Showing 9001 words to 12000 words out of 15526 words

Chapter 4 - BOYAYYAR ALAƘA 1 by ASMY B ALIYU

26 May 2026

11

cikakken minti biyu baiyi ba ta fito ta buɗe kofar
daman kuma tana zaune a parlor tana kallon wani American film ne, daga ita sai pant
a jikinta sai kuma bra, yana rufe kofar ta kwantar da kanta a bayansa gamida lumshe
idonta tana shakar turaren( Burhan) da yagama cika parlorn, duk son kamshinta idan
Junaid dikko na wuri kalar turarukkanta bacewa wa suke bat, da kansa ya kashe kayan
kallon ya kuma kashe fitullun dake aiki cikin parlorn, hannu yasa yaja hannunta
zuwa ainahin ɗakin barcinsa, pyjamas ɗin jikinsa taga ya cire a hankali ya hau kan
bed ɗin, kwantawa tayi cikin kirjinsa tana shafa chest ɗinsa a hankali, tana jin
wani sabon sonsa na sake cika ko ina a zuciyarta, ta mannawa chest ɗinsa kiss wanda
yasa Junaid ya qara riqeta cikin kirjinsa.
Duk da dim light ɗin da suka bari a ɗakin bai hanata hango yadda fuskarsa take ba
"Cigaba da yawo da hannunta tayi cikin jikinsa da wata irin murya mai rauni take
faɗin "Mine yaushe zamuyi Aure?" Wannan karon da gudu ya rufe idonsa zuciyarsa na
wani irin bugawa, ta daɗe tana yimasa wannan tambayar bai taɓa bata amsa ba, ko
yanzun ma shiru ne ya ratsa a tsakaninsu har na sakan goma, iyayenmu nason mu
kasance a ƙarƙashin innuwa ɗaya nima ina son muyi aure Junaid, da gaske ina son
naga ya ƴan mu na halak." Da wani irin sauri ya hankaɗa Khairiyya dake cikin
jikinsa, ya sauka daga kan bed ɗin da sassarfa ya nufi toilet haɗe kansa yayi da
kofar toilet ɗin bai san meyasa yake fusata ba a duk lokacin da yaji Khairiyya na
zancen aurensa daita ba, meyasa bata da tunani? Meyasa bazata taɓa hango aurensu
shi da ita bazai taɓa yuyuba ba, kamar yadda shima yake yawan hangowa, alaqarsu ta
tsaya iya dating alaqarsu ta tsaya kan titi kawai banda gidan aurensu, bai taɓa
hangowa kansa zasu zauna a karkashin innuwar aure ba, shirun sa da Khairiyya taji
yayi yawa ne yasa tazo ta tsaya a bakin ƙofar toilet ɗin tana ƙiran sunan Junaid
ɗin a hankali, dan tabbatar da lafiyar sa, fitowa yayi daga toilet ɗin yana kallon
yadda ta zama tsirara agabansa. Haka yaja hannunta zuwa kan bed ɗin daga nan kuma
komai ya sauya, duk yadda ya makara ga kwanciyya acikin kunnuwansa akayi ƙiran
sallar farko, dakyar ya cire Khairiyya dake manne cikin jikinsa tana barci wanka
yayi gamida fitowa da Alwallah ajikinsa ya zauna gefen bed, ya ajewa Khairiyya
guntun note a Jikin takarda dan yasan ta da dogon bacci, duk kalar tashin da xaiyi
mata bazata taɓa tashi ba, koda ya isa gida ana shirin tada sallah addu'a kawai
yake, kar su haɗu da Abba, har ya aje mota yana ƙoƙarin fitowa daga motar yaji
karar buɗe ƙofa da alamar Abba ne ya fito zaije massalaci sai da ya tabbatar da
fitarsa sa'anan ya fito daga motar yabi bayan Abba, sai kusan 7 suka fito daga
massalaci shida Abba.
Suna tafe yana yi masa bayanin ƙarfe 8 zasu kama hanya, bayan sun shigo gida kai
tsaye part ɗinsa ya nufa dan shiryawa kusan ƙarfe bakwai da rabi yayi sallama a
parlor Mamma.
Sanye yake cikin bakaken italyn suite da suka karbesa, Mamma ce ta ɗaga kai tana
kallonsa murmushi kwance a fuskarta, shima da nasan murmushin ya nufi Mamman, duk
tsayin ta sai ta zama gajera agaban Junaid dikko, dan shi ɗin mai tsayi ne, nan ya
ɗan rungume Mamma yana faɗin “Sabahul khair Mamma." Nan sukayi gaisawa irin ta uwa
da ɗa kafin Junaid ɗin ya zube cikin kujerun da suka ƙawata parlorn daidai lokacin
Abba ya ƙaraso cikin parlorn shima da nasa shirin sai dai shi ba irin shigar Junaid
bace ajikinsa riga da wando ne ajikinsa na kaftan farare sol, gefensa Assha dikko
ce sanye da kayan barci a jikinta da alamar barcin bai gama sakinta ba sai faman
murza ido take, kallon kayan barcin dake jikinta kurum Junaid yai ya kauda kai da
wata irin murya yake faɗin "Ashaa Dikko Hijab! Koma ki ɗauko hijab bana san
shirme.” Murmushi Kurum Abba yayi wani gefe yana alfahari da yaron nasa “Sallama
kawai zamuyi Yaya, komawa ciki zanyi wanka ma zanyi.”
“Na dai faɗa miki karki karaso !" Ya faɗa da precious voice ɗinsa haka yasa Ashaa
ta juya ta koma tana turo baki.

