Showing 1 words to 3000 words out of 24909 words

Chapter 1 - RUHIN FANSA PART 1 BY MARYAM MAJIDADI

ο»ΏπŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
NA
*MARYAM ISMAIL MAJIDADI*


Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa


wattpad MARYAMMAJIDADI123
*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*Ya Allah na rokeka yanda ka bani ikon fara littafin nan lafiya ya Allah ka bani ikon gamashi lafiya,ya Allah na rokeka ka kawar da alkalamina a wurin rubuta sabonka,Allah ka kara mana basira ,kasa kuma sakon da muke isarwa yana zuwa inda ya dace,Allah na rokeka ka bani ikon gama littafin lafiya,littafina kirkirarran labari ne,bamyi shi dan wani ko wata ba,haka zalika salonsa na daban ne*




*Fallow me on wattpad pls real fans at maryammajidadi123*




page 1


ALHAJI SULAIMAN shi ne asalin sunan mai gidan matarsa d'aya HAJIYA KHADIJA yaran su biyu JAFAR DA KABIR .ALHAJI SULAIMAN katsina shine mahaifarsa cikin karamar hukumar BINDAWA ya taso yana da rufin asiri babu laifi yana sana'ar saye da sayarwa ta kayan masarufi ,babu laifi Allah yasawa sana'ar tasa albarka ,suna zaune cikin farin ciki da mutunta juna,HAJIYA KHADIJA tana da k'anwa JAMILA wacce take aure nan kusa da ita,sai dai mijin JAMILA ,MALAN SALE ba wani k'arfine da shi sosai ba,duk da haka be gaza wajen kula da iyalansa ba yarinyar su d'aya BILKISU,BILKISU babu abunda ta bari na halin mahaifiyarta watao JAMILA ,JAMILA akwai san abun duniya da hangen na wani,d'an jin da'in da yayarta ta fita KHADIJA sai ya tsone mata ido,tun daga nan ta k'ulla wani mugun kulli a zuciyarta,zaune suke cikin babban parlon mahad'ar gidan kasancewar anan d'ayan b'angaren su Malan SALE ke zaune,breakfast sukeyi akan teburin cin abinci ma daidai ci.
Gyaran murya ALHAJI SULAIMAN yayi tsoho mai dattako da mutunta kowa ,tsoho na gari mai sanin darajar d'an Adam,ruwa ya kurb'a kad'an sannan yace"ya kamata a yanzu yaran nan auyi aure,kunga babu abunda suka rasa kowa yayi karatunsa daidai gwargwado ga sana'a JAFAR ya gajeni,shima KABIR Alhamdullilah tun da yana aekin company dinsa,BILKISU ma ta gama makaranta".
"wannan shawara tayi kyau Alhaji,gaskiya hakan ya kamata dan bazamu zuba masu ido muna kallonsu ba"Malan SALE ya fad'a,wata uwar harara Jamila ta watsa masa duk da taji dad'in zancen mijin yayar tata,sinne kai BILKISU ta farayi dan tasan dole yanzu za'a fad'awa BABA tana tare da KABIR,gyara zama JAMILA tayi wacce suke kira da Goggo tace "to ae Baban yara zancenka yazo kan gab'a kuwa,domin Kabir da Bilkisu sun gama dai dai ta kansu,sai a tsaida rana kawai".murmushin jin dad'i ya sub'ucewa ALHAJI SULAIMAN(BABA) yace "kai Alhmdllh masha Allah,Allah abun