Showing 75001 words to 78000 words out of 79618 words
Chapter 26 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf
yayi kama masu da likita ba sai dai Jarumin Soja
( Hero ) . Ganin sun fice yasa shi shima fita daga room Ɗin yana dawowa inda Aaaman ke
tsaye da su Inna Turai . Ya ake ciki tana lafiya ko?. Hummm Sauke Numfashi yayi kamin yace "
Inna tana lafiya naga tana motsa ƙafarta Everything will be Okay inshallah . Alhamdulillah shine
kalmar da Su kayi kamin Aydaaannnnn yace muje Nasan yanzu an kammala Shirya Jidderh .
Ɗago da ido Aaaman yayi yana kallon Aydaaannnnn matsanancin Tausayin sa ne ya kama shi .
Hannun sa ya kama yana cewa " Mu tafi . Juyawa suka yi suna nufar Farfajiyar Asibitin inda
moton su yake . Aydaaannnnn ne yasa hannu tare da buɗe Murfin Moton dai dai Aaaman na
riƙe Hannun sa ,wannan yasa Aydaaannnnn juyowa tare da masa kallon meke faruwa ?.
Huuuuhhmm Numfashi Aaaman ya sauke kamin yace " Aydaan Bamu taba Gaba tsakanin Ni
da kai ba , hasali ko sa'in sa bamu taɓa yi ba , Amma mun samu matsala sakamakon Soyayyar
Jidderh da kake yi kuma Nima nake yi . Aydaaan.! Ya kira sunan Aydaaannnnn wanda yake
kallon sa Cike da Rashin Fahimtar inda zancen nasa ya dosa . Ransa na masa Babu daɗi .
Please Aaaman ka bar Ni da iya rashi na da nake yi ,ka dai na dawo mun da Famin dake Cikin
zuciya ta . Na sani Nasan Soyayyar Jidderh a jinin mu yake . Yau ta tafi ta bar mu , Ka fahimce
Ni , yanda kake Son Jidderh babu dalili baka san lokacin da Soyayyar ta yayi maka kamu ba a
zuciya haka Nima . Muyi Hakuri da rashin ta mu Rungumi ƙaddara , mu koma yanda kuke a da ,
abotan mu da kuma zumuncin mu ,wacce muke domin ta yau ta bar mu , kayi Hakuri Ƙwazin .
Aaaman yayi maganan idanun sa na tsiyayar da Hawaye .
Hannun suka Haɗa Aydaaannnnn na Hugging Ɗin Aaman tare da ɗan Girgiza hannayen su
Alamun Komai ya wuce daga Yau . Shiga moto suka yi suna Barin Cikin Asibitin tare da nufar
Gidan Baba don gabatar da jana'izar Hauwa . Sun isa dai dai Ana haramar Fito da Gawar ta ,
Wanda Ta ko'ina bil'adama kake Gani kamar mene , Matan layin kuka suke Sosai saboda kowa
tsakanin sa da Hauwa sai sam Barka . A haka Suna ji suna gani aka yi mata Sallah tare da kai
ta maƙwancin ta gidan ta na Gaskiya . A wannan Rana shiru shiriu babu mai iya Wata magana
tsakanin Aydaaannnnn da Kuma Aaaman. Aaaman idanun sa sun kada sunyi Jajirrr don a
yanzu har Gwara Aydaaannnnn ya nuna dangana . Shi Kuwa Aaaman ya gama tunanin cewa "
Hauwa ta zama tasa zasuyi Rayuwa na har abada ,sai kuma gashi wanda ya fishi Son ta ya bar
da ita duniyar . Haka suka zauna babu mai rarrashin Ɗan Uwan sa . A moto suke Suna hango
shiga da fitar Jama'a .
