Showing 9001 words to 12000 words out of 97469 words

Chapter 4 - RAINON SOJA BOOK 1 COMPLETE BOOK MAMAN TEDDY.pdf

23 Nov 2025

1109

da wasanni suke
yi mata suna kiran sunan ta “Ma'eesha , Areef na wasa da hannayen ta , don kuka ne basa so
tayi . Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke. Da hannun sa ɗaya
ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon
ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu
Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana
kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin
morning exercise sannan sai nayi mata wanka.................!




*Wani aiki sai soja�Rainon soja zamu sha kallo to masu karatu kar ku manta littafin
rainon soja na kudi ne masu ɓukatar fara payment ga yanda tsarin yake. Regular group ₦500

vip group ₦1000 special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar
biya ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ta wannan number 09061466409
yan Niger zaku turo da katin Airtel na 500f ...kar ku manta wurin yi mun sharing zuwa ga
masoya baki daya️.* [1/13, 7:32 AM] +234 704 512 5150: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*




Free page 5



________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Gidan zaurawa
Taɓarah
________________________
"Da sauran su a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na
musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha dukasoja da raino ai abun ba'a
magana labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da
rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon️dadi tun a
yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu

buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka
biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private .
Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group
₦500 Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu
transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f free page ya fara nisa a
page 10 Free zai ƙare maza ku hanzarta wurin biyan naki ana ta paymentNi kuma ina ta
adding to kar a barki a baya, ko kiyi tunanin samun na bulus mutane na yan amana
ne..........!


•••••

Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke. Da hannun sa ɗaya ya
ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon
ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu
Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana
kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin
morning exercise sannan sai nayi mata wanka na bata break ɗin ta kamin mu wuce class .

Humm to yanzu a ina ne zamu bar Ma'eesha kasan ba zai yiwu mu bar ta anan ita kaɗai ba ,
sannan kuma ba zai yiwu mu tafi da ita class ba. Areef ya katse Aliyu Haidar da a wannan
lokacin yana cigaba da tambula Ma'eesha yanda yake mata kaman ɗan namiji....Itako gani take
wasa yake mata dariyar ta take yi abun ta . Ƙwantar da ita yayi bisa gadon nasa yana kama
hannayen ta biyu tare da ɗagota sama yana maida ta kusan mintuna biyar yana mata wannan
salon motsa jinin nasa , yayin da bai Bama Areef amsar tambayar sa ba. Jin shirun nasa na
wasu mintoci babu amsa yasa Areef juyawa yana nufar Toilet shima don ya fito ya kimtsa
sannan sai su cigaba da maganan.

A haka nan dukan su suka shirya cikin shigar su ta uniform ɗin sojoji duka layi ɗaya suke wato
Sojojin Airforce ne. Wannan yasa komai nasu tare suke yi .

Miƙewa Aliyu yayi yana sauke Gwauron numfashi kana ya kalli Ma'eesha da take bin sa da kallo
War War War ta yara . Ina zuwa ma'eesha. Ya furta yana nufar inda yake jin maganan masu
kawo masu breakfast.

“uhm common baby ”. Ya furta a lokacin da yake dawowa hannun sa ɗauke da basket dake
shake da kayan karin kumallon su . Maganan yayi yana sakin mawa ma'eesha murmushi
wanda nan take naga yarinyar ta juya da sauri tana miƙewa tare da rarrafowa zuwa inda yake.
Tea ya fara haɗa mata tasha sosai, kana ya fara kokarin bata shinkafan da mai ne ta ture kan ta
don bata buƙata . Murmushi yayi yana cewa “ Ok bari Nima nayi break fast sai mu wuce aji tare

�” . Humm da rabon yau ma ya ƙara amsar wani horon Allah dai ya kiyaye Ali” .

