Showing 39001 words to 42000 words out of 69832 words

Chapter 14 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

778

now, mun sallameta everything has been cleared by Riyad,
ga magungunan ta nan bari namiki bayanin yanda zatasha” yashiga yima Rashida bayani
gyadamai kai tayi tace “thank you” murmushi yayi yace “Mama yarki kaman Balarabiya akwai
wani akasa ne idan babu kowa ina kam…..” kasa karasa maganan yayi sabida turo kofan da
akayi babu ko knocking duk suka juyo Riyad ne, yasaka wani ash color shadda mai haske yana
wani irin kamshi mai dadi dake banbanta shi da mutane da dama, dasauri Rashida tadauke kai
daga kallonshi mugun haushinsa takeji, takalli Mama tace “Mama tunda na hada komi bari naje
na nemo mana keke napep” kafin Mama tabata amsa ma tajuya ko kallon Riyad batayiba tabi ta
gefenshi tafice, Dr yace “ahh Riyad kaine barka da zuwa” adikile yace “yauwa” dan kallonshi
Mama tayi bata tabajin irin muryan nan tattare dashi ba, kin kallon Dr yayi yawuce wajen Mama
yace “Mama ina kwana nazo nakaiki gida” yakalli kayan dasuka hahhada yaduka ya kwasa
duka da kulolin yafice Dr yabishi da kallon Mamaki, aranshi yace “who are this people to Riyad

cus this is just more than help akwai wani abu akasa, look at the way he’s serving them”
saikuma yakalli Mama yace “Mama Allah kiyaye hanya” yawuce yafita shima, shiru Mama tayi
kaman mai tunanin wani abu sai chan tai murmusa kawai, shigowa yayi yazo har wajen gadon
yace “Mama can you walk? Ko in dauko kujera”? Dan murmushi tayi tace “haba zan iya tafiya
Riyad” saukowa tayi daga gadon ahankali tafara tafiya yana kaffa kaffa da ita dudda bawai
riketa yayi ba Mama ta rame sosai kaman iska zai kadata tafadi sunyi tafiya sun fito cikeda
kulawa yace “zaki huta Mama?” Wlh har cikin zuciyanta tajejin Riyad yanzu, he’s caring and just
too protective da sauri tace “a’a bangajiba da karfina fa muje kagani” murmushi yayi suka fito
har wajen mota baya yabude mata dayake jeep ne sai alokacin ya taimaka mata ta shiga ta
hanyar dan dukawa ya nuna mata shoulder shi yace “dafani ki shiga” kallon shaddan jikinshi
kalkal Mama tayi saikuma ta kalli hannunta dudda bawai datti bane a hannunta amman saitace
“kai haba karna bata maka kaya” ahankali yakai hannunshi yakama nata yadaura akan
shouldershi yana rage tsayi yace “Mama kibata duk albarkanki ne” ahankali Mama tai murmushi
kafin ta dafashi da kyau ta daga kafanta ta taka step din ta shiga motar yana kallonta yace “are
you comfortable Mama” gyadamai kai tayi tace “yes Riyad thank you” daidai lokacin Rashida na
shigowa hospital din tana cikin wani empty keke napep ta hangosu, azuciye ta sauko ta taho
wajen daidai yajuyo, chak ya tsaya yayi folding hannunshi a kirji tundaga kan kafafunta yake
kallo dake cikin wani bakin flat shoe daya gama mutuwa but dudda haka kafanta ya haska flat
shoe din, zuwa skirt dake jikinta na atampa da pink hijabin data saka mai hula ya tasya mata a
guiwa, tana zuwa ta tsaya agabanshi cikeda masifa tace “bakai zaka kaimu gida ba nariga na
kira keke” wani banzan kallon raini yamata yace “then saikije ki sallameshi” yanda yamata
maganan kaman ta kurma ihu mutumin nan dan bala’in rainin wayo ne sabida yaga yanada kudi
da hotel shine zai dinga ma mutane magana yanda yaga dama, wai ina ruwanshi dasu? Cikin
fushi tace “nace maka kafito mini da Mamana daga motan ka, wayasani ma ko dan yankan
kaine kai tunda sai shegemana kake” wani kallo yamata sai kawai yawuce yabude mazaunin
direba ya shiga ya zauna itakuma ta shiga kiciniyan bude kofan back sit, da hannu Riyad yakira
mai keken da sauri ya sauko yazo wajen yace “gani yallabai” kudi dayawa yazaro daga aljihu ya
mikamai yace “gashi kaje” karba yayi yahau godiya Mama tai murmushi ciki ciki dan duk tana
kallon draman tai kaman batasan sunayi ba making sick and tired face, danna glass na window
tayi takalli Rashida dake tsaye tana kallon Riyad kaman zata iya fada dashi akace tayi, Mama
tace “shigo muje kina batama Riyad lokaci zaije aiki fa Rashida” kallon Mama tayi har idanunta
sunyi ja akufule tace “kuje ni bazan shiga motan ba” Mama na kallonta tace “zan saba miki fa
wlh, zoki shiga mota muwuce” kallon Mama tayi bataso ta batama Mama rai yasa ta danne
zuciyanta da kyar ta zagayo harta bude kofan baya Mama tace “tunda ga direba kin samu ko
dole ki shigo baya” wani sweet smile Riyad yasaki ya gyara fuskanshi da sauri yana kallon waje
kaman baisan anayi ba, kaman tayi ihu Rashida ta maida kofan tarufe takoma gaba tabude
kofan ahankali tadan kalleshi ganin waje yake kallo abinshi yasa da kyar tashiga ta zauna ta
jawo kofan tarufe tana harare harare, murmushi yayi yatada yajuyo yadan kallo Mama da
tausassan murya yace “Mama are you comfortable? Natada motan” wani irin murmushin dadi
Mama tasaki tace “I’m comfortable d’ana muje” wani irin zafi Rashida taji aranta yanda Mama
takira Riyad danta kawai saita ciro wayanta ta manna earpiece tasa a kunne, tada motan Riyad
yayi suka tafi baya wani gudu sosai, Mama sai hira takemai kaman tasanshi hakan yakara
tunzura Rashida dudda batajin mesuke fadi but tana ganin bakin Mama na motsi, har