Suna anan a zauna ne suka ga Isowan Salisu ya wani kafa hula yana mutsikar Ido , kowa a
wurin Haushin sa suke ji ,don babu wanda baya da labarin irin azabtar da Hauwa da yayi a
rayuwa daga ƙarshe yayi mata sakin Wulaƙanci . Ba tare da sun shawara da zuciyar su ba ,a
tare su dai kawai suka ga sun fita . Nufar inda Salisu yake suka yi , nan take Aydaaannnnn ya
kai hannun sa yana damƙo sa cikin Mutane . Kamin ya sauke masa hannu tuni Aamannn ya
fara masa Wani irin duka hagu da dama ta ko ina . Shima Aydaaann kai masa hannu yake har a
fuska , mutanen Wurin ne aka taso cikin sauri ana rikesu amma ina Sam sun gaza daina dukan
Salisu . Suka biyu Aydaaannnnn yayi masa Salisu a fuska duka kamannin sa ya sauya , Hancin
sa da bakin sa zubar jini yake yi . Kamin a ƙwaci Salisu a hannun su sai da suka ga baya
numfashi don tuni ya dauke wuta ya sume hau a wurin.
Wasu mutanen Wurin ne da samarin Wurin ke cewa " Ku ƙara mawa matsiyaci mugu , inshallah
ƙarshen ka ba zai yi ƙyau ba . Da ƙyar su Baba suka bar Wurin da su Aaaman da Aydaaann .
**
Hankalin Hibba ne ya tashi Ganin Aaaman ya fita gidan ba A natsuwar sa ba kuma Sannan har
yammaci babu shi babu alamun sa...idan ta kira sa a waya Bata ma samun sa ,wannan yasata
ɗaga waya tana Kirar momyn Aaaman . Ko tsayawa gaishe ta bata yi ba tafara kuka tana sanar
mata da Aaman baya gida .kuma taji ya fita yana Kirar Sunan Jidder , gaskiya Mom Allah ya isa
tsakanin mu da Wannan Yarinyar ta hanani sukuni da miji na . Shiru Momyn tayi cikin Rashin jin
dadi , Jin kukan Hibba yasa Mom cewa " Hibba daina kuka ,ai yau kukan ki ta ƙare , Jidderhn da
kike yi domin ta yau ta bar miki Duniyar ,sai ki tsuma shi ki sha . Ƙitttt Momy ta kashe Wayar
tana barin Hibba da Faɗuwar Gaba . Ta mutu.??? Shine kalmar da take nanata wa a razane .
Kamin kuma ta furta Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un.
**
Abba ne ya da misalin Ƙarfe biyar na yamma ya samu Su Aydaaannnnn aka cewa ya kamata
su tafi gida su ga halin da matayen su suke ciki ,alabar shi sa dawo daga baya . Aaaman ne ya
kalli Aydaaannnnn kamin yace " Aaliyah fa? . Bashi Amsa Aydaaannnnn yayi da cewa " Zan
tsaya anan Har ta ji Sauki sai mu dawo tare da ita ,ka faɗa ma Ammmie . A yammacin Aaman
ya dauko hanya Wanda bai sauka a gida ba sai Wuraren 9:pm . A wannan rana sam baiyi barci
ba yayi kuka kuka kaman mene ? Wanda Hibba taga tashin hankali ,abun da bata taba gani ba.
Tun tana jin ko a jikin ta ,yanda taga Yana yi ta kuma tuna da ita irin Soyayyar da take masa ace
yau shine ya mutu ya barta ya zata yi ,wannan yasa ta itama fara nata kukan , nufar sa tayi tana
zama a jikin sa tare da sa hannu tana Rungume sa tare da fashewa da kuka . Ganin haka yasa
Aaaman tsagaita wa yana tausasa zuciyar sa tare da kokarin kawar da damuwar sa yana
rarrashin ta tare da cewa " Abun da yafi masu shine yawaita mata addu'a . Allah yajiƙan Jidderh
yayi mata Rahma Cousin Aaaman . A sanyaye ya furta Amin Hibba ".
Ɓangaren Sumayya kuwa ji da tayi ance Jidderh ta rasu ,ihu ta saka don su fa basu san
mutuwa ba ,ba'a fiye yi masu mutuwa a dangin nasu ba , aƙwai manya sosai . A Rude take
fadin Jidderh da ,wai Jidderh ce ta rasu ?. Jidderhn da Aydaaann? Haka take sambatu tana
kaiwa da komowa . Jidderh mai surutu da saurin sabawa da jama'a Innalillahi wai'inna ilaihir
raji'un... A wannan rana dai Sam Sumayya taki Ƙwana a gidan ta , Tarkatawa tayi ta dawo
Gidan Moddibo a cewan ta ba zata koma ba sai ranan Da Su Aaaliyah suka dawo . A rana daya
duka sun shiga cikin tashin hankali sam sun manta da Wai faɗan da suke yi akan ta . Ba su
yaran gidan ba har iyayen Gidan sun shiga hanlin jimami.
