Showing 57001 words to 60000 words out of 79746 words

Chapter 20 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf


Ji ta yi kamar an yi mata gafara sabida farin cikin dawowarsa cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido
ba tare da tasan lokacin da ta yi hakan ba. Hajiya tana ta magana, amma ba ta ji Mairo ta bata
amsa, sun yi nisa a kallon junansu kamar yau suka fara ganin juna.

Ta juyo don ta dubi Mairo, a sannan ne ta ankara da inda Mairon ta kafa wa ido. Ta ce "Au, ashe
mijinki kika gani kika manta da ni nake ta sambatu ni kadai?".
Ya yi dariya ya idasa shigowa dakin. Ita kuwa don kunya sai ta zame ta gudu gidanta ba ta kara
lekowa sassan Hajiya ba.
Tana shafa a gaban mudubi, ga dukkan alamu daga wanka ta fito. Daure da tawul iya
cinyoyinta. Ya bude kofar ya shigo cikin bakaken pyjamas, tana hango shi ta cikin mudubin a
lokacin da ya iso gare ta. Ya dora kai a hankali kan kafadunta ta baya, kyawawan fuskokinsu
suka bayyana cikin mudubin a jere, a hankali ya sanyata cikin jikinshi ya lullube da
hannayenshi, yana shakan sassanyan 'bathrobb' dinta na ‘rasasi’ yana lumshe ido. Ya ce
"Tell me how much you misses me, ko ba ki yi kewata ba ne Mairo? Don na ga ke har wata
kiba kika kara abunki, ni kuwa ina can tunaninki ya hana ni sukuni".
Murmushi kawai ta yi har 'beauty point' din mai kara mata kyau ya lotsa ciki sosai. Ya sumbuci
wajen with a very warm kiss, kana a hankali ya soma warware mata tawul din suka soma aikin
lada.

***

Wata guda da dawowarshi, suka yi shiri suka nufo Kano don yi wa Baffa sallama, kasancewar a
cikin satin ne zata koma Michigan. Su Habiba an shiga makarantar ta nutsu don yanzu Mairon
da suke wulakantawa ta zame musu uwargijiya da bazarsu suke rawa.
(To ina ruwan Allah!)
Tuni aka sa Lawan ya gyare musu dakin baki, ya kunna 'burner'. Abinci kam sai wanda suka
zaba. Baffa ya ji dadin ganin yanayin da Mairon shi ke ciki, ta cika ta yi bul, ta zama babbar
mace, kamar kajin Agric jawur da ita.
Ya tarasu duka ita da Amirun ya yi musu kyawawan nasihohi akan rayuwa, da kuma yadda za a
yi a ci ribarta. Ya kare da yi masu nasiha akan muhimmancin riko da sallah akan lokacinta.
“Ita ce idan ta yi kyau dukkan ayyuka za su kyautata”. Amiru na son Baffan Mairo, sabida
sauran mazan jiya ne ba na yau ba, irin wadanda kyale-kyalen duniya ba sa gabansu. Ya cika
su da alheri duk gidan, a washegari suka nufo Michigan.

Dina ce ta zo ta tarbe su, domin Habibu ya yi balaguro zuwa New-Jersey. Mairo ta rungume
'ya'yanta kamar ta tsaga kirjinta ta sanya su. Suna fada mata,
"Mun yi missing dinki Anti Mairo, da gaske ne da Daddy ya ce anyi miki aure da Uncle
Amiru???" Inji Bedi.
Murmushi ta yi, cikin matsanancin nishadi tana shafa kan yaron, amma ba ta amsa musu
tambayar ba. Amirun ne ya ji, ya juyo daga maganar da suke yi da Dina ya bashi amsa cikin
daga gira.
“yes Muhammad da gaske ne, Daddy is absolutely right! Har ma ta kusa ta kawo wa little Mairo
kanwa, nan da wasu watanni kadan”. Da sauri Mairo ta bace a wurin.

