Showing 33001 words to 36000 words out of 79746 words

Chapter 12 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

wannan sakayyar daga gare ku ba….." Ta kai gefen mayafinta ta share hawaye, ta fyace majina, ta ce "Ladidi ke kuwa mai ya kai ki ga
yin haka? Idan aure kike so mai yasa ba ki tsayar da daya cikin tulin samarin naki kin aura ba?
Mai za ki ce da Baffa ranar da ya gane kin yi cikin shege?"
Ladidi ta kufula wai Mairo ta ce ta yi cikin shege, ta ce "Kinga malama bana son wani dogon
Turanci, idan ba zaki rakani ba ne mu raba hanya, wancan karon ma da aka ce na yi cikin ai
nasan inda na je aka kwakule shi. Ko ance da ke kowa ma kidahumi ne, bakauye irinki?
Mtsew!!!" Ta yayyaga takardar likitan da takardar maganin, ta ce
"Ki je ki gayawa Baffan naki ya yi duk abin da zai yi kada ya barni da rai idan shi ne..........."
Mairo ta sanya 'yan yatsu ta toshe kunnenta, ita kuma Ladidi ta tare dan A dai-daita sahu ta
shige, ta ce, ya kai ta Sabon Gari.
Tana shigowa gida Habiba ta ce "Ina kika baro Ladidin?"
Ba tare da ta dubeta ba ta ce "Tana zuwa yanzu". Ta shige dakinsu ta danno kofa. Ta rasa inda
zata sa kanta da tausayin Baffa. Ta soma kuka kamar ita ce abin ya faru a kanta.
Wani sassanyan kamshi ya doki hancinta, irin wanda ba ta taba ji ba a rayuwarta. Daga nan ta
jiyo muryar Baffa yana salati, yana sallamewa. Ta sake saurarawa sosai sai ta ji ya ce
"HABIBU? Wa nake gani kamar Habibu?"
Tamkar wadda aka cakawa mashi. Ta ji wani kululun bakin ciki ya taso ya soketa a kahon zucci.
Amma hakan bai hanata mikewa ta fito ba, don gasgata kunnuwanta.
Wani magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da takwas, wankan tarwada, mai zarkadeden

