Showing 72001 words to 75000 words out of 79746 words

Chapter 25 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

juyo ta dube shi, wasu kibbau na tsohuwar soyayya suka soki idanun
kowannensu. Tsohon tsimi ya tashi, wanda ya yi sanadin tashin tsigogin jikin kowannensu. Da
kyar ba tare da ta sake yarda sun hada ido ba, ta ce.
"Idan iyalinka suka tambaye ka ina ka samo su mai girma V.C me zaka ce musu?"
Babu bata lokaci, ya ce da ita.
"Ya'yana ne, wadanda Mairon Gurin-Gawa ta haifa mini..............."
Kuka ya kece mata, don haka da gudu ta fice daga ofishin tana ji a ranta, ta fasa yin
'conference' din, tunda shi ne ya yi sanadin da ya taso da tsohon gyambon da ya dade da
warkewa a zuciyarta.
Gidan Baffa ta wuce kai tsaye, ta nufi dakin Habiba ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya mai
nauyi. Ta yi juyi a lallausan gadon Habiba tana tariyo abinda ya faru cikin 'yan mintina kalilan.
Baffa ya shigo dakin ya zauna a kujera yana fuskantarta, ta goge hawayenta, ya ce.
"Me ya faru? Ke dai har gobe abun kuka ba shi da wuya a wurinki?

Yanzun nan Habiba ta yi min waya ta ce, kin shigo da gudu kina kuka. Idan ka girma sai kasan
ka girma, ka koyi dauriya da juriya irin ta manya. Ba akan kowanne kankanin abu ka bare baki
ka yi ta kuka a gaban mutane ba".
Ta yi murmushi tana goge hawayen idanunta, ta ce.
"Baffa, Uncle Junaidu na gani, bayan wucewar shekaru goma sha biyu. Ya tuna min da
abubuwa da dama da suka faru cikin rayuwata, shine dalilin kukana, domin na tuna abubuwa da
dama da yanayin shekaru da cigaban rayuwa ba su sani na manta ba".
Ya ce,
"kwanannan naji a labarai anyi ‘appointing’ din shi matsayin shugaban jami'ar Bayero ai. Har
yau har gobe kuma bai fasa zuwa gidan nan yana gaishe ni ba, bai fasa yi min manya-manyan
alhairori ba. Sannan son ki har yau bai barshi ba.
Ban taba ganin 'SOYAYYAH' irin ta Junaidu ba. Don haka ni ma har gobe ban fasa yi mishi
addu'ar budi da nasarar rayuwa ba".
Mairo ta cika da mamakin jin cewa Uncle Junaidu na zuwa wajen Baffa har yau. Amma koda
wasa Baffan bai taba gaya mata ba. Ba ta gama mamakinta ba su Habib suka shigo suna ta
tsalle, kowannensu rike da kit-kit da leda fal 'choculates' suka fada jikinta.
"Mummy mun dawo... Daddy yana gaishe ki".
Sai Baffa ya tashi ya fita, ya tarbi Junaid a dakin bakinshi.
Habiba ta shigo dauke da kulolin abinci. Su Amir suka makale ta suna ta ba ta labarin inda
Daddy ya kai su.
Ta ce,
"Wai wane ne wannan Daddyn?"
Amir ya ce
"Daddyn Mummy ne".
Mairo ta ce
"Rabu da shirmen su Mama, shugaban jami'armu ne".
Habiba ta yi murmushi ta ce.
"To ko da shi za a yi ne?"
Ta yi shiru ta daure fuska bata bata amsa ba. Don ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata
zancen aure.
Baffa ya dawo dakin yana murmushi, ya same ta tana cin abinci.

"Idan kin kare sai ki je ku gaisa da Alhaji Junaidun. Daga nan ya ce yana so zai kai Amir asibiti,
don ya ga alamun ba shi da lafiya".

Matsayin Uncle Junaidun da kimarshi da ke zuciyarta, ya fi gaban ta ce ba zata je ba. Baffa ya
ci gaba da yi mata nasiha mai sanyaya zuciya da sanya imani, akan lokaci ya yi da ya kamata
ta tsaida hankalinta wuri guda ta yi aure, domin cikar mutuncinta a duniya da lahira. Tunda
Amiru da Daddynshi basa bukatar komen.
Ta yi sallama a kofar dakin, yana zaune cikin kujerun (leather) da suka yi wa dakin kawanya,
Habib da Amir akan cinyoyinsa, yana ta haba-haba da su kamar ya maishe su cikinsa. Ya dago
idanunshi da suka yi fari sol, yana dubanta.

