Showing 69001 words to 72000 words out of 79746 words

Chapter 24 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

take kamar Amirun ne ta
rungume a ranar data haifeshi, sai dai dukkaninsu babu mai ra'ayin a yi wani taro sai addu'a da
kowa yake yi wa mahaifinsu, wanda har zuwa lokacin ke kwance cikin halin jinya.
Yara sun ci sunan Habib da Amir, babu kuma wanda ya yarda da a sakaya. Ana kiransu da
sunansu abinsu.
Bayan su Hajiya sun koma Mairo ta ci gaba da rainon 'yan biyunta cikin koshin lafiya da
taimakon (Nanny) Bamaleshiya da Hajiya ta daukar mata.
Kamin watanni hudu sun cika sun yi kiba, sun yi bul kamar 'yan watanni goma sabida samun
kulawa da ruwan nono isasshe. A lokacin ne kuma 'addmission' dinta na yin PhD ya fito a
'university of Malaya'.
A satin da zata fara karatu, Yaya Habibu ya zo Malaysia. Yace tayi shiri suje Najeriya ta kaiwa
Amiru ‘ya’yan shi ya gansu. Don ya samu sauki har ya soma zuwa ofis. Daddy ya samo mishi
aiki a CBN. Don shi Habibun bai yarda su sake yin hadin gwiwar ba kamar yadda Daddy da
Amirun suka bukata, yace saboda halin rai. Ya kuma ce da Daddy akwai kudurin da yake dashi
a kan bankin nan bada jimawa ba. Amma ba wai don yayi fushi da abinda Hajiya tayi ba.
Mairo bata son wannan tafiyar sai don Yaya Habibu ya matsa mata. Amirun ne bata son gani,
don bata son duk wani abu da zai taba zuciyar ta a halin yanzu. Ta riga ta sanyawa zuciyarta
YAKANAH (sunan littafin Takori mai zuwa). Ta koya mata dangana, ta koya mata rayuwa ba
AMIRU. Karatun ta kawai tasa a gaba, da rainon ‘ya’yan da Allah ya bata. Lokacin da Daddy ya gayawa Amiru mairo ta haihu har ‘ya’ya biyu, bai nuna wani farin-ciki ba,
don yana kullace da Mairo, da bata taba zuwa ta dubashi ba har yayi ciwon sa da jinyarsa ya
gama ya gaji ya mike. Bashi da wani sauran buri a rayuwa, tunda ya rasa Mairo.
Sannan Daddy yace babu maganar biko, ba zancen kome, don bai yarda sun gama horuwa ba,
Amirun yayi ta zama a gwauro, ko su aura masa mai haihuwa. Ya kuma ce da Amiru in zai mike
ya fuskanci sabuwar rayuwa to ya mike, in bazai mike ba, yayi ta kwanciya soyayya ta kassara
shi. Don shima yana da nasa laifin. Na kin gaya masa duk abinda ke faruwa saboda tsoro da
son Hajiyarsa. Har saida komai ya lalace. Daddy yace
“ita tana son ka ta lalata maka rayuwa?”

A fannin ita Hajiya, zaman Amirun haka babu iyali ya fara damun ta. Tana so tayi zancen biko a
maida aure tunda saki daya ne, babu fuska daga Habibu da Daddy. Don haka tasa ido, don
ganin hukuncin da suke nufi.
8/9/21, 12:13 PM - Kawata: 33


Saidaifa rayuwar Amiru ta canza sosai. Ya zama babu murmushi babu far’a sai ‘dark-spaces’
kusan koyaushe make a fuskarsa. Sai ayyukan dake gabansa. Ya kudire a ransa idan ba Daddy
ne da kansa ya bude baki yace ya maida Mairo ba da bakinsa, to ya hakura da ita har karshen
rayuwarsa. Yamma lis, suka iso filin jirgin saman Abuja. Dina dasu Muhammad sukaje tareda direba filin
jirgin suka dauko su. Suna zuwa gida Dina ta karbi yaran tayi musu wanka ta shiryasu da kaya
na alfarma. Habibu ya dura su a mota tareda su Muhamnmad da mai rainon su Esta da suka
taho da ita daga Malaysia sai Asokoro.