BOYAYYAR ALAKA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764
Katin wayar MTN ta 07043079282
Shaidar biya ta 07065283730



#ASMY B ALIYU
# BA(secret Relationship)
#Junaid Dikko
#khairiyyah

VIP 1K
NORMAL GROUP 500
[9/20, 8:04 AM] Asmy B Aliyu: BOYAYYAR ALAƘA
(Secret Relationship)

FREE PAGE.


Asmy b Aliyu


7...

Assha ta koma sai kuma ta fito sanye da hijab pink har ƙasa wanda ya qarawa
fuskarta wani irin kyau, a hankali ta zauna gefen yaayanta tana gaishesa. Ya amsa
yana kallon fuskarta yake faɗin "Bacci kou ?" Ta ɗaga masa kai, yace "Ina maganar
barci keda zaki shiga school kin san kuwa yanzu qarfe nawa?" Ta ɗan turo baki tana
faɗin "Babu hutu gabaki ɗaya Yaaya, ko baccin kirki banayi ni na kosa ma na fara
zuwa jami'a, sai naga dama zan shiga lecture babu mai cemin don me." Murmushi sukai
daga Abba har Junaid.
Kai Junaid ya shiga kaɗa mata yana faɗin “Waya faɗa maki karatun jami'a yana da
sauqi?" Assha dikko tayi Rolling eyes ɗinta tana faɗin "Ba dai ina ganin yadda
Amaah keyi ba har 10 take kawai tana baccinta haka da dare sai takai 1 tana kallo,
kai bawa wa ya baka ƙwarin gwiwar duka yin waɗannan abubuwan Yaya Junaid?" ta faɗa
tana wani kwantar da kai, murmushi kurum Junaid yayi gamida jan dogon hancinta,
sallama tayiwa yayan nata shida Abba, ta koma ɗaki dan shirin zuwa school.
Wuraren ƙarfe goma ta soma buɗe idanunta da hasken rana ya gama haske fuskarta,
wata irin miqa ta saki tana lalubar inda zataji Junaid, sai dai wayam taji wurin da
yake, idanu ta buɗe sannan ta miƙe zaune tana riqe kanta, a daren jiya ba ƙaramin
wahala tasha hannun Junaid dikko ba duk Jarabarta da kaunarta da son sexxx idan
tana gado ɗaya da Junaid dikko raina kanta takeyi har mamaki take ta yadda bata iya
ɗauke buqatarsa duka, kalamansa ne suka fara dawowa cikin kunnuwanta "Kina son mu
zama abu ɗaya Khairiyya amman bakya iya ɗauke bukatata? Banga amfanin wannan mugun
kishin naki ba ki barni na nemi wasu matan wanda zan biyasu su sauƙe min da duk
wata bukata dake manne a marata."
A halayyarta tana mugun kishin Junaid dikko, wanda shi baya so "Kishinka ba ƙaramin
abu bane da zan iya ragesa lokaci ɗaya, nayi maka uzuri amman muddin ina garin
Katsina baka isa ka raɓi wata maccen ba, duk ranar kuwa da naga macce ajikinka
wallahi tallahi sai na kasheta!" Tana tuno wasu kalamai da ta taɓa faɗa masa a wani
dare suna tare sai taji yana ƙiranta da sunan wata yarinya, ranar yaga tashin
hankali da masifar Khairiyya, fuskarta ta shafa da hannayenta, hango farar takarda
tai akan bedside na drawer hakan yasa ta ɗan matsa gafda wajen, hannu ta saka ta
ɗauka tana warwarewa a hankali.
"Kin buɗe baki kina bacci, munyi sammako da Abba zuwa Abuja idan mun sauƙa zan ƙira
take ur time." Wani murmushi take saukewa a hankali,
