Showing 18001 words to 21000 words out of 36965 words

Chapter 7 - FUTUHATUL KHAIR Yarinyar Da Ta Zo Da Alkhairi by Xainab Y Hussain

amma kememe taqi fita, ita ba'akwamaceta ba, sai itace, wallahi bazan kulata ba, Idan yaso ta tafi gida yanzu ma
Umma ce tace Fadeela Ba haka ake ba, kuma kedakanki kike cemata haka, idan wani yafada fa, kuma da agabanta kika fad'a bazataji dad'i ba
Kya saurari uzurinta, kafin ki yanke hukunci, kuma ke kanki kika kalleta kinsan badaga qaramin gida ta fito ba
Kurunga jin uxurin mutum, kafin ku yanke hukunci, yarinya mai hankali da addini, plx Fadeela adena arin haka
Kuka naje naga tanayi, kuma yanada nasaba da abinda kikayi mata, narashin kulata da kike
Huum, Umma hakane Insha Allah bazan qara ba, bari naje, dayafi kuwa dan bakiyi daidai ba

Haurawa sama tayi, qofan abud'e take, shiga tai, ganinta tai takifa kanta a pillow, qarasa wa tai, d'ago kanta tai
Akan cinyanta tasaka kan FUTHA, fushi koh FUTHA menamiki kike kuka akan nayi miki magana kibar wulaqanci shine zaki dawo qasa ki kwanta
Kai takad'a bahaka ba, huum to yane?, bayani tafara mata akan batason tafita tarasa yazatayi magana, kuma ita suna zuwa wajanta dan basu san ita bata magana ba
Bayani tamata, sannan ta ringa bata haquri akan bazata kuma ba
Kafin me sai dariya, haka suka kasance har ranar dazasu koma

Kuma Ya Farouq shima aranar ko washe gari zai dawo daga Lagos

@ut@r h@jiy@โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [23/10 7:38 pm] @ut@r h@jiy@โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’ฆ๐Ÿ‘—: *FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA Luv*

*page 79-80*


Tsit kake jin parlour na gidan. Masu hayaniya basu nan, antafi kasuwa siyayya, anbar Umma ita kad'ai agida
FUTHA kinga wani yari wallahi tai kyau, ki d'auka, dariya aka saka saboda yarin wani qatone ga ita kuma batason yari qato
Uhum tace
Haba hajiya ki d'auka mana zan miki ragi, yana magana yana wani kashe ido
Dariya akayi ganin yanda tayi kicin kicin da fuska, jitayi dama tana magana ta zageshi
Babba ne amma sai wani kashe ido yake yana matsowa kusa da ita, hannu ta d'aga alamar ya isheta surutun da yake
Ganin basu gane ba, fita tai ta tsaya har suka gama suka fito

Ko da aka koma gida, labarin aka ringa bayarwa, Umma itama saidata dara tata dariyar
Kayansu duk sungama had'a wa, saijiran driver yazo a tafi,
Hajiya Zainab taso ta had'u da yarinyar da qawarta kebata labari, Allah baiyi ba, lokacin da taje gidan ta kuma tana libiya, shiyasa basu had'u ba

Mama dai tunda Hajya Zainab tazo ta yinarmata taketa kallon ta, takasa sanin ina tasan mai irin fuskanta
Haka ta qaraci tunanin ta ta haqura, Hajiya to bakida pic na yarta ki?, lah inada shi bara kigani awaya, hartafara bud'e gallery, akayi mata waya, shiyasa ita bataga pic d'in ba
Hajiya Zainab matar abokin Abban su Fadeela ce, lokacin da suka dawo Sokoto da zama suka had'u dashi, abota ta qullu ta tsakani da Allah
Matansu ma haka, sosai suke gum inch, su a Sama road suke zaune inda ya tamfatsa gidan sa

Shekaransa 3 da tarewa agarin, abokansa suka matsamasa yafito takara, Allah yabashi sa'a alokacin inda ya kasance yacinye kuriar gaba d'aya, akashi 100 yanada 80

