Showing 75001 words to 78000 words out of 79746 words
Chapter 26 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
don ba shi da ta cewar, bai san me zai ce ba, bayan Allah ya yiwa
Mairo zabin alheri, wannan karon ba zai yi shisshigi ba.
***
SUNA tafe cikin jirgi amma Daddy baya cikin nutsuwa. Tausayin gudan ransa ya ishe shi, ko ma
me ya faru ya tabbata shi ya jawo mishi. Shekaru uku ba kwana uku ba!!! Ya nesanta Amir da
iyalinshi a kan laifin da ba nashi ba. A kan hujjojin sa da basu da karfi.
Don haka suna sauka a jirgi ya bude waya ya kira Amiru yana nishi kamar mai ciwon asthma.
Ya ce,
“Ka bar duk abin da kake ka taho, ka wuce Kano ka nemi sasanci da iyalinka in har kana so. Na
amince maka Amiru, da sanya albarkata.... saura kwana goma sha hudu a daurawa Mairo
aure!!!”
Ga mamakin Daddy sai ya yi murmushi, wanda har sautinsa ya ratso cikin wayar, ya ce.
“Ka kwantar da hankalinka Daddy, na dade da sanyawa zuciyata salama, na yi amanna da
cewa idan akwai sauran zama tsakanina da Mairo, to za ta dawo mini ko ba dade ko ba jima”.
****
Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa ne a harabar gidan Dr. Mairo, wanda ke a Area C cikin sabuwar
jami’ar Bayero suna wasan kwallon kwando, ya yin da a gefensu Habib da Amir ne tare da
wasu sa’o’insu ‘ya’yan makota suke wasan tsaren kekuna, yara masu ban sha’awa. Suna sanye
da kayan sanyi masu laushi farare sol, an rubuta I LUV MUMMY, kafafunsu daure cikin farin
cambas, sunyi kyau har sun gaji kamar ‘ya’yan South-Western.
Daidai lokacin da motar kirar (Camero, 2 Door) ta yi parking and hankali a gefensu, matukin
motar ya duba katin da ke hannunsa ya tabbatar lambar gidan ta yi daidai da wadda ya gani a
rubuce. Sai ya kashe ya fito.
Sanye yake da suwaitar ‘Dolce & Gabbana’ mai dogon hannu, da shudin wandon jeans. Ya yin
da rigar ta kasance fari da ratshin ja da blue. Ga duk wanda ya san shi, ba zai yi gaggawar
gane shi ba, saboda yadda fatar jikinshi ta kara kwanciya, tare da goguwa mai nuni da alamun
hutu. Ya jawo bakin PRADA ya saya kwayar idanun shi. Daidai lokacin da idanunshi suka kai ga
sanyin idaniyarshi.
Ya dade yana kallon su yana murmushi, har bai san tsayin mintunan da ya bata a tsaye ba, ba
tare da yaje gare su ba, don ganin yadda hankalinsu ya raja’a a kan wasansu. Har sai lokacin
da Amir ya karawa Habib keken shi ya fadi, ya sanya kuka.
Da sassarfa ya karasa garesu, ya mika hannuwa ya dauki Habib wanda ke ta kuka ya rungume
a kirjinshi, ya kuma kama hannun Amir suka doshi kofar gidan. Su Lawan suka gaishe shi suka
koma ga kwallon su, Lawan na radawa Ahmed Baban su Amir ne.
Aikin marking takardun dalibai ya kacame mata, ta yi dai-dai da takardu a tsakiyar falon sanye
cikin riga da wandon da basu kama jikinta ba, kanta babu kallabi, tufkar gashinta a tsakiyar
kanta. Fatar nan ta kara zama fresh ta nuna mace danya sharaf, mai wadatar jini a jika, ta
yadda ba za ka yi tunanin ta taba haihuwa ba. Sassanyan kamshin ‘miyaki’ da ta dade da sani ne ya bakunci hancinta. A razane ta cira kai. Ta
sake yin arba, da dan Abdurrahaman Gaya. Rungume da ‘yan biyunshi masu tsananin kama
dashi.