godiya dama ina ta daukin wannan rana ,bana so Bilkisu ta fita waje sai Allah ya ansa addu'a ta,dama shi JAFAR yana tare da yarinyar aminina wato ALHAJI AMINU CHANJI sai ayi komai rana d'aya a wuce wurin".wani mugun fad'uwa gaban Goggo yayi tana maimai ta sunan ALHAJI AMINU CHANJI tasan babu wanda be sansa ba,tab lallai akwai tashin hankali kenan ya fad'a a ranta,take wani mak'ok'on bak'in ciki ya k'ara taso mata,da k'yar ta dannesa tana murmushin yak'e.
KHADIJA(MAMA) kam murna tayi sosai dan tasan yarinyar Alhajin Aminun wata SHA'AWA tasanta sosai natsatsiyar yarinyace gata kyakyawa ajin farko kuma y'ar gata ce dan ita kad'ai ce mace sai yayanta d'aya BASHEER ,tayi zurfin karatu gata da tarin dukiya tun tana da k'ananun shekaru,sosai MAMA tayi murna dan yarda JAFAR baya da hayaniya baza taso ya auri wacce zata bashi wahala ba.haka suka watse daga cin abincin kowa da abunda yake cikin ransa.cikin sati biyu aka gama komai aka tsai da ranar auran nan da wata d'aya,anan cikin filin gidan BABA ya ibarwa yaransa ya gina masu ko wanne part dinsa mai kyau na zamani ,shi da kanshi ya had'a lefe komai iri d'aya ko wacce akwati shidda lokacin biki sai k'ara doso kai yakeyi,ankai lefe sosai aka samu tarbar arziki daga dangin SHA'AWA,na BILKISU kam a nan suka karb'a abinsu tunda tuwana mai na zasuyi,tun da akayi jeren SHA'AWA BILKISU ta tada hankalinta ganin tsadaddun kayan da aka zuba mata,tun daga nan hassada ta shiga tsakaninsu,duk da itama BABA yayi k'ok'ari sosai,sai dai sam idonta yana hango na sama da ita,ba wani bidi'a akayi bikin ranar juma'a dubban al'umma auka shaida auren JAFAR SULAIMAN BINDAWA DA AMARYARSA SHA'AWANATU AMINU CHANJI sai na KABIR SULAIMAN BINDAWA DA AMARYARSA BILKISU SALE BINDAWA akan sadaki naira dubu talatin,haka aka sha hidimar biki har walima cikin mutun ta juna,tun da BILKISU ta daura idonta akan SHA'AWA taji wata muguwar tsanarta danta fita komai kama daga kyau da kuma dace,dan gani takeyi JAFAR yafi KABIR samu kuma haka dinne,balle tun a wurin bikin ALHAJI AMINU yaiwa sirikin nasa kyautar milyan d'aya ya k'ara a kasuwancin sa,itama kuma SHA'AWA tana da kamfanoni da filaye da shaguna.ko kad'an SHA'AWA batajin dadin zama da BILKISU dan makirace bata barinta sakewa sai ta fakaicin idon mutane take kuntata mata,SHA'AWA kam bata da hayaniya ko kad'an shiyasa bata damuwa da BILKISUN ,sosai Goggo ta shiga bokaye ta mallake KABIR tas bayajin maganar kowa sai nata komi ya samo yana sakarwa y'arta,a haka sukayu nasarar saka masa kiyayyar d'an uwansa ,akwan a tashi babu wuya wurin Allah watansu ukku da aure sai ga SHA'AWA da ciki BILKISU ko shiru,ranar da maganar ta fito BILKISU kusan hauka tayi dan