Showing 1 words to 3000 words out of 97469 words
Chapter 1 - RAINON SOJA BOOK 1 COMPLETE BOOK MAMAN TEDDY.pdf
*️RAINON SOJA...!️*
*#Through the gate of love a Valiant, fearless heroical and Sympathetic Story.*
Free Page 1
*Labari da Rubutawa daga:©Ayshatou Maman-teddy*
*December 02-12-2023 .....7:30am*
#Rainon soja#whispering of love#Book 1#chapter 1#hand salute #travelling .
Wata moto ce ke guda a tsakiyar ƙwalta inda babu gida gaba babu baya sai Falfalan dajin
ALLAH.
Mota ce irin ta haya wanda yake dauke da mutane sun kai Goma zuwa goma sha biyu , kallo
ɗaya zaka yi masu ka fahimci matafiya ne wanda suka fito daga cikin garin Zaria zasu iso Garin
Abuja . Kowa hankalin sa yana akan hanya banda Mace Ɗaya wacce tun da suka shigo moton
idanun ta ke tsiyayar da Ƙwallah, daga saman jikin ta kuma yarinya ce Wacce a shekaru ba
zata Haura Ɗaya ba zuwa ɗaya da Rabi a Duniya . Tausayin yarinyar nata take jin yana ratsa ta
haka zuciyar ta na kuka mata . Juyawa tayi tana kallon mai gidan nata wanda shima jimami ne
da kuma tsoro fal a zuciyar sa. Hajara kina ganin idan muka je Muka koma a halin yanzu Ƴan
uwan ki zasu amshe mu? Zasu amince da Auren namu a yanzu kuwa? Hajara ko zamu koma
ne.....Ɗaga masa hannu tayi tana saurin riƙo hannun shi kamin cike da Raunanniyar murya ta
fara cewa " A'a Salihu " kar ka ƙara furta hakan , yanda muka ƙudurci kawo Zahra dangina Don
taga iyayen ta da kakanni a yau babu abun da zai fasu daga yin hakan sai kuma idan ƙaddara
ta Gifta .
Ka janye Tsoro ka manta da komai nasan su ma a yanzu sun manta kuma kowa zai yafe mun
inshallah. Fatan mu a yanzu shine Allah yasa mu sauka lafiya .
"Hummm" .
Sauke Ajiyar zuciya Salihu yayi kana yakai hannun shi yana ɗaukar ƙaramar yarinyar tasu yana
daura ta bisa jikin sa . Ƙurrrr yayi mata da ido kamin yace " Wai Haihuwar ki ce aka ce mun ba
alheri a rayuwa ta Zahra , Ni nasan Allah shine mai yin komai shine wanda yasan ƙaddara ba
ɗan Adam ba. Ko ina raye ko ina a mace ina rokon ALLAH ya kare mun ke da kariyar sa. Shiru
Hajara tayi tana kallon uba da ƴar wanda yake ji tamkar ya haɗa ta da jikin sa ya zamana babu
wani abun cutarwar da zai iso gareta . Murmushi take bin su dashi kamin ta juya tana kallon
dajikan da suke wucewa.
Kaman wanda aka ɗaga moton suka ji tayi sama tayar gaban ta yana fita fittttttt ji kake kwaltan
da tayar suna fidda wani irin ƙugi ƙuuuuuuiiiiiiii nan take moton ta ɗaga tare da kifowa kif kaman
wanda aka dirkake su . A dai dai kuma wannan sa'ilin da babu gida gaba babu gida baya ,sai
falfalan dajin ALLAH . Yanda moton tayi ƙwatsa ƙwatsa jini na malala a tsakiyar titin ga hayaƙi
dake tashi tamkar an kunna Masu fetur da ashana wurin yayi baƙiƙirin kai daga Ni kasan babu
mutum ɗaya daga cikin moton nan da ya shura sai dai muce Allah yajiƙan wanda suka rigamu
gidan Gaskiya .
