke hannun tayi kasa tacikin
bargo taji an daga riganta da vex din sama cikinta abude ga hook na wandonta an bude
ahaukace ta tashi zaune tawani fincike drip din da aka samata taja bargon sama tana kare
kirjinta tai wani irin ihuuu tace “mekamini”? Sauke file din dayake rikedashi yana karantawa yayi
kan coffee table dake gabanshi yakalleta tareda sauke soft boyayyen ijiyan zuciya, yazuba mata
mayun idanunshi daidai lokacin tufkin gashinta ya warware black silky hair nata yawani irin zubo
half ta face nata ragowan ta baya abun just grip his attention dayasa yawani zuba mata idanu
kaman tsohon maye kaman akwai wani abu dayake kallo ajikinta, ihu Rashida tayi sosai taja
bargon tarufe har wuyanta tace “you pervert Allah ya isa ban yafemaka ba wlh mugu azzalumi

kaci amanata ta, wat have you done to me? Dame kai drugging dina? Wani substance kasa
aruwan daka bani, sabida kaga kanada kudi idan kasaba yima yan mata haka ana kyaleka wlh
akaina you’ve messed with the wrong person bazan taba kyale wanda ya batamin rayuwana ba”
gashi takasa tashi sabida yanda aka kwance hook na wandonta daidai lokacin taji an bude kofa
dasauri tajuyo idanunta sunyi jazur wata mata tagani very elderly zatakai 45 tafito daga
bathroom na dakin rikeda bowl a hannunta tace “young Lady calm down” ta taho wajen da sauri
tana ijiye bowl din da Rashida tabi da kallo taga ruwa ne da karamin towel aciki tace “calm
down no one did anything you’re sick, your fainted and Mr Riyad called, my name is Dr Amara
Kennedy, I’m this hotel’s Doctor, incase of any emergency or anything ni ake kira” tadan sauke
ijiyan zuciya tazauna bakin gadon tace “calm down, I came in immediately an kirani, you were
running serious temperature dayasa kikai passing out kina convulsing this is the result of your
blood test” tai maganan tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login