Showing 30001 words to 33000 words out of 69832 words
wazai shigo
bakuwa tayine saitaga Rashida sosai gabanta yafadi ganinta cus bata taba ganin Rashida ta
shigo gida around this time ba, kallo daya ta mata tagane tai kuka dawuya ne Rashida tama
wani abu tai kuka, ita kadai ke iyasa yarta kuka dasauri ta ijiye tray shinkafan tace “lafiya
menene kika dawo dawuri haka?” Murmushi ta kakalo tace “Mama kaina ke ciwo sosai saisa
nadawo” tai maganan tana zama kusada Mama kanta Mama ta taba tace “bari na kawo miki
vitamin C kisha tashi ki cire jallabiyan kisha iska” tashi tayi tawuce ciki Mama tabi jakanta dayay
strange girma da kallo sai kawai ta jawo tabude ganin karikitan ta ne ciki yasa da sauri ta tashi
tabita daki tana tsugunne gaban ganamasgo tana neman kaya Mama tace “an koreki wajen aiki
ne”? Dago kanta tayi ta kalli Mama zatai magana Mama tace “karki kuskura kimin karya an
koreki daga wajen aiki ne?” Ahankali tace “Madam dina tace yau ne last day na aiki na a hotel
dinsu” waje Mama tasamu dasauri ta zauna jin jiri zai dibeta tace “Meya faru tell me everything”
Mama tariga ta ganota hakan yasa tafadima Mama komi ba karya, ba karamin baci ran Mama
yayi ba tace “sau nawa zan gayamiki ki dinga hakuri arayuwa Rashida eh? Zagi na kari ne?
Koko zagi na nunawa ajiki ne? Dan an zageni sai mene” dasauri Rashida ta kalli Mama, Mama
tace “yes dan wata ta zageni and so wat dazaki hau fada awajen aikin ki kina hankade Madam
dinki har sau biyu mai hotel din gabaki dayama shima kinmai rashin kunya” ahankali takai
hannu ta goge hawaye tace “Mama bazan iya daurewa azageki agabana ba ko ace wani abu
mara kyau wlh” saikuma tarushe da kuka tace “narasa me nayima yan layin nan duk inda nake
aiki sai sunsan yanda sukayi sukaje suka batani su fallasani, wlh kowaye meyi ban yafemai ba”
tabama Mama tausayi amman kawai saita wuce tabude drawer tadauko hijabinta har kasa ta
saka da sauri Rashida ta mike tace “Mama ina zaki?” Cikin dan masifa tace “ina zani? Ina kuwa
zani inba wajen aikin naki ba naje nabada hakuri itama yarinyar a nunamin gidansu naje
nabada hakuri, idan babu aikin nan tayaya zaki gama makarantan ki eh? Me zamuci? Dame
zaki sami kudin siyan tufafi? Ga wayanki ta lalace baki dawo da itabama that means bata
gyaruba duk ina zamu samu kudin nan kafin kisami aikin nan kin manta kalan wahalan dakikayi
eh? To zuwa zanyi nabada hakuri” dasauri ta taho takama bakin hijabinta tace “Mama dan Allah
dan Allah karkije kinji Mama” fizge hijabinta Mama tayi tace “inda bakiso kisani naje nabada
hakuri ai da bakiyi abinda zai tursasani inje ba, yau ko basu karbeki ba dolena naje na bada
hakurin abinda kikayi kinma mutanen dake gaba dake reni sannan kin fasama yar mutane hanci
da baki” baki Rashida tabude zatai magana Mama ta nunata da hannu tace “kimin shiru anan”
ta fiziğe hijabinta tajuya tafita fuu Rashida nada zuciya so tasan yarinyar didn’t even realize how
important this work is to them most especially towards karatun ta she will do everything ta
tabbatar Rashida tagama karatun ta lafiya.
Kafa Mama tasa ahanya tana tafiya ahankali kanta na sarawa amman ta daure cus she knows
what school din Rasheeda means to her, she will not allow her to sabotage mean na school
fees payment nata ba, she just hopes darajanta zaisa sumata afuwa.
