Showing 12001 words to 15000 words out of 15526 words

Chapter 5 - BOYAYYAR ALAƘA 1 by ASMY B ALIYU

26 May 2026

10

hostel gabanta ke mugun faduwa, yau bata san da wacce rigimar
Fu'ad yazo ba, addu'a take Allah yasa har su rabu bazai ɗaga mata hankali ba, buɗe
gaban motar tayi ta zauna, gabanta babu abunda yake sai faduwa idan tana gaban
Fu'ad manta kanta take, dogayen fingers ɗinta ta shiga ja, zaman shiru ya ratsa a
tsakaninsu kafin Fu'ad ɗin ya riqo hannunta, tana ƙoƙarin janyewa ya zuba mata
idonsa masu ƙassara ta, idan akwai abunda ta tsana acikin halayyar Fu'ad to bai
wuce yawan ta ɓata da yake ba, tayi masifa har ta gaji.
"Kin gaji ne?" Ta ɗaga kai tana kallonsa sai ya dage mata gira ɗaya still dai yana
riqe da hannunta "Ko muje kici abinci idan yunwa kikeji?" Girgiza kai tayi dakyar
ta buɗe baki tana jin yadda muryarta ke wani harɗewa jin yadda harshenta yayi mata
wani irin nauyi, a hankali ta zare hannunta cikin nasa hannunsa “Daman maganar
birthday party ɗinka ne, gida baza'a barni ba Fu'ad." Ta faɗa da wani yanayi a
muryarta tana ganin yadda ya zuba mata fusatattun idanunsa "Kice min Wasa kike
Amaah?" Ɗaga kai ta shigayi hawaye na cika idonta "Wallahi baza'a barni ba Fu'ad
kasan ka'idar gidanmu." Kallonta yake sama da kasa kafin ya lashe busassun lips
ɗinsa "Daga ranar da kika ƙi attending birthday party ɗina daga ranar munyi breakup
a tsakanin mu." A wani irin firgice Amaah ke kallon Fu'ad bakinta na rawa bata taɓa
tunanin zai yanke hukunci kalar wannan ba “A saboda wannan zaka yanke alaqar dake
tsakaninmu Fu'ad? Da gaske zaka iya rayuwa babu ni?" Ta faɗa tuni hawaye suka fara
forming cikin fiskarta, samun kanta tayi da ɓalle marfin motar ta fice daga motar,
lokaci ɗaya hanyar hostel ta nufa da sauri Fu'ad ya kwantar da kansa cikin seat ɗin
motar yana ƙoƙarin control ɗin anger dinsa. Yana son Amaah dikko da dukkan zuciya
da ruhi ta yadda baki zai iya furtawa ba, amma ya take neman ta wulakanta masa
soyayya a gaban friends ɗinsa? Rai a ɓace ya tada mota a fusace yabar cikin
makaranta dan gwara yaje ya nemi wani abun da zai sha ya bugar masa da wannan bakin
yanayin da Amaah dikko ta bar masa lokaci ɗaya.
Ganin yadda Amaah ta faɗo dakin yasa tasan sunyi halin nasu tasan Fu'ad shine
babban weakness ɗin Amaah dikko ta kuma tabbata yadda take haukan sonsa baya mata
wannan kalar son, dan yana da wasu yammatan a gefe sannan kalar su Fu'ad ba irin na
macce ɗaya bane, ta zubawa Amaah ido wacce ke famar zubar hawaye "To me kuma ya
haɗo ku?"
"Daga kawai nace bazan je birthday ɗinsa ba wai sai dai mu rabu, ban taɓa tunanin
Fu'ad zai iya faɗa min haka ba Rufy?" Amaah ta faɗa muryarta na wani irin shaking.
Rufy ta taɓe baki "Kema dai kin san halinsa ba hankali ne da Fu'ad ba kuma kin san
zai iya, kawai shawarar da zan baki kiyi ƙoƙari kije koda na awa ɗaya ne."
kwanciya Amaah tayi akan bed ɗin Rufy tana ta tunanin inda zata fara.

BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764

Katin wayar MTN ta 07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


#ASMY B ALIYU
#BA(Secret Relationship)
#Amaah Dikko
#Fu'ad
#Rufy


VIP 1K
NORMAL GROUP 500
[9/20, 8:07 AM] Asmy B Aliyu: BOYAYYAR ALAƘA
(Secret Relationship)

FREE PAGE
Asmy b Aliyu


9...

Ta sanyo kanta cikin parlorn shikuma ya saka nasa kan zai fito sukaci karo da juna,
dan ja da baya yayi itama taja da baya ta ɗaga kanta tana kallon sa, yana sanye ne
cikin shadda milk kansa babu hula kusan lokaci ɗaya suka saki murmushi, duk da
yanayin da zuciyarta ke ciki “Amaah Dikko." Ya faɗa wearing a loverly smile
shimfiɗe akan fuskarsa.
Yanayinta kawai ya tabbatar masa daga makaranta ta fito, kwana biyu ko gaisuwa
babu daman nine ke ƙiran naki idan ban ƙira ba ke bakya taɓa tunanin ki ƙirani, ta
ɗan shagwabe fuska tana kallon Abdul-hakeem Datti yadda ya tsaya a gabanta tamkar
ya maidata ciki dan so, bai taɓa son wani a rayuwarsa ba baya ga iyayensa wanda bai
bude idonsa da saninsu ba, kusan rayuwarsa a hannun baffansa yayi ta, abu ɗaya zai
iyacewa kasancewarsa acikin zuri'a dikko family yawan ganin Amatullah Dikko a koda
yaushe ya saka masa zazzafar kaunar Yarinyyar, wasu lokuttan yakan karyata kansa da
haka kasancewar yasan da a kauye ne da yanzu yana da sa'an Amaah dikko tunda can
auren wuri suke, kusan a idonsa Yarinyyar ta girma, bai taɓa faɗawa kowa wannan
sirrin ba dan ko abokinsa Junaid da suke raba damuwarsu a tare bai taɓa sanin
wanann sirrin na nasa ba dan bai taɓa furtawa ba, yasha jin yadda Junaid Dikko ke
ririta kannen nasa, yasha jin sa yana faɗin kannensa bazasu kula kowa ba sai sun
gama karatun jami'a hasalima shi zai zaba masu mazajen Aure, sanda yaji haka bai
san sanda ya ɗaga kai ya kalli Junaid Dikko ba tuni ya harbo jirgin abokin nasa
"Meyasa kake gudun duk wata hanyar da zata ɓata kannenka? Amman kuma kai kake ɓata
kannen wasu? Ko kana tunanin zunubbanka bazasu shafi kannenka ba Junaid? Lokaci
yayi da zaka dawo hankalinka,
ƙannenka girma suke kullum qara tasawa suke,
zunubinka yana zagaye dasu, idan aure shine maganin matsalarka kayi auren ka samu
zunubbanka su rage."
A duk lokacin da Hakeem ya ɗauko masa irin wannan zancen ji yake tamkar zuciyarsa
zata rabe gida biyu, idan kuma wani ya taɓa masa kannensa fa? Dan tsaf zan iya kai
karshen rayuwar duk wanda yayi kuskuren taɓa kanne na.
"Yaaya Hakeem." Kalamanta ne suka dawo dashi daga tunanin sa, ɗage mata gira yayi
alamar yana jinta “Oh nikam sau wawa nake kiranka dan Allah amman duk sanda muka
haɗu sai kayi min gorin bana kira."
“Ƴanxu dai na yadda kina ƙirana, ya makarantar ya kuma karatu akwai daɗi? Samarin
ki kuma nawa?"
Wannan karon zuba masa idanunta tayi tana ɗan waresu akansa, ta ɗan turo baki a
hankali take faɗin “Wannan tambayoyi sunyi yawa, gaskiyya zan amsa maka biyu mubar
ɗaya."