nan ta ɗau ki wayarta tana duba sakunan dake shigowa cikin harda alert ɗin Junaid
da yayi mata na kuɗi, kai tsaye toilet ta wuce ta sakarwa kanta shower, daman
sallah ba damunta yayi ba sai ma idan tana tare da Junaid ɗin ne take ƙoƙarin yi
kasancewar Junaid yana da ibada sosai musamman a ɓangaren sallah zata iya bada
shaidarsa ta wannan ɓangaren dan salloli biyar basa wucesa.
Sun isa Abuja sai kusan ƙarfe goma na dare ya samu ƙiran Khairiyya dan bai samu
kansa ba sai bayan sallar magrib kuma suna tareda Abba har lokaci yanayin muryasa
da Khairiyyah taji ne yasa ta tabbatar akwai gajiya a jikinsa dan itama bayan ta
shirya aranar ta bar Katsina, a kasale tace “Mine ka gaji sosai ga muryarka nan
yana shaking.” Ta faɗa masa cikin sanyin murya, babu abunda yake buqata irin wannan
lokacin yaji macce ajikinsa, jira kawai yake ya samu Abba yai barci ya fita shima
dan Abuja ba bakon wurinsa bane so yake ya fita ko zuwa asuba ne sai ya dawo.
“Khairiyya bacci nakeji na gaji." Ya faɗa mata cike da gajiya a muryarsa.
“Hope a gida zaka kwana ba'a hotel ba?" Tayi masa tambayar tanajin wani kishi na
sake danne mata zuciya “Ina gida tare da Abba.” Yana jin yadda take sauƙe ajiyar
zuciya “Toh na tayaka hira mana har ka samu barci?” Ta faɗa da kalar muryar da take
yi masa magana na jan hankali “Na baka labari?”
“Khairi please!”
“Mine nasan macce kakeso yanzu, karka fara duka awanmu nawa da rabuwa ko ka manta
kwana kayi aikana? Wai meyasa baka gajiya ne? Sai da na faɗa maka idan bazaka iyaba
zan biyoka."
“Khairi kiyi shiru dan Allah kaina ya fara ciwo.”
“Owk sai da safe." Ta faɗa tana katse ƙiran ba tare da ta jira me zaice ba,
kwanciya yayi akan bed yana rufe duka jikinsa da duvet kamar ma zazzaɓi ne yakeson
rufesa dan wani irin sanyi yakeji tun daga cikin tafin ƙafarsa har tsakiyyar kansa.
Ƙarfe biyu na dare sai juyi yake a kan bed ɗinsa, yana jin yadda jikinsa ya ɗau ki
wani kalar dumi ga mararsa da yaji tayi masa wani mugun nauyi, kamar wanda ya sha
wani abu, a hankali ya sauko daga kan bed ɗin, dakyar ya saka casual slippers a
kafansa hannunsa na dafe da wandonsa ya nufi kofa, kai tsaye kitchen ya nufa ya
fara duba cikin fridge yana addu'ar samun lemun tsami, dakyar ya samu kwara biyu
anan cikin kitchen ɗin ya haɗa coffee tare da jefa lemun aciki parlour ya dawo ya
xauna, kusan minti goma sa'annan ya kafa kai ya wani runtse ido sai da yaji babu
komai cikin cup ɗin saannan ya sauƙe, wata irin zufa ya shiga haɗawa lokaci ɗaya,
anan kan doguwar sofa da yake zaune cikin parlor ya kwanta tare da jingina bayansa
yana sauke wani numfashi, duka daren baccin wahala yayi sai dai still bai makara
sallar asuba, ƙiran sallar farko ya buɗe idanunsa, tare sukaje massalaci da Abba,