dogon karan hanci da yalwar idanu farare kal. Da ganin fuskarshi ka ga Malam Bedi, ta wani
fannin kuma Alhaji Abbas sak! Yana sanye da kaftan na shadda Getzner kar-kar da ita, baka
wul! Dinkin tazarce, sumar kansa a kwance luf baka sidik, kasancewar ba hula a kansa. Da gani
babu tambaya, ka ga mutum da ya dama, ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban. Wasu
kyawawan yara guda uku, maza biyu da mace daya, sai rarraba ido suke na rashin sabo.
Mairo dai tana nan rike da labule tana kallonsu, wasu irin hawaye suka zubo mata, ta yi saurin
sakin labulen ganin zai juyo sashen da ta ke. Tana ji su Hajara duk suka firfito suna ta karadi da
sallallami, ita kuwa ba ta kara lekowa ba. Mai ya dawo da shi cikin rayuwarsu yanzun? Bayan
masu bukatarshi sun shude a doron kasa? Mai zai ce, mai zai yi, ya wanke mugun tabon da ya
yi mata a zuciyarta?
Mairo kuka ta ke tamkar ranta zai fita, ba ta son ganin Habibu ko kadan a rayuwarta. Gara ta
bar gidan, kada ace da shi yana da 'yar uwa, mai zai yi mata wanda ALLAH da UNCLE JUNAID
ba su yi mata ba?
Ta soma harhada kayanta cikin jakarta da sauri-da-sauri, tana yi tana fyace hanci da hawaye
duka. Ba ta ankara ba sai ji ta yi Baffa na kwala mata kira daga tsakar gida "Mairo! Mairo!! Ko
Mairo ba ta nan ne?"
Ta yi bakam, ta ki amsawa, ta jawo hijabinta ta zurma ta sungumi akwatinta ta yo waje, suka ci
karo da Baffa a bakin kofa.
Ya ce "Zo Mairo, yau ga Habibu Allah Ya dawo mana da shi".
Ta sa kuka, ta ce "don Allah Baffa ka bani hanya in wuce, bana son ganinshi, ba abin da ya
hada ni da shi. Idan dai zai zauna a gidan nan to ni zan koma wajen Nabilah".
Baffa ya ce "Haba Mairo, waye ba ya kuskure? Ki dinga yi wa dan Adam uzuri cikin kowanne
hali, uzuri sau saba'in, kafin ki kama shi da laifi. Ki saurare shi ki ji da wacce ya zo, sannan ki
yanke mishi hukunci".
Da haka ya lallabata suka nufi dakinshi, inda Habibu da su Habiba su ke.
Habibu ya hada kai da gwiwa sai kuka ya ke, kamar karamin yaro. Ba kuma kukan komai yake
ba, sai kukan jin rasuwar iyayensa daga bakin Habiba. Baffa ya fada su da fada kamar ya rufe
su da duka "Ke kam Habiba ba ki ji dadin halinki ba, ko ruwa ba ki barshi ya kurba ba zaki ce
Uwa da Uba sun mutu, gatsar, babu sakayawa, babu nuni da daukan hakuri da YAKANAH
(Sunan Littafin TAKORI mai zuwa). Ku tashi ku fita ku ba ni waje, iyayen banza, wadanda ban
san yaushe za su san Annabi Ya faku ba".
Sum-sum-sum suka mike suka fita. Habibu ya dago kai yana kallon Mairo. Kyakkyawar budurwa
‘yar shekara sha takwas, wadda ya tafi ya bari tana shekaru takwas. Ita ma ta kalle shi cikin ido,
sai kuma ta dauke kanta. Ta daure fuska sosai. Ya ce "Mairo Yaya Habibun?" Sai ta fada jikinsa
ta sa kukan da ke cinta a zucci. Allah Ya riga ya halicci zuciyarta da kaunar Habibu, babu yadda zata yi, shi ne dolenta a
rayuwa. Suka rungume juna suka yi ta kuka, Baffa ma tunanin dan uwansa ya dawo masa sabo.
Ya soma share ido da habar babbar rigarsa.
Sai da suka yi kukansu mai isarsu, sannan Baffan ya soma lallashinsu. Ya ce "Ni ina nan
Habibu, zan zame muku uwa, uba, kuma abokin shawara. Dukkaninmu na haka ne, kowa jiran
wa'adinsa ya ke".
Habibu ya ce "Kaicona Baffa! Dukiyar da na zauna ina tarawa don Baba ya daina noma, Inna ta
daina girki da icce, Mairo ta yi karatu mai kyau sun tashi a banza!

Na kintata ne zuwa sanda zata gama sakandire sannan in dawo, ashe bazan tadda Baba da
Inna ba, sannan Mairon ba ta ji dadin dawowata ba!!"
Baffa ya ce "Wai haka Mairo? Ba ki ji dadin dawowarsa ba in sallame shi?"
Ta yi murmushi, ta sake sunne kanta a kirjin Yaya Habibun. Ya ja karan hancinta, ya ce "Ko
kallon 'ya'yanki ba ki yi ba, balle mai sunanki, mai kama da ke".
Sai a lokacin hankalinta ya koma ga yaran. Cikin murmushin kaunarsu da ta mamaye zuciyarta
farat daya, ta ce "Ya'yanka ne Yaya Habibu?"
Ya gyada mata kai, "Ya'yana ne. Na yi aure da mamarsu tun sanda na kammala karatun digiri
na farko. Ga Abbas, ga Muhammad (Bedi), sannan ga Mairo".
Baffa ya yi murmushi, ya ce "Taho takwarana".
Abbas ya matsa gare shi, dan kimanin shekaru hudu, Muhammad shidda, Mairo kuma 'yar
shekara biyu ce.
Babban wato Muhammad ya ce "Daddy wannan ne Babanka?"
Ya ce "Eh, shi ne Babana".
Ya kuma cewa, "Wannan ce Aunty Mairo?"
Ya ce "Eh ita ce Aunty Mairo".
Ya matso jikin Mairo ya jingina da kafadunta, ita kuma sai kokarin daukar takwararta ta ke,
amma ta ki, ta like jikin babanta. Ya ce "Ai ita kiwar tsiya gare ta, wanda yake kulaki ba ki kula
shi ba".
Ta yi murmushi ta ce "Abbana, Muhammad".
Ya yi murmushi ya ce "Anti Mairo za ki je gidanmu?"
Ta ce "Insha Allahu".
"Za ki yi min tatsuniyya ta gizo da koki irin wadda Daddy ke mana?"
Ta ce "A'ah, ni ban iya tatsuniya ba, ni sai dai na karanta maka labarin jaruman maza, irin su
Ilya dan mai karfi, da Malukussaif Ibn Ziyyazanun".
Ya yi dariya ya ce "Ni kuma zan tuka ki a jirgina (helcopter) wanda Daddy ya sayo min".
Ta rungume shi ta ce "To Abbana".