Tacigaba da kallanshi tana cewa “Makaranta Alhmdullahi, karatu kuma da sauƙi, kasan
mu sabon shigane sai a hankali." Ta qarasa maganar cikin sanyi muryarta dake narkar
da zuciyar Abdul-hakeem,
"Baki isa ba duka zaki amsa min." Sai ta nufi cikin parlorn tana waiwayensa tana
faɗin “Zuwa wani lokacin Yaaya." Da wani kallo ya bita har ta bacewa ganinsa.
Mamma ta samu a parlor wacce shigowar Abdul-hakeem ce ta fito da ita parlorn, yazo
ne ya kawo mata drugs dan har lokacin wata irin mura ke damunta mai zafin gaske,
Amaah ta gaisheda Mamma wacce ta bita da ido tana kallon yadda idonta suka dan faɗa
"Lafiyan ki dai kou?" Mamma ta faɗa cike da kulawa tana kallon Amaah "Kaina ke
ciwo." "Kije kiyi wanka kici abinci kisha magani Allah ya qara sauƙi." Ta amsawa
Mamma da Ameen ta miqe tsaye ta nufi part ɗin su, kai tsaye ɗakinta ta nufa tun a
mota take ƙiran wayar Fu'ad amma a kashe har wani zazzaɓi-zazaɓi taji yana ƙoƙarin
rufeta lokaci ɗaya, kayan jikinta ta ɗan rage, kai tsaye toilet ta faɗa dan yin
wanka, tana fitowa ta faɗa gado.
Har bayan magrib tana ta kwanciya a ɗaki kuma har lokacin wayar Fu'ad a kashe ta
rasa inda zata tsoma ranta dan taji sanyi ko abinci kasa ci tayi, daman idan suna
faɗa da Fu'ad kasa samun sukuni take watarana har dasu rashin lafiya, kusan
soyayyar tasu rabinta faɗa ne a cikinta, kuma duka fadan da zasuyi Fu'ad ne marar
gaskiyya sai dai ita ta sauƙa ta basa hakuri, ko shi yayi mata laifi bazai taɓa
bata hakuri ba.Kai tsaye ya faɗa mata shi bazai iya baiwa macce hakuri dan yana
sonta ba.
Turo ƙofar room ɗin nata da akayi ne yasa ta qara manna kanta jikin pillow duk da
ba barci take ba, tana son zama ita ɗaya, jin Mum ta ƙira sunanta ne yasa ta ɗan
buɗe idonta da suka ƙanƙance, Mum ta zauna a gefen bed tana kallon Amaah ɗin da
wani yanayi da take hangowa acikin fuskarta, itama Mum ɗin dawowar ta kenan fita
tayi ƴar kawarta ce zatayi aure to sune manyyan iyaye a wajen "Lafia kikazo kika
kwanta a ɗaki? Assha tace tun da kika dawo makaranta baki zauna parlour ba meke
damunki?" Hawaye taji suna cika idonta a hankali, kirjinta har wani zafi taji
yanayi mata.
Duk yadda taso Mum karta ga hawayenta kasa riqesu tayi, baki buɗe Mum ke kallon
Amaah har zata buɗe baki tayi magana da sauri Amaah ta shige jikin Mum ɗin gamida
fashe da kuka mai ciwo wanda ke fitowa daga can kasan zuciyarta. Mum ce ta ɗagota a
ruɗe tana faɗin "Wai laifiyan ki da bazakiyi min magana ba?"
Mum ta ɗan yi maganar a fusace "Mum daman Rufy zatayi birthday jibi shine na faɗa
mata gida baza'a barni ba shine tayi fushi." Shiru Mum ɗin tayi kafin tace "Saboda
sakarci kan wannan maganar zaki zo ki wani ɗaga hankalinki? Wai meyasa kike abun wa
waye?Jibi idan kika shiga school ɗin sai ki kwana a hostel wajen Rufaidah ɗin kuyi
party ɗinku a natse. Ni nasan yadda zanyiwa Abbanku bayani." Wani sanyi Amaah taji