anguwansu hira suke sai kallon motan ake a kofar gidansu yayi parking ya bude kofa ya sauko
yabude baya Mama ta sauko ahankali yabude booth ya kwaso bags nasu Mama tace “key na
bakin jakan” takai hannu tasa blavk jakan aljihun taciromai tabashi yana sane yasan bata iya
bude kofan motanshi ba ya shareta shiga da Mama ciki yayi sai kallon gidansu yake koina a
gyare tsaf zaunawa Mama tayi yace “bari naje Mama Allah kara sauki” Mama tace “nagode
nagode Allah maka Albarka, wai ina Rashida ne hala ta wuce wani waje” baice komiba yawuce
Mama tabishi dagodiya dayake motan tinted ne baya iya ganota but yaga yanda motan ke
motsin ana bubbugata yayi kaman bai saniba yawuce yabude kofa yashiga ya zauna batare
daya kalleta ba yace “wat are you still doing in my car”? Akufule tace “inba dole ba mema zai
kawoni cikin your so called car”? Still yaki kallonta yace “get out!” Kaman yana magana dawata
dabba kirjinta tafarfasa yake tace “ka budemin kaga idan nakara wani numfashi a motan naka”
dan kallonta yayi strictly yace “who are you to make Riyad work for you”? Mamaki ne yakashe
Rashida irin what exactly guy din nan thinks of himself ne, tadai daure ta danne zuciyanta da
kyar tace “to ai ban iya bude kofan bane ni” dan juyowa yayi yayi facing nata yace “then learn to
soften muryanki and ask for help politely miss” ido cikin ido take kallonshi ya zubamata mayun
idanunshi dayasa kawai taji jikinta namata wani iri, duk yanda taso ta daure tacigaba da
kallonshi itama saita kasa tadauke idanunta dan kasa jure kwayar idanunshi tayi, ta hadiye wani
abu da kyar dataji yaa tsayamata a wuya tadan runtse idanu kai kasan she’s about to say
komene zatace ne out of compulsion tace “kadan budemin kofan motan nafita” sosai yake
kallonta sabida yanda kawai yaji muryanta pierce his heart, this is the first time tunda ya santa
takemai magana softly but da gangan dan ya kureta yakaita bango yace “soften your voice
more and add please cus no one command Riyad!” Da sauri ta kalleshi wani kallo yamata na
idan baki fadi ba zanja motata nayi gaba abuna, kaman tayi ihu takeji shine namiji na farko so
far so good tunda ta girman nan ya iya tankwarata yakuma juyata haka, batasan mesa ba
batakaimai duka ko kokawa ba the normal ita datuni takaimai duka suyi dambe but shi takasa,
agogon hannunshi yakala kirar TAG Heuer yace “you have 5secs left ko i will go wherever zani
u will be here is none of my business” yayi maganan yana kunna motan ma abinshi, wani ijiyan
zuciya ta sauke ta sauke muryanta kasa kaman ba ita ba sounding like a Baby tace “kadan
budemin kofan motan” dan juyo da kanshi yayi ya kalleta muryanta is the best muryan mace
daya tabaji in his entire life, yanda yake mata wani irin kallon yasa ahankali kaman ba itaba lips
nata na rawa rawa tace “p……..p….lease…..please!” sannan ta dauke kai da sauri kaman tai
abin kunya din nan, sabida son yakaita bango gabaki daya shikuma annoyingly and
authoritatively yace “good gurl!” kaman wata damusa ta kalleshi for the first time Riyad yasakin
mata wani kalan murmushi dayasa taji zuciyabta yabuga rasss! Yana beating dum! Dum! Dum!!
Da sauri ta dauke kai trying to control yanda zuciyanta ke beating takasa, dan tasowa yayi daga
sit din dayake ta gefen ido taga ya nufota da sauri ta juyo da kanta ta kalleshi dan kaman zai
hugging nata, hada ido sukayi gashi yaki daina kallonta kaman akwai wani abu dayake son gani
game da ita sai kawai lips dinta yahau rawa tawani koma baya da sauri ta manne jikin kujeran
kaman zata nitse ciki har hannunta rawa yake barin yanda kamshin turarenshi ke shiga
hancinta jinshi dab da ita infact yadin kayan jikinshi ke tabata ta she was scared, lost, shaking, it
was just a freaking reaction jikinta keyi dabatasan na me ba, he could feel heartbeat dinta, he
could clearly see kwayan idanunta, this whole fadan nata is just an act! A mask! Hannunshi
yakai ahankali kaman baiso yabude kofan still looking at her ya bude kofan tareda komawa seat