Kasancewar ranar Lahadi ce, Daddy yana gida shida Amiru a karamin falonsa, suna aiki cikin
takardu da kwamfuta. Habibu ya yi sallama rike da mai sunan sa yayinda Muhammad ya biyo
bayansa dauke da Amir. Ya saki takardun hannunsa ya bisu da kallo. Ba zaka iya karantar halin
da zuciyarshi ke ciki ba. Suka yiwa kansu mazauni a falon Esta tana waje, Daddy sai murmushi yake yayinda Amiru ya
zamo mutummutumi, tsigar jikin shi na tashi cikin kauna da shauki. Ya matso ga Habib dake
zaune a cinyar Habibu, ya durkusa a gabansa ya mika mishi hannu, siraran lebbansa dauke da
wani irin ni’imtaccen murmushi, da bai taba yi a rayuwarsa ba. Wata irin kauna ta da da mahaifi ke fizgar zuciyar shi. Amma sai Habib ya noke a kafadar Yaya
Habibu wato, bai san shi ba.
Yaji ba dadi, ya koma ga Amir yana karkada mishi ‘ya’yan mukullai, da wayo da dabara ya samu
ya yarda ya dauke shi. Ya rungumeshi sosai a kirjinshi yana sunsunar shi. Yana shakar kamshin
turaren Mairo (Fahrenheit) daya kama jikin yaron. Ganin dan uwanshi a hannun shi sai shima
Habib ya miko hannu, ya hadasu su duka biyun a kirjinsa, sai yaji kamar Mairo ce ya rungume.
Amma don mazantaka, bai yarda ya zudda hawayen da suke son bashi kunya ba.
Daddy da Habibu suka bisu da kallo cikin tausayi. Daddy yace “saukar yaushe?” Yace
“dazunnan muka iso”.
Dai-dai lokacinda Hajiya ta shigo falon cikin kwalliya ta alfarma. Bakinta ya fadada da far’a da
murmushi. Tace
“A’ah! Sababbin masu gidan sun zo, tsofaffi sai su zo su fice…” tana kallon Daddy tana dariya.
Ya harareta don yasan dashi take, yace “da tsohuwar zuma ake magani. In dai wadannan ne da
ba mazauna ba ai gaki gasu, da sun tafi zaki dawo min ne kina rara-gefe”.
Ba yadda bata yi ba don ta dauke su amma sun like jikin Ubansu. Ta fita ta kawo ‘teddy’ na
‘ya’yan Nina da suka zo hutu sannan suka yarda da ita. Daddy yana son ya tambayi Habibu mai
yasa Mairo bata zo ba? Yaga babu dalilin da zai yi masa wannan tambayar sai yayi shiru.
Shikuwa Amiru Allah kadai yasan abinda ke cin zuciyar shi. Mairo ta daina son sa……! Mairo
bata son ganin sa…..!!

Har goma na dare suna can, yaran suka soma rigima, duk da an basu madara. Uwarsu suke so
haikan. Amma Amiru ya kasa bada su. Saida Habibu yayi mishi alkawarin kafin su tafi gobe zai
kai mishi su ofis sannan ya dauko su har motar Habibu, bayan Hajiya ta cika su da toshi. Daddy
ma ya bada check na kudi masu yawa yace a dinka jamfa, baya son ganin su da daura ‘suit’
irinna Ubansu.

Mairo tayi shirin barci a dakinta dake gidan Yaya Habibu. Ta sanya yaranta a gabanta tana
kallon su da fuskar mahaifinsu. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ wanda ya tuna mata da
‘those precious moments’ da suka shude a baya. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ da
suka kwaso, wanda ya dawo da so da kaunar mijinta sabo fil a zuciyar ta. Ta shiga tsakanin su ta rungume kowanne a jikinta. Ta soma sheshshekar kuka a hankali, na
tashin tsohon mikin daya jima da samun sauki. Shiyasa bata so zuwa ba, amma Habibu ya
takurata. Ta fadi a ranta Amiru ya daina son ta.......! Tunda har bai damu daya ganta ba. A
karshe ta hakura ta sanyawa ranta salama. Tunda ance komai yayi farko, to inshallahu yana da
karshe WATARANA!