A zahiri Maironshi ce, sai dai fa wannan Mairon babbar mace ce 'yar shekaru talatin da doriya,
wadda kuma a idanunka da kiyasinka ba zata fi shekaru ashirin da biyar ba.
Wannan bakauyar da aka kawo mishi kafafuwanta jawur cikin lalle tsohuwa ta fada kwata, fatar
kamar shuni, yau idan ka dube ta, tsammani zaka yi Balarabiyar Omman ce, ba wai 'yar asalin
kauyen Gurin-Gawa ba.
Kallonta ya ke, kallon da ke nufin al'amura da dama. Ita ma kallonshi ta ke, kallon da ke tuna
mata da al'amura da dama. Da gaske Uncle Junaidunta ne, sai dai wannan ya kara yi mata
GiRMA. Ta TUNA BAYA... ta tuno ALHERInsa gare ta, ta tuno SIRADIN RAYUWArta, ta yi
ALKAWARI ko BAYAN RANTA matsayinshi ba zai taba canjawa daga zuciyarta ba. Cikin muryar
GIRMA ya ce.
"Mairo, ina Amiru Abdurrahman?”
Ta kai gefen mayafin abayarta ta dauke wasu siraran hawaye da suka kawo mata zarya. A
hankali tace.

“Mun rabu!”

Duk suka yi shiru na 'yan dakikai. Can kuma ta kawar da shirun da cewa.
"How comes kai ne sabon V.C dinmu, amma ban taba sani ba?"
Shi ma ya yi murmushi ya ce.
"Ni nasan kina cikin 'proffessors' saidai ban tabbatar ba, sannan ban taba tunanin ba kya tare
da maigidanki ba, a wane dalili zan nemeki? Sannan bani da tabbacin ke din ce ko ‘namesake’
dinki ce, na dai ga sunan da ya tsayamin arai ‘among the proffessors’,
Sannan ai ban dade ba ai, banyi dadewar da zaki san ina cikin makarantar ba” tace “haka ne”.
Ta sunkuyar da kai kafin ta dago ta sake cewa
"Ikon Allah kawai".
"Ni ma sai ki dauke shi a hakan, wato kudurar Allah, ta fi ga haka".
Ta jinjina kai, ta ce
"Kwarai kuwa".
Suka maida idanunsu akan Habib da Amir, wadanda ke ta dabdalarsu cikin dakin, dukkaninsu
sai suka yi murmushi, yaran suka burge su.
"Kuruciyarsu na da ban sha'awa".
Ya fada a zuci, bai san cewa a fili yake fadi ba.
"Kamar kuruciyar Mairo, Mairon Baba da Inna, Mairon Kausar da Nabilah…….."
Ta yi dariya ta juyar da kanta. Wani ala’amari mai girma na cin zuciyarta. Sai dai ba irin wanda
take ji a tsohon mijin ta ba. Ya kura mata ido, zuciyarshi na harbawa.

"Ina labarin Nabilah da Yaya Habibu?"
"Nabilah tana nan Kano, 'ya'yanta biyar. Yaya Habibu yana Abuja".
"Nima na yi aure Mairo. A lokacinda na riga na sallamawa zuciyata cewa na rasa ki, bazan
same ki ba, kin riga kin yimin nisa, kin zama matar wani na. Wanin da nake da tabbacin ko
mutuwa yayi bazai tafi ba tareda igiyoyin aurenki ba.
A halin yanzu Ina da 'ya'ya biyu, tareda ‘yar uwata Ikhlas. Sai dai har wannan lokacin da tunanin
Mairo nake kwana nake tashi. Sannan dashi nake ‘functioning, will you believe it?”