A wannan shekara Sokoto tayi sa'ar governor, mai hankali da kirki, ga aiki, ga taimakon talaka
Matarsa ma tana taimakonsa da shawara ta gari, shekarar sa 4 yana a matsayin, kafin wani ,zaben yazo
Mutane sin so ya qara fitowa amma yaqi, badan komai ba, yanason kasancewa cikin iyalansa amma ba hali, kuma shi baywani son hayaniya sosai, wannan dalilin yasaka shi qin kara fitowa
Ayanzu haka shine Senator ne, Abuja yake da ,zama, amma sannu sannu ya dawo sokoto gaba d'aya, kodan garin ya amfana dashi
Tunda annunamasa hallaci da qauna a garin, bashida matsala a rayuwa, sai d'aya wadda akullum da ita suke tashi daga shi har matarsa da ita
Rashin tilon 'yarsu da sukayi, amma wani ikon Allah saidai suyi tunanin ta, amma ba ikon yiwa wani magana akanta (aikin asirine, wanda baikaryeba)

Tanada kirki sosai Hajuga Zainab, qawartace sosai, sunyi wajan 10 years tare, tanada kirki, bata d'aukan kanta wata
Yaranta 3 duk maza suna business tare, kaya ake kamu su, kafin yanzu kuma da saidai su bayar ana kaiwa Saudi, senigalies da Atamfa Super da shaddoji a d'inke su ake kai musu
Abotarsu sai san barka, kansu a had'e yake kamar ya da qanwa ko wacce tana takatsantsan wajan kiyaye abinda zaika rashin jituwa tsakanin su
[23/10 7:50 pm] @ut@r h@jiy@โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’ฆ๐Ÿ‘—: Sahaf bataso zasu tafi su barta ba, tana da biki na qawar tane aminiya miss Hafcy, da babu abinda zaisa bata bisu ba
Har da kuka da zasu rabu, ita kanta FUTHA tayi sabo da su, haka motarsu ta d'aga sai birnin shehu

A mota tunsuna hira har bacci ya kwasesu, dan akwai tafiya tsakanin Kano da sokoto sosai, shiyasa har sukai baccin su suka tashi ba'azo ba
Alhamdulillah sun fita daga gida asa'a sun dawo asa'a, godiya ga wanda yake kare bawansa alokacin da yaso
Mama tayi mutuqar murna da dawowar yaranta, bare FUTHA itama tayi missing mama, wanka ko wacce tai akanbaje ana ta bada labarin Kano
Mama FUTHA tayi miji, takusa kamiki suruki mai hankali kuwa
"Allah sarki 'yata Waye shi a ina suka had'u?
Ita FUTHA sakin baki tayi jin zatayi mata qarya ina ta had'u da saurayin, amma bara dai taji wacce qaryan zatayi
Mama ai yari da sarqa yake saidawa kinga wani kallo na love daya ke mata, ya mato akanta sosai, saurayi dashi bakinsa Maikyau
Dariya ita FUTHA tai jin wannan tsohon akecewa Yaro
Ko mama ma dai dariya tai, dataji gaskiyan labarin
Huum kinga gobe yayanku zai dawo, saboda haka saiku tanadi mai za'a girka masa

Kai Ya Farouq ya kusa, lallai watan fita yawo da cin dad'i, yazo

Nan tafara bawa FUTHA labarin yayanta dama dai tasanshi abaki sauran ganin sa

@ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿปโœ๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [24/10 8:23 am] @ut@r h@jj@juโœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’ฆ๐Ÿ‘—๐ŸŒน๐Ÿ“š: *FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to Bilkisu(FUTHA Luv)*

