Showing 3001 words to 6000 words out of 15526 words

Chapter 2 - BOYAYYAR ALAƘA 1 by ASMY B ALIYU

26 May 2026

13

yanzu.” Ya mutse fuska ya shigayi tamkar Mamma na agabansa yake
faɗin “Toh ya barni na wakilcesa mana Mammah ba dole sai yaje ba." Aran Mamamh tace
ja iri saboda kaje ka sheki ayarka ko? Allah ya shirya min kai Junaid. idan tace
kaddarar Junaid bata damunta zatayi qarya idan tace kaddarar Junaid tana hanata
barci ana din ma ƙaryar zatayi, a duk safiyar Allah har fargabar take yaron nata
yafita batasan yaran mutane nawa ya lalata ba, kalar qaddarar tasa nayi mata wani
irin nauyi a kirji “Ka tabbata kayi shafa’i da wutri kafin ka kwanta?” Mamma ta
faɗa cike da kulawa “Insha Allahu Mamma, ki kula da kanki ina kaunarki fiye da
komai a duniya." Murmushi Kurum Mamma tayi gamida sauƙe wayar, ƙiran Khairiyya ne
ya shigo a wayar tashi tamkar bazai ɗaga ba dan fushi yake da ita sosai akan wani
vedio nata da ta saka a duka kafafen sada zumunta, wanda tsaraici ne zallah a
cikinsa, wata irin ajiyar zuciya ta shiga saukewa jin ya ɗaga wayar "Mine meyasa
kake azabtar da zuciya tane? So nawa xan baka hakuri akan wannan vedio ɗin, kuma
kaje ka duba tun ranar da naga ranka ya ɓaci naje na gogesu duka." Still kin magana
yayi, tamkar zatayi kuka take faɗin "Dan Allah kayi min magana idan ba so kake nayi
hauka ba."
"Khairiyya zan kashe wayar idan kin gama barci zanyi," ya faɗa da wani yanayi mai
tattare da fushi a muryarsa, me zanyi ka yadda dani dan Allah."kittttt taji ya
katse wayar, kashe wayar yayi duka bayason takura yasan nacin khairiyya bazata
daina ƙiransa ba,
Shi kuma still fushi yake da ita sai ya gaji dan kansa sa'annan zai sauko,wani
murmushi yayi wanda iyakarsa a fatar bakinsa "Tayaya Mamma take hango masa
khairiyya zata zama matar aurensa har ta zama uwar yayansa tayaya? A kullum
tambayar da yake yawan yiwa kansa kenan, da gaske yana bukatar aure cikin rayuwarsa
kodan Mamman sa ko zai samu zunubban da yake manne dasu zasu rage.
Washe gari bai tashi ba sai wuraren qarfe 11 na safe, ya na tashi kai tsaye toilet
ya nufa dan yin wanka, daman daga shi sai boxer ne ajikiinsa dan baya kwana da kaya
ajikiinsa, idan kaga Junaid Dikko da pyjamas a jikinsa to a parlornsa yake yana
aiki da laptop ko zai shiga cikin gidansu da kuma ya fito zai ciresu, komai sanyi
baya kwana da kaya ajikiinsa, a hankali ya saki shower ajikinsa tururin ruwan zafi
na shiga cikin jikinsa, kasancewar lokacin hunturu ne.
Yafi awa ɗaya a toilet ɗin sai kace wanda zai canja fata .ya fito ɗaure da qaramin
towel a waist ɗinsa sai kuma wani akansa da yake tsane gashin kansa dashi wanda ya
cika masa kai asalin gashin hausawa, wanda sabida mayyunka masu tsada da yake shafa