Washegari Habibu ya cika alkawari, ya sake diban Amir da Habib da Esta ya zuba su a mota zai
fita da niyyar kaisu office din Amiru suyi sallama kamar yadda yayi alkawari. Yana kokarin tada
mota Amiru na sanyo hancin motarsa ‘camero’ cikin get din Habibun. Don haka Habibun ya
dakata har ya bude motar ya fito. Ya karbi ‘ya’yansa ya soma ‘kissing’ kamar bazai bari ba.
Daga can saman bene Mairo ta yaye labulen dakinta don iska ta shigo. Nan ta hango su. Ta
kurawa Amir ido. Bayan muguwar ramar da yayi, ya bar lallausar kasumba mara tsari ta cika
fuskarshi, abinki da mai yawan gargasa. Sannan ya saya kwayar idon shi cikin ‘dark-spaces’
wanda ya hana mata gano halin da kwayar idanun shi ke ciki. Karan hancin ya kara fitowa, zirit, kamar karas. Wani irin so na fizgarta. Ta saki labulen a
hankali ta koma da baya ta fada a gadonta. Tana mai fidda numfashi da sauri-da-sauri. INAMA
ACE…….hannun agogo zai dawo baya???
***








Washegari suka koma Malaysia. Mairo ta fara karatunta cikin nasara, tana barin yaran a gida
wurin mai rainonsu da yake an fara ba su madara. Kafin su cika watanni tara suna gudunsu
ko'ina, musamman Alh. Abdurrahman ya bude mata 'account' a nan ‘Kuala-Lampur' duk wata
yana sako mata makudan kudi na fita hankali, don lalurorinta da kula da ‘yan jikokinsa. Bayan kuma ba abin da Ambassada ya rage su da shi, ga na Yaya Habibu. Gaba da baya gata
ya lullube Mairo da 'ya'yanta, abin sai godiyar Allah.
Shekaru ukku cif, wadanda suka yi dai-dai da cikarta shekaru talatin a duniya, da kwalin digiri,
master, da digiri na kololuwa.

Dr. Maryam Muhammad Bedi, ta tattaro ta dawo gida Najeriya a garin Abuja, zuwa lokacin
Habibu ya yi ficce, bankin ‘Habib Bank’ ya samu habaka zuwa 'branches' a dukkan 'thirty six
states' da muke da su a gida Najeriya, kamar yadda Amiru Abdurrahman ya yi fata. Yau ga ci
gaban ya samu, ba tare da Amiru ba.
A wannan ranar da ake (ten-year anniversary) na cikar bankin shekaru goma da kafuwa,
Habibu kuka yake, maimakon ya yi farin ciki.
A yayin da al'ummar taron suka dauka kukan farin ciki yake yi, amma shi kadai yasan dalilin
kukansa, wanda bai wuce na alhinin samuwar cigaban shikadai, ba tare da Amiru ba.
A kalaminshi na karshe, bayan ya yiwa mahalarta taron godiya mara iyaka. Ya ce,
"Ya tafi ya bar bankin da kewa, bayan shi ya kirkireshi. Ya bar bankin da babban gibin da har
gobe bai cike ba. Na kuma tabbata har abada ba zai cike ba. Sakamakon dumbin ALHERINSA

gare ni. A yau na tashi daga mamallakin ‘Habib Bank’, na kyautar da shi ga 'ya'yan AMEERU
ABDURRAHMAN GAYA".

Amiru ya daga ido yana kallon shi, extremely puzzled! To haka Alh. Abdurrahman. Ashe
wannan shine kudurin da Habibu yace yana dashi kenan akan bankin, ya ki yarda amaida
hannun jarin Amiru cikin bankin?
Ya sanya hannu cikin takardu, lauyoyi suka diba, su ma suka rattaba hannu. Sannan ya ce,
“as a servant, zan ci gaba da juya musu dukiyarsu har zuwa girmansu”.
Hajiya ma ta dauko duk takardun dukiyar Amiru dake tare da ita, ta danka mishi. Ya hada dana
wajen Habibu ya adana a bankin. A wannan ranar Habibu yayi kuka, kawai sabida tausayin
AMEERU. Don gabadaya rayuwarshi ta canza ‘completely’ ta zama ‘no meaning…’ kamar
yadda ya fadawa Mairo a baya.
“My life has no meaning......idan ba tareda ke ba”.
***