**
Ɓangaren Aaliyah kuwa Miscarriage tayi Wanda anan akayi mata Wankin ciki da Sauran su . Ba
kuma ita ta farfaɗo ba sai Wuraren Safiyar washe Gari . Ware idanun ta tayi ba tare da ta lura
da Suwa ke akan ta ba ,ta diro a gadon tana sa hannun ta tare da fincike ƙarin Ruwan . Da
Sauri Aydaaann ya riƙo ta yana komawa da ita saman Gadon ,wani irin ihu take tana Kirar
Sunan Hauwa , Adda Hauwa Ya Aydaaann ,ina take da gaske ne ko mafarki nayi , Ya Aydaaann
Adda Hauwa na bata mutu ba ko? Ta ƙare maganan tana kallon fuskar Aydaaann da idanun sa ,
Girgiza mata Kai yayi yana shirin mata nasihar ƙwantar da hankali ,kawai sai ta kuma fashewa
da wani irin kuka mai ratsa zuciya , shikenan Ya tabbata bani da kowa , Ta tafi ta bar Ni Wayyo
Ni Aaliyah na Wayyo Allah Adda Hauwa ki dawo gare Ni don Allah..... Aaaliyah Umma ta kira
sunan ta cikin dan daga Murya ,ya isa ..! Kiyi Hakuri kiyi mata Addu'a ba kuka ba , Ta tafi ba
zata taba dawowa ba . Umma Umma Umma me yasa zata tafi ta barni Umma , itama ta tafi
kamar yanda Umma n mu ta bar Ni ? Ta bar mu tare ,shine yanzu itama ta mutu ta bar Ni ka ɗai
. Aaaliyah ba gani ba , kina dani , Zan kula dake tamkar Jidderh . Ɗago da idanun ta tayi da
suke zubar Ƙwallah tana kallon Aydaaann da idanun sa sun sauya ko ba'a faɗa maka ba yana
cikin tashin hankali . Ya Aydaaann Ta tafi kenan.? Shiru yayi mata , hannun sa yasa yana
ɗaurawa a saman yatsunta tare da matsa mata a hankali yana furta " Kiyi Hakuri Kinji?. Ko
mawa tayi tana ƙwantar da kan ta a saman pillow tana cigaba da kukan ta tamkar ranta zai fita .
Nurse din dake gyefen su ne ta sa hannun ta tana goge Hawayen idanun ta ,don sosai suka
bata tausayi .
Sir Aydaan Ku rarrashe ta ba'a so tana yawan kuka saboda jinin ta yayi ƙasa ,kuma kasan
Miscarriage tayi . Umma ne tayi saurin cewa " Aaliyah Kiyi shiru , Baki da Lafiya , ɓari kika yi ,ki
natsu Kiyi ma Hauwa Addu'a halin ta na gari ya cimma ta . Shiru Aaliyah tayi Hawayen ba tare
da sun daina zuba mata ba , tana jin Maganan Nurse wai tayi miscarriage tambayar kan ta take
a yaushe ne ciki ya shiga jikin ta . Amma sai ta kawar da wannan tunanin don ba ta kan shi
take ba yanzu na rashin yar uwar ta take yi ,wanda tayi babban rashin da Bata taba yin sa ba a
rayuwa .
A wannan ranan ne kwanan Hauwa Ɗaya duka dangin Moddibo's family ,iyayen su da yara su
Hibba Sumayya Mubarak maza da matan su ,suka tarkato duka zuwa Yobe Don kawo ta'aziya .