**
Nigerian defence academy ( NDA)
#Nd 1 .
Yaran sojoji ne birjik a ƙame rana na dukan tsakiyar kan su , amma yanda wurin yayi shiru da
yanda sukya a ƙame tamkar wanda ruwa yaci yacinye su . Mutumin dake daga nesa ba zai taɓa
kawowa da akwai mutum ko ɗaya a wurin ba,bare kuma sojoji da sun haura 100 ɗari duka a layi
. Kasancewar su Nd 1 yasa duka yawancin su yara ne matasa wanda daga secondary ne suka
shigo , duk girman yaron dake wannan wuri babu guda ɗaya da ya haura 18 . Duka ƙasa da
haka ne sai kuma 18 din , ciki har da masu 15 years yayan manyan kenan masu faɗa aji a ƙasa
. Sune suke kawo yaran su tun da yarinta .
Cike da Wani irin ƙaraji tamkar zai tashi wurin da yaƙi Muryar Major ɗin su ya katse su yana
furta " Hand salute! Daram dam dam....kaji takon su duka ya sauya suna juyawa ga Major ɗin a
lokaci guda suna ɗaga yatsunsu tare da ƙamewa da ƙafafun su . Bin su da kallo yayi dukan su
Sanye suke cikin t.shirt na sojoji sai wandon su mai ratsin tambarin su na soja.
Idanun Major Jibril ne ya sauka akan Wani kyaƙyƙyawan yaron dake daga can tsakiyar layi , su
duka a ƙame suke amma shi a wannan lokacin Wayar hannun sa yake latsawa cike da kula
murya ƙasa-ƙasa yake furta " Mami...Hello .
Wani irin Tsawa Major Jibril ya daka masa Wanda sai da Hantar cikin Duka yaran ya kaɗa yana
bada amon ƙulululu... Mamaki ne ya kama su Ganin Yanda Aliyou Haidar bai Girgiza ko ya saki
wayar tasa tayi ƙasa ba ,sai ma ƙara mannata da yayi da kunnen sa yana furta " Mami I'm in
trouble Major Jibril ya na mun magana bye bye .kamin ya jira jin mene Zata furta ya datse kiran
da Sauri yana maida Wayar cikin Aljihun sa .
Cike da shouting da ɗaga murya irin na Sojoji Major ya furta " Who are you ? ....kamin ya rufe
baki cike da Ƙwarin gwiwa tare da gigiwa irin na Aliyu ya furta" ALI HAIDAR ". yana furta zancen
tare da ƙamewa kaman yanda suka saba yi don respect. Kallon shi Major Jibril yayi kana ya
bashi umarnin ya fito wajen layin . Cike da kuzari da Sauri ya fito yana gyara tsayuwar sa , kallo
Ɗaya Major yayi masa yaga tsayayyen namiji ne a gaban sa tun kan ya girma a yanzu ma zaka
fahimci hakan , ƙwayar idanun sa ya kalla ganin rashin tsoron sa yasa shi Furta " Waye Soja a
tare da kai ? .
Sorry sir
Fa furta yana kame ma Major ɗin , Tambayar ya kara nanata masa karo na biyu wato a dangin
sa Waye soja? Wanda a wannan karon kai tsaye Ali haidar ya basa amsa da my Dad...! Ya furta
da ƙarfi yana Ƙara ƙame ma Major Jibril . Meye sunan Mahaifin ka ? General Saleh Yelwa .
Girgiza kai Major Jibril yayi tamkar General ne a gaban sa , don yasan Waye General Yelwa
babban sune shine ya basu horo a lokacin tasowar su .
Kallon Aliyou Haidar yayi kana ya cigaba da cewa " Ya ake yin Hand salute?
Ok sir . Ya furta yana Sara masa tare da hade ƙafafun sa .
