Showing 66001 words to 69000 words out of 79746 words

Chapter 23 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

da
rabonsa na ALHERI.

Jikin Daddy a masifar sanyaye, da mamakin wai itama Hanan an saketa. To shi yana ina aka yi
duk wannan kazamin aiki? Lallai Hajiya ta bashi mamaki. Ya kuma soma zargin koma menene
itace ummul-haba’isi, haka kawai za’a kashe masa Da a banza.

Habibu bai bar jinyar Amiru ba, duk da tabbacinsa na sakin Mairo da yayi. Duk da zafin hakan
dake ranshi. Duk wai wata kusan tafi wata kusan. A wurinshi ba Mairo ce ta hada shi da Amiru
ba balle ta zamo silar rabuwarsu. Allah ne ya hada su, ya sanya kaunar juna da soyayya a
tsakaninsu, ba kuma zasu rabu a dalilin ta ba. Ko ba komai Amiru ya wanke mishi zuciya da
baiyi mummunan saki ba wanda Allah baya so. Yayi kokari ya karanta hargitsatstsen rubutun ya
ga saki daya ne. Kullum kafin ya fita ofis zai zo, haka in ya tashi yana nan tare dashi har goman
dare.
Amiru yana shaida kowa, amma baya magana. Sai bin kowa da ido. A ganin shi rayuwar bata
cancanci a cigaba da itaba, ba tare da abinda zuciya da gangar jiki ke so ba. In za’a bashi zabi
gara mutuwa da rayuwa babu Mairo.
Kasancewar Daddy da Habibu na kula da shan magungunan sa akan lokaci, ya sanya kullum
sauki na kara samuwa.
Daddy ya shigo falon da ‘ya’yan sa, Hajiya da Hanan ke zaune, kowanne kai a kasa. Jiki yayi
la’asar babu laka. Ita kanta Hanan ta tsorata da ganin yadda Amiru ya koma cikin dan lokaci
kalilan. Sau daya ta shiga part dinshi, tausayi bai barta ta kara komawa ba. Ko babu soyayya

Amiru dan uwanta ne wanda take ji har cikin kashi da bTa kuma alkawartawa ranta fadiwa
Daddy gaskiyar duk abinda ya tambayeta ba tareda shayin Hajiya ba, don Yaya Amiru ya samu
lafiya, ya samu abinda yake so, ita tayi hakuri, ta auri Ramadan wanda ke son ta kamar ya
kashe kan shi. Amina kadai ake jira a falon wadda bata karaso daga Switzerland ba har yanzu. Don haka
ganin ana batawa ‘majority’ lokaci, akan mutum daya, Daddy ya yanke hukuncin ayi taron bada
ita ba.
Ya bude taron da cewa kowa yayiwa Annabi salati goma. Ya ja doguwar addu’a suka shafa.
Yasa gilashi ya soma duban ‘ya’yanshi mata su goma sha daya da fuska mara walwala. Ya
maida dubanshi ga Hajiya A’isha yace
“Hajiya, keda Hanan kune a gidannan sanda abin ya faru, don haka ku zan fara tambaya. Yaya
aka yi Amir ya saki matansa biyu duk a lokacin daya?”
Hajiya tayi shiru, ta soma share ido da gefen mayafinta, abinda ya riga ya zame mata jiki tun
ranar da aka dawo da Amiru wai yana fama da ciwon zuciyar data yi tsammanin yayi hannun
riga da shi. Tararradinta shine idan ta rasa Amiru ina zata tsoma ranta? Mutumin da ke yi mata
biyayyar da duk cikin ‘ya’yan ta babu mai yi mata kwatankwacinta? Mutumin da ya sadaukar da farin-cikinshi akanta. Bama wannan ba, ina zata kai hakkin Mairon
da bata ci mata ba, bata sha mata ba, biyayya take yi mata tamkar tayi mata sujjada, kawai don
Allah As-samadu bai bata haihuwar da bata isa ta baiwa kanta ba? Ta tabbatar ba komai ya kai
ta yin umarnin data yi ba, bacin ran sakin da yayiwa Hanan ne. Wadda ita bata damu ba, kamar
dama jira take, yana sakinta ta hada ya-nata-ya-nata tayi tafiyar ta, babu ko cikakkiyar sallama.
Sai yau ta ganta cikin taron da bata zata ba.
Amma ko waya Hanan bata kara yi mata ba. Gatanan da ranta da lafiyar ta ba abinda ya
dameta. Sai nata dan data jefa cikin halin ha’u’la’i. zaiyi-ba zaiyi- ba Allah masani.
Ta dubi Nina, kamar ta tsinka mata mari, domin dai ita ta kaita ga abinda bata taba tsammanin
yi a rayuwarta ba. Wato bin malaman tsafi Yarbawan Lagos, haka-kawai zasu fidda ita a imanin
ta. Kukanta ya tsananta ta kasa baiwa Daddy amsa.
Don haka ya juya akalar tambayarsa ga Hanan. Ta sunkuyar da kai ta soma fada masa duk
abinda ya faru, tun ranar da Hajiya ta aika ta zo, abubuwanda ta rinka bata wai tayiwa Amiru
amfani dasu, har zuwa ranar daya saketa, da tirkeshi data yi ya saki Mairo. Daddy ya jinjina kai
cikin al’ajabi da mamaki, yaushe Hajiya ta koma haka? Ya ce da Hanan ya gama da ita, kuma ya gode. Kuma menene ra’ayinta kan zama da Amiru?
Tana so idan Allah Ya bashi lafiya zata dawo dakinta ne ko a’ah?
Ta sunkuyar da kai tace “ka fahimce ni Daddy. Ba wai bana son Yaya Amiru ba, amma shi
wallahi-wallahi baya so na. Matarshi kadai yake so Daddy. Kuyi kokari ku dawo mishi da abarshi
cikin gaggawa in har kuna son lafiyar shi fakat. Nikam har ga Allah na hakura, zan auri mai so
na. Daman kuma babu iddarshi a kaina”.
Daddy ya sake jinjina kalamanta, yayi mata godiya ya sallameta ta fita ta koma wurin Amiru.
Inda aka baro su shida Habibu. Daddy ya dubi Hajiya cikin wani irin fushi da ‘anger’ da bata
taba gani daga gareshi ba. Fuskar shi tayi jawur abinki da bafulatani, jijiyoyin kansa sun fito
rada-rada, idanunshi sun canza launi daga farare sol zuwa jajaye. Jikinshi na tsuma, tsigar
jikinshi na tashi yace