Baffa ya ce "Amma Habibu na yi mamaki da ka iya yin wadannan shekarun ba ka waiwayi gida
ba, ko gaisuwa ce ai ka aiko mana, idan ba ka zo ba (a lokacin ba kowa ke da wayar hannu ba,
sai wane da wane)".
Habibu ya ce "Kuskuren da na yi ke nan, amma kusan kullum ba a rasa masu zuwa Najeriya
daga Malaysia. To sai dai ita kanta Maleshiyar na dade da barinta, tun bayan da na kammala
karatun digirina na farko.
Dina abokiyar karatuna ce, diyar Ambassadan Nijeriya a kasar Maleshiya. Mun dade muna
soyayya, mahaifinta ya so mu dawo gida ayi auren gaban iyayena, na nuna masa ni ba yanzu
zan koma gida ba, ina da babban uzurin da ya rabo ni da gida, idan na koma mawuyaci ne
Babana ya barni na dawo. Don haka ya tsaya tsayin daka har muka yi aure. Da taimakon mahaifinta na samu aiki na wucin gadi (temporary) ina yi a wani kamfanin kera
takalman fata. Na dade ina aiki a nan kuma na samu alheri yadda ba kwa zato. Daga baya wani
abokina Amiru da taimakon mahaifinsa ya yi min hanyar da na samu gurbin karo karatu a
Michigan din Amurka, akan kwamfuta da duk abin da ya shafe ta. Ina gamawa ba da jimawa ba
na samu aiki a Bankin Barclays reshen kasar Amurka, don haka muka koma can. A can aka

haifi Alhaji da Mairo, Muhd ne kadai aka haifa a Kuala-Lampur (Malaysia). To kun ji, don haka
bazan dade ba, don wajen aikina suna bukatana, ina so zan tafi da Mairo".