nashi ya zauna bude idanunta tayi da sauri he was expecting tamai rashin kunya but saiyaga
duk ta dimauce ta sauka da sauri kawai ta maida kofan tawuce ta shiga gidansu da sauri sai
kawai ya girgiza kai yatada motan yawuce yabar anguwan.
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI


✍M SHAKUR

EPISODE 1️⃣7️⃣

KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA
AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA?
MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI
SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA

CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461

Tana shiga gıda Mamag tace “ke kuma an ina kika tsaya?” Ahankali tace “waje” kawai tashiga
ciki zata kwaso kayan abinci dan daura girki Mama tace “kibar girki inada abincin da Riyad
yakawomin har yanzu da zafinsu a kula shi zanci, kizo kije school daganan ki wuce aiki, Riyad
yace kidawo” dasauri tafito daga dakin ta kalli Mama tace “Mama nifa yau na dauki permission
bazanje school ba” saikuma ta taho ta zauna wajen Mama tace “Mama wai kinsan mutumin
chan ne”? Mama na kallon kwayar idanunta tace “wani mutumin”? Cikeda mugun hali tace “shi
wannan mutumin daya kawomu naga kunatayi kaman daman kunsan juna ne tun chan” dan
murmushi kadan Mama tayi tace “a’a amman kawai zuciyata ya natsu dashi kaman na sanshi
daga wani wuri, kema kinsan dawuya nake natsuwa da mutane amman shi kawai yayi fuce
araina, mutumin arziki ne mutunci da dattaku, yanada halaye da dama nagari, bantaba gani a
idanunshi yamin kallon mai wata cuta ba, gakuma yanda yabiya kudin asibiti akamin komi,
wanda yamaka Akhairi kasoshi” ranta adan bace tace “Mama ni na tsaneshi” baki Mama tasaki
tana kallonta ganin da gaske take, yunkurawa tayi tace “kuma konawa ya kashe miki a asibiti
saina biyashi alkawari ne ko zanyi shekara dari ina neman kudin” dan dariya Mama tayi tace “zo
ki juye abinciccikan ki wanke kulolin nidai fitina’u” wucewa tayi ta kwasa batai musu ba haka dai
tai aikin komi Baba Liman ma yashigo gaida Mama wuraren 1 ta shirya ta tafi aikin sabida
yanda Mama tace “saitaje” ga mamakinta ko kallon banza Madam bata mata ba hakama sauran
ma’aikatan dudda bataga Hussy ba, kin zuwa office na Riyad tayi tadaiyi duka ayyukanta idan
tana gaban desk aka kira ana neman cleaner a so so room ta taje, harta tashi by 6 bata ganshi
ba bakaramin dadi tajiba ta tafi gida.

Washegari da sassafe ta tafi hospital nasu yau pediatric surgery departmant zasu to watch not
to do itada team dinta zasu, direct tawuce inda suke ijiye bags nasu ta ijiye aka dan musu
lectures kadan sannan tawuce tashiga shirye shiryen shiga surgery tsayawa tayi tana wanke
hannunta wata tazo itama ta tsaya kusada ita tai murmushi tace “Hi” saikuma ta kalli Labcoat
nata tace “Rashida I’m Maimuna but Maimoon ake cemin, tun ranan monday nake noticing naki,
can we be friends pls”? Dan tsayawa Rashida tayi tana kallonta like a weirdo dasauri Maimoon
tace “please” dan lumshe ido Rashida tayi yarinyar seems very cool and calm ahankali tace “I
don’t know yanda ake friendship gaskiya” murmushi sosai Maimoon tamata tace “I know and I
will teach you, let’s go” shiga cikin operation room din sukayi duk hannayensu a sama aka