“A’isha! Hanan gaskiya ta fadi ko karya ne?”
Ta juya kai cikin tsoro da tashin hankali, nadama da yin kaico da kai, don bata taba ganin shi
cikin wannan halin ba. Tace
“batayi karya ba anyi haka. Sai dai kuskure ne da ajizanci irin na kowanne dan adam. Na tuba
Alhaji na bi Allah na bika. Sai dai komai ya faru ne da zuga da taimakon wadannan……….”
Tana nuna Nina, Ni’ima da Khalisa.
“Su suke karbo komi a Lagos wallahi ban taba zuwa ba. Don nasan zuwa wajen irin wadannan
mutanen haramun ne. Na roke ka, kada ka bari Habibu yaji wannan magana don GIRMA NA
ZAI FADI A IDANUN SA don ba iyakarta kenan ba…….”
Cikin nishi Alh. Abdurrahman yace “sai kuma me?”
Ta yarfe hawaye da majina tace
“Na sanya shi ya janye hannun jarinsa daga bankinsu shida Habibu……duk takardun dukiyar
shi suna hannu na yanzu, bari inje in dauko…”.
Tana shirin mikewa ya daga mata hannu “bayan Nina, Ni’ima da Khalisa sai kuma wa?” tace
“sai mutanen Gaya. Su suke cewa “juya” ce. Don haka ne na kulla auren shi da Hanan don ya
samu ‘ya’ya kawai wallahi, amma ba don in raba shi da matarsa ba….. kai shaida ne akan cewa
tsakani da Allah ina son Mairo”. Ya kalli Nina da Khalisa da suka yi tsuru-tsuru, jikinsu sai kyarma yake. Don sun gigice da ganin
‘tension’ din mahaifinsu mai son su da gudun bacin ransu, tareda kyautatawa rayuwarsu tun
daga yarinta har girma. Rayyah tace “wallahi babu ruwana……” Sabah tace “wallahi babu
hannu na…..” Mami tace. “ni Daddy da ba a kasar nake ba, wallahi bani da masaniyar komai…….”.
Juyawa yayi gefensa ya fizgo wayar talbijin. Ya soma binsu yana tsula musu. Duka na tashin
hankali. Da masu ruwan, da wadanda suka ce babu ruwan su. Yana hawaye yana tafkarsu,
yace
“Kun yi asara! Kun kashe auren mutumci da amana da soyayya ta gaskiya!!
Bazan yi muku baki ba. Amma kuji tsoron hakki. Kuje duniya kadai ta isheku, tunda kuma mata
ne kuma aure kuke kamar yadda Mairo ke zaman aure.
Sannan abinda kuka yiwa Mairo, kuka sa aka yi mata, zai iya faruwa da kowaccenku. Dan
uwanku kuma idan yana da hakkinku Allah zai fitar masa, muddin ya mutu bai yafe muku ba.