*page 81-83*

Mama ikon Allah flight en qarfe nawa zaibiyo?
"Naji dai yace wai sai wajan magbree zai iso gida, amma 4 zai sauka
" hum, dama broth haka yake, mu muna d'okin ganinsa shi kuma saiya gama yawansa cikin gari sannan zai dawo gida
Ke kuma banda abinki ai ko ya sauka ko da gida yafara zuwa dole dai sai yaje o office nasu na nan, kinga kuwa bagara yagama da su ba?
Haka ne to, Allah mam na qagu naga broth 2 month ban ganshi ba
Wanccen zuwan da yai duka bana nan, shi kuma nasan murna yake da bana nan
Kyaji da shi, ai ya huta kuwa, ba fita kullum muna tare
Haka kikace koh?, eh mana
Itadai FUTHA murmushi take, komai nasu yana burgeta, yanda suke yin wasa da dariya
4:24pm agogon Niger da 9ja ya buga, adai dai lokacin ne Custom Farouq Yake sakkowa daga airport na sokoto, danzuwa mahaifarsa bayan wata d'aya da sati 2 daya shafe bai ziyarci gida ba
" Farouq mutum ne, wanda yasan yakamata yanada hankali, daidai yanada biyayya, rayuwansa simple ce, namiji ne har namiji kyakyawa ne ajin farko, yanada kwarjini da Haiba, da farin jini, ga jajircewa wajan aikin sa, shine assistance chief na Nigerian Customs duka, yana zaune a Lagos inda cibiyarsu take, baya d'aukan hauka ko wargi ga masu hannu da shuni akan kayansu Idan aka kama
Baya amsar bravery nd corruption ga kowa, wannan yaqara siyamasa mutunci ya kuma d'auka ka darajar sa
Tsayayyene akan aikin sa, rashin aikata mugun hali wa qasar sa itace tasa duk inda yashiga yake da kwarjini
Duk wata barazana bata sashi firgita akan abinda yasaka agaba, baya shakka yakama kayan kowaye indai ansami akasin abinda qasa takeson shigowa dashi,
Addu'a ta Iyayensa ita take riqe dashi, da tsarin ubangiji amma da tuni saidai wani bashi ba, wannan kyawawan halayyen nasa, sune suka saka yakeda wannan matsayin ayanzu
, bawai dan shekaransa yakai ba, abashi ba wannan matsayin ba, a'a ikon Allah da kuma tsayuwa akan gaskiya ruwa da iska
Yai fice afad'in 9ja duka, a Lagos yake da zama, amma yana zaga all 36 states d'in, dan ganin yanayin aikin kowa
Farouq kenan, d'a tamkar da dubu, iyayensa suna alfahari dashi dama jama'a baki d'aya
Qanwarsa guda Fadeela, komai nasa natane, yana sonta matsalanta d'aya tana takuramasa da broth akaini guri kaza, daga andawo taqara cewa nan, sosai yake qaunar ta, wataran suyi fad'a wataran ashirya
Iyayensa suna son yai aure, shima haka bawai yaqi bane, amma yammatan ne abin tsoro, suba tangaren bane bare a kwankwasa aga ne tagari, kuma ba kwarya ne suba, yanzu zakaga mace har mace amma halin nata sai a hankali
Ansha shine ya warke, ya tab'a yin budurwa Aneesa A Rimi, (Anee), sosai yake sonta itama haka, amma nata Iya bakine, bawai dan Allah take sonsa ba, saidatagama cinye kud'in sa, ya isheta sannan ta fara masa wulaqanci ya sota sosai, bayanda baiyi da ita ba, amma taqi kunsan 'yan katsina da son kud'i
Haka yarinyar tamasa, baifi da wata biyu ba, saijin bikinta yai, dama ankusa shine dai tace bara taci kud'insa tayi wasa da hankalin sa
Wannan yasa yake tsoran mace, amma duk da haka, baiga wadda tamasa ba, daya fara dating nata

*Labari*
* * *

Saukarsa keda wuya, ya hango driver na gidan su, yana washe baki
"Oga barka da zuwa"
"Ansha hanya, wallahi kuwa, sannu to
Briefcase nasa ya amsa, shi kuma gaisawa ya tsaya
gaisawa da mutane wanda yasan su, dama wanda baisani ba, tunda kusan ince 'yan kasuwa sunsan da zaman Farouq
Kodan adalcin dayake musu, ga hira dashi da ake gidan TV akan matsalan da ake fama na Brivery and corruption da ake fama
Yasan yanzu qananan ma'aikata suna can ana murna, dodo baya nan
Ganin zaib'ata lokaci kuma yan son zuwa Office kafin gida, yasa yaiwa kowa sallama ya tafi

@ut@r h@jiy@โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [24/10 9:30 am] @ut@r h@jj@juโœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’ฆ๐Ÿ‘—๐ŸŒน๐Ÿ“š: *FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Page 84-86*


*Gidan Hajiya Zainab*

Mami ! Mami na'am yan gidan Mami, ya akayi ake kirana haka
Kai wani qayataccen parlour ne nagani yaran sun shiga, kujerune royal na qasar Saudi azagaye aciki, sai labulaye masu kyau, ga manyan prems na gani na fad'a
Daga one side Shower ce manya kai komai yayi, gidan senate fa, kuma former governor, abinda yafi haka kaf nagani, part 2 agidan, flowers na gidan Kansu, abin kallone, ga d'awisu da yawa dasu barewa, sunata yawo
Gate 3 ne agidan, parlour ba adadi, kowa nasa parlour en yaran daban

