Showing 63001 words to 66000 words out of 79618 words
Chapter 22 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf
nima
na sadaukar Da Soyayyar ga Adda Hauwa, tun ina yarinya take saka Ni jin dadi take kuma
sadaukar mun da dukkan Wani Abu nata ,komun soyayyar da take mawa wannan Abin zata
bani shi halak har abada . Nima .....shiiiii it's Okay .yayi Maganan yana rufe Bakin ta da hannun
sa . Saurin janye jikin ta tayi da Sauri da kuma gudu tana barin Falon . Kan sa ne yaji yana
mugun masa ciwo , idanun sa na sauyawa daga Fari zuwa Jah . Saurin juyawa yayi tare da bin
bayan Aaliyah Hankalin sa ya kasu gida biyu....!
**
Hauwa Hauwa....² Baba ya shigo gidan yana ƙwaɗa Kirar Sunan Hauwa cikin Wani irin murya
wanda yasa Hauwa Saurin Afa Ƙwayar da Dr Jamilu ya bata tana korawa da Ruwa , Cikin Sauri
ta fito tana amsa Kirar Baba dai dai Umma na fitowa daga ɗaki tana kallon Baba tare da cewa "
Malam Lafiya ? Me yake faruwa ne?. Kai-kai-kai Wannan yaro wannan yaro ya cuce Ni ya cutar
da Rayuwar Ki Hauwa , Kuma Wallh sai nayi Shari'a dashi . Cikin Sauri Umma tace " Malam
Wake nan? Wane ban da Wannan mugun shashashan Yaron Salisu . Yanzu Malam Bala yake
sanar mun da baƙar Wahalar da ya ba wannan Yarinyar ,wai shine daga ƙarshe har da tuƙucin
Saki......?
#Mmnteddy*️SEXXI'ES HOUSE️*
#Mmnteddy
Forty-three
43
*Littafin na kudi ne Regular Group₦300 vip group₦500 SPC₦1000 via 6037312299 Mohammed
A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932/09061466409 ....*
___________________
Cike da mmkin maganan nasa Umma tace " Malam yau kai da bakin ka kake faɗin Hauwa ta
sha baƙar Wahala a hannun Salisu? Yau kai da kan ka kake nuna tausayin ka akan baƙar
izayan da Tasha a hannun Salisu? Kai Alhmdlh Allah na gode maka , dama komai ya farko
zaiyo ƙarshe , Abun da na dade ina addu'ar Allah ya fahimtar da kai akan zaluncin Salisu da
yake mawa Hauwa yau gashi Ka fahimta hakan daga bakin mutane mabanbanta . Amma don
Allah Malam kar ka kaishi ko ina ,muna nan Zaka gani Wallh sai Allah ya saka mawa Hauwa ko
da Rayuwar mu ko bayan Ran mu . Aaaa Umma don Allah kuyi hakuri , Babu komai ....Hauwa
tayi Maganan cikin sanyin Muryar ta wanda hakan ya zama mata jiki . Hauwa duk wannan
bakar uƙuban da kika sha kice Na rabu dashi ? Baba yayi Maganan cike da mmkin kalaman
Hauwa . Baba ku rabu dashi komai yayi mun yasan bai mun Adalci ba kuma bai mun dai-dai ba
, Amma na bar shi da Mahaliccin mu,kuma ku bar shi kawai . Numfawa Baba yayi cike da
gamsuwa da Maganan nata kamin yace " Ƙwarai haka ne , Allah zai saka muki Hauwa'u ,
Maganan ki kin yi gaskiya kin kuma yi dai-dai . Ta shi ki tafi Allah yayi miki Albarka ". Murmushi
Hauwa tayi irin na majinyata Wanda basa da Wadataccen Lafiya kamin tace " Amin Baba .
Umma bari na shiga daga ciki . To Hauwa .