Sai dai wannan AMIRUN ya sha banban da wanda ta bari shekaru uku a baya. Ya sirance, ya
bar lallausar kasumba ta bata kyawun shi da tsarin shi, duk da haka yana nan a Amirun sa, dan
gaye, mai kyau, kuma mai sanyi, wanda idaniya ba za ta taba gajiyawa da kallon shi ba.
Mikewa ta yi tsaye kamar an umarce ta da yin hakan, alama ce ta girmamawa a wajen bature.
Ta rasa cikin yanayin da ta tsinci kanta tsakanin rudewa da gigicewa. Sannan wani sanyi ya
tsirga a zuciyarta, ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar shi din ne, ba mai kama da shi ba.
Kafin ta yi wani action ya daga dogayen kafafunshi da sassarfa ya isa gareta, ya hada ta ita da
yaran ya rungume, jikinshi in ban da kyarma ba abinda yake. Ya kankame ta ita da yaran
hawayenshi na sauka a gadon bayansu. Ya ce,
“Mairo kin yi min alkawari........ ba za ki taba barina ba, kin yi min alkawari...... we are meant for
each other. Me yasa kika karya?
Kin riga kin sani kowanne numfashina yana fita ne tare da sunanki. Me yasa kika amsawa
Uncle Junaidu, kika kasa jirana mu maida auren mu? Kika kasa yi min uziri? Uzurin da zan yiwa
Daddy biyayya, kada ya ga rashin juriyata?
Ya ya zamu yi da ’ya’yan da Allah ya bamu bayan fidda rai da samun su? Baki yi sha’awar ki
rayu tare da su ba? Ki basu tarbiyya irin taki? Jarrabawa ce Allah ya yi mana, kuma mun cinye
ta da ikonsa, yanzu ne ya kamata mu karbi sakamakon mu.
Zan nemi Uncle Junaid in roke shi alfarmar ya bar min ke, ko da hakan na nufin zan durkusa
masa akan gwiwoyina, don na fishi bukatarki, ‘ya’yanmu sun fishi bukatarki.
Kalle ni. Am all alone Mairo, leading a shattered life.........!!!
Dukkansu basu ankara da wanzuwar mutum a falon ba, tsayin lokacin da suke rungume da juna
suna kuka dukkaninsu, su suna yi ‘ya’yan na yi. Sai jin karar rufe kofa da aka yi a hankali, suka
juyo dukkanninsu, babu kowa!
Amma kamshin ‘Irresistible Givenchy’ da Mairo ta ji, ya tabbatar mata da ko wane ne ya shigo,
ya kuma fita, ba tare da ya yi wani motsi da zai katse su daga kololuwar duniyar shaukin
soyayyar juna da kewar juna da suka fada ciki ba.
Hankalin Mairo ya tashi, ta tabbatar Uncle Junaidu ya ga Amiru, cikin halin da ita kanta ba ta
san wanne ne ba. Ta zame da karfi, da gudu ta biyo bayan shi amma sai kurar motarshi da
hasken fitilar motar shi ta gani.
Ta rasa ina za ta sa kanta, sai ta kifa kai cikin tafukanta ta soma kuka. La shakka maza biyu
take so, ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.
Lallashi na duniya, ban baki na duniya Amiru ya yi amma Mairo ta ki ce da shi komai. Ransa ya
fara baci, amma ya danne fushinsa, tunda mai nema.....baya fushi. Ya ce,
“Shi ke nan na tafi Mairo, na ba ki daga yau zuwa gobe ki yi tunani, zan je wajen Baffa daga nan
zan wuce inda na yi masauki, sai gobe insha Allahu”.
Ya dauki Amir ya kama hannun Habib za su fita, ta taso da gudu ta rike rigar shi ta baya cikin
kuka ta ce,
“Ina za ka kai su?”
Ya harare ta ya ce, “Gidan ubansu, tunda bakya son ubansu to suma bakya son su”.
Ta ce, “Ni na ce hakan?”
Ya yi mata kallon rahma, sannan ya ce, “Za su taya ni kwana ne”.