Komai cikin alfarma aka yi shi moto guda da kayan Abinci na sadaka shinkafa buhu² mangyaɗa
jarka² duk wani nau'i na hatsi an kawo ,wanda Ammmie Hankalin ta ya ƙara tashi ƙwarai jin
Halin da Aaliyah ke ciki , don ɓarin da tayi ya ɗaga Hankalin Momyn Hibba Don ita Dr ce ,tasan
illahn ɓari akan Mahaifan da bata taɓa haihuwa ba . Wannan yasa su a yammacin suka dauki
jiki suka taho asibiti duba Aaliyah ,wanda ƙwarai tayi mamakin ganin su ,amma sai ta kauda
Abun . Yanda momyn Hibba ke nan nan da ita ,ita da Hajiya Rahina yasa Ta mamaki matuƙa . A
taƙaice Hajiya Rahina momyn Summy ce tace ita zata Zauna tare da Aaliyah har a sallame su ,
Su kuma su zauna a gidan su Dake nan Yobe har zuwa ranan da Za'a yi baƙwao .
#mmnteddy
#Ramadhan kareem*SEXXI'ES HOUSE*
50
#Mmnteddy
*Complete littafin ₦500 ne via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta
Wannan number 08081202932 /09061466409....*
___________________
Haka Ƙwana ki suka Cigaba da tafiya Komai Aaaliyah ganin sa take tamkar a mafarki , tun tana
Ganin al'amarin tamkar Wasa Adda Hauwa zata dawo har ta Danga na , sai dai kawai addu'ar
da take mata babu dare babu Rana . Magana ta daina yin shi Sai jefi-jefi Ta koma tamkar
Wacce ta rasa Uwa Da Uba , Ɓangaren Su Momy kuwa Sai da Hauwa tayi Sati Guda a ƙasa
sannan suka tarkata suka yi sallama . Anan ma Aaaliyah fir tace ma Aydaaann ita ba zata koma
ba , a Yobe zata cigaba da zama . Hankalin sa yaso tashi ,amma sai Aaaman ya ƙwantar masa
da Hankali tare da bashi Haƙuri kan ya bar Aaaliyah ta ƙara Ƴan ƙwana ki . Yana yi yana Gani
Ya yi mata sallama don a yanzu tana Gidan Abba da zama . Misalin Ƙarfe biyu na rana ne
Aydaaann ya taho Gidan Su na Yobe yana parking duk wani kayan bukatan sa kana yace "
Summy ta fito da sauran Su hibba ,don sun ce tare da su zasu dawo . Cike da takun nan nata
take ƙarisowa inda Aydaaann yake , Tun ka ta isa Garesa ƙamshin ta ya gama kululluɓe shi .
Kauda kan sa yayi yana sa hannu tare da juyawa Yana bude Murfin Moton zai shige . Yaya
Aydaan Ina Aaaliyah ? Ba tare da ita zamu koma ba ? . Shiru yayi yana juya Kalaman Summy
da kuma sunan da ta kira shi dashi Yaya Aydaaann sunan da ya nanata kenan a ƙwaƙwalwar
sa . Hummm Kin fitar da hanyar da ta dace dake . A yanzu kin gane cewa Ni ne gaba da ke ,kin
sauke girman kan kenan ?. Murmushi Summy tayi kamin tace " Eh Na yarda , amma kasa Ni na
samu sunan ne daga Bakin Aaaliyah ita naji tana ce maka hakan wanda kuma yayi mun dai-dai
. Kallon ta yayi kaman zai mata magana sai kuma taga ya shige Moton yana cewa shigo Mu
wuce . Suuuuuiiii Jikin ta yayi sanyi , To ita Aaaliyahn fah.? Idan ba zaki shigo ba zan tafiya ta .!