A ranar Amiru ya juya Washigton don karasa wasu hidimominsa tare da jaddawa Dina amanar
rayuwarsa, wato Mairon da ta dusar da hasken sauran matan duniya baki daya daga idanunshi.
Sun kulle a daki ita da Dina ana labarin bayan rabo. Dina ta kura mata ido ta ce

"Anya Mairo? Jikin nan naki babu bayani? Irin wannan fari da kyau haka sai ka ce mai
shafe-shafe? Ko dai kwanan nan za fara goyo ne? Naji Amiru na fadawa yara dazu na dauka
wasa yake"
Mairo ta rufe fuska da tafukan hannunta, ta ce "Kai Anti Dina, wallahi ba ni da komi. Karewa ma
yanzu haka period nakeyi. Ni fa tunda na je gidan dakina daban nashi daban. Kuma ba sai ana
kwana daki daya ne ake yin cikin ba?". Dina ta kyalkyale da dariya ta ce.
"Amirun? To abar kazar cikin gashinta tunda ba kya son a fige ta kada in zama babbar banza".
Ta jawo lokarta ta soma fiddo mata magungunan mata masu kyau da tsada 'yan Indonesia data
ke saya tana yi mata bayanin tsarin shan su.
Mairo ta ce
"Maganin mene ne?"
Dina ta murmusa, ta ce, "Maganin basir ne, ke dai ki dinga sha don da alama akwai basir a
jikinki tunda ga shi nan duk kin yi fari".
Mairo ta yi dariya. Ta rasa dalilin da yasa kullum Dina ke treating dinta yarinya kamar Little
Mairo.
Idan dai wadannan magangunan ne ai tunda ta zo gidan ta ke ganin Dinan na shansu, sai dai
ba ta taba tambayarta ko na mene ne ba. Amma yanzu ai ta yi girma da hankalin da zata san
amfaninsu.
Daga baya ko me Dinan ta tuna? Ta zaro ido ta ce "Ke! Bani magungunan nan bai kamata ki
fara amfani da su ba, sai mun je asibiti anyi checking dinki don ban yarda da ke ba. Mai juna
biyu ba ta amfani da irinsu".
Mairo ta bata fuska kamar ta yi kuka, don gani ta ke kamar Dinan na kallon abin da ta ke yi a
goshinta. Ta tashi gudu tayi dakinta.
Dina sai ta yi dariya, kuruciyar Mairo da halayenta na alkunya suna burge ta matuka.

Satin Amiru daya da tafiya sai ga shi kamar an jefo shi. Tana kicin tana hadin salad don haka
Dina ce kadai a falo, ita ma ba ta jima da dawowa aiki ba, ta sanya Mairon ta hada mata salad
zata ci.
Kararrawar kofar shigowa ta yi kara, ta umarci Lynder ta bude. Amiru ya bayyana a falon cikin
bakaken suit-spanish. Ta daga kai tana kallonshi tare da amsa mishi sallama, ganinshi wani 'as
a smart pace' (afujajan) ya bala'in ba ta dariya.
A gajiye ya zauna cikin kujera idanunshi a kwance ya ce "Dariyar me kike yi min?"
Ta ce "Ganinka na yi kamar an jefoka, lafiya dai ko?"
Ya ce "Da babu lafiyar ai ba za ki ganni ba, sai dai sako. Ina kanwar takin nan ne? Yanzu haka
kina nan kina hadata da wadannan girke-girken naki na tsiya".
Ta ce "Au na tsiya ne, amma idan an baka kake ci?"
Bai amsa mata ba ya nufi kicin inda ya jiyo motsin tangaraye.
Ta juya baya ta takarkare tana bude gwangwanin 'heinz-beans' ya mika dogayen hannuwanshi
ya rungume ta. Ya soma sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kwanaki bakwan nan da ya yi ba tare
da ita ba, jinsu ya yi kamar shekaru bakwai. Ka zalika ita ma Mairon, don dai ta kasance mai
zurfin ciki da kawaici ne. Amma ta yi missing din mijinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Sun yi nisa cikin duniyar faranta ran junansu, kafin Mairo ta ankara da inda suke, ta yi kokarin
kwatar kanta. Ya dago habarta da hannun damanshi yana son kallon kwayar idanunta, amma