Tanakai junction ta tare keke da taso taje da kafa ne, amman taji jiri na dibanta bazata iyaba,
har hotel din aka kaita ta sauko tabiya kudin tajuya ta kalli tamkeken hotel din almost duka inda
Rashida take aiki ta sani musamman take binta dan tasan inda diyarta ke aiki incase wani abu
yafaru she knows inda zataje neman diyarta amman bata taba shiga wajajen aikinta ba, ijiyan
zuciya ta sauke jin yanda heart nata ke beating saita dan natsu kafin ta shiga building din
motoci cike anyi parking, hotel din yahadu bana wasaba, karasawa tayi zuwa entrance door din
zata shiga from yanda take looking security guard dake gadon kofan shiga reception din yace
“Hajiya wakike nema? Idan zancen taimakone Oga yace jibi ranan juma’a za’ayi rabon abincin
azumi you can come by 10AM” ahankali Mama tanuna kanta tace “nine Maman Rashida
sannunku da aiki, Rashida na aiki anan maybe kasanta, to tayi laifi ne shine nace bari nazo
nabawa Oganta hakuri dan Allah akomar da ita sannan nabama yarinyar hakuri” kallon Mama
sukayi sannan suka kalli juna kafin daya ya nuna mata kujera dake chan gefe wani plastic chair
yace “guest da ma’aikata kadai ke shiga ciki jeki zauna achan Oga nada baki amman zai fito
anjima kadan sai a gayamai” Mama batai musu ba tace “toh” wucewa tayi zuwa kujeran dasuka
nuna mata ta zauna tabuga tagumi tai shiru burinta kawai karsu kori Rashida addu’anta kenan,
gabanta sai faduwa yake cikeda fargaba.
Tunda yaje office nashi yayi shiru bakin dasukayi ma yawanci Munir ke kulasu, agogon
hannunshi kiran Rolex ya kalla 5 tayi na yamma kaman an tsikaresh ya mike duk kallonshi
sukayi “excuse me” yafadi tareda wucewa wajen kofa yafice Munir yabishi da kallo kafin
yacigaba da abinda yake samin kanshi yayida shiga elevator ya sauka kasa, he doesn’t even
know why he’s doing this but samun kanshi yayi da zuwa hanyar changing room din ganin kofan
wangale abude yasa yadan leka ciki babu kowa wajen fuzar da iska yayi yajuyo yafito daidai
Madam zata shigo hanyar chak ta tsaya ganinshi surprisingly tace “Yallabai wani abu kake
bukata”? Kaman bazaiyi magana ba saikuma yace “where is she”? Kallon hanyan Madam tayi
tace “wa she? Oh mahaukaciyan nan”? Dan lumshe idanu kadan yayi hakanan yaji kalman
azuciyanshi yadai daure bai nuna wani abuba ya kalleta, dasauri tace “ta tatare kayanta ta
kwashe komi na locker ta tatafi tabar aikin da kanta kafin mu mata official kora” yanda taga
yahade fuska yasa dasauri tace “sorr….” Ahankali yace “sack the other gurl Hus….” Cikeda
Mamaki Madam tace “Hussyn Yallabai”? Babu wasa akan fuskarshi yace “I don’t want her
working for my company, just compensate for the injury, give the other gurl a call tadawo aiki”
yana maganan yawuce baki Madam yakasa kulluwa tana kallonshi, yarinyar data barar da ita
yake cewa akirata back, wacce aka jibga yayi sacking, dan ijiyan zuciya tasauke aranta tace
“his company his rule!” Tawuce ta tafi office nata.