ita ko b'atan wata bata tab'a yi ba,haka taita renan cikinta da dadi da babu,duk da tanajin dadi sosai wurin mijinta da kuma iyayensa da BABA da MAMA da MALAN ba daga baya ba wurin kyawawan hali da son mutane wurin Goggo da Bilkisu kadai take samun matsala,a haka har tazo lokacin haihuwa duk da ta sha wahala amma cikin ikon Allah ta haifo yaranta kyawawa har biyu duka maxa masu matuk'ar k'ama da JAFAR,tun da BILKISU taji labari ta fad'a d'akin Goggo tana ihu tana watsi da kaya kamar sabuwar mahaukaciya,da k'yar Goggo ta lallasheta tace"ki daina wannan kukan ,kina dani banfa mutu ba bare kiyi kukan maraici,ba sai munbar yaran da rai ba sannan zatayi maki sisi ba,yadda jininki be taka gidan nan na,haka zalika babu wanda ya isa ya taka wannan gidan,dolo muga bayansu zamu shirya komai kafin a sallamesu asibiti".Sosai BILKISU taji dad'i dan tasan halin Goggon tata,BASHEER da ke tsaye bakin tagar ya sauke ajiyar zuciya yayi saurin barin wurin kada su fahimci wani yaji b'angaren k'anwarsa SHA'AWA ya shiga ya ibi kayan da zai iba yafito uabar gidan tare da neman mafita,har ya isa asibitin baya da mafita sai shawarar d'aya da zuciyarsa ke basa na ya d'auke yaro d'aya ya gudu da shi wanda ko y'ar uwarsa ba zata gane hakan ba,danshi ya dad'e da yin aure yana zaune a k'asar CANADA amma har yau matarsa ko b'ari bata tab'ayi ba,da k'yar ya shawo kan DR din daya k'arb'i haihuwar sai da sukayi rubuce rubuce kuma yayi masa rantsuwa bazai tab'a cutar da yaron ba,duk da DR din yasan yayi zalinci amma haka ya daure ya daukko yaron SHA'AWA babban yaba BASHEER ,can kuma ya saka gawar wani jaririn yace Allah yaiwa d'aya rasuwa,sunji babu dad'i sai dai sukayi hakuri akayi masa suttura aka ruhoshi,har rawar murna BILKISU ta taka tana fad'an sora d'ayan shima,tun da BASHEER ya k'arbi yaron be k'ara kwana ba ya wuce CANADA sosai matarsa ta tausaya masa,ta kuma k'arb'a ,sukayi karyar tana da ciki ,kuma zasu tafi wani aeki dan nan da wata d'aya zata haihu idan sun dawo zai kawo masu baby in Allah ya sauketa lafiya,sosai ALHAJI AMINU yayi masa fad'an ya boye matarsa tana da ciki har sai da ta kusa haihuwa zai fad'a,shikan BASHEER hakuri yayita basu.kwanansu biyu a asibiti jikin SHA'AWA yayi kyau dan hakan da dare za'a sallameta ko da mahaifinta yazo nan take ya mallakawa jaririn babban Company dinsa na sarrafa ashana ya bawa JAFAR takardun aka maida sunan jaririn wanda JAFAR yayi masa huduba da AMINU dan karamcin mutumen,sai da BILKISU ta fakaici idon kowa sannan ta share kwallah ta kuma kudiri aniyar yau zata zartar da shawarar da zuciyarta ke bata,sai da bayan isha'i sannan tace zata tafi,ganin babu kowa d'akin yasa tayiwa SHA'AWA sallama