bai yi nasarar hakan ba sabida matsananciyar kunyarshi da ta lullube ta. Ta yi azamar hankade
shi sabida warin 'aspen' da ta tsinkaya cikin bakinshi.
Ya sake kamota ta fuzge, ya ce, "Haba Mairo? Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu?"
Zata fice ya sha gabanta a galabaice, ya ce, "Kina so Mala'ikun rahma su soma tsine miki ko,
bayan da kina ta kwasar lada?"
Inda abin da Mairo ta tsana to wannan furucin ne, kamar ta yi kuka ta ce,
"Ni na ce ka sha taba?
Tun a gida ka ce min ka daina sha, amma ai ga shi nan na ji-ta a bakinka".
Ya rufe mata baki, ya ce, "Wallahi bazan kuma ba. Wannan din ma a jirgi aka ba ni. Ba kudina
na sanya na siya ba. Ce miki nayi “bazan kuma sayen taba ba”, ba “bazan kuma shan taba ba..”
Sun ba ni 'wine' ne, ni kuma na ga da na shata ai gara na sha tabar".
Ta zumbura baki, tana toshe hanci ta ce.
"Ni don Allah ka ba ni hanya na wuce..."
Amma fa banda kaduwa ba abinda jikinta ke yi, Amiru ya bala'in sanin 'weakness' dinta. Karfin
halinta da jarumtakarta suna ba shi mamaki. Kiri-kiri ga shi tana cikin kewar mijinta, a idanunta
da gangar jikinta, amma a fatar baki ta nuna ba haka ba ne.
“Ko in baki (hanky) ki toshe hancin da kyau??”
Kanshi ya tura cikin gashin kanta ta baya, bayan ya cillar da 'bound' din da ta daure gashin da
shi. Yana shakar kamshin kumfar 'pert-plus' da ta ke amfani da shi ba tare da ta sa wa gashinta
'relaxer' ba. Amma sai ka rantse kullum 'relaxer' ta ke shafa mishi.
Can cikin kunnenta yake rada mata. "Rakiya za ki yi min Mairo".
Da sauri ta ce
"Zuwa wajen budurwarka?"
Ya yi dariya, ya ce.
"Ga budurwata nan ina tare da ita, shopping zan yi".
Ta ce "Ni ba zan bika ba kullum kana yawo da wadannan gardawan masu shegen kallon tsiya
kamar wasu 'body-guard' dinka". (Raymond da Franklyn).
Yayi dariya. Ya ce
"To zan sallame su. Mu biyu zamu yi tafiyarmu, sannan ba shan Aspen a hanya, in kin ganni
zan saya ki kwace credit card din, hakan ya yi miki?"
Ta gyada kai cikin gamsuwa.
"Amma kai zaka fadawa Anti Dina".
"Idan don wannan ne, ta kwana gidan sauki, uuwata ce ita ko kanwar ubana? Daga kawo
ajiya?”
Abin ya bata dariya amma ta gimtse.
"To bari na karasa hada mata salad din, yunwa take ji".
Har zuwa lokacin bai sake ta ba, ya bi ya kankane ko'ina na jikinta. Sai faman sunsunarta yake
yi kamar zai hadiyeta. Sai da ta hada da magiya sannan ya sassauta rikon da ya yi mata.
Tare suka fito ta isa ga Dina ta mika mata farantin, ta nufi dakinsu don ta kimtsa.
Wanka ta sake ta zuba riga da siket na wani material yellow mai santsi, ta nada dan bakin
mayafi a kanta, ta matse da fil ta kara feshe jikinta da turaren (fahrenheit). Tana kokarin saka
takalmi ta jiyo Dina na kwala mata kira, don haka ta dauki jakarta 'polo' mahadin takalmin da ke
kafarta ta fito.