Wucewa kawai yayi yabar wajen yafito, security daya budema wani guest kofa dazai shigo ne
ya hango yallabai hakan yasa yashigo ciki da gudu daidai zai shiga elevator yace “Yallabai
barka da hutawa dama wata mata ke nemanka awaje” wani kallo Riyad yamai irin wata wa? Shi
kuwa? Dasauri security yace “tace wai itace Maman yarinyar da aka kora tazo tabada hakuri
tana waje, she’s Rashida’s Mom Sir” hakanan Riyad kawai yaji gabanshi yafadi but yadaure
yace “why is she sitting outside?” Dan sauke kanshi kasa Security yayi yace “uhmm Yallabai
cewa akayi cutan kanj……” fuuu Riyad yawuce zuwa entrance door din kafinma abudemai
kofan dayake glass door ne yana iya hangota yanda tazauna kan kujera tayi tagumi tana kallon
waje daya cikeda tsananin damuwa and kana kallon matan kasan she’s really sick she looks so
skinny and pale jiyayi zuciyanshi yamai ba dadi sosai yanda security sukai trashing nata awaje
haka, dasauri yafice bayan an budemai kofan yayi wajenta direct yana zuwa kawai saiya duka
cus bemasan mezaiyi ba, she’s the mother of the girl that save his life kome yayi bai biyataba,
cikeda girmamawa yace “Mama” firgigit Mama tadawo daga dogon tunani datake tajuyo ta
kalleshi, dasauri tace “Naam Bawan Allah kaina mai wajen nan nazo nabada hak…..” kafin
takarasa maganan dasauri yace “Mama” hakanan Mama taji yanda yakirata yataba zuciyanta,
yanda yakira sunnan just touched so many things a zuciyanta kawai sai hawaye, life and
sickness nata have made her so emotional, muryanta na rawa tace “dan Allah dan Allah kuya
kuri nasan Rashida da zafin zuciya ga fada ga taurin kai, kome akace tama yarnyar nan nasan
tayi dan Allah kuyakuri kurufamin asiri kada ku koreta daga aikin nan dan Allah ku taimakeni” tai
maganan tana jan kujeran baya zata duka dasauri Riyad yakama knees nata ahankali yace
“Mama dan Allah karki rokeni, ban koreta ba zata iya cigaba da zuwa aiki” da sauri Mama ta
kalli fuskanshi tace “da gaske?” Gyadamata kai yayi yace “eh” ijiyan zuciya Mama ta sauke tace
“to inane gidansu yarinyar naje na bada hakuri” ahankali yana sakin knees nata yace “basai kin
bada ba lafiyanta kalau Mama, is just normal misunderstanding da kananun maganan yara
yajawo fadan kada ki damu kinji” gyadamai kai tayi tace “Allah maka albarka” murmushi yamata
kadan baice komiba, Mama tace “bari natafi gida to Alhamdulillah nagode nagode nagode kaji”
daga yanda take maganan kasan hankalinta ya kwanta gyadamata kai yayi, Mama tace “to sai
an jima” “saida safe Mama” yafadi ahankali, Mama ta wuce cike da farin ciki tafara tafiya kadan
kadan sabida yanda kanta ke sarawa, tayi tafiya daya biyu uku ana hudu kawai ta yanke jiki
tafadi, Riyad na tsaye yanama security magana sukaji karan fadin abu juyowa sukayi ganin
Mama yasa dawani irin gudu Riyad yayi wajenta suma security din haka dago kanta yayi yana
tapping hannunta yana kiranta. “Mama Mama Mama” amman shiru dasauri yace “help me”
daukanta sukayi yabude bayan motanshi yasata yakoma yashiga gaba yatada motar sai wani
babban private hospital dayake zuwa anytime yake Kano yana zuwa aka karbi Mama sai
emergency yawuce office na Dr dinshi ya shiga Dr ya sallami patient dayake tareda shi yace
“Ranka shi dade mai Martaba” dan yatsine fuska yayi yace “don’t call me that I have a patient
tana Emergency I want you to be on her case fast” tashi Dr yayi suka fito tare ya shiga
emergency din, shi ya tsaya agaban wajen yarasa yanda zaiyi sai kuma yakoma office na Dr ya
zauna, yana nan zaune yana jiranshi har aka kira magrib saiya tashi yafito yawuce mosque
yana gani Munir na kiranshi yaki dauka salla yayi yafito yawuce ciki yakoma office na Dr
yazauna sai gashi Dr yashigo dasauri Riyad yatashi yace “how is she ta farfado?” Gyadamai kai
Dr yayi yace “da kyar muka samu ta farfado amman tana bacci” saikuma ya zauna ya kalli
Riyad yace “kasan wacce ka kawo? Who is she to you?” Batare daya amsashi ba yace “does
that matter? Meke damunta? How can I help?” Gyara zama Dr yayi yace “she’s HIV patient!”