aranta duk da tana jin qaryar da tayi tana danne mata kirji "Sai ki tashi ki fito
kici abinci ga ɗinkunan ku na Anko da na karbo maku wajen Salma tace ranar Friday
za'a saka ranar da ake dinner." Kusan tare suka fice ɗakin da Mum kai tsaye kitchen
ta nufa, sai a lokacin ta dawo hankalinta, tasan tana jin yunwa, text tayi ma Fu'ad
na ban hakuri akan zataje birthday ɗinsa_Dan Allah ka ƙirani bazan iya barci ba
idan banji muryarka ba._ Har kusan qarfe 10 tana tsammanin jiran ƙiran Fu'ad ɗin
dialling lambarsa tayi ta shiga sai dai line busy ake danna mata, kusan minti
talatin ta qara gwada kiran still line busy, nan take zuciyarta ta bata da wata
yake waya tura wayar tayi ƙarƙashin pillow tana jin wani abu na zagaye xuciyarta
lokaci ɗaya, gaskiyyar Rufy ne da take faɗin Fu'ad yana da yammata sosai wanda suka
fita wayewa da bariki idan zata waye ta kwato Fu'ad ɗin hannunsu toh, idan kuma
zata zuba idone sai a tafi a haka, dan tana ganin kalar rayuwar da Fu'ad ɗin yake
so ko ta ɓata yayi yanzu nan zata fara complain bancin yanzu kai ya waye......
"Ya dai bari idan ya aureni sai ayi haka."Amaah ta faɗa ma Rufy a wani lokaci can
baya, Rufy batace komai ba sai ta taɓe baki ta ɗauke kai aranta take faɗin, mudai
je zuwa Yarinyya indai Fu'ad ne duk wannan taurin kan naki zai sauke maki shi, haka
zai ja ra'ayinki dan har lokacin Rufy kallon shasha take yiwa Amaah gata dai da
kalar waye sai dai da suka zauna na ɗan lokaci zaka san babu wata wayewa a tareda
ita.
Ssi kusan 12 ya ƙira dan har barci ya fara ɗaukarta karar wayarta ya tasheta Fu'ad
ne mai ƙiran, ɗauka tayi ba tareda tayi magana ba dan har lokacin zuciyarta wani
zafi-zafi take yimata "Bakiyi barci ba?" Ya tambaye ta can kasan makoshi "Har na
fara kai ka tasheni, dawa kake waya Fu’ad?" Tayi tambayar da sanyi a muryarta “Da
Jawad ne." Tasan karya yake yimata sai dai bata qara tada zancen ba sai cewa tai
“Baka ga saqona ba?"
“Yes nagani...."
“Toh baka ce komai ba ko baka farin ciki?"
“Inayi sosai finally zaki haɗu da manyan friends ɗina."
"Uhm....” Kaɗai ta iya faɗa, hira ya riqa yimata sama-sama har sai da ya fara jin
saukar numfashinta alamun bacci sannan ya katse wayar.
Washe gari da ƙarfinta ta tashi tamkar babu abunda ya faru ko da suka haɗu school
da Rufy ta faɗa mata yadda sukayi da Mum daria kawai Rufy tayi tana faɗin "Da kyau
yar gidana da alamar kin fara shigowa gari." Murmushi kawai tayiwa Rufaida a gefe
kuma tana tunanin me zata siyawa Fu'ad a matsayin birthday gift ɗinsa, sai kusan 4
suka haɗu dashi fitowarsa kenan daga lecture daman ita yau 12 kawai suke da lecture
shi ta tsaya jira, ta kwantar da kanta jikin seat na motar tana kallon cikin
idanunsa "Yunwa kakeji Fu'ad kaga yadda kayi wani zuru-zuru?" Murmushinsa na gefen
baki ya sakar mata ya tada motar yana faɗin "Muje muci abinci."
Gida taso tafiya amma sanin halinsa yasa tayi shiru bata qara faɗin komai ba.

BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu

Katin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730

#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#Amaah Dikko
#Hakeem Datti
#Fu'ad

VIP 1K
NORMAL GROUP 500
[9/20, 8:17 AM] Asmy B Aliyu: BOYAYYAR ALAƘA
(Secret Relationship)


https://arewabooks.com/u/asmybaliyu


FREE FAGE.
Asmy b Aliyu



10.

Da kansa ya shiga restaurant yabarta a mota sanin halin Amaah ɗin ya dawo da kusan
ledojin biyu a hannunsa, back seat ya buɗe ya saka ledojin, makaranta suka koma
kusan a cikin motar sukaci abincin, duk yadda Fu'ad yaso ya sauketa a gida kin
yadda tayi tace masa driver zaizo ya ɗauketa, sannan ta faɗa masa gobe zatazo
hostel sai yazo ya ɗauketa anan ɗin. Ya rigata wucewa itama bata daɗe ba driver
yazo daukarta, koda ta koma gida ta samu su Abba sun dawo ta yiwa Abba sannu da
zuwa da kuma Yaya Junaid dake zaune cikin parlorn Mamma yana danna wayar hannunsa.
Da ido ya bita ganin shigar dake jikinta, wani irin sanyi taji aranta daman tun a
hostel ta cire veil ɗin jikinta ta mayar jaka. Washe gari ya kama Wednesday sai
kusan 10 ta fita daga gidan daman kuma duk yinin ranar lecture ɗaya zasuyi 2to4.
Drivern Junaid ne ya sauketa a makaranta, tun kafin su tafi dama ta shiga ɗakin Mum
ta faɗa mata tayiwa driver bayanin ita zataje da yamma za'a zo da yamma a ɗauka ta
suna da bikin Yar kawarta kuma Abba yasan da bikin. Haka Mum ta fita ta faɗa masa.
Ƙarfe 2 suka fito daga lecture Rufy ta rakata siyayyar gift ɗin da zata bawa Fu'ad
ɗin wanda daman duk qarshen wata Alh Dikko ya ware kuɗin da yake turawa duka ƴaƴan
nasa har Junaid da kuma matansa, so kuɗi ba matsalar Amaah Dikko bane ba. Kusan
shaddar 50k ta daukarwa Fu'ad ɗin kala biyu sai kuma Agogon Rolex da kuɗinsa ya kai
70k karshe ta haɗa masa da turarruka masu tsadar gaske, Rufy ta gyaɗa kai tana
faɗin. "Lallai kina ji da Fu'ad ɗin nan Besty, irin wannan hidima haka? kusan fa
200k kika kashe masa fa." Murmushi Amaah Dikko tayi tana ɗan juya ido take faɗin.
"Kin san kuɗi ba matsala ta bace kuma kin manta Fu'ad yadda yake a wajena ne?"
Gyaɗa kai kurum Rufy ta shiga yi, haka suka dawo hostel ɗin, da yammah suna shirin
tafiya Amaah ta sake yin wanka riga da wando ne a jikinta, sai maroon Turkish abaya
da ta ɗora kanta gamida yin rolling kanta da veil ɗin abayar tayi wani irin kyau na
ban mamaki. Baki Rufy ta saki tana kallon Amaah. "Kice min mafarki ne Besty, badai
da wannan shigar zaki tafi birthday ɗin Fu'ad ba?" Da mamaki a fuskar Amaah ke
faɗin. "Toh a ya kike so na tafi Rufy?" Tace, "Nifa na zata da riga da wandon nan
kaɗai zaki tafi, wallahi baki ga yadda kikayi kyau acikinsu ba dan sun fito da
ainahin surar da Allah yayi miki. Please dan Allah ki cire wannan abar da kika wani
ɗora." Da mamaki Amaah ta shiga girgiza kai. "Ni ake son gani a wajen ko jikina
Rufy? a hakan ma nayi ƙoƙari wannan shine karo na farko da zanje party fa." Rufy
tace. "Amman wallahi xaki xama ƴar kauye a wajen." Shiru Amaah tayi ba tare da ta
qara tankawa Rufaidah ba, itama Rufy ɗin bata qara magana ba. Sai kusan shida har
da rabi Fu'ad ya shigo cikin makarantar, wayar Amaah ya kira yace gashi cikin
makarantar, ta sauke wayar ta kalli Rufy da ta haɗe cikin riga da wando tamkar ba
