Showing 15001 words to 15526 words out of 15526 words

Chapter 6 - BOYAYYAR ALAƘA 1 by ASMY B ALIYU

26 May 2026

9

nufi hanyar stairs, sai da ya bacewa
ganinta sannan ta zube a ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlorn tana sauke
numfashin da take riqe dashi, banda faduwa babu abunda gabanta keyi, ta fito da
wayarta dake cikin hangbag ɗinta taga har lokacin sallar magrib ya gabato. Sai
kusan 7 har da minti goma Fu'ad ɗin ya fito cikin wandon troser da kuma farar shirt
da ta kama jikinsa sosai da sarqa a wuyansa irin wanda ƴaƴan manyya ke sakawa, sai
zuba kamshi yakeyi. Har ya qaraso cikin parlorn bata kallesa ba tsayawa yayi
agabanta yana qare mata kallo. "Ke bazaki shirya ba?" Ta dago kanta ta zuba masa
idonta ta girgiza kai tana faɗin. "A shirye nake Fu'ad dare yanayi mu tafi." Ta
miqe tsaye ta miqa masa bag ɗin hannunta tana faɗin. "Ga gifts ɗinka." Ita da bag
ɗin da hannunta ya haɗa ya rike kafin ya jawota cikin jikinsa duka yana sauke mata
numfashi a cikin wuyan ta, duk yadda taso ta kwaci kanta kasawa tayi dan riqon da
yayi mata bana wasa bane. karo na farko da wani ya riqeta kamar haka a jikinsa,
banda kadawa babu abunda jikinta keyi, tana jin yadda ya riqe kugunta sosai. "Kin
san ina sonki ko?" Ya faɗa da wata irin murya da Amaah ta kasa fassarawa. Ta ɗago
tana kallon cikin idanunsa da suka kankance lokaci ɗaya suka canja kala da yanayin
su ke baiwa Amaah Dikko tsoro. "Mu tafi Fu'ad." Ta sake faɗa cikin rawar murya.
yatsansa ya saka yana zagaye bakinta dashi sai kuma ya saketa a hankali yana ɗan
jada baya da murmushi akan fuskarsa yake faɗin. "Am so sorry kin san idan ina
gabanki kasa controlling ɗin kaina nake yi, muje." Ya faɗa yana barin bag ɗin da ta
bashi a kan kujera yace idan ya dawo zai duba. Sai da suka bar cikin gidansu Fu'ad
ta samu ƴar natsuwa. (Katsina Trousit Lodge) Har ya gama parking motarsa acikin
parking lot Amaah bata motsa daga inda take ba, haɗe jikinta tayi wuri ɗaya tana
jin sanyi na shiga jikinta a hankali haka tana jin wani yanayi mai alamar zazzaɓi
yana san sauka ajikinta. Da ido Fu'ad yake kallonta. "Are you ok?" Ya faɗa yana
zuba mata idanunsa, ta kallesa tana ɗaga kanta take faɗin. "Awa ɗaya kawai Fu'ad,
da kayi cutting cake zan tafi." Ta faɗa murya can ƙasa. Fu'ad ya wani yamutse fuska
yana faɗin. "Kice min wasa kike min? duk tarin laifin da kikayi min na hadiye abuna
banyi magana ba karki ɓata min rai." Kallonsa take alamar tana son taji laifin da
tayi ya wani furzar da iska a bakinsa yana faɗin. "Kalli shigar da kika shigo wajen
nan dashi, Abaya ce fa ajikin ki Amaah sai kace ba girl friend ɗina ba? any way
tunda kin zo banda matsala da wannan." Ya faɗa yana balle marfin motar ya fito.
Zagayowa yayi ya buɗe mata murfin motar banda faɗuwa babu abunda gabanta keyi karo
na farko da ƙafarta ta tako cikin hotel da sunan zuwa birthday ɗin saurayi. Kai
tsaye hannunta Fu'ad ya riqa ɗayan hannunsa kare da waya, entrance ɗin shiga hotel
ɗin suka dosa......


*_Anan na kawo karshen free pgs mai son cigaban littafin ya nemini da wannan
lambar_* 08086207764


BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764

Katin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730



#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#fu'ad
#Amaah Dikko

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login