Showing 12001 words to 15000 words out of 69832 words

Chapter 5 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

774

Munir wanda da dan tafiya sai gaidashi
ake bai amsa kowa har gaban flat din tsayawa yayi jimmm awajen sai chan yasa hannu yabude
kofan da sallama ahankali hada idanu yayi dawata mata dake zaune a falon sanye da hijab da
charbi a hannunta kaganta kaman ita tai kakinshi ta tofar sunyi kama sosai, itama tanada haske
kaman shi, sauke kanshi yayi kasa da sauri sannan ahankali yashiga ciki tareda maida kofan
yarufe yama kasa magana, tadade tana kallonshi sannan tasauke kanta kasa tace “Munir
nasama kaje ka sameshi” gyadamata kai yayi sai chan kaman me tsoron magana yace “ina
kwana Mami” batare data kalleshi ba tace “yajikinka dafatan basu maka komi ba”? Dan dago
kanshi yayi yakalleta ganin kanta akasa yasa shima ya maida kanshi akasa yace “I’m fine”
daidai lokacin Munir yaleko daga sama daure da towel yace “ina fitowa daga bayi naji kamshin
turarenka wlh daukomana breakfast kataho dashi” mugun kallo yamai saikuma kawai yawuce
dinning din yazauna yana bude warmers din saman table din, ganin shayi dayaji kayan kamshi
mai zafi dasauri ya zuba a cup ya debi waina da pepper soup yadade rabon dayaci traditional
food kawai yahauci bini bini Mami na dago kanta tana kallonshi dudda yabama falon baya,
sosai yakecin abincin dan yanada ci yana cikin ci wayanshi yahau ringing ganin Mom yasa