Ta dago fararen idanunta ta haske shi da su. Tace “sabida me Uncle?”
Babu jinkiri, babu inda-inda ya rausayar da kai ya ce
"sabida Soyayyarki Mairo!
Soyayyar da na ke yi miki a wancan lokacin Mairo, ta zarta hankali, ta zarta duk wani kokarin
hankali na ya fassarata. Mahaukaciyar soyayya ce Mairo, wadda ta makantar da ni daga daga
ido na dubi sauran mata. Ta dakusar da hasken mata ta Ikhlas daga cikin idanuna.
Na tabbatar tunda na rasa Mairo, to bazan samu makwafinta ba. Don haka ne Hajiya tasha
wuya da fari kamin inyi aure. Don nasan ko na yi, to bazan baiwa matar hakkokin da addini ya
ce na ba ta ba. Ba zan iya sallama mata zuciya da gangar jikina ba".

Ya taso ya tsugunna a gabanta, yana so su hada ido, amma ta ki hakan. Ya dora hannunshi
akan tafin kafarta. Ta lumshe ido a hankali ta bude su akan yatsun hannunshi da ke bisa tafin
kafarta. Ya dauke hannunshi ya zauna sosai a gabanta, ya ci gaba da cewa.
"Hajiyata ta shiga tashin hankali mai yawa, ta yi kuka, ta yi rokon duniya akan na yi aure, na
kasa Mairo.
Daga baya sai malamai ta sa suke yi min rokon Allah, sun tabbatar mata da zan yi aure, sai dai
da sauran LOKACI, tunda zuwa yake. Daga baya sai ta koma nasiha, amma zuciyata ta riga ta
bushe. Na tabbatar mata idan dai ba so ta ke na auri matar na dinga daukan alhakinta ba, to ta
kyale ni. Haka ta hakura ta zuba min ido, amma ta ce ba ta fasa yi min addu'a ba. A yau ina da yakinin
Allah Ya amsa addu'arta. For the first time da na ke ji a jikina LOKACI ya zo da zan yi AURE ba
irin na Ikhlas da ya zamto hadin iyayen mu ba. Wanda akayi ba tareda anyi shawara dani ko
neman yarda ta ba. 8/9/21, 12:19 PM - Kawata: 66


khlas diyar kanin mahaifina ce da Hajiya ta nema min aure bayan na kammala phD dina. A
yanzu haka muna da Maryam (namesake) dinki da Sabir.
Yau ne na ji wani 'feeling' a zuciya ta mai tuna min da cewa nima namiji ne KAMAR SAURAN
MAZA. Wadanda ke da buri a rayuwa, da kuma ‘hope’ (fatan) cikar burin nasu. Shin za ki tallafe
ni Mairo? Ki auri tsoho in his fourteeth?"

Hawaye na gudu a kundukukinta, ta ce.
"Uncle Junaidu idan ka kira kanka 'tsoho' ni kuma na kira kaina me? Tsohuwa?? (second
hand)? Ka bazawara...???"
Ya yi saurin kai hannu ya toshe mata baki ba tareda yayi niyyar hakan ba. Da sauri kuma ya
dauke hannunsa...
"Ni har gobe a Maironki na sanki, koda kuwa ace ke kika haife B.U.K baki dayanta…..."

"Idan haka ne, ni ma har gobe a Uncle Junaidu na sanka, bana son kara jin wannan kalmar ta
fito daga bakinka 'tsoho’.
Ya yi murmushi, ya ce.
"Da dai ana sakewa tuwo suna ne Mairo..."

Ta ce
"Ni ma ban ce a sake masa ba, a barshi a tuwonsa, don haka zauna a Uncle Junaidunka ba
V.C Junaid ba, na zauna a Mairona…....".
Suka bi junansu da kallo, kallon yarda, so da kauna da aminci. Gaskiyar masu iya magana da
suka ce, 'Soyayya ba ta tsufa, sai dai msoyan su tsufa’. Don haka sai mu bi JUNAID da MAIRO
da fatan ALHERI.
***









Alhaji Abdurarhaman ne ke zarya tsakanin falonshi da falon Haj. Aisha yana duba agogon
hannunshi, yana kuma azalzalarta kan ta yi sauri ta shirya jirgi ya kusa tashi, wanda zai tashi
dasu zuwa Kano a sanyin safiyar ta ranar litinin.
Amiru baya nan ya je China, don shigo da wasu kwanfutoci sabon shigowa, Zuwa wannan
lokacin ya yarda da nadamar ‘ya’yan nasa, da cikar YAKANAH da jarumtakar Amiru. Shekaru
uku kenan da rabuwar shi da Mairo ba tare da ya kara sanya ta a idanunshi ba.
Ya tattara karfin zuciyarshi ya karbi rayuwa ba Mairo, yana ganin lokaci ya yi da ya kamata yai
surprising din sa, da abin da zuciyarshi ke ciwo dominta. Da abinda rayuwarshi ke muradi.........
Duk wasu experiments.......... da ya dora shi a kansu...... bai fadi ko daya ba!!!.