Mairo ta yi azamar dago kai ta dube shi, da gaske ya ke ko wasa ya ke? Babu alamun wasa ko
kankani a fuskar Habibun. Shi kuma ya kafa mata ido cike da tsoron, kada ta ce ba zata zauna
da shi ba. Shi kam nan duniya bai ga abin da zai sake raba shi da 'yar uwarshi ba, wadda ta
rage mishi kwal a duniya. Baffa ya ce, "Anya a yi haka? Ni dai na fi so inyi mata aure, hankalina
zai fi kwanciya. In lissafina dai-dai ne shekarunta goma sha takwas cif, aure shi ne ya dace da
ita".
Cikin murmushi Habibu ya ce "Ta fitar da mijin ne?" Ya fadi yana kallon Mairon, ta yi hamzarin
sunkuyar da kanta. Baffa ya ce, "A'ah, ita ko zancen nan da samari irin na su Ladidi ba ta yi,
idan ka ganta ta fita, to muhimmin abu ne ya fitar da ita. Amma akwai wani abokina Alh. Salisu
da ya yi min maganarta tun wancan watan na ce ya dakace ni sai na yi shawara da ita tukunna". Habibu ya ce "Har nawa Mairon ta ke? Ka yi hakuri Baffa ka ba ni ita makaranta zan sa ta, idan
ta soma ko ba ta kare ba idan mijin ya fito sai a yi auren, amma Alh. Salisu ai ya yi mata tsufa".
Baffa ya ce "Ni ma abin da na yi la'akari dashi kenan, shi yasa ban baiwa zancen wani
muhimmanci ba, sai ka yi mata fasfo ku tafi, Allah Ya sa hakan shi ne alkhairinta".
Habibu ya ce "Amin". Ya dubi Mairo ya ga ta sunkuyar da kai, ba ta dago ba ya ce "Mairo ko ba
kya son zama da ni da 'ya'yanki?"
Ta yi murmushi ta ce "Mamarsu zata yarda?"
Shi ma ya tayata murmushin, ya ce "Kada ki damu. Dina mace ce mai fahimta, ga kirki da
hankali. Na yi mata kyakkyawar shaida. Ta sanki, ta san labarinki ba tun yau ba. Ta fi ni
damuwa da a dauko ki, ina gaya mata akwai lokacin da nake jiran isowarsa ga shi Allah Ya
kawo". Baffa ya ce "Ita tana ina?"
Ya ce "Tana garin Dutsinma, can home town dinsu, gobe insha Allah zan je na dauko ta".
Rahma diyar Hajara ta shigo da kular abinci da farantai ta aje ta fita, Mairo ta matso ta zubawa
Habibu, ya karba yana cewa, "Yaushe rabona da cin dan wake?"
Baffa ya yi dariya ya ce "Ai ga Mairo nan sai ta dinga yi maka dan wake, idan matarka ba ta iya
ba".
Ya ce, "Tana yi min na fulawa (gudun kurna), amma ba irin shi nake so ba, wannan da ake yi da
rogo da kuka shi na fi so, don ya fi sulbi, yafi saukin wucewa a makogaro".
Mairo ta zuba filet daya da yaran ta ja su suna ci, Baffa na bai wa Habibu labarin bayan rabo.
Habibu ya kammala ya ajiye farantin, ya tsiyayi ruwa a jug ya sha, ya ce "Na zo da ma'aikata
Baffa, gobe insha Allahu za a rushe gidannan a yi ginin zamani yadda su Inna Habiba da
sauran yara za su fi sakewa". Baffa ya yi murmushi ya ce "Allah Ya ba da iko Habibu".
Ya juya ga Mairo ya ce "Je ki share min dakina na zaure, anan zan sauka zuwa gobe, yaran ki
kwana da su, ni zan shiga cikin gari wajen tsoffin aminai, gobe idan Allah Ya kaimu sai mu je
can immigration maganar fasfo".
Ta ce "Ita kuma Anti Dinan a ina zata sauka idan ta zo?"
Ya ce "Tana da inda ya fi nan ne? Duk nan zamu sauka".
Ta tasa yaran a gaba suka nufi cikin gida. Habiba da Hajara dai duk kunyar Habibu ta ishe su,