Habibu ya watsa mata takardun neman aiki, a manyan jami'o'inmu, tun daga Ile-Ife, Ahmadu
Bello, Nsukka, Bayero, Lasu da sauransu, ba don neman kudi ba, sai don al'ummar Najeriya su
amfana da ilimin da ta wanzar da rayuwarta tana nema, don su amfana.
Ba da jimawa ba jami'o'i har biyar suka dauke ta, ciki kuwa har da jami'ar Abuja, wadanda ta
bari a baya. Amma ta zabi BAYERO domin a ganinta al'ummar Kano su ne al'ummarta.
Habibu bai takura mata da zancen aure ba, ko tayin ta koma gidan Amiru. Sai dai shima yana
ganin lokacin yayi daya kamata a maidawa Amiru matarsa sabida yadda zawarawa
manya-manyan kusoshi ke yi mishi rubdugu, a gida ne ko ofis. Alh. Abdurrahman ya fara
tsawatar mata da cewa, ba zata koma Kano ba har sai ta fidda miji ta yi aure. Sai ta sa musu kuka tana rokonsu, kada su kara yi mata zancen aure, idan ba so suke ita ma
CIWON ZUCIYAr ya kamata ba. Me zata yi da wani da namiji ba Amiru ba? Me zata nema a
jikin wani namiji bayan Amiru? Amiru yasa ta raina sauran maza, ta yadda har basa burgeta,
duk ilminsu da mukamin su kuwa. Gashi da alama Daddy baya son komen nasu. Tunda koda wasa bai taba furtawa ba. Ya kama
Mairo da Habibu ya rungume kamar shi ya haife su, ya jibanci dukkan al’amuransu, amma baya
ko son kallon Mairo da sunan matar Amiru. Itama kuma tunda hakane bazata taba nuna tana
son komawar ba, koda hakan na nufin ta auri wani ne ba shi ba! Alh. Abdurrahman ya ce,
"Aure ya zama dole Mairo, domin shi ne cikar kima, mutumci da darajar diya mace. Duka
wadannan kwalayen naki aikin banza ne idan babu aure".
Ta yi masa alkawarin su barta ta fara aikinta, a hankali za ta zabi wanda hankalinta ya kwanta
da shi. Ya so ya karbe yaran, amma ta roke shi ya bar mata, zuwa wani dan lokaci kalilan, don
suna debe mata kewa.

Gida guda suka bata cikin 'new site', suka tare ita da 'ya'yanta da mai rainonsu, mai suna Lami.

A lokacin Lawan da Ahmad 'ya'yan Baffa suna karatu a Bayeron, sai suma suka dawo gidan
suna zaune a baskwata.
Baffa yana zuwa duba su akai-akai, su ma suna zuwa idan sun sami lokaci. Mairo ta fara
'lecturing' a 'department of sociology' cikin nasara da sanin makamar aiki. Ta sanya yaranta a
'staff-school' kullum su Lawan suna kaisu su dauko su, da yamma kuma su kaisu islamiyya da
ke nan cikin 'New-site'. Ta dade da fara rubuce-rubuce tun tana Malaya akan fannin da ta ke karantarwa, wanda ya
kaita ga matakin zama 'proffessor' cikin dan lokaci kalilan.
Kyawunta, zurfin iliminta, sakin fuskarta da yawan taimakonta ga dalibanta, ya sanya ta zamo
abar so ga dalibanta. Sai dai fa kowa yana bin kwakkwafi ya yi mamaki idan aka ce ba ta da
aure. Sukan ce kyakkyawar mace kamar wannan ace ba ta da aure, ai abin mamaki ne sosai.
Sannan kallo daya zaka yi mata ka tabbatar ba da wannan aikin ta ke cin abinci ba. Tana dai yi
ne don ra'ayi, amma ba don neman wani abu wai shi 'kudi' ba.