yahadiye wainan bakinshi da sauri yakai wayan kunnenshi kafin yayi magana cikin kakkausan
murya strictly Mom tace “kana ina Riyad?” Kasa magana yayi yay shiru cikin masifa sosai Mom
tace “okay sabida na barka tareda Munir shine yanzu gidansu kake zuwa kasan nida matan nan
bamayin juna but you keep going there kana ganin gidan nan kowani yaro najin maganan
uwarsa ni ban isa kaji nawaba ko ai shikenan kayi duk yanda kakeso…..” “Mommm!” dip ta
katse wayan dasauri yatashi yajuyo sauke kanshi kasa yayi cikeda girmamawa yace “Mami bari
naje in Munir yafito yasameni awajen Gwaggo” ahankali Mami tace “okay” kofa yayi dasauri
yabude yafita tabishi da kallo sai kawai ta sauke ijiyan zuciya, wajen Gwaggo yawuce, Babban
flat ne uwa gari guda, ga hayaniya ana shiga da fita masu aiki sai gaidashi ake kaman anga
sarki amman ko kallon mutum daya baiyiba harya shiga dankareren falon Gwaggo, dudda dakin
yacika da mutane yana shiga Mai Babban daki ta sallami kowa falon yarage daga ita sai shi
yawuce wajenta yazauna yayi shiru, fuskanshi Gwaggo ta taba sannan takama hannunshi tabi
da kallo tana dube dube tace “yaro jiki uwa na baturai kai kenan baka isa kaga kazanta ba”
murmushi yayi ya fizge hannunshi yace “Gwaggo ni na warke kidena dubamin jiki dan Allah”
tsuki tayi tareda hankadeshi tace “kaga shashasha” Hararanshi tayi tace “ni shiga dakina ka
dauko huran dana dama maka daga babanka sai kai kap cikin jikokina keson furana” jikinta yayi
sanyi shima haka sai yayi shiru ganin yanda yayi yasa da sauri tai murmushi tace “bance kamin
fuskan mara lafiya ba, Allah shiya bani babanku kuma shiya amsa Alhamdulillah d’ana yayi
abubuwan alkhairi da dama aduniya yayi shukoki daban daban, ya gina makarantu, rijiyoyi,
gonaki dan haka banda nadama Allah ubangiji yakai haske kanarinsa jeka dauko” tashi yayi
ahankali yadauko kwaryan fura yazo yazauna yafarasha anatse tana kallonshi harga Allah
itama zatazo Riyad yazama sarki cus yarone mai tausayi mara hayaniya ga kwarjini ga biyayya
sannan ga kwazo, baida sa ido, shine yaro na farko kap yaran sarki daya fara neman nashi da
kanshi, tun ana gulma ana cecekuce but marigayi yace abarshi yayi abinda yakeso dudda kalan
kudi dayake dashi baitaba raina wani ko yadingaji yafi kowaba gashi da tausayi ya tsani yaga
wani na fushi ko kunci sanadiyanshi dan haka itama Riyad ne zabinta daman tariga ta jefamai
kuri’a. Ahankali tace “zabinka ne diyar Waziri ko zabin Mamanka Maryama dan nasanta da
tsinannen taurinkai, dason saka kabi ra’ayinta sabida taba Allah ya yoka me biyayya, kaika zabi
Haleematu”? Abu yaji ya tsayamai awuya but ya daure ya gyadama Gwaggo kai batare dayayi
magana ba, Gwaggo tace “ai shikenan za’ai magana idan anyi bakwai na babanka muji, zanma
Baffan ka Muji magana nama kirashi daman” daidai nan Munir yashigo yana zama akai sallama
Mujitapha yashigo yana sanye da manyan kaya daya fito da katon teban daya ijiye sai kyalli
shaddan jikinshi yake kana ganinshi kasan yasha kudi ya koshi waje ya samu ya zauna hakan
yasa daga Munir har Riyad suka gaidashi atare. “Ina kwana Baffa” binsu yayi da kallo shikebin
mahaifinsu yanason yaran wanshi baida matsala dasu, yanason ya gaji sarautan but then again
idan baisamu ba no big deal idan any of yaran wanshi suka samu, adai dauko wani sarki ne
daga cousins nasu da sauransu shine bazai yarda ba, anatse yace “kai yajiki? Kasami lafiya?”
Gyadamai kai Riyad yayi Baffa yace “har yanzu ana kan investigation koma su waye sukai
kokarin kasheka za’a kamasu, so don’t worry, it’s good zakai aure koda bakai maganan ba ma
yana cikin plan dina nace kafito da mata you need to settle down shi lokaci baya jiran kowa
mutuwa ake kullum” Munir ya kalla daketa sunnar dakai yace “kaikuma fa yaushe zaka fito da
taka matar?” Dasauri Munir yadago kanshi saikuma ya nuna kanshi foolishly yace “Baffa ni”
akufule Baffa yamai dakuwa yace “a’a ni” Gwaggo ta zubamai rankwashi tace “dan kaniyanka

kaima kafito da mata akace” kabar da hannun Gwaggo yayi yana turo baki yakalli Baffa yace
“toh Baffa zan fara nema daga yanzu” gyadamai kai Baffa yayi yace “kutashi kuje toh lemme
speak to Mama” tashi sukayi suka fice daga dakin.
Direct dakin Mom yayi yana bude kofa Mom tace “get out Riyad” gaban kofan ya tsaya yace
“sorry Mommy please Munir naje kirafa yarakani wajen Hajiya”