ma kan yasa ya nannaɗe ya koma kamar na larabawa.
Asali su….
Aliyu Dikko haifaffen garin Dikko ne dake cikin jahar Katsina, matan aurensa guda
biyu uwar gidansa mai sunan Hajiya larai Dikko, yaro ɗaya Allah ya mallaka masu a
duniya wato Junaid Dikko, daganan haihuwar ta tsaya masu kusan shekaru talatin da
bakwai babu asibitin da basu shiga ba amman ko wane asibiti abu ɗaya ake faɗa masu
daga uwar har uban lafiarsu kalau, a haka Abba ya auri Hajiya Rafia itakuma asalin
yar Bauchi ce, suna da ya'ya biyu a tsakaninsu Amatullah itace yarsu ta farko mai
shekaru goma sha bakwai a duniya yanzu ne ta shiga jami'a aji na farko a jami'a,
babu yadda Mum batayi ba da Alhaji dikko ya kai Amaah ƙasashen waje tayi karatu har
ya yadda Junaid Dikko ya ɓata komai, anan yake faɗawa mahaifin nasu macce ce idan
ta tsallaka ta tafi waye zai kula da tarbiyarta?? Bakaramin ciwo Mum taji ba daga
ita har Amaah, gashi dama wasu kawayenta da sukayi secondary school a tare
kasancewar iyayensu nada hali duk ƙasashen waje aka turasu karatu, a karo na biyu
Mum ta qara neman alfarma a wajen Abba, akan yabar Amaah ɗin taje Bauchi tayi
karatu tunda iyayen Mum ɗin na a raye sai ta zauna a gidansu, buɗar bakin Abba a
lokacin yake sanar da ita Junaid ya riga da ya samar mata gurbin karatu a (Umar
Musa Yar'adua) haka Amaah ta hakura ba dan taso ba ta fara karatu inda take
karantar (Accounting) daman can jininsa bai wani haɗu da Amatullah ba, tsanani yake
yimata a duk inda zata shiga security ne a tare da ita har a makaranta.
Sosai abun ke damun mum akwai ranar da ta kasa hakuri ta kalli cikin idon Junaid
ɗin tana faɗin an faɗa maka yadda kake ɗan iska haka kowa yake ɗan iska? Sannan ba
ta fatar zunubin Junaid Dikko ya shafi ƴaƴanta yabari idan ya tara nasa ƴaƴan sai
su raba zununbin a tare, Mammah na gun lokacin a tsaye bata san lokacin da hawaye
suka fara Rolling akan fuskarta ba tun daga kurciyarsu har girmansu basu aikata
wani abun da zai mannewa Junaid Dikko ba, basu taɓa aikata wani zunubi na saɓon
Allah ba daga ita har Aliyu Dikko, kawai dai sunyi imani da Allah qaddarar Junaid
ɗin ce a haka suna masa addu'a a kullum ba tareda sun gaji ba dan sunyi faɗa sunyi
hantara abun ya faskara tun Junaid na ɓoyewa iyayensa halinsa har abun yazo ya
bayyana.
"Meyasa bazakayi aure ba Junaid idan mata kakeso Allah ya baka ikon ka aje macce
har hudu a karkashin kulawarka, meyasa sai mata kazamai? Matan bisa titi kana jin
zaka yiwa Allah wayau ne na taka tsantsan da kakeyi da Rayuwar naka kannen? Kasan
kannen mutane nawa ka ɓata ka san iyaye nawa kasa bakin ciki akan lalacewar
ƴaƴansu?" Ya ɗaga kai ya kalli Mamman sa a lokaci wani irin abu ta ke hangowa cikin
