Showing 45001 words to 48000 words out of 79746 words

Chapter 16 - A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

da ta yarda sun kara hada ido ba.

Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa
daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata
munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina.
"Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?"
Dina ta yi shiru, ya ce "Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta
magana ni kadai?"
Ta ce "To me ya faru?"
"Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a'ah?
Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?"
Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce
"Am... Eh, ai sako zata kai wa Amirun".
A fusace ya ce
"Sakon me?"
Ta ce "Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu".
Ya yi dogon tsaki, ji kake 'tsiiittt!' Ya maida kallonshi ga Mairo
"Ba ni wayarki".
Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta
mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi
ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin.

Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga
mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba
ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri.
Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce "Kin same shi?"
Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo.
Dina ta sa yatsunta tana share mata, "Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah.
Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da
shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga
neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba".

Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba
ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu
bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga
shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta.
***
A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk
'yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani.
Maryam Muhammad Bedi, ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta
kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin
ko da dar a zuciyarta ba.
Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su
furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud's stages of
psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga
phallic-stage... Anal stage... da 'yan uwansu. Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!!
Habibu da ke cikin 'yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka.
Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace... Malam Muhammad Bedi, zai
dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al'umma.

Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar
ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan
ajinsu don yayi supervising hakan.
Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta
yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo.
"Mairo 'yan makaranta......Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu".
Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce.
"Zo zauna, mota zan sake miki".

Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa "Gaya
min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai
da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta
fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa
zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai.

Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al'amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi
sati daya, me kike so in kawo miki?
Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da
sauransu. Ke kuma fa?"
Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, "Ladidi nake son gani".
Ya ce
"Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba

zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki
zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta".
Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta.
Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta
sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman
sociology. Habibu na addu'ar Allah Ya sa ba sociology'n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba.
Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke
so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato
Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba.

Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo
ga Ladidi. Ita da Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da
ya kare, sannan suka nufi wani kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta
zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya,
ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida.

Duk a kokarinsa na son farantawa 'yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina,
ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta
samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba.
Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka
lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu.
Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba ta damu ba, ta ci gaba
da ayyukan gabanta.
Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma
an sanar da ita wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta
samu Habib ba.
Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba
ta shiga. Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba.
A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da
labarin Habibu? Sun kasa samunshi a waya.

Baffa ya yi gyaran murya ya ce
"Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja
wajenshi ban san halin da suke ciki ba".
Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya
kasance ciwon Amirun yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al'amuran
rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da
baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban ikon Allah. Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba.

Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda
iyakacinsa fatar bakinta, ta ce
"Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi".

Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce "Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai
ko? Tun ranar da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba".
Dina ta shirga karya
"Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba".
Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo
ta wutsiyar idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu'azzam Kanti, ke kwararowa.
(Alkawari bayan rai). Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta,
da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha
ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani
bakon al'amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba zata ce mene ne ko na mene ne
ba.

Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta
yaye labulen dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature
yin harkokin gabansa ba.
Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma
duk lullube suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani
wajen rage azabtaccen sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba.
Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat
da bakin wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk
bakake wul. Sakonnin suka soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da
sabbin sakonni guda goma sha biyar. Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta
kasa samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh
inda ita kuma ta ke sanar da ita cewa akwai test' karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin.
Sai na wani dan ajinsu Henry baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don
mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta
ba.
Ta yi mishi ta'aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta,
kasancewar an yi shi ne cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya
aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin rubutun a gurguje.

"Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu
kansu cikin gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a
banza.
Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na
zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci
gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci
ko matsatsi na rayuwa ba". -mai son ki.

Ta karanta ya fi cikin 'ya'yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba.
Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon

daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da
zuciyarta ba.

To haka washegari, mai 'logo' na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.

"........ Some one misses you!".

Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A
ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin
Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga
can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga
mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu,
wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.
Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce "Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene
ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina
a tashe ya ke".
Ya ce "Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don't want to lose AMEERU. (bana so in rasa
Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai
yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo".
Dina ta kidime "Lafiya? Me ya faru da Amirun?"
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so
ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah
Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce.
8/3/21, 9:03 PM - Kawata: B
Cikin dauriya ta ce "Habib, me ya faru da shi? Ka gayamin don Allah. Sai dai na taho ni kadai,
Mairo jarrabawa zata fara zanawa, wadda idan ba ta yi ba, sai ta maimaita shekarar".
Da budaddiyar murya ya ce.
"Karatun ma, ai ina jin ta barshi kenan. AURE zan yi mata".