Kuma sai kun maimaita wannan magana agaban Habibu, sai Habibu yaji wannan maganar.
Ke kuma Hajiya ki tattara ya-naki-ya-naki ki tafi Gaya, sai na nemeki…….bana bukatar ganin ki
a cikin gidana yanzu……”. Kowa a falon kuka yake, yana rokon gafara. Basu kara tsananta
kukansu ba, saida suka ji wannan danyen hukuncin da Daddy ya zartas akan Hajiya. Suka
rirrike kafafun shi suna bashi hakuri yace “ni baku yi min komai ba. Wadanda kuka yiwa su zaku nema gafara amma ba ni ba. Sannan
bazan taba sanya baki Mairo ta dawo gidan dan uwanku ba. Tunda bakwa son ta.
Ku aura mishi duk wadda kuke so tazo ta cika muku gida da ‘ya’ya. Ko ya mutu, ko yayi rai, na
barwa ALLAH! Ku bace min da gani dabbobin banza. Hajiya ina kara gaya miki, kada in dawo in
ganki cikin gida na….”.

Ya yarda wayar ya fice, yana share hawayen da suka cika mishi ido.

***


Wasa-wasa sai da Mairo ta kwashe watanni uku cur cikin wannan halin, a lokacin cikin jikinta ya
fito sosai, domin ya shiga cikin watanni na biyar.
Rannan daga ita sai Hajiyar Dutsinma a dakin, ta farka daga barci, ta kurawa silin ido, al'amuran
suka soma dawo mata tar-tar.
Ta tuna wai Amiru ya sake ta, ba tareda ta yi mishi laifin komi ba, alhalin suna tsaka da son
junansu. Bayan ta mallaka mishi duk wata soyayyarta.
Sannan ya auro Hanan, ba ta fita daga wannan bacin ran ba, ya dankara mata saki, ta tabbatar
bisa tursasawar Hajiya ne, amma Amirun ba zai taba yi mata haka akan-kanshi ba, ko giyar
wake ya sha.
Tana mai sa ran bada jimawa ba za su dai-daita da mijinta ya maida ita ta zauna lafiya da
Hajiya Aisha, tunda abin da Hajiyar ta kwallafa rai, har ta tsane ta a kanshi, ga shi Allah Ya
bayar.
Sai kuma ta tuno wai an fada mata ya kara kamuwa da ciwon zuciya irin wanda yayi a baya,
aka samu rayuwarshi da kyar da taimakon ta. Gashi yanzu basa tare. Kai ita ji tayi ma kamar
ance ya rasu! Daga bakin Hajiyar Dina da ba zai taba yi mata karya, ko zolaya ba.
Ta soma kuka a hankali, kukan sabo, soyayya, kauna da kewa. A tsayin zamansu na shekaru
takwas, bai taba bata mata ba, sai bisa kuskure. Soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi a nuna
mata, wani abu ne da ba zai taba kankaruwa daga zuciyarta ba.
Tunda ya aure ta ya haramtawa kanshi sauran mata. Bai kara hada jiki da wata diya mace ba,
bayan ita, har inda yau ke motsi. Har kuwa wadda ya aura da auren sunnah. Taji wannan a
bakin Hanan ba a bakinsa ba. Duk da matakin rayuwa irin nashi, wannan bai shagaltar da shi
daga rudin duniya ba. Ta tabbata ta yi babban rashin da har abada ba zata mayar da makwafinsa ba.

Ta mika hannu ta shafi kasan mararta, inda babynshi ke kwance, yana wutsil-wutsil cikin koshin
lafiya. Ta lumshe ido a hankali, hawaye masu dumi suna zirara ta gefen idonta suna shiga cikin
kunnuwanta. Ba ta damu da ta share ba, haka zuciyarta ba ta daina kokawa ba.
A wannan halin Habibu ya tarar da ita. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta. Ya ce.
"Mairo, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu..."
Ga mamakinshi sai ta fado jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya. Ta ce.
"Yaya Habibu da gaske mun rasa AMEERU?"
Ya ce
"Mun rasa auren shi dai Mairo, da gaske mun rasa auren mai kaunarmu da gaskiya da amana.
Amma Ameeru yana nan a raye.
Duk wanda yace dake ya rasu, ya fada miki ne kawai don ya tayar da hankalinki. Ko kuma baki
tsaya kin saurara dai-dai ba. Amma yana gida, kwance a dakin ki. Akan gadon ki.
Kwanciyar shi ciwo da rabuwar auren ku ya barni da kewa, da katoton gibi a zuciyata. Wanda
mayar da shi wani abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. Don haka ki dage da yi mishi addu’a. Allah
ya bashi lafiya cikin gaggawa.
To lose a friend like him, will be the GREATEST lose of all losses. To lose a husband like him, is