Mami kinga ya Samad wai dole sai nasaka butter acikin bread en, nikuma kiri kiri zansa, kuma wai sainayi karatu zan farayin break
Kai nashiga uku, wai ya kukeso dani, ga Abban kuje wajansa saini, yanzu Ahad yace Halim yad'aukarmasa bike nasa ya fita, kaikuma akan break fast kunzo
Mami nayi karatun fa, ba yanda ta iya haka tayi sasanci har kowa ya gane
Dariya taji daga bayan ta, uhoo ashe kanjina dasu, wallahi sunfiya rigima daga wannan sai wanccen, kuma kana gani saidai kabarni da rabo
To ya zanyi, wallahi Mamin yara nima ina shiga fad'an, guna sukaje, sunfara bayani nace kutafi Mami na qasa
Alhaj Abdallah Idan kaganshi daga shi har matarsa bakace sun haifi yara haka ba, kuma bakace sunkai shekarun suba
Rigane da skirt na Atamfa exclusive a jikinta, gashin nan an bazashi, ga qunshi maroon a qafanta, abinka da farar mace, komai nata in gentle take
Kaikace yarinya yar 25 Idan kaganta, shima haka, yaran su farare tas, su kama sukai da Abban su, fari da gashi na Mamin su
Suna a SS 2 ayanzu, yaran ga tarbiyya, saidai fad'a, Dan kullum cikin rabon fad'a take, shiyasa daga anyi hutu ko weekend take turasu gidan Aunty Meenah ko gidan granny

Triple ne, shekarun su wajan 13 amma girman jikin da suke dashi kamar na 'yan 17 ko 18 years

Abba Ahad ne yake magana Wanda shigowarsa kenan, yes Freind ya kai, dayake haka yake cemusu
Abba wai ni intambayeka mana?
" inaji, nasan canja machine ne ko system, ko abokin ka kaza bashida wani abu,
Ba haka bane
To yane?
Yauwa Abba ni naji mutane suna fad'in kanada 'ya wai Bilkisu amma ni kaf family indai ba Libya mukaje ba, ban tab'a jin kunyi maganar taba?
Kuma naga pics nata da yawa, amma Idan muka tambayi Mami sai kawai muga ta fashe da kuka?
Kai Alh Abdallah ta d'aga yace Ahad wallahi ni kaina nakasa tuna komai akan da, nasan dai narasa wani abu mai mahimmanci kuma ko gida naje itama Hajiya zanji tana cewa akwai maganar datake so tayi amma sai taji ta manta kuma takasaiwa kowa magana

*(kunsan asirin da akayi, shiga jikin FUTHA yai, kuma an had'a shi da mantau, kowa zaimanta ta, Zainab akayi yafada kan 'yarta, shiyasa tun alokacin ba wanda yaqara maganarat, koda abubuwa sukai normal, shi asirin yana nan)*
Sai hawaye shar abin tausayi, ganin haka shima kuka yasa, saida sukai ya ishesu sannan ya miqe Ba tareda yace komai ba
'Yan uwansa ya tara sukai magana, akan Lallai suje wajan Baban abokinsu, malamine babba, ya taimaka da addu'a akan ko menene Allah ya warware, dan saida yawa suna ganin iyayensu cikin damuwa
Shawarar tayi, hakan sukai kuwa, driver yakaisu, bayani sukai masa na komai, addu'a itace mafita shima yace, 100k suka ajiye masa akan haka
Amma yaqi, yace subari komai ya daidaita Addu'a taci, saidai sadaka da za'a ringa yi
Kud'in suka d'iba, Dama ko wanne cikin account nasa ya ciro kud'i, suka had'a
20k dai suka ajiye masa, suka tafi

*Farouq*

Acan su Fadeela anyi girki, kala kala harda Masar Bauchi, da white rice da stew, sai plantain haka sukayi masa, sai juice da FUTHA ta had'a cucumber juice dana kankana, haka suka shirya table yai kyau
Fadeela ce tace wallahi FUTHA kinyi aikin banza broth bayashan juice na had'i, shidai yafison yasha na kwali kona gwangwani, na fad'a miki saida kikayi
To ina ruwanki inji Mama, sai kiga yasha, Allah yasa yabaki kunya
Haba dai, nasan halin sa, haka sukayi wanka, ita FUTHA abincin taci, ta haye Sama, saboda tanson yin karatu
Shikuma saidaya gama abinda ,zaiyi, sannan ya tawo gida

@ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿปโœ๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [24/10 1:26 pm] @ut@r h@jj@juโœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’ฆ๐Ÿ‘—๐ŸŒน๐Ÿ“š: *FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 87-90*