idanun Junaid Dikko “Da gaske ina son na bari Mamma, ke shaida ce da nace zan bari
koda na sati ɗaya ne sai na yi zazzaɓi, kuma Mammah matan nan da ake magana akan su
bani ke kawo su ba da kakafunsu suke zuwa, ni babu maccen da na taba samu a Virgin
a empty suke kawo kansu." A lokacin Mamma ta ɗaga kai tana kallon yaron nata tana
mamakin rashin ta idon Junaid.
Aysha Dikko yanzu ne take ss 2 a secondary school, itace kuma fav sis ɗin Junaid
Dikko bayaga Mamma da Abbansa, Assha Dikko itace mutum ta ukku wacce yafiso a
rayuwarsa. Gabaki ɗaya karatun Junaid Dikko a Oxford University yayi sa degree na
farko da na biyu, degree na farko under business Administration yayisa sai digree
sa na biyu medical science, sabida Mamman sa wacce itama a ɓangaren lafia ta
karanta (political science) Tana aiki da (Dikko special hospital) ko kaɗan Junaid
Dikko baya da ra'ayin business da ƙarfi da yaji mahaifinsa ya turasa cikinsa, tunda
shi kaɗai ne ɗa namiji tal wanda ya mallaka a duniya, Aliyu Dikko yana ɗaya daga
cikin masu kuɗin Nigeria wanda sukayi suna yana da kamfanonin da bai san adadinsu
ba anan gida Nigeria da kasashen ketare, yana da gidajen manfetur, gas, plaza's,
hotel's, Companyn sai da motoci da machine. Yafi ƙarfi akan kasuwanci fiye da
likitanci, Amman duk da haka shine family doctor na Dikko's family.
Mum itama ƴar kasuwace tana da shops sun kai goma kuma tana siyar da different
abubuwa acikinsu, itama tana da ma'aikatan dake ƙarƙashinta, idan kaga kiyayyar Mum
to ɓangaren Junaid Dikko ne wanda keyi mata iko da ya'yanta fiye da uban da ya kawo
su a duniya,
Aliyu Dikko shima a wajen mahaifansa shi ɗaya suka haifa har suka bar duniya sai
ƴaƴan ƴan uwan dake zagaye dashi, wanda wasu ma a karkashinsa suke aiki kuma yana
taimakon ƴan uwansa sosai, qaddarar Junaid bada garesu bane daga Allah ne, Allah ne
ya ɗorawa Junaid Dikko neman mata tamkar hauka, sunyi faɗa sunyi nasiha sun razanar
duk a banza, dan haka suka zubawa Junaid Dikko ido sai dai a duk safiyar Allah suna
yiwa yaron nasu addu'ar shirya, da ga uwar har uban sun buɗe massalatai da
islamiyya masu sunan (Junaid Ali Dikko ) suna nemar masa sassauci a wurin Allah,
baya ga halin neman matan banza Junaid bayada wani hali wanda ba'a so kuma shi ɗin
mutune na Jama'a haka abun hannunsa baya rufe masa ido. Kallo ɗaya zakayi masa
kasan Mamma ta haifesa komai nata ne har kalar fatar watau baki, da wasu irin idanu
Masha Allah wanda mafiyawancin idanunsa suke jan hankalin wasu matan, tsayawa zuba
maku bayanin kyan Junaid Dikko zai ci mu lokaci ba'a gama ba yana da kyau sosai, ko
kaɗan baya kama da Aliyu Dikko kasancewar Ali Dikko bafullatani ne kuma ɗan tsurut
kun san jikin Fulani yadda yake saɓanin Junaid ɗin dake dogo kakkarfan namiji.