sannan tare suka dawo Abba.
Suna tafe Abba yana faɗin ya kwanta ya huta zuwa 10 zasu fita, shima zai ƙara
kwanciya dan wani irin ciwon ɓarin kai kansa keyi "Ko sai kaga likita ne Abba?"
Abba ya girgiza kai yana faɗin “ No! Nasan bacci ne idan na tashi zai wartsake
kafin nan kayi mana order na break fast." Nan ya ɗagawa Abba kai alamar bin
umurninsa sai da yabi bayan Abba har ɗakin barcinsa ya tabbatar da ya koma barci
sannan ya fito ya nufi nasa ɗakin, wani wankan ya sakeyi ya saka kananun kaya
ajikinsa ya ɗau ki car key, agoggo ya kalla yaga kusan ƙarfe bakwai nan ya fice
daga gidan.
Kwance take tana juyi a gado a katafaren hotel ɗin da ya kama musu, wayar Junaid
dikko dake gefen pillow ta ce fara ringing ɗaukar wayar tayi tana duba sunan,
Khairi taga an saka ɗan taɓe baki tayi ta ɗaga wayar tana faɗin "Sorry mai wayar
baya kusa ya shiga wanka." A wani irin fusace Khairiyya ke faɗin "Ke wacece kuma me
kike da wayarsa da safen nan?" Khairiyya ta faɗa sounding very harsh a muryarta,
har zata buɗe baki tayi magana taji qarar buɗe kofa, alamar ya fito daga wanka.
Junaid sanye yake da ƙaramin towel a waist ɗinsa sai ƙaramin dake bisa kansa yana
goge gashin kansa dashi, da mamaki yake bin wayarsa da ke hannunta da kallo a wani
irin fusace ya ƙaraso ya fisge wayar still Khairiyya na kan layi.
Wani mugun kallo ya watsa mata kafin ya fice daga ɗakin zuwa parlor.
"Khairiyya!" Ya faɗa can qasa maqoshi "Wacece wannan? Me take da wayarka?" Sau nawa
zan riqa ansa maki wannan tambayar tunda kin san wacece ni bai zama dole kullum sai
kin tambaye ni ba."
"Meyasa kakeyin haka Junaid?" Yana iya kirga sau nawa Khairiyya ta ƙira sunansa
cikin rayuwarsu " Bana son rigima zuwa anjima zamuyi magana." Tun kafin ya katse
wayar ta katse wayar.
A fusace ya koma ɗakin ya kalleta da masifa cikin idonsa yake faɗin "Meyasa zaki
taɓa min waya?"
Ta haɗe rai tana faɗin "Ƙira fa tayi na ɗaga da niyar na faɗa mata baka kusa,
shine zata riqa faɗamin bakaken maganganu, idan matar ka ce meyasa ta kasa riqeqa
kake bin wasu matan?"
Yarinyar tana gama faɗa a fusace ta shige toilet, da wani irin kallo ya bita a
gurguje ya shirya ya aje mata kuɗaɗenta akan bed ko sallama bai tsaya yi mata ba ya
fice daga room ɗin.
Eatery ɗin dake cikin hotel ɗin ya tsiya yayi masu oder breakfast shida Abba, koda
ya ƙarasa gidan kusan goma saura, addua kurum yake aransa Allah yasa Abba ba ya
parlour har ya shiga cikin parlourn baiji motsin Abba ba, kan dinning ya qarasa ya
aje ledojin da ya taho masu dasu sannan jiki a sanyaye ya nufi ɗakin barcinsa,
kayan jikinsa ya canja ya shirya kansa cikin bakaken Japanese suit, gefen bed ya
zauna yana ƙoƙarin kiran Mamma a waya line busy yaji ana nuna masa miqewa yayi
tsaye gamida ficewa a ɗakin.


BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764

Katin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730

#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#Junaid Dikko


VIP 1K
NORMAL GROUP 500
[9/20, 8:06 AM] Asmy B Aliyu: BOYAYYAR ALAƘA
(Secret Relationship)

FREE FAGE.


Asmy b Aliyu


8.

Yana tsaye a ƙofar ɗakin sai da ya fara yin knocking jin shiru yasa ya kama handle
ɗin ƙofar sannan ya tura hango Abba yayi tsaye jikin window da farar jallabiyya
ajikinsa yana kare da waya a kunnensa. Jin qarar buɗe ƙofa ne yasa Abba ya ɗan
waigo, zama Junaid yayi a cikin sofa ɗin ɗakin yana jiran Abba ya gama wayar da
yake. Abba ne ya qaraso gabansa yana miqa masa wayar hannunsa, hannu Junaid yasa ya
karɓi wayar tare da karata kunnensa, jin muryar Mamma ne yasa ya gaisheta da
respect ta amsa tana tamabayarsa ya yake "Mamma naji muryarki wani iri kamar kina
mura."
“Murane tun tsakar dare na fara amma zan shiga clinic yanzu shiyasa ban sha magani
ba."
“Mamma baki da lafiya ki kwanta ki huta mana? Doctor Hakeem yana gari nasan zai
kula da komai."
Junaid ya kalli Abba yana wani dakune fuska yana miqa masa wayar yake faɗin “Ka
faɗa mata tasha magani mura take Abba." Ya ƙarasa maganar yana miqawa Abba wayar ya
ciro tasa wayar dan kiran Abdul-hakeem din, kusan Abdul-hakeem ya zama kamar ɗan
uwa a wajensa, duk da abokinsane tare sukayi karatu a Oxford University dake
England wanda scholarship ya samu qarqashin PTDF da wannan ne har ya taka matsayin
da yake a yanzu. Kasancewar Abdul-hakeem ɗin ya fito ne daga gidan tallakawa,
hakan ne yasa Junaid dikko yake kaunar Abdul-hakeem ɗin ganin karatunshi ne a
gabanshi duk da Hakeem ɗin shima ba wai saboda dukiyar Junaid ɗin suke tare ba,
kawai dai sunyi karatu waje ɗaya ne haka idan yaga Junaid ɗin yayi ba daidai ba
yana basa shawara.
Yanzu ma saboda Junaid ɗin ne yake aiki da (dikko special hospital) Yai ta ƙiran
wayar Hakeem ɗin a kashe yasha mamaki sabida Abdul-hakeem ɗin baya kashe waya dole
ya hakura.
Da suka fito falo suna breakfast yana yiwa Abba bayani idan suka koma garin Katsina
zai haɗa meeting da duk wanda ke karkashin(Dikko hotels) kuɗi sama da miliyan biyar
sun fita, wanda ba'a san ta hanyar da suka fita ba Abba ya bashi dama akan yai
binciken, shi Junaid dikko yafi zargin Manager ɗin wurin ne wanda ya kasance
abokine ga Ali dikko koma dai menene sai ya gano ta inda kuɗin nan suka fita.
A hankali ta turo kofar dakin Mum, lokacin tana tsaye gaban closet ɗinta tana
shirya kayan gugar da aka shigo mata dasu da safen nan ta juyo tana kallon Amaah
dikko wacce tayiwa kanta masauki gefen bed ɗin ɗakin Mum dai kallonta kawai take
tana kallan Mum ɗin tace “Mum zan shiga school.” Baki buɗe Mum ɗin ke kallonta "Dan
zaki shiga skull sai akace ki saka hijab dama da hijab kika saba zuwa makaranta?"