Yana tsaka da fara break fast din ne dukan su sauran abokanan nasa suka iso don sun
kammala shirin su suma , zama suka yi suna fara nasu , wanda kamin su gama ne suka ga
Aliyu ya miƙe yana kai hannun sa zuwa inda Ma'eesha take , ɗaukar ta yayi yana nufar Toilet da
ita . Da ido Areef ya bishi , yayin da Ibrahim yace “ Aliyu fa ba zai iya yi mata wanka ba , Mene
ya iya , nifa mamaki ma nake yi yanda yarinyar har take dariya da nuna so idan ta gannshi , bai
iya komai ba Wallahi , Don Allah ku dakatar dashi Bara na kira Joy tayi mata Wankan just give
me 1 minute I'll be back ”. Yana Ida maganan yana miƙewa cikin sauri tare da nufar ɗakin da su
joy suke. Suma tare suke duka a wannan shekarar suka fara karatun duka .

Miƙewa Areef yayi yana biyo bayan Aliyu tare da shiga Toilet ɗin , kallon kallo suke yi don zaune
ya tadda Aliyu ya tasa Ma'eesha yana kallo ya rasa ta ina zai fara wanke ta . Wani dariya ne ya
taho ma Areef amma sanin halin Fushin Ali da jarabar sa yasa shi danne ta don dole . Aboki ka
dakata yanzu joy zata taho sai tayi mata wankan . Areef ya furta yana ƙariƙawa zuwa ga Aliyu.
Kallon sa Aliyu yayi kana juya yana kallon Ma'eesha, ba tare da ya kalli Areef ba idanun sa na
kan ma'eesha yace “ Ai matsalar baka gani ba , bafa baf ɗin wanka duba ka ga , to a ƙasa ne
za'a yi mata wankan? .

Eh mana yo shi yasa Nace ka kawota mu kai ma mummyna nasan zata kula da ita sosai.

Please stop saying that..”! Ni zan iya kulawa da Ma'eesha tun da mami ta wulaƙantani akan ta ,
dole da kaina zan raine ta kuma zata girma cikin kulawa ba zata mutu ba . Cikin sauri Areeef ya
ware idanun sa a zuciyar sa yana cewa “ Ai ko indai kai ne zaka raini ma'eesha har girma to ko
bata mutu ba ,zata ɗanɗana azaba . Ni kaina azabtar dani kake yi bare kuma ita dakake iƙirarin
zaka raine ta ka bata tarbiyya . Sorry for you ma'eesha ”. Yana tsaka da wannan tunanin ne
Ibrahim da joy suka shigo Toilet ɗin . Wata irin gabjejiya ce a tsaye take kaman namiji, Ya ne
mutumin ? How are you?. Tayi maganan tana kai hannun ta tare da kama hannun Aliyu wanda
yayi kinini da rai . Ali ya kake ?”. Ta kuma tambayar sa a karo na biyu wanda a daƙile yace “
Lafiya” . Wannan ce yarinyar ? Wow cutie . Kyaƙyƙyawa ta furta tana kai hannun ta tare da
amsan ma'eesha. Wasa ta fara yi mata tana cire yagalgwalin rigar jikin ta irin ƴan gobe sunan
nan , da gani kasan yarinyar ta taso ne in a poor condition sai dai duk da haka kyawunta bai
ɓoyu ba don tun a yanzu kyaunta mai fuzgar hankali ne ƙwarai . Sauke ta tayi ƙasa tana fara
takawa da ƙafafun ta kana Joy ta sauke heater tana sirka ruwan. Skirt ɗin jikin Ma'eesha ta
sauke , yayin da su Aliyu suka ja daga baya suna jiran ta kammala ko nace yana jiran ta
kammala ya saɓa kayan sa .