Unuguwar Alu quarters driver yayo dashi, cikin Wata arniyar motarsa Benz 2016, red colour ce, ga tashin qamshi dayake tashi ciki
Ga kakinsa Maikyau daya sha guga kamar sabo, kai kace yanzu ne yasaka kayan baiyi yawo dashi ba
Sajensa shine abinda ya qawata masa fuskarsa, system nasa yake dannawa, tana kan cinyansa, ya qame abaya kaikace wani basarake ko wanda muqaminsa yafi haka
Sannu a hankali ake tafiya, saboda baison gudu shi arayuwan sa, dats why yake tare da Bakari driver ya iya aikin sa, kuma yasan yanda yake tafi da komai nasa
A haka har suka qaraso karafaren gidan su, Horn yai Sani yazo ya bud'e, saida ya Shiga second gate sannan ya murd'a murfin qofar ya fita bayan tsayuwan motan a wajan da aka tanada dan ajiye motoci
Laptop nasa da wayar sa yake kwashewa saijin an ruqunqumeshi yai, ko baijuya ba, yasan Fadeela ce
Oyoyo broth shine sai yanzu kazo mana, bayan tun 5 yakamata kazo, bayansa ta d'ane tanamasa wannan maganar
Fadeela plx ki taimakan ki sauka akaina, wallahi zaki karya ni, narasa matar aure, kinyi qatuwa da yawa
Qi tayi, ganin zata gaji dashi yasaka hannunsa d'aya ya juyo da ita, haba sis kinji bayana saikace wanda yad'au Container, waih amma kina aiki, inq zan auri mace mai qiba haka?, ta murqusheni
Shidai Bakari dariya yake, yanakuma qara jinjinawa maigidan nasa abisa yanda yake tafi da kowa cikin lumana
Broth inamaka oyoyo amma kake mun haka, dankaga ina kewarka, shine zakace wai nayi nauyi, ba ruwana da kai
Qoqarin kwace hannunta take amma takasa
Hannu yasa ya d'ago fuskanta, yace haba qawalli ta, wasa nake aike bakifi 90 km ba, lalala 90 kace wallahi 60 nake, kaji koh kaqara yankata
Dariya yai yace, ni matsa ko uwata bangani ba, ki cika ni da magana, ga shi inajin yunwa
To tawo kaci, nasan bacci zakace zakayi, da munje Na.... Bata qarasa ba, yace ba inda zani
Dama nasan welcome en da akamun bata Allah bace
Wallahi broth ta Allah ce, OK naji muje tiqemun kayana
Haka suka jera sai main parlour na gidan
Mama fito Broth yazo, naji shi ai, bayan kin tsaremun d'a da surutu
Haba mama nid'in, ai yafini surutu, haka ki kace dai
Tsugunawa yai, "Mama ina yini munsameku lafiya?, lafiya Lou Umar ya garin ya aikin kuma?
Sai alheri Mama, yauwa Allah yaimaka albarka yaqara karemun kai daga sharrin masu sharri
" Inye saboda d'ankine kike masa irin wannan addu'a haka, Lallai Ameen to "
Abba ne yake wannan magana
Gaisar dashi yai, anan suka d'an zauna, daga nan yace Mama lemme go nd take bath, I'm tired sosai wllh
Ok, kayi sauri, ga abinci yana jiran ka, tom uwa tagari
Wata qofa naga yabi, waje ya b'ullo anan naga yai wani part shima mai kyau, but she plat ne.
Key ya cire cikin pocket nasa, anan yafara dubawa haryaga wanda yake nema, sawa yai ya bud'e, wow pink colour shine komai na part d'in, hatta toilet danaga yashiga shima pink ne, Italian bed nasa haka ma
Shap shap ya shirya, qananan kaya yasaka, sai turaren passport for love, takalminsa yasaka ya fita
A dining ya gansu, shima layi yabi, abincin yamasa sweet sosai yaci ya qoshi
Jug yagani akan dining en, yasan ba'a shan lemon had'i agidan shiyasa kawai ya tsiyaya a cup baran daya ganshi fari ne, baki yai dashi direct, instant of yaji ruwa, sai
wani irin testing da qamshine ya ziyarci bakin sa, kamar ya tsaya da sha, amma saiya kasa, tas ya shanye yaqara, 2 cup yai yaqara, nunfashi ya sauke wani irin farin ciki yaji, wannan wani irin juice ne mai dad'i, wani jug yaqara dubawa nan ma yaga lemon, baiyi sanya ba yaqara d'aura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login