Yayi maganan yana kallon fuskan Riyad dayaga bai chanza ba saima yace “me da me take
bukata yanzu”? Ahankali Dr yace “is like she’s on medication so bahsine abinda ke damunta ba
bashine kuma dalilin yankewan jikinta tafadi ba, abinda yafi komi damunta is BP, BP ta yayi
raising sama sosai I don’t think zan sallameta yau ko gobe ko jibi ma sef, sai ya sauko sannan
zan sallameta, just get wanda zai zauna da ita and then drugs” yashiga rubuce rubuce duk
Riyad na kallonshi saida yagama komi sannan yanunamai takardan, tashi Riyad yayi yazaro
wallet dinshi ya ijiye akan table din cikeda izza yace “take any amount kake bukata for drugs,
bills, pin is 6648” yana maganan yawuce yafita akasaitance yasauka kasa dakin dayaga an
shiga da ita yawuce shiga yayi ahankali ya tsaya bakin gadon an cire hijabinta daga ita sai riga
da zani da hulan dake kanta an samata drip, shiru yayi yana kallonta sannan yajuya yafice daga
dakin yawuce yaje motanshi yashiga yadau wayanshi yana shirin kiran Munir wayanshi yashiga
ringing Munir dinne yana dagawa kafin yayi magana yace “Munir open file na employees dina a
desktop get info na Rashida I need address nata ASAP” kafin yayi magana ya katse wayan yayi
shiru chan saiga Munir din yakira yace “suna Ranji, wajen tudun Murtala” baimasan inane wajen
ba but haka ya katse wayan ya kunna google map yashiga driving….
Tunda tai magrib ta zauna tai shiru tana mamakin ina mama taje harta dau hijabi kota bita hotel
dinne ko wani case dinne akeyi achan but karta kara bata ran Mama taje wajen hakan yasa ta
daure ta hakura, kuma zai iya yuwa tadawo takai karanta wajen Baba liman ne dantana haka
wani zubin hakan yasa ta zauna adaki zugum kaman wata marainiya idan aka kira isha’i bata
dawo ba zatasa Hijabi taje ta nemeta….
Shigowa layin yayi ga majalissar maza gaban shaguna ana zance rage wutan motan yayi karya
haskosu yana karasowa yakashe motan kawai ya bude ya sauko yazo wajen yamika musu
hannu yace “Assalamu Alaykum” atare duk suka amsashi suna karban hannunshi ganin arniyan
motan dayake ja, yace “dan Allah tambaya nake” dasauri sukace “Allah sa mun sani” anatse
yace “gidansu Rashida nake nema” tsit wajen sukayi kaman ba su ba saikuma daya daga cikin
samarin yatashi yace “bismillah yallabai zomu kebe mana” binshi Riyad yayi sujkaje wajen mota
kaman mutumin arziki yace “nasan ba laifinka bane Rashida kam nada kyau Masha Allah
yarinya kaman Balarabiya amma dai kyan dan maciji ne, yanda muke gayamaka dinnan haka
muke gayama duk wani saurayi dazaice zaizo nemanta hakkinmu ne na yan unguwa, hakkin
makotaka tunda su basu fadin gaskiya” tunda yafara magana Riyad yaji ranshi na baci amman
ya daure dan he wants the address, mutumin yace “kagadai uwar yarinyar nan fasika ce garin
kwashe kasheta ta kwaso kanjamau Rashidan ma muna kyautata zato tanada shi tun acikinta
tasam….” “Zaka fadamin adreshin ko bazaka fadi ba”? Riyad tafadi sounding bitter and angry
baki mutumin yabude zaiyi magana Adamu mai chemist da tun zuwan Riyad ya hangoshi daga
chemist yace “kaje chan kasan layi zakaga gida mai jan kofa nan ne gidansu Rashida” kallonshi
Riyad yayi yace “thank you” yawuce yakoma mota yatada mota yabar wajen, gaban gida mai
red door yayi parking ya sauka ya tsaya gaban kofan yakai hannu yayi knocking, Rashida na
zaune kan dadduma taji ana knocking hakan yasa ta tashi dasauri batare data cire pink hijab
dinta ba tafito silipas ta zura gabanta sai faduwa yake ta taho zaure tana mamaki Mama ta kulle
kofan ne dazu dan idan aka rufe yana shiga jam, ganin kofan abude ga wani arnen black car
parked agaban gidansu wani mutumi a tsaye yajuyama kofan baya so bata ganin fuskanshi