Cigaban labari..


BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu shaidar biya ta 08086207764

Katin wayar MTN ta 08043079282 shaidar biya 07065283730.


VIP 1k
NORMAL GROUP 500
#ASMY B ALIYU
#BA(secret relationship)
#Love, Romance and Destiny
#Junaid Dikko
[9/17, 11:31 AM] Asmy B Aliyu: BOYAYYAR ALAƘA
(Secret Relationship)


FREE FAGE.


Asmy b Aliyu




INA KUKE MATA....INA NUFIN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU NA MATA, MATA MASU AJI MASU
GYARAN KANSU, KUZO DAKU NAKE MAGANA NASAN KUN YARDA DA KANKU KUMA ZAKU KASANCE
ABOKANAN TAFIYA, *HUMKAN GIDAN GIDAN ƘAMSHI* TAZO MAKU DA KAYAYYAKIN DA ZASU SAKE
KANKARO MAKU KIMA DA DARAJARKU TA CIKAKKIN MATA, KAYAN DA ZASU SAKA FARASHIN
MUTUNTAKARKU ƊAUKAKA A IDANUWAN MAZAJENKU, HMMMM WATA MIYAR FA SAI A MAKWAFTA
HAJJAJU DOMIN KUWA A GIDAN *HUMKAM GIDAN ƘAMSHI* KAƊAI ZAKI IYA SAMUN ABUBUWA KALA-
KALA DA ZASU CANCAREKI A DUK INDA KIKA SHIGA KIRIƘA JIN KANKI DABAN SABODA YANDA
KIKAYI ZARRA ACIKIN ƳAN UWANKI MATA, KAMA DAGA KAN *HAƊAƊIYAR ZUMARMU* DA MUKAYIWA
LAƘANI DA *MAI CIZO* SABODA YANDA TAKE ƘWANTALO SOYAYYA GA ZUCIYAR MAIGIDA, GA KUMA
*SPECIAL HAƊIN AMARE* DA MUKE FARA SHIRYASU ANA SAKA RANAR BIKI SABODA SAKA
MALLAKAR ZUCIYAR ANGO DA KUMA SAKE ƊAUKAKA JIN ALFAHARINSA, BAYAN NAN MUN TANADI
SINADARIN MU NA MUSAMMAN DOMIN JIN DAƊIN MA'AURATA DA MUKAYIWA LAƘANI DA *HARBI
GADO*😍 CANCARAKWAI KENAN! ƳAR UWA KE DAGA JIN WANNAN HAƊIN KINSAN IDAN BA AGIDAN
ƘAMSHIN HUMKAM BA BABU INDA ZAKI SAMU DON ITA ƊIN FA GWANACE, KAWAI KU SHIGA DAGA
CIKI ZAKU TABBATAR DA HAKAN, BA'A NAN KAƊAI TA TSAYA BA HAJIYA SAI DA TAYI MAKU
TANADIN *TURARUKKAN MANYAN MATA MA'AURATA* DON SAMA MAKU CIKAKKIYAR NATSUWA A
GIDAJEN AURENKU DA IRIN SIHIRTACCEN ƘAMAHINSU DAKAN NARKAR DA ZUCIYAR MAIGIDA YA
KASA FITA, GA KUMA *SHU'UMAR HUMRAH* TA MUSAMMAN DA TAYI MAKU TANADI MAI SUNA DAGA
NI SAI KAI MIJINA DA ZATA RIƘA RIKIRKITA DUKA TUNANIN MAIGIDA IDAN YANA TARE DAKE,
HAR YAU DAI *HUMKAM GIDAN ƘAMSHI* BASU BARKU A HAKA BA SAI DA SUKAYI LINƘAYA A
DUNIYAR NAGARTA CIN MAGUNGUNAN DA ZASU SAMA MAKU WARAKA GA MAFIYA MATSALTSALUN DA
SUKA ADDABI MA'AURATA HAR MA DA ƳAN MATA SUKA SAMO MAKU *ORIGINAL INFECTION KILLER*
NASAN DAI KO BAN FAƊA BA KINSAN WANNAN MAGANI GANGARIYA NE DA ZAI YI YAƘI DA DUK
WATA CUTA DATA SHAFI:
✓CIWON MARA
✓ƘAIƘAYI
✓FARIN RUWA
✓ƘURAJE
✓DRYNESS
✓LOW LIBIDO
✓IRRIGULAR PERIOD
✓ABNORMAL DISCHARGE
✓MILD INFERTILITY
✓VIGINAL ODOUR
✓OVERIAN CYSTS
✓FABROID E.T.C
Wannan maganin duka zai sama maku waraka daga wuɗannan cuwurwukan da yardar Allah,
kuma zaku samu duka wuɗannan kayan a *HUMKAM GIDAN ƘAMSHI* bisa farashi mai sauƙi
da kuma girmamawa domin ita ɗin mai ƙaramci ce ga abokannan kasuwanci da kuma
mutuntawa, ga mai buƙatar kayanmu sai ya tuntuɓemu ta wannan lambar kai tsaye
+2348132506044. HUMKAM GIDAN ƘAMSHI na maraba da masu sayen ɗaya ko sari.
4..