Jin Wannan maganan nasa kuma sarai tasan Halin sa yasa ta cewa " Ok tana shigewa Moton
tare da rufowa . Shiru tayi masa tana raba ido har suka fara barin garin Yobe , tana so tayi masa
magana akan Aaaliyah amma kuma shakkar sa da tsoron sa a yanzu da take ji yasa sam ta
kasa . Tafiya suke yi sosai baice Mata komai ba har t cire rai da jin amon Muryar sa ,sai kuma
taji Hannun sa y Ɗaura a saman Taffan hannun ta . Saurin kallon sa tayi amma sai taga sam shi
baya ta kan ta ,hankalin sa na akan Driving ɗin da yake yi . Murza Ƴan yatsun ta yayi wanda ya
sata jan Wani numfaahi mai cike da Abubuwa ma banbanta tana saukewa da Ƙarfi . Wani irin
kallo yayi mata kamin ya motsa bakin sa a Miskilance yana cewa " Aaaliyah ba zata dawo a
wannan satin ba sai next week inshallah . Hummm okay na Gane , Amma Me yasa bamu bi
Flight kaman yanda su Momy sukayi ba , Zamu dade kamin mu kai gida . Hummm wannan Ni
nayi niyya , me yasa baki faɗa mun kina ra'ayin Flight ɗin ba ?, Da sai nasa ke ki tafi Ni taho Ni
kadai ....Allah ya huci Zuciyar ka My Boss ya wuce .! Yanda tayi maganan yasa shi sakin
murmushin da bai shirya ba. Summy dama haka take ba dai iya daɗin baki da ƙwantar masa da
hankali ba , tun da ya faɗa matsalar Soyayyar sa ta farko ita ce mai rarrashin sa , daga haka
itama Ta faɗa Tarkon son sa ,Wanda a ƙarshe ta gane bata da Wata Sauran gurbi a zuciyar sa.
**
Yau ƙwanan Su Aaydaan Uku da komawa Inda Adda Hauwa tayi ƙwana goma babu ita a
duniyar . Wuraren Ƙarfe Biyar na yammaci ne Aaaliyah ta saka hijab tana ce mawa Inna zata
ɗan leƙa Ta shiga kasuwa taga gari . Jin hakan yasa Inna Turai matuƙar jin Daɗi wannan yasa
Ta cikin rawar jiki miƙa mata Naira Ɗari biyu tare da cewa " Gashi ki sayi wani Abin don nasan
bakin ki baya Miki daɗi Saboda Daga ciwo kika tashi . Murmushi Aaaliyah tayi tana amsa tare
da mawa Inna Turai godiya duk da Aydaaann ya bar mata kudi Sosai ƙaroko har ATM card ɗin
sa ya bata akan ta cire ko nawa take da buƙata . Juyawa tayi tana shirin fita Inna Turai cikin
sauri tace " A'a Aaaliyah taho ga Wayar ki can ,kin san yanzu Zaki g Kirar Aydaaann baya Wuce
mintuna Goma bai kira ba , kuma ban san ranan dawowan ki ba . Murmushi Aaliyah tayi tana
saka hannu tare da Amsan Wayar naga da ya kasance Aydaaann ya bata ka min ya taho
Iphone 14 , juyawa tayi tare da cewa " Inna sai na dawo . A dawo lafiya Allah ya kiyaye Hanya .
Amin tace tana ficewa daga Cikin gidan . Ɗan nesa tayi da layin su , tana tsayawa t bayan Wani
majalisa kawai tsintar kan ta tayi da kallon komai na Unguwar tana tuno da Rayuwar ta da Adda
Hauwa tun yarinta . Tuno da baƙar Huƙuban Salisu da ya bata yasa Ta a sarari furta " Adda
Hauwa inshallah sai Allah ya saka Miki , kuma sai Kinga Sakayyan ki akan Salisu ko da bakya
duniyar nan , Allah ya nuna Miki . Ai yanzu uban sa yake ci , Yaje ya Auro tsohuwar mata yar
shekara Arba'in , Sukolar ta shi keyi , sharar gida ,sharar Ƙwata , Ga ta ƙatuwa kaman Tifa ,
farkon ranan da ya fara yi mata iskanci ka masa tayi t zauna a kansa tafi a wa guda sai da ta
kusa halaka shi aka ce . Ƙhhhheeeƙhhhheeeee majalisar ta hargitse da dariya . Muryar Wani
daga cikin su Aaliyah taji yana cewa " Ai Haƙkin matar sa ta farko ne Hauwa Jidderh ,yanzu
gashi nan yana cin ƙaniyar sa ai . Nan take Aaaliyah ta fahimci wa ake nufi . Juyawa tayi da
Sauri tana nufar Gidan Salisu da ke bayan kantin sha'aban .
Tun a soron gidan take jin sababin matar gidan , wanda daga ji kasan uwar mu ce . Iskancin
banza Nine zaka Shanya daga yanzu zaka fita ka sayo mana kayan yaji .