yasa ta fito kai tsaye cikin muryanta mai bala’in dadi tace tace “kaine kai knocking wa kake
nema?” Har cikin zuciyanshi yaji sanyin muryanta hakanan, cikeda wani irin kwarjini yajuyo
yana zuba hannun cikin aljihun rigan dake jikinshi, hada ido sukayi ta kalleshi ido cikin ido dan
akwai wuta a kofar gidansu mamaki da tunani yacika kanta, ba mutumin nan bane mai hotel
dinda take aiki ba? Ko idanunta gizo yake mata? How is he agidan su? Ganin ya tsaya yana
kallonta bayako kyafta ido yasa tadan dauke kai tattare bakin hijabinta tashigayi tana tabawa
saikuma takai hijabin bakinta, saichan tacire, saikuma chan ciki ciki kaman an sata dole
ahankali tace “ina yini” he’s looking at her mostly sabida baisan mezai fada mata ba, chan yace
“Mama wants to see you” hakanan gabanta yayi bala’in fadi dasauri ta kalleshi baki tabude zatai
magana saita kasa sabida yanda kirjinta ke bugawa da gudu da sauri sai kawai ta tsugunna,
wani irin tausayi yaji tabashi yakasa cemata komi, da kyar kusan 30sec sannna ta mike jin
tadawo daidai cikeda karfin hali tace “ina Mama wat happened to her? Nace mata kartazo
tabada hakuri but taki jina, normal Mama da tuni tadawo, tana ina yanzu? Just tell me wat
happened to my mother mekuka mata? Me kuka gaya mata? My Mom is very sick, tell me tana
ina yanzu?” Tai maganan hawaye na cika idanunta harwani kyalli suke adake still kallonta yake
yace “she’s fine now but tana hospital” hannuwanta biyu ta daura a fuska saikuma ta juya takai
hijabinta ta goge fuskanta tass tajuyo ta kalleshi da jajayen idanun hijabinta daya jike da kuka
ya kalla sannan yakalleta, cikeda dauriya da karfin hali tace “inane asibitin bani address din
natafi” batare dayay magana ba yajuya yace “get few things da Mama zata bukata lock the
house I will take you there is late bazakije da kanki ba” yayi maganan authoritatively yawuce
yabude motan ya shiga gaba, kallonshi tayi sai hawaye sai kawai tajuya takoma cikin gida,
drawer tabude takwaso simple t-shirt tasa ajaka tadaga kayansu ta dauko ledan duka kudin
dasuke ijiya 139k, tadauki dadduma da zanin gado wankakke tasa ajakan bayanta takashe
wuta tafito sai goge hawayenta take tarufo kofan waje tasa key sannan tajuyo ta kalli motan,
bata taba shiga mota babba haka ba, ahankali yakawo hannunshi yabude kofan ganin yanda
take kallon motan kaman matsoraciya, daurewa tayi ta matso ta shigo ta zauna agaban ta
maida kofan tarufe wani sanyi da kamshi na dukanta ta rungume jakan a hannunta gam.
Tada motan yayi ahankali sannan yafara tafiya bini bini tajuyar da kanta takalli gefen window
tana goge fuska, sunyi tafiya na kusan 30min sannan sukakai asibitin da saida ta firgita ganin
kyanshi dan tasan zaiyi tsada tayaya zata biya kudin?
Parking motan yayi yafito, kokarin bude kofanta tashigayi tafito takasa, cus ba irin normal kofan
mota data saba dashi bane, abinma yana nema yakarasata kuka ta daure ganinshi ya zagayo
ta inda take yana kallonta ta glass dan wannan motan ba tinted bane, bude mata kofan tayi da
sauri ta sauko batare data kalleshi ba ta tsaya gefenshi dan nesa dashi maida kofan yayi yarufe
sannan yafara tafiya tabiyoshi abaya da saurinta suka shigo cikin hospital din har zuwa dakin da
Mama take kwance kafinma yasa hannu yabude kofan da sauri tasha gabanshi ta rigashi tura
kofan tashiga ta tsaya chak tana kallon Mama dake bacci an samata ruwa an makala mata
wasu abubuwa a hannu yarda jakan dake hannunta tayi awajen tawuce dakin da gudu taje inda
Mama take kawai ta kwanta jikin Mama ta manna fuskanta akan wuyanta tana kuka sosai
wanda babu kara idanba ka kalli kakkarwan da