Proffessor Maryam Muhammad Bedi, ta zamo daya daga cikin malaman da ake ji da su a
jami'ar Bayero, ko sabida karyayyen harshenta na Turawan America zallah. Don haka da yawa
suke bin kwakkwafi akan rayuwarta, har su san inda ta samo wannan 'background' din. Wani
dalibinta ya soma rubutu a kanta, sai dai duk yadda ya so ya ji tana da aure ko ba ta da shi, ba
ta bada wannan damar ba.
Dr. Mairo ta shiryawa dalibanta masu fita a wannan shekarar 'conference' mai taken, “YADDA
ZA A GYARA AL'ADA TA YI DAI-DAI DA ADDINI” Wanda take so Mai girma sabon V.C ya
halarta. Don haka ta je ta nemi 'appointment' na ganin V.C a ofishinsa. Aka sanya ta cikin jerin
wadanda za su ga V.C a safiyar washegari. Da ta dawo gida ta tarar Lawan ya dawo da su Habib, Amir yana kwance shiru cikin kujera ba
kamar yadda ya ke ba. Ta dora hannu a kanshi, zafi rau, Lawan ya ce.
"Amir ba ya jin dadi tunda safe".
Ta ce
"Za mu je asibiti da safe, idan na ba shi 'paracetamol' zazzabin bai sauka ba".
Ta dauko 'paracetamol' cikin 'first-aid box' dinta ta ba shi da dan kankanin cokali. Har zuwa
washegari zazzabin bai sauka ba. Ga shi kuma tana da 'appointment' na ganin V.C, don haka ta
sa yaran a bayan mota suka nufi cikin makaranta da zummar idan ta ga V.C sai ta wuce da su
asibiti, don mawuyaci ne daya ya yi ciwo dan uwansa bai kama ba. Ba ta barsu a mota ba, sanya su ta yi a gaba suka soma taka matattakala wadda zata sada su
da ofishin V.C.

Mutum biyu ne a gabanta, sai da ta jira suka fito, sannan ta kama hannun Habib da Amir suka
sanya kai cikin ofishin, bakinta yana mai furta sassanyar sallama.

Ya juya baya yana zakulo wasu takardu cikin loka. Idanunshi saye cikin farin gilashi, sanye cikin
farar shadda 'excelsior' dinkin Muhammed Abacha. Hular kanshi na aje bisa teburinshi.
Gaban Mairo ya yi wani irin mugun faduwa, takardun da ke hannunta suka kwace suka watse a
kasa. Amir ya tsugunna yana tsince mata. Shi kuwa Habib tattakawa yakeyi da cambos dinsa.
Ko mutuwa ta yi ta dawo, ba zata mance surar UNCLE JUNAID ba, wanda ke tsaye nan a

gabanta. Sai dai wannan Junaidun, ya sha ban-ban da wanda ta sani shekaru goma sha biyu a
baya. Wannan cikakken magidanci ne, da yasha gwagwarmayar rayuwar neman ilmi cikin
fanninnika daban-daban, ba dan saurayi Junaid Galadanci ba.
Duk da alamun shekaru da suka hau kansa, har yanzu yana nan a Junaidunsa da ta sani,
ma'abocin zati da kamala, gami da kwarjini bayyananne daga Sarkin halitta. Ta rasa cikin halin
da ta samu kanta, rudewa ce ko gigicewa ce? A'a, ko kuwa gaba daya makuwa zata ce ta yi?
Ta juya da baya–da-baya zata bar ofishin, ya juyo a hankali ya dubi mai shigowa.

"Mariama!"

Maironshi da a kullum ta ke zuwa a farke, ko cikin mafarkinshi. Mairon da dai-dai da rana daya
cikin shekaru goma sha shidda, zuciya ba ta taba hutawa da kaunarta ba. Ruhi bai bar
mafarkinta ba, haka tunani bai taba kuskuren manta ta ba.
Ya dago Habib ya dauke shi tare da kama hannun Amir ya zauna a kujerar da mutane suke
zama don ganawa da shi. Cikin wata irin kassararriyar murya, ya ce.

"Ya ya za ki koma? Ko ba ke ce 'Proffessor Maryam Bedin ba?"

Ta ja tunga a jikin kofa, ba tare da ta juyo ba. Ita bata fita ba, ita bata juyo ba. Hannunta jikin
marikin kofa, ta ce
"Ni ce".
Ya ce
"To mene ne ajandar?"
Ta ce
"Na zo neman alfarmar V.C ya samu halartar 'conference' dina ne".
Ya yi murmushi yana dauke da Amir ya tako har inda ta ke tsaye. Wani irin sassanyan kamshi
da ba zata ce ko na wanne turare ne ba a duk iya sanin da ta yi wa turare ya kassara mata
gabbai.
"Na kasance ma'abocin son 'twins' Dr. Mairo, ko za ki bani aronsu? Na dawo miki da su bayan
awanni goma sha biyu?"
Wannan karon ne ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login