Kallon Sauran sojojin abokanan sa yayi shigowan yanzu Nd 1 kana cike da Arrogant voice ɗin
sa ya fara cewa Hand salute!
"You raise the right hand smartly in the most direct manner a kuma lokaci guda extending and
joining the fingers ...keep the falm plat and facing the body.
"Yana maganan tare da nuna masu yanda ya kamata suyi don haka Majorn ya sanar dasu a jiya
. "
Komai dai dai ya faɗa , Wannan yasa Major kallon sa yana basa horo da ya fita can Rana ya
fara tsallen kwaɗo shine punishment ɗin sa na yau , Gobe ba zai ƙara kuskuren da yayi irin na
yau ba.
Ficewa Ali haidar yayi yana nufar inda Major yace yayi tsallan kwaɗon , Ɗan waigawa naga yayi
yana kallon wani direction yana murmushi .
Gani nayi wani Matashin yaro wanda ba zai haura 17 ba yana kallon Aliyu idanun shi sunyi ja
na damuwa ga gumin dake karyo masa , damuwa duka sun bayyana ƙarara a fuskar shi . Haɗa
ido suka yi da ƙanin nasa yana jifan sa da harara tare da cewa a zuciyar sa " Yaushe Haidar zai
daina rashin ji ne? Yau sai ya sani bari ya gama mu koma . Murmushi Aliyu haidar yayi yana
furta to menene na dumuwa Yaya Khaleel bafa wuya ne dashi ba . Yanzun xanyi na gama .
Tsallan ƙwadon ya fara yi su kuma sauran sojojin suna fara fareti . Fiye da Awa ɗaya yake aikin
tsallan ƙwaɗon amma babu alamar gajiya a tare da shi , don shi jin sa yake tamkar training din
da suka saba yi ne a gida yake yin sa a yanzu. Ni Ko nace yo ba dole ba , Mahaifin su soja
mahaifiyar su babban Ƴar sanda ce , Wanda a yanzu take da matsayin mataimakiyar
Commissioner of police. Hajiya Nafisat Yelwa kenan . Ƙaramar ƙanwar su kuma jidderh itace
take makarantar yara na karatun architecture . Sauran labari zamuji shi a gaba inshallah ku dai
ku cigaba da biyo wannan Golden pen din don wannan tafiyar ta musammance .
Ali Are You not tired ? Baka gaji ba Haidar? Muryar Areef ya katse shi wanda yake fareti dai dai
inda Aliyou Haidar yake . Cike da hade gira tamkar wani bad boss yace " Na riga da na saba da
ko wani horo na soja tun kamin nazo nan. Ɗan wannan tsallen kwaɗon ba zai gajiyar Dani ba .
Da kyau!
Muryar Major Jibril ya katse su wanda basu san yana tsaye da a bayan su ba. Tabbas wannan
yaron yana da jan rai da zuciya kangararriya , haka ake son soja ya kasance , Major yayi
maganan a zuciyar sa yana juyawa tare da kallon Manyan sojojin dake bayan sa. Ina so ku bi
mun bayan Ali haidar Yelwa yayi gudu tun daga nan Kaduna jaji har zuwa Zaria ya dawo a ƙasa
ba tsayawa ko Hutawa yanzu . Ok sir ......! Suka yi maganan cike da amsa kuwa . Juyawa Ali
haidar yayi yana kai hannun sa tare da miƙa yana miƙewa tsaye . Da sauri ya furta " Major idan
ba damuwa zan iya ɗaukar Helmet da Armor idan ba damuwa da ruwa ma . Wani irin kallo
duka suka bi shi dashi , yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba ,
You Are under punishment now , shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi
me zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo .......................!