Kusan cin karo sukayi da sauri Amaah Dikko taja da baya tare da zaro ido, bata taɓa
tunanin Junaid Dikko yana gida a irin wannan lokacin ba, tun daga kanta har zuwa
kafafunta yakebi da kallo, Atamfar super wax ce ajikinta wanda aka yi mata ɗinkin
fitted gown ajikinta wanda ya lafe cikin jikinta haka rigar ta ɗan dage mata, har
ana hango sarƙar ƙafar da ta sa ka a ƙafarta ta daban, idonsa suka sauƙa a kan
sarqar kafarta ta, ya sha ganin sarqa a kafafun kadangarun bariki yana ganin kyanta
ga mata, wanda yayi alƙawarin matar aurensa zatayi masa kwaliyya dashi acikin
gidansu kawai idan zasu fita baya buqata, a wani irin haukace ya ɗago kansa yana
kallon Amaah Dikko wacce take kanƙame jikin kofa da ɗan qaramin veil
ɗinta(Chantilly) wanda ta ɗora akan kafaɗa, ya tsaida idonsa cikin fuskarta tamkar
mai son gano wani abu, ganin wani mugun haske da ta qarayi har farin nata yaso yayi
yawa kuma yana kashe ido, ga kananun pimples da suka fara taruwa a fuskarta da
alama tana using da mayyukkan dake qara haske fata, tana ganin Junaid ya saka hannu
a wandonsa yana ƙoƙarin ciro belt din jikinsa ta zubara ta yar da qaramar handbag
ɗinta ta juya ta koma cikin Parlon da gudu tana kwalawa Mamma ƙira da mum ɗinta,
daman Mamma na kitchen Mum dake sama ta riqa jin ihun Amaah wacce yanzun nan tayi
mata sallama akan zata shiga school, da sauri take saukowa kan stairs ɗin tuni
Amaah Dikko tayiwa kanta maɓoya bayan Mamma, still Junaid dikko bai fasa binta ba
"Metayi da safiyan nan zaka wani ciro belt irin ga jaka ka samu? Waini yaushe
xakayi xuciya ka daina shiga sabgar ƴaƴana Junaid Dikko?" Mum tayi maganar so
pissed up.
Wani irin fisgota yayi a bayan Mamma, saukar belt taji a bayanta, a fusace Namma,
ke faɗin "Wai meke damunka? Me tayi maka??" Mamma ta jeho masa tambayoyin lokaci
ɗaya rai a bace, shima rai a ɓace yake faɗin "Kalli da shigar da za ta je makaranta
tamkar ba yar musulmi ba kalli shegen mayafin da ta saka Mamma? Kalli ƙafanta
sarqa ne ta ɗora ki kalli face ɗinta yadda ta canja Mamma? Duk farin da take dashi
bata godewa Allah ba sai tayi bleaching dan tana yar iska?" ya faɗa a tsawace.
Wata daria Mum, ta fashe dashi tana tafa hannayenta tana ganin qarfin hali wai
Junaid ke faɗin wasu yan iskane "Muje ki tattara mayukkun da kike shafawa ki
kwasosu duka, haka duk wata tsinannar sutura da kike sakawa ki tabbata kin fito
dasu yau ɗin nan."
A tsorace Amaaah ta juya ta nufi stairs sai famar hawaye take tana tsinewa Junaid
Dikko aranta, wannan takura har ina? Itama Mum tama kasa magana sabida bakin ciki
dan duk ihun da zatayiwa Junaid bazai saurareta ba, ita kanta tana ɗan shakkarsa.
Kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kaga ɗakin ƴar gata babu abunda Babu a dakin, tun daga Tv
, fridge, a tsorace ta qarasa gaban mirror ta kwaso duka mayukkan da take using
dasu, hannu Junaid ya saka ya ɗau ki daya ya shiga dubawa "Ki jawo ɗaya daga cikin
trolley ɗinkin ki zuba." Babu musu tayi yadda yace dan har lokacin zafin belt ɗin
da ya zuba mata bai gama sakinta ba, haka ya sakata a gaba ta fitar da duk wani
sutura da tayi ɗinkin banza, haka ya tattara duka veils ɗinta ya zuba acikin bag
din. Ya kalleta yace ta ɗau ki wasu kayan ta shiga bedroom ta canjasu yanzun nan
babu musu tayi yadda yace, still yana tsaye yana jiranta ta fito ta saka rigar da
ta cire cikin bag ɗin tamkar zatayi kuka ganin duka rabin suturarta Junaid Dikko ya
kwashe, wani mayafin ta ɗauko zata saka, wani mugun kallo yayi mata yace "Daga yau
daga yanzun nan na haramta maki saka mayafi idan zaki school hijab." Tamkar zatayi
kuka duka hijab dinta babu ƙananu har qasa suke sallah kawai take dasu "Bani car