sassaka musu handglove ga yaron da za’ama operation din da baifi shekara biyar ba anyi
sedating nashi shigowa surgeon din yayi wanda Babba ne bawai yaro ba aka samai nashi
handglove din yawuce surgical table din student Doctors din dasuke su bakwai duk suka tsaya
a gefe, Dr yace “yaron nan dake kan table din nan nada hydrocele wazai gayamin procedure da
zanbi in this surgery, and ya sunan surgery din”? Maimoon ce tafara daga hannu tabata amsa
yace “wrong” almost dukansu saida suka bada amsa yace “wrong” yakalli Rashida dabatai
magana ba dan ita bata show off ko a aji, yace “make attempt miss” dan ijiyan zuciya ta sauke
Rashida confidently cikin turencinta that is good muryanta kuma makes it sweet a kunne tace
“zamuyi Hydrocelectomy surgery to remove the hydrocele daga scrotum din, zamuyi making
incision anan…..” tafara bayanin procedure din da sai kawai Dr ya tsaya yana kallonta exactly
abinda zaiyi tafadi kaman ta tabayi, hannu yamikama head nurse yace “scalpel” samai wuka
akayi a hannu yarike yadauki marker yamikama Rashida yace “come close” ahankali ta matso
kusada surgeon din gabanta nadan faduwa yabata marker yace “draw the line” karba tayi
ahankali taja, to her biggest shock yace “make the cut” dasauri ta kalleshi, confidently yace “I’m
here you won’t make a mistake so go ahead” dan tsayawa tayi Dr yace “we all start ahaka, go
for it, I’m right here ina kallonki” bismillah tayi ahankali ta karba tana kokarin kallon fuskan yaron
yace “don’t look at his face” ijiyan zuciya ta sauke tareda rufe ido what is her biggest motivation
da inspiration na son zama likita? Ahankali tace “Mama! I want to become the best Doctor for
Mama! I want to make research nagano yanda ake curing HIV for Mama! I want to make Mama
better, I want to be the best Dr in Nigeria da kewaye da al umma zasuyi alfahari dasun samu”
daidainan tabude idanunta kawai tashiga cutting Dr na tsaye kusa da ita yace “suction” aka
kwashe jinin, wasa wasa da shi da Rashida sukai surgery din nan tass yasake barinta tai
stitching yaron up, her stitching style kadai saida ya kalleta almost 10yrs yana aiki in this
surgery student Doctors daban daban interns but baitaba ganin skilled yar baiwan Dr like this
girl ba ita kanta for now bama tasan wacece itaba imagine abinda take iyayi in year5, sallaman
su yayi yakalli Rashida yace “makesure you become a surgeon Doctor R” dan sunnar da kanta
tayi batare datai murnushi ba cus she hardly smile outside tawuce tafita Maimoon tabiyota tace
“wowwww you are amazing Rash kai! I can never do that” ahankali tace “thanks” dasauri
Maimoon tace “let’s go grab some drinks” wayanta Rash taciro daga jaka taga 2:30 tace “ohh no
I have to go to work” taciro log book dinta da sauri tawuce taje aka mata signing tajuyo takalli
Maimoon tace “gobe” bata jira amsanta ba tajuya dasauri Maimoon ta tsaya awajen tai shiru
tana kallonta, tace “she’s unique, Bilal you loose a rare gem”. Wajajen 3 takai hotel din dan
saida ta tsaya tai salla tana shiga tawuce changing room tafito kenan saiga Madam tace “yanzu
ne lokacin zuwa aiki i will deduct 5k from salary naki” sauke kanta tayi kasa tawuce tashiga aiki