ta fito,lab'ewa tayi ko da taga ta shiga bayi aeko ta shigo da sand'a ta murd'e wuyan jaririn saboda rashin imani ,da sauri ta fice abunta,tana fita kuma SHA'AWA ta fito ganin Babyn baya motsi yasa ta saka kuka daidai haka JAFAR ya shigo an kira DR ya tabbatar murd'e masa wuya akayi amma kab aka rasa wanda yayi hakan,wannan dalilinne yasa JAFAR rokar SHA'AWA akan kada ta fitar da dalilin mutuwar yaron suyi hakuri Allah zai kuma basu wani,tayi kuka sosai na rashin yaronta,BILKISU na zuwa ta iske rasuwar harta rigata isowa ta hau murna tana fad'awa Goggo meya faru,murna fal ransu,haka SHA'AWA ta dawo da kewar yaranta,watansu bakwai ta rasuwa yayin da BILKISU ke dauke da ciki tsawon wata shidda sai cika take tana batsewa ita a dole mai ciki,tab'ara kawai takeyi da tuna isa ,a haka lokacin haihuwa yayi ta santalo yaronta namiji kyakyawa dan duk ya fisu kyau da fari,sosai kowa yayi murna har SHA'AWA da lokaci d'aya taji kaunar yaron ranar suna yaro yaci SULAIMAN zasuna kiransa da (AHAAD),sakarwa SHA'AWA shi BILKISU keyi a yunaninta wai ta zama y'ar renonta dan ko yaushe yana wurin SHA'AWA nono kawai take kaishi yasha wurin BILKISU .wani irin shakuwa da soyayya mai karfi ta shiga tsakanin SHA'AWA da AHAAD ko motsi zatayi yana mak'ale da ita hakan yasa take jinsa kamar ita ta haifesa cikin gwaranci har yake ce mata UMMU JAFAR kuma ya kirasa ABBU ,BILKISU yace MUMMY KABIR kuma yace masa DADDY,shekararsa hudu BILKISU ta muma samun ciki sai ta k'ara fita harkar AHAAD babu ruwanta dashi wai karya takura mata,yayin da ita kuwa SHA'AWA har lokacin shiru bata kara koda b'atan wata ba.lokacin haihuwa BILKISU ta k'ara haihuwar namiji ranar suna yaro yaci SALE suna kiransa (AMAAN),tunda MUMMY ta haifi AMAAN sai ta k'ara mantawa da AHAAD babu abunda take so sama da AMAAN ko motsi yayi yanzu tahau tambaya ko ina tana mak'ale dashi,wannan dalilinne ya k'ara sanya rashin sabo tsakaninta da AHAAD ,tun tashin AHAAD wani murd'ad'en yaro ya taso ko kad'an baya magana sai ta kama baya son hayaniya baya shiga harkar kowa,tun a yarinta yake matuk'ar son aekin SOJA ,ko mai nashi a natse yakeyin shi dan a lokacin yana tunaninma UMMU ce mamanshi,AMAAN kam ya taso sakakken yaro bayajin bari babu abunda ya saka gaba sai gadara da tsabar rashin ji suna da kishiyoyin halaye shi da AHAAD wannan yasa ko kad'an basa zama inuwa d'aya,shekarar AHAAD sha hudu lokacin yana SS1,dan AHAAD badai kok'ari ba a lokacin kuma saukarsa biyu,AMAAN kuma yana da shekara goma yana JS1 saboda shegen wasa kullun cikin dawo dashi baya akeyi,kuma a lokacin ne BILKISU wato MUMMY ta kuma haihuwar y'arta mace,sosai sukayi murna,duk da su MAMA rashin haihuwar SHA'AWA yana