Sannan Mairo ta kammala karatunta cikin kwanciyar hankali, duk wasu burirrikan rayuwarta ta
cika su, kamar yadda dan uwanta ke so. Ya kira Habibu a waya ya ce su hadu a Kanon gidan
Baffa suma za su taho yanzu.
Amina ta fito daga daki cikin shiri itama ta ce,
“Daddy don Allah zan biku Kanon, ina son ganin Amir da Habib”. Ya ce “Wuce muje Amina ‘yar
albarka”. (Amina mijinta ya rasu ne, a yanzu haka zaune take a gida).
Hajiya ta fito cikin shirinta, suka nufi cikin chevrolet din Daddy zuwa filin jirgi, inda suka tarar
jirgin ya kusa cika, don haka suna shiga ana rufe jirgin. Ba da jimawa ba ya soma keta hazo ya
lula cikin sararin samaniya.

Suna isa Airport din Malam Aminu, suka tarar da Habibu ya riga su isowa, ya kwashe su zuwa
Yakasai gidan Baffa.
Daidai lokacin da Mairo ta yowa Uncle Junaid rakiya zai tafi, tana dauke da Amir yana dauke da
Habib. A kuma daidai lokacin da Habibu ya sanyo hancin motarsa wadda ke dauke da su
Daddy harabar gidan. Daga Habibu, Daddy, Hajiya da Amina babu wanda zuciyarshi ba ta buga
ba da ganin Mairo da wannan sankacecen mutum, ma’abocin zati da kamala, da kwarjini
bayananne daga sarkin halitta.

Karo na farko da Uncle Junaid ya dora idonshi a kan Yaya Habibu da baya bukatar a gabatar
mishi, sakamakon tangamemen hotonsa dake sitting room din Baffa.
Shima Habibu a take ya gane wannan shi ne JUNAIDUN MAIRO, da Baffa ya kyankyasa mishi
a waya, cewa ya dawo neman auren Mairo.
Jikin Habib a sanyaye ya fito daga motar, gwiwoyinshi kamar an rarrade su da murfin kwano.
Suka yi hannu da Uncle ya yin da Uncle ya kai gwiwoyinshi kasa yana gaida Alh.
Abdurrahaman. Amina ta mika hannu ta karbi Amir a hannunshi suka hada ido da Junaidun. A
take ya ga fuskar Amir da Habib a fuskarta, ita kuma ta ji wani ‘magnet’ na jan zuciyarta a kan
wannan mutum da ba ta sani ba, ba ta taba gani ba. Ya dago suka hada ido ta yi saurin
sunkuyar da kanta.
Mairo na son gabatar da Yaya Habibu ga Uncle amma kunyar su Daddy ta hana ta. Ya shiga
mota ya tafi su Amir na ta kuka sai sun bishi. Hajiya ta kama hannun Mairo, Amina kuwa
rungume ta tayi tana hawaye, a haka suka shiga dakin Habiba. Shi kuma Habibu da Daddy
suka wuce falon bakin Baffa. Cikin dan lokaci Habiba da Hajara sun baibaye su Hajiya da cima ta girmamawa da ruwa da
lemu, sun zauna ana ta gaggaisawa. Mairo da Amina dakin Hajara suka wuce suka bar Hajiya
da su Habiba. A nan ne Amina take labartawa Mairo rasuwar Ghali (mijinta) watanni biyar da
suka gabata. Ba tare da Allah ya basu haihuwa ba. Mairo har da hawaye na tausayawa Amina, don ita kanta shaida ce a kan matsananciyar
soyayyar da suke yiwa juna. Mairo na so ta tambaye ta AMEERU ba ta so ta bada kanta. Amiru
ya yi mata miki mai girma a zuciyarta. Tunda suka rabu bai taba nema ko sau daya ya ganta ba,
sai ‘ya’yansa. To akan me ita zata nemeshi? Ta tabbata duk inda yake yanzu ya dade da shafe ta a babin rayuwarsa. Watakila ma ya kara
aure bayan Hanan, ya sallamawa wata wannan gangar jikin da ada ta dauka mallakinta ne ita
kadai. Don ta san Dan Abdurrahaman Gaya, ba zai iya kaiwa tsawon wannan lokacin ba tare da
aure ba, in ta yi la’kari da halittarsa, na mutum mai tsananin yawan bukata. Sannan Hanan,
bata da surar irin matar da yake son aure. Ko kuma watakila ya komawa banasariyar matarshi?
Allah masani.