*Ina kuke masoyana nasan yawan ku kun haura irin billions ɗin nan kuyi mun share page
ɗin nan ga mutanen ku nasan ƙaranci yanda nake da jama'a billions haka kuma ƙaranci 1
million people. Ga masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take zaki zanzare
kuɗin aljihun ki ayi Miki tallah don samun customers sai ki tuntuɓeni ta WhatsApp ga nombibina
nan a daga ƙasa*
*Labarin RAINON SOJA na kudi ne kar ki fara karantawa tun fari idan kin san baki da kuɗin
saya don Allah... Book 1 free ne shine wannan ,idan mun gama shi book 2 na kuɗi ne kar azo
ana ayi haƙuri da sauran su , Sannan group din littafin guda uku ne 3 , muna da na ƙasa shine
₦500 (regular group) sannan aƙwai yan tsakiya shine ₦1000 (Vip group)sannan aƙwai na sama
shine ₦1500 (Special payment)...Zaki iya payment din ki ta wannan account number
6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta wannan number
08081202932 idan Vtu transfer ne ga MTN numbern da zaki tura tanan 09061466409 zaku iya
fara payment naku tun yanzu don na samu damar sakaki group da wuri kamin mutane suyi
yawa kunsan hidimomin da yawa ...to hajiya ta wannan salon tafiyar ta daban ce kar ki bari ayi
babu ke a barki a baya .labari ne mai ɗauke da darussa ✨yanda yazo a ƙarshen shekara
haka daɗin sa ya kasance na musamman kun san alƙalamin mmnteddy baya rubuta labari mara
ma'ana ato.*
*Anty Aysha Mamanteddy*[1/13, 7:32 AM] +234 704 512 5150: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and sympathetic story.*
_Book 1_
_Free page 2_
*Littafin rainon soja book 1 free ne , book 2 na kuɗi ne regular group ₦500 Vip group ₦1000
special payment ₦1500 .*
*Zaki turo da kuɗin ki ta wannan account number 7782217014 Mohammed Hassana FCMB
shaidar biya ta wannan number 08081202932. Idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan
number 09061466409 ku fara payment da wuri a page 10 Free page zai ƙare*
Maman Teddy.
Marubuciyar
My Lady boss
Yar tsakar gida
Bafullatanan Ruga
Walijaam
The sexy Boss
Gidan Ƙwarata
Siyasata
The virgin maid
Habibi da'iman
Mr romantic
Duniyar shahara x world
Yar Aiki
Dijama yar Fulani
Zuma da maɗaci
Kwarton manya
Da sauran su .
Yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under
punishment...shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi? , Amfanin mene
Helmet zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo ban yarda ko Hutawa kayi
ba . Cike da ɗaga murya tamkar saukar Aradu Aliyu ya ƙame tare da furta " Yessss sir ". Yana
furta hakan ya fara cika umarnin Major Jibril yayin da Wani soja dake gaba dasu ɗan ND 3 yake
bin bayan Aliyu haidar da ya fara gudun sassarfa kaman yanda Major yace dashi . Tun daga jaji
yake gudu a wani irin tartsatsin rana gashi ba hulan su ta soja wanda yake tare dukan Rana ,ko
ruwa kuma ba'a yarda mishi yasha ba .
**
A hankali take bin bord ɗin da kallo , tana sakin Murmushi tare da kai laɓɓanta tana kissing ɗin
zanen fuskar Aliyuu Haidar . I love You Booo mie. Ta furta tana shafan giran sa wanda yake a
tattare ya haɗe kaman hadari. Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta saurin juyowa tana kallon inda
Mami ke saukowa cas-cas-cas cikin shigar suit ƙafarta tasa cover irin na mata , Fuskar ta cikin
baƙar gilashi da gani kasan no respect ba zaka taɓa cewa itace ke da yara uku maza biyu mace
ɗaya ba wato jidderh, Khaleel da kuma iyayen kafiya da naci wato Aliyu haidar. Mami....!
Ƙaramin Muryar Jidderh ya katse Ni cike da yarinta tana sakin mawa Mahaifiyar nata fara'a .