ƴar musulma ba, ga kalabar gashin doki da tayi dake ta faman reto a tsakiyyar
bayanta. "Fu'ad ya qaraso." Rufaida ta kalleta tana faɗin. "Ku tafi zamu taho tare
da Jawad." Kasancewar Jawad ɗin abokin Fu'ad ne kuma boy friend ɗin Rufy ne. A
tsorace Amaah ke faɗin. "Ba sai mu tafi tare ba sai ya samemu duk acan." Amaah
Dikko ta faɗa da ɗan tsoro a murya ta. "No kawai ku tafi nayi masa alkawarin zan
jirasa idan yazo ya tarar bana nan zaiji ba daɗi." Har bakin mota Rufy ta raka
Amaah da duk jikinta ya gama yin sanyi, wani irin strange feeling ta rinqaji a duk
kan cikin jikinta tamkar bata da lafiya. Tunda suka fito Fu'ad ke kallonta har
Rufaidah ta buɗe back seat ta saka bag ɗin dake ɗauke da gifts ɗin Fu'ad ɗin. Ɗan
hugging ɗinta Rufy tayi ta ɗago gamida ware mata ido tana faɗin. "ya naga jikinki
duk yayi sanyi ke kin san fu'ad bazai cutar dake ba idan kin hango kalar son da
yake yi miki. Dan Allah kiyi ƙoƙari kiyi enjoying wannan ranar tare dashi, karki
bawa Fu'ad kunya a idonsu Mufeeda, sai na qaraso nima yanzun zan kira Jawad." Rufy
ta faɗa tana buɗewa Amaah gaban motar ta shiga ta rufe ƙofar, da suka haɗa ido da
Fu'ad sai ya sakarwa Rufy wani irin murmushi babban yatsansa ya juya alamar ya
gode. Tunda suka ɗauki hanya bata yi masa magana ba, a karo na farko cikin
rayuwarta da taji wani iri akan kebewa wuri ɗaya da Fu'ad, cikin minti talatin suka
karasa cikin gidan mahaifinsa dake cikin G.r.a., banda faɗuwa babu abunda gaban
Amaah yake yi kuma tsoro ya hana ta tambaya Fu'ad ɗin nan ina ne? Dan beyi kama da
hotel ɗin da yake magana ba akan acan za'a yi birthday party ɗin nasa. Maigadi yazo
da sauri ya buɗe masa gate, a hankali ya nufi wajen da aka tanada dan parking ɗin
motoci ya kashe motar ya juya yana kallonta yana hango bayannen tsoro cikin
fuskarta, lokaci ɗaya ya kamo hannunta yana murzawa cikin nasa a hankali, wani irin
yanayi ta tsinci kanta cikinsa ga wani miqewa da taji tsintar jikinta nayi. "Nan ne
asalin gidanmu baby tunda tsoro ya hana ko ziyara ki kawo min, kamarki ace baki san
asalin gidan mahaifina ba?" A hankali ta zare hannunsa anata tana ɗan yarfi da
hannun jin yadda yayi mata wani irin nauyi. Buɗe ƙofar motar yayi yana faɗin. "Muje
part ɗina na canja kaya sai mu tafi." Girgiza masa kai ta shiga yi cikin rawar
murya take faɗin. "Zan jiraka a mota Fu'ad." "Amaaah please!" Ya faɗa da
bayyanannen sauti a muryarsa, da haka ya saka hannu ya buɗe motar ya fito ya zagaya
ya buɗe mata nata ɓangaren, da ido take roqonsa lokaci ɗaya ya haɗe rai. "In har
bazaki shiga part dina ba kawai muje na mayar dake gida bama sai kinje birthday ɗin
ba na yafe zuwan." Ya faɗa da fushi a muryarsa ganin lokaci ɗaya yadda fuskar Fu'ad
ɗin ta juye yasa ta fito daga motar, back seat ta buɗe ta ɗauki bag ɗin, hannunta
ya kama suka nufi wani bangare na daban ma'akanta gidan sai gaishesa suke cike da
girmamawa suna mamakin wannan kalar rayuwar da Fu'ad ɗin keyi. Har ya ƙarasa dasu
ainahin part dinsa wanda baxan iya misilta muku kyansa ba kallo daya xakayiwa wurin
kaga part din dangata, a falo taja ta tsaya. "Kaje ka shirya zan jiraka a falo." Ta
faɗa tana kallonsa, ɗaga kai yayi kawai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login