Ba ta san me ya fadawa Dina ba, ta ce
"Amiru ya ce za ki raka shi shopping ko? To sai kun dawo".
Suka hada ido ya daga mata gira, ya kashe ta da murmushi. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta.
Ya mike yana kiran Raymond ya fada mishi su je sai ya neme su, yana tare da Madam dinshi.
Ya karbi makullan motar Mairon hannun Dina, suka fito.
Tafiya suke sannu a hankali, irin tafiyar da ke sanya nishadi a zuciyar ma'aurata, kuma irin
tafiyar da ke kara wa masoya kusanci da juna. Babu wanda ke cewa uffan sai zuciyoyi kadai
suke magaba. Ya mika hannu yana karo sautin Abdurrahman Sudaith da ke tashi a hankali cikin
radiyon motar, cikin suratul Anfal. Hankalin Mairo na kara nutsuwa da mijinta, wanda dan zaman da suka yi na tsayin watanni ya
sanya ta ke fuskantar kyawawan halayensa a hankali. Wadanda ada bata yi tsammani ba. In
tayi la’akari da irin tsarin rayuwarsa da bigiren da yake rayuwa a ciki, da kuma irin mutanen da
yake hulda da su. Ko su Raymond sun isa su dulmiyar dashi cikin dabi’un nasara. Sai ta tadda
akasi ga tunaninta.
Da farko dai ta fahimci Amirun ba’a kada shi a magana, ko me ka gaya masa zai baka amsa
daidai da maganarka, ko ya baka wadda ta fita daraja, kuma ba shi da munafunci, kai tsaye
yake fadin abin da ke cikin zuciyarshi ba tare da la'akari da cewa, zai yi wa mai sauraronsa dadi
ba ko a'ah? Sannan Amiru mutum ne mai kula da sallah, da ba ta dukkan hakkokinta. Har ga tabon sujjada
nan rangadede a kan goshinsa. Ga son 'yan uwansa da iyayensa da kulawa da su, irin mazan
da duk son da suke wa mace ba sa hada shi da na iyayensu.
Yana da ban dariya, yana da barkwanci, sai dai idan miskilancin ya motsa ya fi mahaukaci ban
haushi da takaici.
Ba ta kai ga gama tunaninta ba ta ji yana zungurin kugunta da mukullin mota.
Ta juyo a hankali tana kallonsa, soyayyarshi na kara kamari a tare da ita. Kamar yasan me ta ke
tunanin, ya kamo hannunta ya rike cikin nasa, ya kwantar da kai a kafadunta, ya dora mata
dukkan nauyin jikinshi... "Mairo kada ki bar ni. Ba ni da harshen da zan fada miki adadin
soyayyarki da ke cikin zuciyata. Ban taba son wani abu a rayuwata kwatankwacin yadda nake sonki ba, idan kika dauke
iyayena. Ban taba yin soyayya ba Mairo sai a kanki. Nasan kin aure ni ne ba bisa son ranki ba,
amma......"
Ta yi hanzarin kai yatsunta ta toshe mishi baki. Ta kankame shi sosai jikinta yana rawa.
"Kayi min alfarma kada ka kara yi min wannan zargin, domin kuwa Allah shaidata ne akan cewa
na aureka ne da zuciya daya, cikin amincewa kaina cewa, kai ne mijin da Allah Ya zaba min; kai
ne zabin Allah a gare ni.
Daga lokacin da na fara ganinka, na ji wasu abubuwa sosai a zuciyata. Duk da soyayyar Uncle
dina da nake fama da ita a wancan lokacin hakan bai hanani ba ka wani muhimmin gurbi a
zuciyata ba, gurbi na ‘auratayya’ ba soyayya ba.
Na kalubalanci tunanina ne a lokacin da cewa yaudara ce. A hankali na gane hakan ma ba ya
zuwa sai da soyayya! Soyayya ta da Uncle Junaid wani abu ne da ya shude a wata rayuwata ta
can a baya..., Past is past Ameeru, and you are my present...!!!"
Amiru ya wani irin kankame Mairo yana mata sumba mai tsayi da zurfi, tsayin wani lokaci mai
tsawo, kamin su samu nutsuwa cikin zuciyoyinsu. A yau ya samu wani irin kwanciyar hankali irin