Cikin fushi Mom tace “tell me Riyad akwai abinda kataba so daban maka ba? You showed me
duk cikin yan uwanka Munir kakeso dudda ban shiri da mahaifiyarsa but nabarka dashi but na
gayamaka kadena zuwa side dinsu banso banso yare nake maka daka kasa fahimtata eh?”
Ahankali yafara tafiya yakai inda take sai kawai ya rungumeta ashagwabe yace “I am sorry
Mommyyyy bazan karaba kinga banda lafiya karki fushi dani please am missing Dad already
abin zaimin yawa” shiruu tayi saikuma ahankali tace “okay nahakura but baka ba ita that woman
is the reason har Babanku ya rasu baya shiri dani she come between ni da shi, allow me to plan
your wedding and coronation in peace kaji” sakinta yayi sai kawai ya daura kanshi kan cinyanta
ahankali yace “Mom kimin auren na yarda but please Mommy banson nazama sarki dan Allah I
am too young to be Sarki, Mom I want to tour round the world with my wife in peace” cikeda
fada tace “kaje sama da 58 countries wani tour round the world ne yarage bakayi ba? Is time
kayi taking responsibility naka Riyad, you are royalty Riyad, kai Royal blood ne ba normal
samari out there ba, duk wanda aka haifa a royal family akwai high possibility zai iya zama king
so accept your calling, and Babana zai turo bodyguards dazasu dinga binka anywhere and
everything” dasauri yatashi yace “Mom banso wlh banso” wani kalan kallo tamai tace “did you
even know su waye da waye ke kokarin kashe ka?” Kallonta yayi yace “suwaye?” Tana
kallonshi tace “I don’t know but my gut is telling me Yayanku from the way yake eye service dan
he’s everywhere, da yarinyar nan bata cecekaba I don’t know what would’ve happened” dan
ijiyan zuciya Mom tasauke cike da damuwa tace “kullum bana baccin dare sabida tunanin wasu
out there are trying to kill my son” dan lumshe idanu Riyad yayi ahankali yace “Mom lemme see
the footage” iPad dake gefenta agadon tadauka ta bashi daidai lokacin akai sallama yar aiki ta
gayamata tai baki tashi tayi tawuce tafita shikuma ya kwanta ahankali kan gadon tareda playing
footage din da aka samo daga airport din yana kallo kusan footage biyar ne daban daban tun na
shigowan shi arrival hall dana elevator saina bayin wanda shine na ukun, tsare cleaner yarinyar
da ido yayi, a lokacin da abin yafaru bai wani kalleta ba dan yana cikin tashin hankali sai yanzu
yake kallonta on this footage dudda is not that clear video karkar dinnan but yanda ta turashi
cikin sharan yakala da yanda tarufe da how she handled everything ahankali yace “who is this
feisty gurl”? The way takebin music yake kallo, he was actually watching the footage to see
kozai gane criminals din but yana fara kallo attention nashi kawai yadawo kan cleaner, har
footage data kaishi wajen dumping shara yakala da yanda take tafiya sai kawai yayi pursing
video tareda zooming face nata yace “who are you? You saved my life.”
CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK

wa.me/+2347012181461
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI

✍M SHAKUR


HAPPY JUMMA’AT GIFT

EPISODE 7️⃣
Zaune suke dukansu afada, dan kowa yanzu is at home babu wani maganan zuwa aiki ko wani
abu zaman makoki suke, yawanci Kabir ke attending, Riyad na zaune inda yake hardly yake
magana, wayanshi ne yahau ringing ganin Mom yasa yadauka yakai wayan kunne batare
dayayi magana ba, Mom tace “come nayi arranging private outing dakai da Munir da 2 security
personnel da Doddo (Baban Mom Attorney General na Nigeria) ya aiko maka dashi daga Abuja
kuzo kuje kaga Haleema gobe zata wuce school” jiyayi kawai ranshi yabaci amman yadaure
ahankali yace “okay” yazare wayan daga kunne, kallon yayinshi yayi yace “Mom nakirana bari
naje” gyadamai kai sukayi banda Kabeer dako kallonshi baiyiba, tashi yayi a tsanake yana
gyara zaman milk jumper rigan dake jikinshi nawani attajirin yadi, fadawa sukahaumai kirari.
“Takawanka lafiya Babban mutum! Yariman dashi kadai aka haifa agarin Riyad mai martaba
yabashi suna Riyad, dan kwalisan zakaran da ya riga yayi cha…..” wucewa yayi dasauri yafice
dan baiso yawuce side na Mom a falo yasameta ita kadai tai murmushi ta taso dasauri tana
gyaramai gaban wuyan riganshi tace “Masha Allah, yarona akwai kyau wlh, bama saika chanza
kaya ba” ashagwabe kaman zaiyi kuka yace “Mommmm” dan hararanshi tayi tace
“shagwabanka will not work nabiye maka u will never get married ko Doddo yayi na’am da
decision din” ahankali yarike hannun Mom din kaman dan yaro yace “but Mom I don’t even
know the girl balle na sota” dan shiru tayi tana kallon yanda yake mata wanda halinshi ne duk
girmanshi idan bayason abu haka yake mata shagwaba at this point so take ta lallabashi dan
batason tasake fada da yaronta datakeso sama da komi aduniya cikeda so tace “Son you are
from royal family yawanci haka ake aure, first wife din Baban ka Maman su Kabeer da 2second
wife dinsa Maman su Munir duk auren hadine baya sonsu, mai Babban daki ta zabamai su ya
aura dan bayaja da maganan mahaifiyarsa, daga kan Maman su Shuibu dakuma ni last wife
dinsa ne matan da marigayi yaso yakumayi soyayya damu is a normal thing haka abun yake,
gidan sarauta kenan with time zakaso Haleematu she’s a good girl duk agaban mu nan ta taso
and she really loves you kaman kamata asiri d’ana badai farin jini ba” Mom tai dan dariya
dayasa kawai ya rungumeta tareda daura kanshi kan kafadanta wlh zaka dauka karamin yarone
murya chan ciki yace “to Mom at least Baba yayi koda 7days ne kafin nafara zuwa neman wata,
Mom I am still moaning my father I am not in the right state of mind to meet any girl ko talk to
her” cikeda lalama Mom ta shafa kanshi tace “I know but do it for me kaji ko akwai abinda
bazaka iyamin ba ni Maman ka?” Ahankali yace “babu” murmushi tayi tace “yauwa dan albarka,
Oya tafi jeka shiga mota suna jiranka abaya” gyadama Mom kai yayi yasaketa ahankali wani
kalan murmushi Mom take tabishi da kallo tana kara wani son yaron nata da alfahari dashi
wucewa yayi yazaga baya budemai bayan wata mahaukaciyar tinted jeep akayi ya shige
security yarufe kofa kallon yanayinshi Munir yayi ahankali yace “chill kawai being born from this
family I guess comes with all this abubuwan” fuzar da iska Riyad yayi yakalli gefe baice komiba