Ba ta yi magana ba, ta shige daki ta hado musu duk abin da za su bukata cikin karamar jaka ta
ba shi. Suka ce, “Mummy bye-bye”. Ita ma ta daga hannun tana yi musu bye-bye din har suka
fice daga falon.
Cikin hanzari ta dauki waya ta soma kiran nambar V.C Junaidu, bugu daya ya amsa, babu komi
cikin muryarshi sai kulawa ya ce,
“Ya aka yi MARYAMA?”
Ta shafe hawaye ta ce,
“Ka fasa zuwa yin ‘dinner’ din?”
Ya yi murmushi ya runtse idonsa, tsigar jikinsa na wani irin tashi saboda KISHI. Idanunshi na
tariyo mishi hoton abin da ya gani, wani image da bai taba ganin mafi muninsa a rayuwarsa ba,
cikin sanyin murya ya ce,
“Na zo na tarar kina da bako, don haka na tafi”.
A raunane ta ce,
“Ba bako bane Baban su Amir ne ya zo ganin su”.
A ranshi ya ce,
“Ka ji rainin hankali irin na ‘ya’ya mata....”. Amma a zahiri ya ce,
“Ki saurare ni, idan na gama da Baffa zan kira ki”. Ya kashe layin.
Damuwar duniya ta ishe ta, ta kuma rasa abin yi, ta shiga halin rudani. Wadannan dakarun
maza, jaruman soyayya sun sanya ta a kwana. Tana neman Dina, tana neman Nabilah..... don
neman shawara, tunda an ce “Aikin mai shawara baya baci”.
Ta kira wayar Nabila, ta ce, “In kina gari zan zo gobe around 11”. Ta ce,
“Ina nan amaryar uncle sai kin zo”.
8/9/21, 9:04 PM - Kawata: 87
Junaid na yin parking a harabar gidan Baffa, shima Amiru na sawo kai, suka yiwa juna
kallon-kallo, bayan kowanne ya fito daga motarsa. Kwayar idon Amiru har girgiza take saboda
KISHI, akwai wani feeling na kishi iri daya a zuciyar kowannen su, sai dai babu wanda ya bari
nashi ya fito fili. Da sauri Amir da dan uwansa suka balle kofa suka nufi Uncle Junaid suka rungume kafafun shi,
ya russuna ya kama kowannen su da hannu daya ya dauke su, suna ta zuba mishi surutu wai
Mummy tana kuka, don Abban Abuja ya taho dasu. Ya yi murmushi ya ce,
“Zamu je mu lallashi Mummy ta daina kuka”.
An ce “mai Da, wawa..... sai Amiru ya karaso a hankali, ya mikawa V.C hannu, suka yi
musabaha, aka rasa wanda zai fara janye hannunsa. Dai-dai sanda Baffa ya fito, ya yi musu
jagora zuwa falon ganawa da bakinsa.
Kallo daya zaka yiwa Alh. Abbas, ka san cewa shima a rikice yake, ya debo gorar ruwa da
tambulan cikin firij ya baiwa kowannen su. Aka rasa mai fara sha, aka rasa mai fara magana.
Har shi kansa Baffan kuwa, kafin Junaid ya yi gyaran murya cike da tausayin Baban Amir da
Habib da ya ke ratsa zuciyarsa. Da ganin wannan ‘giant’ kaga wanda ke fama da dingimemiyar
soyayya, wadda ta rasa madafa. Yaran sun baibaye Uncle Junaidu sun kwanta a jikinsa.
Ya ce,
“Baffa na janye niyyata ta auren Maryama! Na hakura har ga Allah na barwa Baban Amir da
Habib, ina bayan Maryama ta koma dakin mijinta uban ‘ya’yanta, don samun kwanciyar
hankalin kowannen mu.
Ba lallai sai na auri Mairo ba shi ne zan nuna ina kaunar ta, a’a, ni da Mairo mun wuce haka,
Yaya ne da kanwarsa, alakarmu hadi ne daga Allah, ba don mu yi aure ba.
Ina son ‘yan biyu su tashi gaban uwa da ubansu......kamar yadda Maryama ta tashi gaban
Innarta da Babanta, ta san dadin iyaye, tasan amfanin su. Nikuma ina bukatar addu’arku Baffa,
da fatan dorewar zumunci na har abada a tsakanin mu”.
