ENGLISH DESCRIPTION
A storm covers the city, lightning splits the sky, and hearts are filled with hidden secrets. In this intense moment, a powerful woman named Nafisa returns home bringing jealousy, control, and chaos that threatens to destroy the fragile peace.
On the other side is Fati, a quiet and patient woman whose once loving marriage has turned into suffering after the arrival of a rival wife. Love becomes pain, the home becomes a battlefield, the children are caught in the middle, and the truth slowly begins to unfold. Will Fati endure the humiliation, or will she finally rise and fight for her dignity
But the story does not end there. A young woman named Khadija is pulled into this dangerous web, given a risky mission to save a broken marriage destroyed by jealousy, manipulation, and dark secrets. Can she soften the heart of a cold and distant man, or will she fall into a trap of love and deception
This emotionally charged novel is filled with jealousy, rivalry, power struggles, and the harsh realities of marriage, in laws, and survival. It reveals the hidden battles women face behind closed doors and delivers powerful lessons that will keep you hooked from beginning to end
If you are searching for a gripping Hausa novel about jealousy, co wives, complicated love, manipulation, marriage struggles, and family conflict, this story will capture your heart and refuse to let go
Step into the world of Sarautar Mata and uncover the truth hidden behind smiles and silent battles
HAUSA DESCRIPTION
Hadari ya rufe gari, walkiya na tsage sararin sama, kuma zuciyoyi na cike da boyayyun sirrika. A cikin wannan yanayi ne wata mata mai suna Nafisa ta dawo gida da iko, da kishi, da kuma hatsarin da zai tarwatsa zaman lafiya gaba daya.
A gefe guda kuma akwai Fati, mace mai hakuri da kunya, wadda rayuwar aurenta ta juya zuwa azaba bayan shigowar kishiya. Soyayya ta koma zafi, gida ya koma filin yaki, yara sun shiga damuwa, kuma gaskiya ta fara bayyana a hankali. Shin Fati zata iya jurewa wannan wulakanci har zuwa karshe, ko kuwa zata tashi tsaye ta kare martabarta
Amma ba anan labarin ya tsaya ba. Wata sabuwar budurwa mai suna Khadija ta shiga cikin wannan rikici, an dora mata wani aiki mai hadari domin ceto wani aure da aka rusa ta hanyar kishi, sihiri da yaudara. Shin zata iya canza zuciyar namiji mai sanyi da fushi? Ko kuwa zata fada cikin tarkon soyayya da makirci
Wannan littafi mai cike da zafi, tashin hankali, kishi da buzuwa, yana tona asirin rayuwar aure, dangin miji, kishiya, da gwagwarmayar mata a cikin gida. Labari ne na gaskiya da darasi mai zurfi wanda zai sa ka kasa ajiye littafin.
Idan kana neman Hausa novel mai dauke da kishi da kishiya, soyayya mai sarkakiya, sihiri, makirci, rayuwar aure, da rikicin gida, wannan littafi zai dauke hankalinka tun daga farko har karshe.
Shiga cikin duniyar Sarautar Mata ka gano gaskiyar da ke boye bayan murmushi da kishi.