damunsu,sai dai sun mik'awa Allah buwayi gagara misali lamarinsu,ranar suna yarinya taci suna FADILA,sosai AMAAN ke matuk'ar son FADILA yana cewa shima AHAAD yaje mamanshi ta haifa masa tashi,kasancewar FADILA ita kad'ai mace sai kowa ya mik'a kulawarsa gareta,shekarar FADILA d'aya UMMU ta samu ciki,sosai sukayi farincikin da suka dad'e basuyi ba,JAFAR kam har sadaka yayi don murna,kulawa kam ba'a maganarta a ta ko wanne ba'angare,cikin ikon Allah lokacin haihuwa UMMU ta haifo yaranta masu masifar kyau kamar aljannu duka mata ,duk ko kwantonka baka isa ka iya ganesu ba,yaran har sunfi UMMU kyau ga farinsu da daukar ido,murna a wurin AHAAD ba'a magana dan rasa inda zai saka kansa yayi,ko da ALHAJI AMINU yazo nanma sai da yayiwa jariran kyautar kudad'e masu tsoka,BILKISU kam haushi kamar ya kasheta tace ita data haihu wai kad'an ya bata(kuji k'arfin hali ba ja'ma'aπŸ˜‚),ranar suna anyi shagali na gani na fad'a,nera tayi kuka kuwa,yara sukaci suna NAJWA da NAJMA,sai muce Allah ya raya,tun daga wannan lokacin duk wani gata da kula ya dawo kan NAJWA da NAJMA mussamman NAJMA wacce ke da fara'a da son mutane tana yarda da kowa,inko taga AHAAD har tsalle takeyi,shima yana masifar sonta dan yafi daukarta ma akan NAJWA duk da ba'a ganesu shi yana iya ganesu,watan su NAJMA 7 ,Allah yayiwa mahaifan SHA'AWA rasuwa ta dalilin hatsarin jirgin sama ta hanyarsu ta dawowa daga Canada sunje ganin jaririn BASHEER din, mutuwar data girgiza kowa a garin katsina kasancewar ALHAJI AMINU sananne ne,anyi kuka sosai d rashin ,BASHEER ma da matarsa yazo tare da jaririnsu,kafin ya tafi aka raba gado,sosai yayiwa y'ar uwarsa nasiha sannan ya kwashe iyalanshi suka tafi yana kuma begen k'anwarsa,bayan rasuwar da wata biyu shima BABA ALHAJI SULAIMAN Allah ya k'arb'i kayansa shi da JAMILA (Goggo) da SALE ,a motar MAMA kad'ai aka fidda da ranta,sosai ahalin suka girgiza dan BILKISU har d'an k'aramin hauka tayi saboda rashin Goggo,sai dai muce Allah yajikansu,tun daga wannan lokaci JAFAR ya koma LAGOS yayi masu tanfatseten gini ya kwashi MAMA da iyalansa da kuma KABIR da iyalansa suka dawo lagos da zama,NAJMA ta taso yarinya marar tsoro duk da k'ananun shekarunta idan su MUMMY sukawa UMMU abu takan dage ta rama mata,ko kadan bata da tsoro,ga son mutane da fara'a badai kaga tana fushi ba,yayin da NAJWA ta taso yarinya mai sanyin hali ko kad'an bata damuwa da abunda ke faruwa a gidan,sai dai in anyi ta bawa UMMU hak'uri,suna da shekara 10 YAA AHAAD ya samu aeki ya fito a CAPTAIN na sojojin k'asa,yasha gwagwarmayar rayuwa,yayin da ya ida zama babban saurayi kuma d'an gayu na gani na fad'a,sab'anin AMAAN take aekin zaman Office a Campany din ABBU.