Muryar Joy yaji tana dariya tare da cewa “ Oh my God, this girl she's beautiful...Areef kaga
yarinya tun tana ƙara da shape da hips ? Jikin ta luwai........Keeeeee.....!!! “muryar Aliyu ya
katse ta cikin doka mata Wani irin tsawa mai kama da saukar Aradu sai da joy ta firgita , ba ita
kaɗai ba ma Har ta ma'eesha kuka ta saka cike da tsoro tana ƙanƙane hannun joy.
“Dama ku Arna babu wanda ya kai ku Iskanci, to amma ke naki iskancin yafi na kowa , yar iskar

banza ...wasu irin ashar yake Aunata mata tamkar wanda yayi zaman tasha, yanayin sa kaman
wanda zai buge ta , don jikin sa har tsuma yake yi . Shi kan shi bai san mene ya hasala shi bisa
kalaman nata ba . Fice mun daga nan kar ki sake dawowa.

Kuma malamai duka ku fita Nine zan rinƙa mata wankan ta da koman ta bana buƙatar taimakon
kowa , tun da abun ya koma harijanci . Gimtse Dariya su Ibrahim suka yi don yanda joy
take kyarma daga taimako sai ta baka dariya . Da sauri ta fice bata ce dashi komai ba . Haka
suma suka fita ,suna barin sa daga shi sai Ma'eesha.
Hannun sa yakai yana ɗago Ma'eesha tare da fara cire ƙaramin Pant ɗin jikin ta. A kan ƙafafun
sa ya zaunar da ita yana fara Wanke mata jikin ta don yanda ake ma yara wanka bai fa sani ba .
Sai da aka gama wanke jikin ne ya fara zuba mata ruwan ɗumin yana mata Wasa da ruwan
tana dariya, a haka ruwan da ya ƙarar mata a jiki yafi ƙarfin bokiti babba uku , yanda take
dariyar shi yake sanyaya zuciyar sa .

Kallon Areef Ibrahim yayi kana yace " saura mintuna biyar fa mu makara ”. Shiru Areef yayi
kana Adam yace “ Leka kace masa yayi sauri ”. A'a kai dai kaje . Hahahahaha....suka fashe ma
Areef da dariya . Ibrahim ne yace “ Wai tsoron Ali kake yi ne ?”. A'a bana ce ba ,amma kai zaka
iya zuwa ”. Ok ya furta yana kama hanya tare da kutsa kan sa cikin Toilet ɗin . Wasa yaga yana
yi mata da ruwan suna dariya , Dariyar da bai taɓa ganin Aliyu yana yin irin shi ba . Shi da ko
murmushi ne sai yaso yake yi. Amma yau dariya har da kyakyatawa da ƙaramar yarinya . Aliyu
saura mintuna biyar mu makara ”....Wani ɗauke wutaaa Aliyu yayi cikin fushi da ɗan ɗaga
murya ya furta “ Dole sai dani zaku tafi , zaku iya tafiyar ku abin ku ”. Jin haka yasa Ibrahim
juyawa har yakai ƙofa Yaji Muryar Ali ya katse shi da cewa “ Daga yau kar wanda ya sake shigo
mun Toilet indai ina tare da Ma'eesha . Saurin kallon sa Ibrahim yayi kamin yayi magana
Nan Take Haidar yace “ Yessss haka nace kar wanda ya sake shigowa ko baku ga mace Bace
ita , Idan ina mata Wanka kar wanda ya ƙara shigomun ka faɗa masu ”. Sakin baki Ibrahim yayi
yana ficewa daga Toilet ɗin tare da isa inda Su Areef suke yana mai labarta masu yanda suka yi
da Ali yanzu a Toilet .


Wani irin dariya Areef keyi har da buga ƙafa kana Adam yace “ Ok to shi ba namiji bane kenan,
me zamu kalla a wannan jaririyar yarinyar? Kai nifa Ban gane ba ne ma . Ya furta yana kama
ƙwiɓin sa . Fashewa da Dariya Ibrahim yayi kana yace “ Kasan halin Aliyu fitina ce kawai irin
nashi yake neman kan wa zai sauke ,kaga kuwa ba Dani ba , Ni nayi na class kuma zaku tsaya
ne ko na tafi Ni kaɗai .

A'a mu jira shi ya fito sai mu tafi duka.