aka tada motan fita daga gidan sukayi tawani secret gate basu da nisa nan da nan sukakai
gidan Waziri lafiyayyen kayattacen iso aka musu aka kaisu wani lafiyayen falo suka zauna
wayanshi yaciro yana dannawa kawai, Maman Haleema ce tafito cikeda farinciki tace
“sannunku da zuwa Yarima Riyad da Munir sannu sannunku” anatse Munir yace “ina yini Anty”
anatse shima Riyad kanshi na kasa muryanshi baya fita sosai yace “ina yini Anty” washe baki
tayi kaman ta yaga zuciyanta sabida farin ciki tace “aahhh Riyad call me Mama ai yanzu
anzama daya sannunku da zuwa bari naje gatanan zuwa” tashi tayi tabar falon bata wani dade
da fitaba Haleema tafito tana sanye dawani ubansu exclusive atampa an mata dinki Riga da
skirt daya kamata dam ajiki, ta yano karamin gyale tayi makeup tai matukar kyau da black
beauty ce abinta mai kyau tana kamshi, kallo daya tama Riyad zuciyanta yakusan tarwatse,
gogan yayi masifan kyau yayi wani zama kaman shugaban kasa yana danna waya abinshi
batare daya nuna alamun yamasan an shigo falon ba, zama tayi kujeran dake facing nasu cikin
murya mai laushe da dadi tace “barka da zuwa Yarima Riyad ina yini” ganin Riyad wayanshi
yake dannawa yasa da sauri cikin barkwanci kartaga kaman yamata wulakanci Munir yace “auu
ni za’a watsama kasa a ido ni hoto ne a falon nan ko Riyad kadai kika gani”? Dan murmushi tayi
tace “ai kaima zan gaidaka kawai nafara gaida wanda zai kasance mijinane kuma uban y’ay’ana
nan bada jimawa ba” “uh uh uhmmmm” Munir yayi gyaran murya yana kama baki sai kawai
yamike cikeda wasa yace “bari naje waje abuna tunda abun hakane, nima Allah yabani tawa
uwar y’ayan” yataba Riyad ganin yaki dena taba waya yace “ina waje” gyadamai kai Riyad yayi
yawuce yatafi zai cigaba da danna waya dasauri cikin murya mai sanyi Haleema tace “bismillah
yallabai ga abinci da abunsha na ijiye maka a dinning” dan dago idanu yayi ya zubamata su
dasauri tasauke nata idanun kasa dan bazata iya jure kallonshi ba, idanunshi kaman an wanke
da madara, tana wani irin jin dadi aranta kaman an gama biya mata bukatunta na duniya, daga
sama zuwa kasa ya kalleta yaune rana na farko dayake kallonta baiga wani makusa ba she’s
fine, educated classy but shi baiji that feeling of love da akace anaji in his heart ba, his heart is
not racing, daya ganta his heart didn’t flutter, infact zuciyanshi is beating normal, breathing
nashi bai chanza ba, ya kalleta and he don’t feel like looking at her again, she’s fine but batai
making heart nashi fine ba, he’s not having butterflies nor goosebumps acikinshi da jikinshi, he’s
not finding her intriguing dudda tai makeup etc, nothing about her is enticing his aura, he read
alot barinma lokacin PHd nashi, he knows the signs of love and baiji ko daya game da itaba, he
sees her just the way he sees kowace diya mace aduniya nothing special nothing different, all
this look and assessment yayishi ne in secs na kallonta kawai ya dauke kai yacigaba da danna
wayanshi ayangance batare dayace mata uppan ba har lokacin.