inga ruwan comments sai na k'arawa alk'alamina kauri.pls share


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'araheπŸ™



STYLISH STAR⭐
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
NA
*MARYAM ISMAIL MAJIDADI*


Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa


wattpad MARYAMMAJIDADI123
*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


page 2


lab'e take jikin window sai aekin turar baki gaba takeyi,ga fuska ta shagwab'e kamar zata fashe da kuka,jin k'arar bud'e gate yasa ta juya da sauri dan ganin waye ya shigo,ganin motocin AMAAN ya sakata fad'in "yauwa Allah",shikam cikin takun k'asaita da nuna zallar ya cika namiji ya k'araso wurin fuskarsa dauke da murmushi,hannunta ya kama yace"wa kuma ya tab'a satauniyar gidan nan haka?".wani far tayi da ido dukda k'ananun shekarunta saika dauka hakan kamar yanga takeyi sai dai kuma haka hallittarta take,cikin sonyin kuka tace"Yaa Amaan ba Ummu bace ba",yasan sarai wani rashin jin tayi dan NAJMA ba dai rashin ji ba,wannan dalilin yasa ya jawota jikinshi da soyayyar k'arya dansu cinma wasu nasarorin su,"rabu da Ummu kinji,ae yanzu na dawo zo muje ".be jira ansarta ba ya kama hannunta zuwa part dinsu,sai da sukazo daidai k'ofar d'akinsa sai taja ta tsaya tare da sunkuyar da kai k'asa,shima kallonta yayi yace"yadai?,shigo mu tafi mana",hud'ubar Ummu ta fad'o mata a rai kamar yanzu take maganar na cewa kada ku sake naga kuna shiga d'akin mazan gidan nan in ba ta kama dole ba,girgiza hannunta da yayi yasa ta dawo daga tunanin data tafi"no ka shiga dai zan jiraka a parlo"ta k'are maganar cikin sanyayyar murya da d'an k'aramin bakinta .isowar MUMMY wurin yasa duk suka juyo suna kallonta tace"AMAAN ina ka tsaya haka?,kuma nasan kasan yau Yayanku zai dawo ko?".yatsine fuska yayi cikin isa yace"to da me zan masa?,nifa MUMMY nace ki daina had'ani da wannan mishkilin mai daukar kansa yafi kowa,karma ya dawo ni ba abunda ya dameni dashi"Amaan ya k'are maganar cikin gadara"Allah ya baka hakuri Son ,zo muje NAJMA kafin ya kammala shirinsa"hannun NAJMA taja sukayi room dinta,siririn tsaki AMAAN yaja ya wuce d'akinshi da tunani kala kala.
suna shiga bedroom din MUMMY ,NAJMA ta langwab'e fuska tana narai narai da ido wanda gashin ido gazar gazar suka cika idon saika dauka ta k'ara ne"MUMMY da gaske Yaa Ahaad zai zo yau?,naga Ummu da masu aeki sunata girki da yawa".murmushi Mummy tayi najin dad'in sunyi nasarar jan NAJMA jikinsu tace"eh mana,yana k'araso har Idi ya tafi daukoshi tare da DADDY "zaro dara daran idanuwanta tayi masha Allah na fad'a da ganin yadda idanuwanta ke da girma,ta daura hannu a kai tace"munga ta kanmu,yanzu zai hanani zaman parlo da magana a gida",shafa kanta Mummy tayi tace"karki damu zan maki maganinsa bazan bari ya tab'amun y'ar lelena ba"da sauri NAJMA ta rungume Mummy tana dariya da jin dad'i fal ranta.da sauri suka mik'e sukayo waje danjin k'arar motoci na shigowa ,mota ukku ta shigo sukayi parking,tsayawa sukayi kowa fuskarsa dauke da murmushi yana jiran fitowar gwarzon wanda ya dad'e baya k'asar,harsu Ummu sun fito,sojoji ne suka fito tare da zagaye motar tsakiya Daddy kam tuni ya fito ya k'araso wurin su Mummy,koda Emanuel ya bud'e masa motar ya dad'e be fito ba,sannan a hankali ya fara zuro k'afarsa dake sanye cikin takalmin sojoji bak'ak'e,ya dad'e kafin ya idasa fitowa baki d'aya,masha Allah sanye yake da wandon kakin soji sai bak'ar T-shirt,hannunsa daure da agogon soji wani sanyayyan k'amshi ya feso tare da iskar dake kad'awa ,kallona na mai da garesa,fuskarnan kamar kullun daure take babu alamun wasa,fari ne ga idanuwa masu daukar hankali da rikita marar gaskiya,yana da tsayi sosai ga faffad'adan k'irji,lumshe idanuwansa yayi wanda suke dauke da tarin gajiya ,duka hannuwansa ya saka cikin aljihun wandonsa ya fara takowa cikin izza da tsantsar mulki,tafiyar AHAAD kad'ai abun kalloce,cikin natsuwa ya k'araso garesu ,kai tsaye gaban Ummu yaje ya duk'a har k'asa cikin sanyin murya wanda saika natsu sosai zakaji me yake cewa yace"UMMUna sannu da gida?".cikin dauki da murmushi dake nuna tsantsar soyayya ta daura hannunta akan kafad'arsa ta dagoshi tace"yauwa Babana,barka da dawowa,ka tafi kabar mana kewa"murmushi kawai yayi,gaisuwar da NAJWA take masa ya sakashi juyawa yana kallonta,cikin murna tace"Yaa Ahaad sannu da dawowa,ya hanya?",kallo d'aya yayi mata ya gane NAJWA ce ,"Alhmdllh "kawai ya fad'a,ya wuce wurin MUMMY rungumeta yayi tare da daura kansa akan kafad'arsa yace"i miss u mom",duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login