Adam ne ya kalli Areef kana yace “ Ok tom mu jira shi kaga ikon Allah yana fitowa zaice mu fita
daga waje ya shirya Ma'eesha kar a ga mata jiki . Yarinya kaman kazar turawa wata can
ƙasa da ita gata fa gijib. Dariya suka saka baki ɗaya cikin sauri suna ficewa tare da nufar inda
ajijiwan karatun su yake.

Shi kuwa Aliyu koda ya fito yaga babu su bai damu ba ,don dama ya kuɗurta a ransa indai ya
fito ya gansu sai yasa sun fita sannan zai shirya ma'eesha su tafi aji tare ....jama'a kuji mun
Bala'i, ta ina zai yi karatu da yarinya abun da ba'a taɓa yi ba kenan.

Kallon ta yayi yana tunanin to wani kaya ma zai sanya mata ? Palmers oil ya shafa mata yana
ɗaukar kayan da ya cire mata yana mai da mata . Idan kina buƙatar wani Abu Kice Uncle Zan
sha ruwa ? Ko zanci abinci idan fitsari zakiyi sai ki mun magana kinji Ma'eesha? Yayi Maganan
yana kallon ta , da itama take bin sa da kallo ganin babu alamun ta gane Hausan nasa ne yasa
shi cewa “ Bata ma fahimta ba ,muje ”...ya furta yana kai hannun sa tare da goya ta a bayan sa
, hannun sa ɗaya yana ɗaukar jakar bayan sa .

**
Shigar sa ajin yasa duka kowa kallon sa tare da bin bayan sa da kallo ganin kyaƙyƙyawar
yarinya tayi lamo kan ta ko hula babu , gashi a warware yanayin tsayin gashin ta da cikar shi
kaman yarinyar larabawa yafi komai tafiyar da hankalin su gare ta. Hango Su Ibrahim yayi da
Areef Adam a can sama Captain Isma'il yana basu horo , wani kallo Ali yayi masu yana kauda
kan sa a Zuciyar sa yana cewa “ Taɓ ashe duk ma saurin da suke yi sun makara ,aikin banza
kenan”. Nufar mazaunin sa yayi yana aje Ma'eesha kana ya dawo gaban inda Captain Isma'il
yake yana ƙamewa tare da cewa “Morning sir” .

Ya akayi ka zo a makare? Me yasa baka kai yarinyar section ɗin su ba ? . Captain yayi
maganan yana kallon Aliyu don a tunanin sa Ma'eesha makarantar yara na cikin NDA ɗin take
yi. Magana ce ta fara tashi ƙasa² . Ai ƙanwar Aliyu ce . Joy ne tace “ Eh nima naga suna kama
sosai ”. Ɗauke ta ka kaita idan ka dawo kayi joining ɗin abokan naka . Captain Isma'il yayi
Maganan tare da kallon ɓangaren da su Areef suke .

Ok sir . Aliyu ya furta yana isa inda Ma'eesha take , taho ma'eesha ”. Hannun sa yakai yana
ɗaukar ta tare da ficewa da ga class ɗin.

“Khaleel dake can nesa mamaki yake yi a ina Aliyu ya samu yarinya? Gaba ɗaya kan sa ya
kulle , Ya rasa wane zai tambaya ,gashi abokanan sa sai tambayar sa suke yi wai dama bayan
Jidderh suna ƙanwa ce? . Shi dai ya kasa basu amsa , zuciyar sa fal tsoro halin Aliyu na
damunsa. A jikin sa yake jin da wani Abu dai gami da yarinyar haka kurum Aliyu ba zai goyo
yarinya ya taho da ita ba . Shi da ko magana bayayi bare wai ya tsaya bata lokacin sa akan
yara .

Bayan Fitan Aliyu kai tsaye section ɗin yara ya nufa da ma'eesha , ba tare da jin tsoro ko abun
da zai kai yakawo ba ya kutsa kan sa zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login