Baffa ya ce,
“Allahu Akbar! Allahu akbar!! Wannan shi ne halin GIRMA, halin ‘yan aljannah!! Da gaske ne
kai da Mairo kun fi karfin soyayyah!!! Sai ‘yan uwantaka, mun gode da wannan karamci
Junaidu, Allah ya biya maka bukatunka na duniya da lahira, ya kara maka daukaka, ya baka
duk abinda kakeso a duniya da lahira......”.
Amiru ya cira kai ya tsura ma Junaid ido ya ce, “In aka yi hakan, ni kuma na so kaina.......”.
Junaidu ya ce,
“Ni kuma ba zan auri Mairo alhalin zuciyarta na ga tsohon mijinta ba”.
Amiru yace
“nayi rantsuwa da Allah! Mairo tayi maka son da ni bata yimin ba, na aure ta ba da son ranta ba,
sai a hankali na koya mata soyayyata. Uncle Junaidu kana da matsayi mai girma a gun Mairo,
wanda ni bani da shi.....”
Junaid ya rausayar da kai cikin jin wani irin frin ciki a zuciyarsa, koda wannan ya tsira ya
tabbata ya isheshi rayuwar duniya, yayi murmushi ya ce,
“Kauna ce tsakanina da Mairo Amiru ba soyayyar aure ba tun daga ranar dana fara ganinta, a
halin yanzu jin nauyin junanmu ya fi yawa, wanda da kyar za mu iya sakin jiki da juna mu yi
rayuwar aure yadda ya kamata. Ka yarda ko kada ka yarda, kai Mairo take yiwa soyayyar
aure....!”
Amiru ya lumshe ido, ya ce,
“Uncle Junaid, bani da bakin da zan gode maka....... bani da abin da zan biyaka wannan
alfarmar da ka yi min.....” Uncle ya yi murmushi ya katseshi yace,
“Kana dashi Amiru!.
Mairo ta sha bani labarin soyayyar da kanwarka Amina take yi mata, wannan wadda suka zo
mai kama da kai. Ta shaida min cewa maigidanta ya rasu. Ka bani Amina in aura Amiru, don
wanzar da dauwamammen zumunci a tsakanin mu”.
Cikin al’ajabi Amiru ya ce,
“Amina is special a gare ni ko a cikin kannena goma sha biyu, lallai Amina is among the
luckiest....
Na taba gayawa Habibu zan roke ka ka bar mini Mairo, ni kuma in baka kannena hudu ba lefe
ba sadaki. Na fada ne kawai a fatar baki, ashe Mala’iku sun amsa. Uncle Allah ya kara
GIRMA!”.
Suka hade hannunsu suka cure kamar ba za su saki ba cike da wata shahararriyar kauna daga
Allah, Baffa ya ja su doguwar addu’a suka shafa. Baffa ya ce, su barshi da Mairo, su ci gaba da
shirye-shiryen su, yana so zai yi mata ba-zata ne. Suka yi murmushi. ***
Kwana ta yi tana gwada lambar Uncle Junaid ba ta samu ba. Ta shiga damuwa sosai. Tsoron ta
kada Allah yasa fushi ya yi saboda ganinta da ya yi tare da tsohon mijinta.
Abu kamar wasa Uncle har kwana uku babu wayarshi babu kafarsa cikin gidanta, don haka ta yi
tattaki har office amma ba ta same shi ba. Shima Amiru ko sallama bai zo ya yi mata ba, ya
kwashe ‘ya’yansa ya tafi Abuja dasu ba ta kara jin duriyarsu ba.
Da albishir mai dadi ya tari Alh. Abdurrahaman da Hajiya Aisha, ya kuma gaya musu bukatar
V.C na auren Amina. Daddy da Hajiya suka yi ta hamdala tare da kara yawaita sadaka. Ko da
Amir ya tuntubi Amina ya yi mamakin amincewar ta nan take. Bai san ita tunda ta dora ido a kan
Junaidun ba ta kara gane kanta ba.