thank God yau Friday gobe ba aikin, tass tagama aikace aikacen ta wuraren 5 Madam ta kirasu
hall duk suka wuce, abinci tagani an kakkasa buhun shinkafa, jarkan mai, indomie, madara da
milo sugar sai gero da taliya tace “kowa ya tafi da abincin azuminshi gida courtesy of Oga” sai
murna ake, tunda tafara aiki dasu da Ramadan ana basu abinci last year an bata is not new
thing amman saitakeji yanzu kaman karta dauka sabida Riyad but kuma idan bata dauka ba
za’ayita surutu daman ance tanada girman kai, Madam tace “zansa security su taya kowa fita
da nashi sai kuje ku kira keke, Happy Ramadan to everyone” ihu duk sukayi ana shouting thank
you Ma sannan ta sallamesu wucewa tayi ta chanza kaya ta goya jakanta tafito taje ta taho da
keke tana zuwa security suka tayata lodawa abayan keken ta tafi.

Yau sunday tana so taje kasuwa tadan yo musu yan kananun cefenen azumi tunda batada aiki
yau, atampa tasaka green shima ya kwana biyu tadau wani black hijabi ta daura asama mai
hula ya tsaya mata a knee aiko yamata kyau tafito falo inda Mama ke zaune tana kirga kudinsu,
zuwa tayi kusada Mama ta zauna Mama tace “yauwa kin shirya”? Gyadama Mama kai tayi,
kudin da Mama takasa agabanta kashi biyu ta dauki me yawan tabata tace “ga wannan kudin
dubu talatin ne nakine kisai dan atampa da takalmi da yan kayan kwalliya da turare kema kiyi
kyau da salla kuka dawo sai akai dinki ko” dasauri ta maidama Mama kudin tace “Mama bana
bukatan kayan salla, kayan danake dasu zan iya sawa da salla, Mama we have important
things to do, drugs dinki, abinci, school fees dina dakuma kudin da mutumin chan ya kashe na
asibiti ni sai na biyashi”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login