another GREAT loss. (rasa aboki kamar sa, ba karamar asara ba ce daga manyan asarori,
kuma rasa miji kamar sa, shima babbar asara ce.) Sai dai mu cigaba da yi mishi addu'a. Allah
ya bashi lafiya.
Wannan ne kadai babbar sakayyar da zamu yi wa masoyi irinshi. Amma ba da son ranshi ya
sake ki ba.
A matsayinmu na musulmi, ma'abota imani da yarda da kaddara, muna da tabbacin cewa, duk
abinda ya faru damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka
muna da kyakkyawan zaton Zai tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar
da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah
zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa.
Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce.
"Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da
muka rasa auren Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da
Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har mu cinye jarrabawarmu.
Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da 'yan uwanshi suka yi, kan halinda
yake ciki. Kuma Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti.
Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi
gafarar ki sun rasa. Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana.
Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a
gabana don na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi
mana, yayi mamaki nima nayi mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya
akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun soma gani tun a duniya, tunda Amirun na
neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko kofar gida Amiru bai kara
takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki.
Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya
rage ya saketa saida nasa baki tukunna ya hakura.
Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki
shikuma ya gaya musu.
Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari
ne ga mai juna biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa
ki……...bani da Uwa, bani da Uba, sai ke da abinda zaki haifa…."
Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa.
Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce.
"Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye".
Ya ce,
"To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz...
Mairona!".
Ta ce
"To ba ni in ci".

Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman
kaji ya yi lugub. Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika
mata. Ta karba ta soma ci sosai har tana taune harshenta sabida yunwa.

Dina ta shigo rike da kwandon kayan abinci, suka zauna akan kilishi suna ci ita da Habibu.
Mairo na kallonsu tana raya abubuwa a ranta, wato ranar da aka kaita gidan Amiru ya takura
mata sai ta ci abinci akan idonsa.
Ta kai hannu da sauri ta goge hawayen da suka kara shimfido mata, don ba ta son Yaya Habibu
ya gani, ranshi ya baci. Amma ta riga ta san kuka ta dinga yinshi kenan, har karshen rayuwarta.
Tunda yanzu itada Amiru sai dai a TUNA BAYA……Yaya zatayi da dimbin soyayyar shi data
kankanewa zuciyarta????








An sallami Mairo ranar wata asabar bayan likitocinta sun tabbatar komi nata ya koma dai-dai. A
lokacin cikinta ya cika watanni shidda cif, wanda ya yi dai-dai da cikar Amiru watanni hudu yana
jinya.
Suka dawo gidan su Dina, inda a washegari Habibu da Dina suka yi shirin tahowa gida
Najeriya. Gidan ya rage daga Mairon sai Hajiya da masu aiki, don Abban Dina bai cika zama ba
sai a weekend, kullum yana ofis.
Bata tashi daga inda ta yi sallolin farilla guda biyar, ba tareda ta yiwa Amiru addu'ar neman
lafiya daga Ubangiji ba.
Hajiyar Dina na kula da ita yadda ya kamata, ko Innarta iyakacin kulawar da zata yi mata kenan.
Watan Hajiyar Dutsinma biyu tare da su jikinta ya yi kyau ta koma gida.

Kwanaki na mirginawa su zama watanni, har watan Aprilu ya kama, wanda shi ne EDD dinta.
Sai dai Mairo ba ta yarda anyi mata ‘scan’ ba. Ranar wata alhamis nakuda ta tashi cikin dare,
haihuwa gadan-gadan. Don haka ba da bata lokaci ba Hajiya ta tuka su da kanta suka nufi
asibitin da ta ke awo, nan da nan aka karbe ta a (labour ward), nakuda ta tsayin awanni uku cur,
kan Hassan ya bullo, kamin likitocin su yi wani yunkuri, shi ma Hussaini ya biyo dan uwansa.
Aka turota dakin hutu, Hajiya na rungume da jariran tana yi wa Allah sarkin halitta tazbihi,
sabida kamar Amiru ya yi kaki ya tofar. Sannan ‘identical twins’ irin wadanda banbacesu zai yi
wuya.
Sai dai da alama Hassan kalar Babanshi ne, wato (choculate), yayin da Hussaini ya debo
hasken fatar Mairo.
A take Hajiya ta yi waya ta sanar da Habibu, ya yi hamdala ya kuma nemi wayar Alh.
Abdurrahman ya sanar da shi, don haka a karshen satin suka dungumo har Hajiyar Amiru dasu
Sabah suka iso Malaysia.
Farin ciki a wajen Hajiya Aisha da Alh. Abdurrahman abin ba’a cewa komi. Hajiya har da
kukanta na nadama, ga dai ‘ya’ya ba daya ba har biyu Mairo ta Haifa, duk kunyar Mairon ta

isheta, ta kama 'yan jikokin ta rungume tana yi musu addu'a, ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login