Toshi yanzu mezai fadamata? He doesn’t even know what to say, watsapp yashiga yama Mom
magana yace “Mom” nan da nan Mom saiga reply tace “ya akayi yaron Mom kunkai?” Da sauri
yayi typing. “yes but I don’t know what to say to yarinyar Mom” reply Mom tamai da “start
conversation ask her to tell you about herself” reply yamata da “Yaya zan fada?” Mom tace
“Haleema tell me about yourself” kaman zai fashe da kuka yace “too long Mom” salati Mom
tabuga a chatting din tace “zan bata maka raifa tell her now!!!” Da dago kanshi yayi yakalleta
karaf suka hada idanu dan kallonshi take kaman tasami video dasauri yadauke kanshi murya
ciki ciki ba yabo ba fallasa yace “tell me about yourself” wani irin murmushi tayi na jin dadi tace
“okay but bari nakawo maka drinks tukunna tunda bakaso kaje dinning” batare data kalleta ba

still yace “no banso” wani abu taji yanda yayi maganan bako kara amman tadaure takoma ta
zauna tace “where do I even start, okay I am 24yrs, nayi sauka last 2yrs, ina karanta
international relation a Oxford, ina final semester zan gama nan da 1month, ina business I have
a cafe and na iya makeup but banama mutane kaina nakemawa, I love traveling too like you”
tayi maganan tana kallonshi expecting reaction amman ko motsi baiyiba tace “I love having fun
celebrations irin su biki, zuwa wedding dinner friends and I love shopping and I love reading
novels mostly english ban iya karanta hausa books ba I think basically that’s all, ohh I have
plenty friends” daga wayanshi yayi yama Mom typing tagama gayamin about herself Mom natafi
ko? Dasauri Mom tace “common tell her about yourself too” ahankali yace “Mom I hate sharing
u know ni nagaji i want to come back home I don’t like their house is making me feel sick” kawai
yafito daga whatsapp din kafin Mom tace wani abu yamike zumbur yace “bye” kallonshi tayi
kaman tahanashi tafiya tadai daure tace “tom nagode” so take yabata numbers shi koda shi
bazai karbi nata ba amman bemayi maganan ba.


Yana fita yashiga mota Munir yabishi da kallo yanda yake cire boturan wuyan riganshi da sauri
sauri sai kawai yahau dariya yace “banda business da yawo gari gari banga uban abinda ka
iyaba Riyad wlh” wani juyowa Riyad yayi yamai mugun kallo baice komiba Munir ya kyalkyace
da dariya zaiyi magana wayan Mom yashigo yakalli wayan kaman zaiyi kuka yadafe kanshi
yace “ohhhh Mom nadamuna wlh” murmushi kawai Munir yayi baice komiba daga wayan yayi
Mom tace “kana ina”? Ahankali yace “muna hanyan dawowa” katse wayan kawai tayi jin ana
kiranta adayan wayan ganin batamata rai Riyad yakeson yi da ranan nan, ganin Waziri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login