Cikin sauri Mami ta nufo inda take tana rage tsawon ta tare da hugging ɗin jidderh tana cewa "
Morning my baby love". Ana nan kina kallon Khaleel da Aliyu ? . Yes mami i really miss Booo
mie da kuma Ya Khaleel . "Hummmmmm" Hajiya Nafisat ta sauke Sanyayyar ajiyar zuciya
kana ta kai hannun ta tana shafa kan Jidderh cikin sanyi da Muryar rarrashi ta furta " Sorry my
lav zasu dawo nan kusa bada jimawa ba '.
Gyaɗa ma Mami kai jidderh tayi tana sakin Murmushi haƙoranta da wawulo na bayyana wannan
yasa Mami dariya tana cewa"Alright muje kiyi breakfast sai na kai ki school daga nan Ni na
wuce Office . Hannunta ta kama suna nufar Dinning room.....yanda Mami ke tafiya kadai zaka
fahimci zaman gidan Na sojoji ne masu kaki komai oya-oya ake yin shi babu shauƙi irin na mata
, tun tasowar yaran nasu a haka cikin gidan ya kasance, Daddy Soja Mami Police yar sanda
. Haka suka taso basu san suga iyayen su kullum a tare ba ,idan yau Daddy yana hutu to gobe
Mami zakaji an sauya mata wurin aiki ko bata gari , dukan su yaran sun taso cikin horan sojoji
ne ,don gidan baki ɗaya har ta masu girki cook sojoji ne , masu kulawa dasu sojoji masu kai su
school sojoji Wannan yasa duk horo suke shan baƙar wahala , gashi General Saleh Yelwa ya
ƙudurci son ganin yaran nashi sun zama tamkar shi Wato Sojoji . Wanda a yanzu a lokaci guda
Duka su biyun suka fara NDA . A yanzu Aliyuu Haidar shekarunsa sha shida ne Bama ce ya
cika ba ,sai Khaleel babba shine gaba da Haidar shi kuma shekarun sa 17-18 don tazaran su
ba nesa bane shiyasa kan su yake daya ,sau tari wanda basu sani ba ma kiran tagwaye suke yi
masu .
Sai dai Khaleel na fama da shan Wahalar Aliyu saboda Neman magana irin nasa ga kafiya da
fusata ga saurin ƙufula da zuciya, a haka kuma yake zafin son Ƙanin nasa . Wannan shine
taƙaitaccen labarin Gidan General Saleh Yelwa da iyalan sa . Bari mu Jah gaba muji wani hali
Aliyu yake ciki a yanzu .
**
Tafiya ce suka yi ta mai dogon zango yayin da Ali ya haɗa gumi iya gumi a wannan lokacin har
sun kai wuraren Gwargwaje sannan suka kuma juyowa zuwa jeji. A tsakiyar wani ƙaramar jeji
ne kan hanya idanun Aliyu da Yaron Captain Lawal suka sauka kan Wata moto da tayi ƙwatsa
ƙwatsa a titin wuta na tashi ta sama da ƙasanta . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kalmar da
Lawal yayi kenan yayin da Haidar ya cigaba da Gudun sassarfa yana ƙoƙarin wuce moton .
Amma kai baka da Hankali Wani irin mara imani ne kai Ali ? Wucewa zaka yi kana ganin halin
da Mutanen moton ke ciki . Tsayawa Haidar yayi yana ƙamewa tare da seniority ya furta " I'm
under punishment Sir ".
Kama kai Lawal yayi kana yace " Mu ceci mutanen nan ka dakata da Wannan Gudun da kake yi
haka nan ,idan mun koma xanyi ma Major bayani . Ok sir . Aliyu ya furta yana saurin ƙarikowa
inda moton yake hannun sa yasa duk da ƙarfen da tayi zafi ga moto ba karama ba . Tura moton
suka yi da ƙarfin na sojoji suna ɗaga ta , Saurin rufe ido Ali yayi don wannan shine karon shi na