“To ya zanyi? Mum kin manta yadda yaya Junaid yace idan na kara karya ɗaya daga
cikin rules ɗin da ya kafamin cireni a makarantama za'ayi? Kuma Abba ya yadda kina
gani agabansa amma baice komai ba?”
“Ke kuma dan kina shasha sai kibi yadda yakeso shi gasa ubanki kou?” Mum ta faɗa a
fusace tamkar zata kaiwa Amaah ɗin mari "Kin san yadda nakeson karatuna Mum Right?
Ni bana son wani abu ya taɓa min karatuna idan na shiga school zan riqa saka
mayafi, ga shinanan ma a bag ɗina." Ta faɗa tana xuge zip ɗin jakar tana nunawa Mum
ɗin ɗan qaramin mayafin da ta ɗauko mai shige da kalar kayan jikinta, dan takaici
sai Mum ɗin tayi shiru bata qara magana ba ta cigaba da gyaran kayanta "Please
mum." Amaah ta faɗa da wani yanayi a muryarta “Ki ɗauki car key ga shinan akan
mirror dressing."
“Drivern Yah Junaid yana waje yana jirana." Wani irin kallo Mum ɗin ke bin Amaah
dashi yadda taga yar ta ta canza lokaci ɗaya duka saboda dokokin Junaid dikko na
banza"Mum sai na dawo.” Da haka Amaah ta nufi ƙofa ta fice daga room ɗin bata jira
mai Mum ɗin zata sake faɗa ba ta fito suka wuce school.
Suna zaune da Rufy kusan qarfe biyu na rana, Rufy na kallonta tana faɗin “Ya zakiyi
da zuwa birthday ɗin Fu'ad dan naga wannan yayan naki zafin kansa yayi yawa."
Tamkar Amaah zatayi kuka take kallan Rufy tace "Ban san yadda zanyi ba Rufy ke kin
san qarfe shidda na yammah kawai muke a waje, a duk inda muke ka'idar gidanmu ne
haka, ina ga kawai zan fadawa Fu'ad ya hakura bazan samu zuwa ba dan da gaske bazan
iya haɗa karatuna da kowa ba Rufy, ina kaunar karatuna bazan so wani abu ya taɓamin
karatuna ba, dan daga ranar da Junaid dikko yasan muna dating da Fu'ad nasan tawa
ta qare."
"Kina nufin ba zaki je ba kenan? Amman kin san Fu'ad bazaiji dadi ba kou?" Rufy ta
qarasa maganar da rashin jin daɗi a muryarta "Kawai ki faɗawa Mum nasan bazata
hanaki ba, nasan birthday party ɗin nan iyakarsa an dade idan an kai 10, dan Allah
be a gud girl Amaah."
Itadai Amaah jin Rufy kawai take dan bata gamsu ba, ganin wayarta ta soma ringing
ne yasa ta fiddota cikin bag ɗinta sunan Fu'ad ke yawo a jikin screen ɗin wayar,
ɗauka tayi ya faɗa mata gashi ya shigo cikin school yana mota yana jiranta, ita
kuma ta faɗa masa tana zuwa "Karkije ki fusata sa kin san bayada hankali ko kaɗan
Amaah" Rufy tai maganar tana kallanta, ita kanta a tsorace take da Fu'ad ɗin duk da
tana yiwa Fu'ad ɗin soyayyar da bata san lokacin da ta fara ba, sai dai wani irin
mugun tsoronsa da takeji, sanadinsa ko mazan ajinsu bata kulawa saboda mugun kishin
Fu'ad idan kuma wani ya kulata a cikin school ɗin ko yayi mata magana a ranar
tashin hankali za'ayi acikin makarantar, ko maza yaga suna kulata a social media
suna liking ɗin posting ɗinta anan zai riƙa mata bala'i ya ɗora laifin akanta yace
ita take kulasu.
Tun da ta fito daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login