sakamakon rashin arzikin da suka san suna yi wa Mairo. Ba su taba zaton Habibu zai dawo ba,
ga wata irin galleliyar mota da ya iso da ita mai nuni da lallai Habibu ya kama kasa, ga 'ya'ya
firda-firda kamar 'ya'yan kajin gidan gona, da gani babu tambaya iyayensu sun gama samun
nasibin rayuwa.
Habiba ta karbi 'yar daga hannun Mairo, ta sa zani ta goyata, ta ce da Mairo "Ladidi har yanzu
shiru, ina kika barota ne?"
Ta ce "Tana can asibitin ta ce zata dan jima".
Baffa ya fita ya dawo da gyararrun kaji guda goma, ya ce a yi wa Habibu girki. Mairo ta je ta
share dakin Habibun da ke soro, ta kunna turaren wuta ta gyare ko'ina. Ta shigar da kayan
Habibun, bayan ta ware kayan yaran. Daga Hajara har Habiba sun shiga hankalinsu
musamman ganin yadda ake sauke buhunhunan shinkafa, katon-katon na taliya, garewanin
mai, katon na juices, na gwangwani da na kwali, buhunan sugar, doya, dankali da sauransu,
duk aka jibge musu a store.
Ladidi ba ta dawo gidan ba sai dare, wujiga-wujiga da ita, ba wanda ya ga shigowarta sai Mairo
don duk sun yi barci, ta lallaba ta kwanta a katifarta, ga dukkan alamu ta je an cire mata cikin.
Ladidi sai ta daina bai wa Mairo mamaki, ta koma ba ta tsoro.
Washegari ta shirya ta yi wa yaran wanka ta shirya su, Hajara ta ba su abin kari koko ne da
kosai da agada, da suka kammala suka tadda Habibu a dakin Baffa suna kalaci shi da Baffan.
Yaran suka nufi Babansu suka baibaye shi, ya ce "Ba ku gaida Baffa ba Muhammad".
Suka hada baki suka ce, "Baffa ina wuni?"
Ya ce "Ina kwana dai takwara na, kamar ba haihuwar Turai ba, Hausa ras a bakinku".
Habibu ya ce "Ai ni bana yi musu Turanci, Mamarsu ce ta ke musu. Ita ma ina hanata don kowa
yabar gida gida ya barshi".
Baffa ya ce "Wannan haka ya ke, Allah Ya raya mana su cikin addinin islam, amin".
Suka bar yaran wurin Habiba, suka nufi Immigration office, can hanyar farm center cikin dan
lokaci aka yi wa Mairo passport aka ce su dawo bayan kwana uku su karba.
A hanyarsu ta dawowa Habibu yana tuki cikin nutsuwa Mairo tasa ido tana kallon shi yana
burge ta, ya yi kyau ya yi girma, ya zama ingarman cikakken mutum ma'abocin kwarjini na
musamman da cikar zati. Ta fadi a ranta gaskiya wannan Dina ta caba miji. A ranta kuma tana
kissima shin ita kuma Dinar yaya zata kasance? Jikinshi ya ba shi Mairo kallonshi ta ke, ya yi
wani irin murmushi mai ban sha'awa har fararen hakoranshi suka fito. Ya dan juyo ya ce
"Ya ya dai Mairo? Irin wannan kallo haka? Ko na yi kama da saurayinki ne?"
Kunya ta kama Mairo, ta rufe fuska tana dariya, "Ni ba ni da wani saurayi. Ka yi kyau ne da
yawa Yaya Habibu, ka zama babban mutum mai ban mamaki, don Allah mai Anti Dinar nan take
ba ka ne?"
Ya yi murmushi ya kai hannun hagunshi ya shafi kwantacciyar sumar kanshi, ya ce "Soyayya ta
ke ba ni Mairo. Duk wata kauna ta duniya Dina ta ba ni tun a lokacin da nake dalibi, ba ni da
komai, ba ni da ko kwabon da zan aure ta, a matsayina na dan kauye da matsayinta na diyar
Ambassador. Habibun kawai ta ke so ba wai wani abu da Habibun ya mallaka ba". Mairo ta ce
cikin zuciyarta, "Kamar ni da Uncle Junaidu". Ba tasan cewa furucin ya subuto ya shiga
kunnensa ba
7/31/21, 8:31 PM - Kawata: 990

Ya rage gudun motar ya dube ta sosai, hawaye ne fal idanunta "Kika ce mun ba ki da saurayi,
Mairo". Ta kai 'yan yatsu ta share hawayen idanunta "Kuka Mairo? Mairo me ya sanya ki kuka?"
Ba amsa, karewa ma, sai ta soma shesshekar kukan sosai.
Ya sauka gefen titi ya kashe motar. Ya mika hannu ya kama hannunta, ya damke cikin nasa
"Daga yau ba zaki sake kuka ba Mairo, tunda ga ni. Babu abinda Allah bai mallaka min ba. Gida
a America, gida a Abuja, motocin hawa sai wadda ranki yake so. Ga babban aiki da BARCLAYS
BANKS, ga takardun ilmi har zuwa PhD, wanda nake da yakinin daga mu har jikokinmu da
'ya'yan jikokinmu babu mu babu talauci.
Jami'a sai wadda kika zaba cikin kasar America. Gaya min wane ne Junaidu? Ni kuwa in aura
miki shi ko shi ne beran masallaci sabida talauci, ko shi ne Bill Gates sabida arziki, amma fa sai
idan yana da ilmi, ya kuma yi alkawarin zai rike min ke da amana".
Mairo ta sunkuyar da kai, ta ce "Ai bai taba cewa yana sona ba!".
Habibu ya ce "Ke ce kike sonshi ke nan?"
Ta ce "Ni ma ban sani ba ko son nasa nake yi. Alherinsa da kyautayinsa masu yawa ne a gare
ni. Ya tsaya tsayin daka akan karatuna, ya tsaya tsayin daka akan lafiyar Baba da Inna, ya ce
nima cikakkar mutum ce a lokacin da nake jin kaina cikin inferiority compled. Don haka bazan
iya ce maka Uncle Junaidu saurayina ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login