key din motarki?" Ya faɗa fuska a ɗaure, miqa masa tayi tuni hawaye sun fara zuba
cikin fuskarta da haka ya sakata gaba still har lokacin Mamma da Mum na cikin
parlorn ganin Junaid Dikko ya fita da trolley ɗaya, a fusace Mum ta qaraso tana
kallon Amaah tun daga sama har kasa ranta yayi balain ɓaci, a mugun tsawace take
faɗin "Gidan ubanwa zaki tafi da wannan hijab ɗin ba makaranta zakije ba?" Tuni
Amaah Dikko ta kasa riqe kukanta ta fashe da kuka take faɗin "Yaaya ya hanani saka
mayafi."
"A saboda yana ubanki ? Maza cire shegen hijab ɗin nan tunda ke ba dangin su malam
shehu bace."
"Ke wuce muje na saukeki a makaranta kina ɓata min lokaci!" Junaid Dikko ya faɗa a
mugun tsawace, a wani kalar razane Amaah Dikko ta juya tabi bayansa, with so much
shock Mum kebin Junaid da Amaah da kallo har suka fice daga falon, a wani irin
haukace ta nufi bedroom ɗinta wayarta ta ɗauka ta shiga ƙiran Abba, banda tafasa
babu abunda zuciyarta keyi. Abba yana ɗaga wayar ta fara da faɗin "Aliyu zanyi maka
wata tambaya??" shi kansa Abba sai da yaji wani iri bazai iya tuna wane lokaci Mum
ta ƙira sunansa kai tsaye ba "Ina jinki ai kunne ke ji." A kufule take faɗin"Da ni
da kai muka haifi su Amaah ko Junaid dikko ya haifa mana su?"
"Meya faru Rafee'a?" Duk da Abba yasan kwanan zance a fusace ta shiga yi wa Abba
bayanin abunda ya faru, idan na dawo gida zamuyi magana Rafee'a "Yanzu akwai aikin
da nake." Ba tare da Abba ya qara bata damar yin magana ba ya sauke wayar gefen bed
Mum ta koma ta zauna ta ɗau ki ƙafa ɗaya ta ɗora a ɗaya tana wani irin girgizawa me
zatayi ta kun ta tawa Junaid? Me zatayi masa yayi zuciya ya fita sabgar ƴaƴanta
yadda tasan Junaid Ali Dikko da shegiyar zuciya bata yi tunanin duk maganganun da
take yaba masa zai iya zuciya yabar kula ƴaƴanta, tunda ta sansa haka yake tamkar
mahaifinsa da shegiyar xuciya da bakar kafiya babu wanda ya isa ya tankwasa su akan
ra'ayinsu watarana ma har yafi mahaifinsa.
Har cikin makarantar ya kaita idonta har sun kumbura sabida kuka, yanzun ta ina
zata fara shiga school? Da hijab har kasa ai sai ta zama abun daria da kaskantarwa
ita addu'ar ta ma ɗaya Allah yasa Fu'ad bai shigo ba.
Ya kashe motar ya kalleta fuskarsa babu wani walwala da wani precious acikin
fuskarsa wanda ke gigita kannensa, a natse yake faɗin "Wannan ya zama ranar na
farko na qarshe da zaki fita da mayafi zuwa makaranta." A duk ranar da na kamaki da
mummunan shiga da sunan zuwa makaranta na rantse da Allah kin gama zuwa jami'a har
abada." Kalmar data gigita Amaah Dikko kenan gyada kansa yayi yana kara tsareta da
idonsa alamar da gaske yake, tuni hawaye suka fara taruwa a idanunta
"Idan an tashi ki ƙirani zanzo na daukeki daga nan zamuje ki zabi wasu kayan akai
wajen mai ɗinkin." Ɗaga kai ta shigayi kurum tamkar wacce akayiwa shegen duka, sai
da ya bata izini ta fice daga motar tana daga tsaye har yabar wajen, da gudu ta
koma bayan bishiya ta fashe da wani irin kukan bakin ciki, wayarta ta ciro ta shiga
ƙiran wayar Rufaida.
Ta na ɗauka cikin rawar murya take faɗin "Kina hostel?" Daga can bangaren Rufy ke
faɗin "Yanaji muryarki wani iri baki da lafiya ne?"
"Ki amsa ni Rufy dan Allah."
"Ina hostel." Kashe wayar tayi ta maida cikin jaka, miqewa tayi tsaye tana rufe
rabin fuskarta da hijab ta fara tafia a hankali zuwa hostel wajen Rufy. Amaah na
shiga dakin nasu, Rufy ta wani riqe baki tana faɗin "Yau kuma Malama Amatullah kika
zama?" Sai kuma ta fashe da daria tana kallon Amaah Dikko, daga sama har ƙasa dan
bata ma lura da yanayin fuskar Amaah ɗin ba data canja kala sabida kuka. gefen bed
Amaah ta zauna tana cire hijab ɗin jikinta sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login