Amina ta ce
“Rayuwa tafe take tare da destiny (kaddara) kala-kala Aunty Mairo, kin manta da brother, kin
bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki, kin kara kyau, kin kara kiba, kin kara haiba da
kamala. Sabanin shi da a kullum yake kara lalacewa.
Cikin shekaru ukun nan ban kara ganin dariyar Yaya Amiru ba, ki yafewa mai kaunarki wanda
ya sadaukar da zuciyarsa ga soyayyarki. Ku tallafi juna, ku baiwa zuciyoyinku abin da suke so.
Hajiyata da ‘yan uwana sun yi kuskure, sun kuma gane kuskuren su, sun yi nadama mai suna
nadama amma ku, (keda Amiru), Daddy da Habibu har yau kun ki karbar tuban su, ban san me
yasa ba”.
Mairo ta yi murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce,
“Mun karbi tubansu man? Watakila dai iyakar zaman ke nan, babu saura, tunda aka kawo
wannan lokacin. Shi ya gaya miki yana son komen? Yana da mace irin Hanan a gefe?”
Mamaki ya kama Amina, ta tabbata Mairo ba ta san tare suka yi waje ita da Hanan ba. Ta ce,
“A kan sakin Hanan aka yi naki, Allah sarki brother! Zurfin cikin shi na bani mamaki. A halin

yanzu Hanan tana Porthercourt ‘ya’yanta biyu tare da mijinta Ramadan wani ma’aikacin
kwastom”.

Mairo ta yi shiru, kamar an zuke jinin jikinta. Tausayin Amiru ya kama ta, Allah kadai ya san
halin da rayuwarshi ke ciki.
Ta tura hannu cikin jakarta ta zaro wasu kananun katina da aka yiwa rubutu da kumfar golden,
ta dorawa Amina a cinya.

A kasalance Amina ta dauka, kati ne na gayyatar daurin auren PROF. JUNAID ATIKU
GALADANCHI da DR. MARYAM MOHAMMAD BEDI, wanda za a gabatar kwanaki goma sha
hudu masu zuwa. Ba ta kai karshen karanta katin bikin ba Amina ta rushe da kuka.
Ashe masu kukan suna da yawa, domin a can falon Baffa ma Hajiya ce ke ta kuka tana rokon
Alh. Abbas ya yi wa Amiru uziri, su ne da laifi ba shi ba. Su kuma ba su yi hakan da nufin A
BARI YA HUCE...... ba, sai don a bawa Mairo dama ta sarara ta cika burin neman iliminta. Cikin
nutsuwa da kwanciyar hankali
Daddy ya ce.
“Idan da mai laifi to ni ne, don ni na hana Amiru yin wani yunkuri na dawo da iyalinsa har
tsawon wannan lokacin. Ina so in koya masa jarumtaka, in nusar da shi cewa;
“kallafa rai a kan abin da ake so, da amanna da cewa samuwar abin nan kadai shi ne samun
lafiya da kwanciyar hankali ba shi ne ba”.
Dauriya, hakuri da juriya da tawakkkali sune halayen da ake son namiji ya suffantu dasu. Kuma
na gode Allah....... DUK WASU EXPERIMENTS DANA YIWA AMEERU BAI FADI KO DAYA
BA..............!!!”

Baffa ya jinjina kai ya ce.
“Nima in son samu ne, na fi son Mairo ta koma wurin mijinta ta tarbiyanci ‘ya’yanta a gabanta.
Amma Alh. Junaidu ya zarta duk yadda kuke tunani a wurin mu. Don haka bana cikin wannan
magana..... Zabi yana ga Mairo, tunda ita Allah ya baiwa damar zaben mijin da za ta iya zama
da shi a halin yanzu. Don haka ku bani kwana biyu zan tuntube ta”. Habibu bai ce komai ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login