Ya yiwa gidan Habibu tsinke a daren bakinshi ya kasa rufo, zumudin ya gaza boyuwa. Habibu
ya dafa kafadarshi ya ce
“Angon Harrit ya aka yi?”
Ya harare shi ya ture hannunsa daga kafadunshi, ya ce,
“Kai komi mai muhimmanci sai kasa iskanci da shakiyanci a cikinsa, to bani goro in baka
albishir”. Ya ce,
“To bari ina zuwa”.
Ya fito jim kadan bayan shigarsa da kwalin ‘Aspen’ da ‘Lighter’, ya zari daya ya kunna ya manna
mishi a baki. Da sauri ya ture ya bige hannunsa, tabar ta fadi, ya bi ya take da takalminsa, cikin
takaici ya ce,
“Wai don Allah Yaya Habibu, yaushe za ka girma ne?”
Ya yi dariya ya ce,
“Sai ranar da son Mairo ya daina kai ka hanyar lahira, ya daina kwantar da kai a asibiti, wato
ranar da ka zama namijin duniya”.
Dina ta yi dariya ta ce,
“Rabu da shi Amiru, muna nan muna jiran nashi turn din, idan ya gano wata ‘yar kwailar. Irin su
Habib ba ciwo suke a kan soyayya ba, rijiya suke fadawa dungurungum su kashe kansu in sun
rasa samun wadda suke so....”.
Ya ce,
“Amma kin yanke ni ke da sirikinki bashi kuka ci, akwai ranar da zaku biya shi”. Amiru ya ce,
“Na ma fasa baka albishir din, tunda da Taba za ka hadani, ka jawo min fushin Mairo, ban ji ba
ban gani ba......”.
Ya kamo hannunshi ya fizge, yana dariya ya ce, “Haba dear.... tuni na ji albishir din, ai Baffa ya
gaya min komi yanzun nan, kun yiwa V.C Junaidu fin karfi kun toshe masa baki da Amina”. Ya yi
dariya ya ce,
“V.C mutum ne mai saukin kai, yadda na zaceshi ba haka yake ba, ya ji tausayinmu ya tallafi
rayuwarmu shima Allah ya tallafesa. Bani da abin da zan biya shi wannan sadaukarwa da ya yi
min koda na bashi my favourite sister. Wanda na san zai karba ne ba don so ba, sai don
kulluwar zumunci a tsakaninmu”.
****
Tana shirin fita office wayar Baffa ta shigo, da hanzari ta amsa cike da girmamawa. Bayan sun
gaisa ya ce,
“Kina gida ne yanzu?” Ta ce,
“A’a, ina shirin fita ne zan ba da lacca 8-10”. Ya ce, “To in kin fito ki zo ina son ganin ki”. Ta ce,
“Babu damuwa Baffa sai na iso”. Suka aje wayar a lokaci daya.
Karfe goma na safe ta fito daga ‘twin-theater’ cikin rakiyar zugar dalibanta, wadanda suka riko
mata jakar hannunta da takardunta har zuwa inda ta adana Terrain din ta, ta karbi kayan
hannunsu suka yi sallama suka koma, ita kuma ta zaburo mota sai Yakasai gidan Alh. Abbas.
Bayan sun gaisa da Habiba da Hajara da su Rahama, ta samu Baffa a falonsa, ya nuna mata
waje ta zauna, ta zamo daga kujera ta dira gwiwoyinta a kasa ta gaida shi. Ya amsa yana duban
ta sosai, ganin yadda ta ramar da kanta cikin ‘yan kwanaki kalilan saboda damuwa. Bai nuna
mata komi game da zuwan Junaid da Amir ba, tambaya ta farko da ya watso mata ita ce.
“Mairo maza biyu za ki aura ne???”
Ta cira kai da sauri ta dubi Baffanta, ya girgiza kai ya ce, “Yo maza biyu mana?
Kin amshi maganar Junaidu, an gama komi sai shafa fatiha kadai ya rage, sai kuma ki turo min
Alh. Abdurrahaman da kansa ya zo bikon ki? Sannan shima Amiru ya zo, dukkanninsu da rokon
a maida aure.
To dukkansu akwai mutunci da ganin girman