Dina ta kyafkyafta 'yan idanunta ta sato kallon Mairo, cike da fargabar Allah Ya sa ba ta jiyo abin
da Yayanta ya ce ba. Ta ga hankalinta ba ya kanta, ya tafi ga lallashin Little Mairo ta ci abincin
da ta ke ba ta da dan kankanin cokali. Ta godewa Allah da abin da ya darsu a ranta (mutuwar
Amiru) ba shi ne ba. Ta kawo gwauron numfashi ta ce "Kano za mu taho ko Abuja?" Ya ce
"Ku biyo jirgin Abuja, idan kun sauka ki kirani zan zo na dauke ku".

Don haka a daren yau bakidayansa Dina ba ta samu isasshen barci ba. Tausayin Mairo ya cika
mata zuciya. Irin yadda ta ke wahala akan karatun nan, ta kwallafa rai a kansa, kullum cikin
‘solving assignments' ace ya tashi a banza! Shekaru biyu cur! Sai dai kwarin gwiwar da ta ke da
shi, shi ne Habibu ba zai kai 'yar uwarsa inda za ta tozarta ko ta wulakanta ba. Duk son da ta ke

yi mata ta tabbata bai yi rabin-rabin wanda shi yake yi mata ba. Sannan akan Amiru ba abinda
bazai iya ba.
Da safe karfe takwas ta yi shirin fita don yi musu booking din tickets na jirgin ‘Lufthansa’ wanda
zai tashi karfe goma na daren ranar. Sannan ta dawo, ta cimma Mairo ta fito daga wanka tana
shafa akan stool ta ce (tana mai kawas da kai) "ki hada kayanki masu dan yawa, gida Najeriya
zamu tafi, ban san kuma ranar da zamu dawo ba". Tana mai kawas da idanunta daga gare ta, don ba zata iya fada mata abin da Habibun ya gaya
mata ba.
Cikin mamaki Mairo ta ce
"Me ya faru? Irin wannan tafiya haka unexpected?"
Dina ta ce
"Bai fada min ba, amma dai ya ce lallai mu tafi".
Kamar ta yi kuka, ta ce "Ina da 'test' yau, kuma jibi za mu fara jarrabawa, kuma Yaya Habibu ya
sani, yaya yake so in yi?"
Dina ta ce
"Hakuri za ki yi, haka Allah Ya shirya miki. Wani hanin ga Allah baiwa ne".
***




J
irginsu ya sauka a Abuja karfe biyar na asubahi. Ban da kunci da kumburi ba abin da Mairo ta
ke yi. Dina sai lallabata ta ke tana ba ta hakuri. Idan takaicin ya yi takaici, sai ta kai hankici ta
tsane hakwayen da ke 'racing' a fararen kundukukinta.
Idan Dina ta ce "Ki yi wa Allah Mairo ki yi hakuri..."
Sai ta ce
"Haba Aunty Dina? Shekaru biyu ina wahala, in fadi, in tashi amma ace sun tashi a banza?"

Wani farin dattijo, dan kimanin shekaru sittin da biyar, wanda alamun jin dadi, tsantsar ilimi da
gogewar rayuwa ya boye shekarun nashi. Sanye cikin kaftan na wata irin farar sassalkar
shadda da akalla ta baiwa naira dubu dari baya, yana da tsagin biyu-biyu a gefen fuskarsa na
Fulanin Gaya. Biye da shi escort ne har guda biyu cikin bakaken suit wadanda harsashi na
kowacce irin bindiga ba ya huda su, sun maka 'dark-spaces' fuskokinsu kamar hadari, sabanin
dattijon wanda kyakkyawar fuskarsa ke yalwace da ni'imtaccen murmushi wanda da alama
tabbatacce ne akan fuskarsa cikin kowanne yanayi.
Abin nufi, cikin halin bakin ciki da farin ciki, kwanciyar hankali da tashin hankali, wannan
sassanyan murmushin ba ya gushewa daga fuskarsa. A takaice dai na halitta ne, watau 'nature',
shi ne a gaba wajen tarbar su Habibu a baya.
Don haka kwarjininshi da haibarshi ya sanya dole Mairo ta daina kukan da ta ke, ta tsugunna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login