wanda bai taba samu ba tun haduwarsa da Mairo. Tada motar yayi suka harba kan titi. Ba su
tsaya ba sai a shagunan da ke karkashin 'Sommerset mall'.
8/6/21, 1:16 PM - Kawata: 55555555555
Shi kadai ya shiga ya yo musu duk sayayyar da zai yi. Ta duk abinda zasu bukata na kwana
uku. Ya bar Mairo cikin motar. Tsabar kishi irin na Ameer bai yarda da shiga da Mairoßs irin
wadannan wuraren ba, bai tsaya a ko'ina ba sai a otel din 'Hyatt Regency' inda Amirun ya yi
masauki. Hotel ne na manya, na daga wane sai wane. Ta dube shi a razane, a sanda ya kashe
motar, sanda ta fahimci cewa a otel suke. Kamar ta yi kuka ta ce.
"Haba don Allah? Me zan ce da Anti Dina?"
Ya langwabar da kai abin tausayi a masangalin kujerarsa, tsayin lokaci bai ce mata komai ba, a
cikin lumsassun idanunshi kadai ta gama samun amsar duk wani uzurin sa da dalilinsa, da kyar
ya ce. "Ba kya tausayina ko Mairo? For quite a week kenan ina suffering. Sabida ke nazo, tun
daga Nigeria har Michigan. Sannan idan na tafi na barki zan jima ban zo ba, sai kun yi hutun
karshen semester, ban sanki da halin rashin tausayi ba. kada ki fara ta kaina…...!!!”
Kalaman sa sun gama kashe duk wani kuzarinta. Kwayar idanunsa sun gama kassarata. Ba
yadda ta iya, dole ta zuro kafafunta ta fito. Zuciyarta na gaya mata ko akan titi Ameeru yakeso
su rayu yau zata kasance tare dashi, gata dama da rarraunar zuciya, wadda ta afu ga son
Ameerun with infatuation. A kwanaki ukun da suka yi cikin otel din 'Hyatt Regency' tamkar wani
sabon babin amarci ne Amiru da Mairo suka balle.
Mairo ta ga soyayya a gun Ameeru irin wadda a duk karance-karancen Novels dinta, ba ta taba
katari da irinta ba, domin Amiru karshe ne, a fannin nuna soyayyah.

A yau zai maida ita gida, domin jirgin karfe hudu na yamma zai bi zuwa gida Najeriya. Tunanin
Mairo na yadda za ta fuskanci Dina ne da Yaya Habibu idan ya dawo ya ji ta bi miji, kwana da
kwanaki ba a gansu ba.
Har kuka ta yi saboda damuwa, don ta lura shi ko a kwalar rigarshi. Ba karamin tausayi da
dariya Mairon ta ba shi ba. Don haka ya shiga lallashinta, yana nuna mata wannan ba wani abu
ne na tada hankali ba.
"Shi Yaya Habibu da Dinar ba daki daya suke kwana a gabanki ba? Su ba su ji kunyarki ba, sai
ke ce mai jin kunyarsu akan haka?"
Ta balla mishi harara cikin hawaye. Ya tarairayota ya rungume yana dariya, ya ce.
"Shikenan ki barni da su, ni zan fitar da ke".
****
Lokacin da suka iso gidan Habibu da Dinan ne suke 'lunch' tare da su Muhammad. Cikin
bagararwa Yaya Habibu ya saci kallon Mairon da ke bin bango tana son ta shige dakinta, ya ce.
"Ai na dauka kun wuce gida Najeriya ne?"
Amiru ya yi dan murmushi, sannan ya ce.
"Idan mun wuce ina ruwanka? Ni bana son aikin sa ido wallahi".
Dina ta yi murmushi tana jinsu suna ta yi, Amirun na cewa.
"Sa ido sana'ar banza, Yayan banza, Yayan kwabo".
Habibu ya dube shi, ya ce.
"Na ji dai, tunda ni dai mace ba ta taba kwantar da ni a gadon asibiti ba".
To a nan ya kashe bakinsa, don bai kuma tankawa ba.

***


C
ike da himma Mairo ta dasa karatunta daga sabuwar shekara, duk da su Ir'eesh sun wuceta, ya
kasance ta koma farkon shekara ta biyu.
Habibu ya ba ta wayarta, bayan wadanda Amirun ya mallaka mata guda biyu irin wadanda ba ta
taba gani ba. Don haka duk dare suna makale a waya suna fadawa juna how much they miss
each other.
Yadda ba ta iya sakewa su yi hira fuska da fuska, a waya idan ka ji su, sai ka sha mamaki.
Kullum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login