**
Hannun ta Tasa tana kama hannun Aaman Kamin ta numfasa tana cewa " Aaaman .! A hankali
ya ware idanun sa tare da maido da duban sa ga Momyn nasa wacce gaba ɗaya hankalin ta
yake ba Ƙwance ba,ta kasa gane gaskiyar inda lamarin Aaaman ya nufa ,shin son Jidderh yake
da gaske a jinin jikin sa ,ko kuwa tausayi ne ?. Momy tunanin me kike yi?. Ya katse ta yana
kallon fuskar Momy wanda ta sakin masa murmushi kana ta shafa suman kansa tana cewa "
Aaaman yanzu fa , Nasan ka fahimta ba Son Hauwa Jidderh kake yi ba, kawai dai Zuciyar
ka....Momy Da gaske Ni ina Son ta.! Kuma dai dai da sakani ɗaya ban ji soyayyar ta ya ragu a
zuciya ta ba sai dai ƙaruwa ma da yake . Momy ko wani lokaci a duk sa'ilin da zuciyata ta buga
,bugawa yake da Soyayyar ta a haɗe . Ina nufin soyayyar Hauwa ƙaruwa ma yayi daga Wanda
kika sani a baya . Shiru yayi yana kauda kan sa don baya tsammanin Momy zata so jin Hakan
daga bakin sa . Sauke Ajiyar zuciya Momy tayi kamin ta ƙara murmushi tana cewa " Ina bayan
ɗa na ,akan Abun da yake SO ɗari bisa Ɗari . Kuma na sanarwa Abban ka shima ya bani goyon
baya akan ka ,kai mijin mace hudu ne ,idan zaka iya adalci tsakanin su , Bama Jidderh ba ko
wa kake da buƙatar aure Indai iyayen ta zasu baka ,bani da matsala da Wannan ,sai dai nace
Allah ya tabbatar da Alheri . Ohhh Mom...!!thnkyou very much momy. Aaaman yayi Maganan
cikin nuna matsanancin Farin cikin sa tare da kama hannun momy yana rikewa ƙaaamm . Ina
son Abin da kake so ne Aaaman , Kasan ina Son ka Ni Mahaifiyar ka ce ,zan soka fiye da kowa
. Murmushi su duka suka yi kamin ya miƙe yana cewa " Momy ina tunanin a yau zan tafi Yobe
Na duba Jidderh acan . Kaiiii Saurin mene kake yi haka? Kasan aƙwai Aiki a gaban ka ko? Dole
sai ka rarrashi Ƙanin ka Aydaan don ya amince ,saboda kasan Wacece Jidderh a wurin sa
,Sannan Bikin ku fa yau ya rage saura Ƙwana uku Ɗaurin Auren ku , dole Ku kasance tare da
Amaren don ku ji abubuwan da suke buƙata, Sannan kuma kar ka manta tun yanzu fa Abokan
ku sun fara cika gida , Zaka tafi ka bar su ne . Hajiya Kaka ta faɗi cewa " Ba zaka Auri Jidderh
ba sai An kammala komai na Auren ku anyi an watse sai daga baya . Shiru Aaman yayi jikin sa
ya ɗan yi sanyi . Momy yanzu haka zan Zauna har tsawon ƙwana ki Uku ban gan ta ba ,ban
kuma faɗa mata Abun dake zuciya ta ba . Ƙwana ki biyar dai ,ba daga Auren bane washe gari
zaka tafi . You have to think about ok?. Gyaɗa ma Mommy Kai yayi alamun ya fahimta kamin ya
juya yana barin Falourn Momyn zuciyar sa cike da jin dadi .
**
Ruwa take yayyafa ma ƙasan Tsakar gidan tare da cigaba da share tsakar Gidan . Salisu ne ya
shigo gidan tare da faɗin " Inna An aje mun Ragowar Tuwon ko?. Aje tsintsiyar Innan Salisu tayi
kamin tace " Eh yana nan na Rufe maka , Ya Maganan neman Auren naka da yar gidan malam
iro ?. Ai Inna Komai lafiya yanzu ma haka sun bani izinin na tura iyaye . Yauwa mashaallh , Ai
yanzu ne zaka san kayi Aure Salisu , da wahala kake yi ba Auren jin dadi ba .....ina zan iya , ai
gwara da kuka rabu dama babu Ɗa bare jika Allah raka taki gona . Haka tayi ta
haibaice-habaicen ta yanda kasan ance mata ga Hauwa kusa da ita . Zagi kam Hauwa tasha
shi a wannan rana kaman mene har ta gode Allah .
**
A Falo ya tadda Aaliyah zaune ta kama Gyefen Kuncin ta Hawaye na cigaba da Zuba mata ,
Haushin kan ta take ji , Haka zuciyar ta ke yi mata tambayoyi akan ya akayi Aydaaannnnn
yasan ta kamu da Son sa , Kuma me yasa zuciyar ta ,ta yaudare ta ,ta fara Son Aydaan Wanda
ta ɗauke sa tamkar Yayan ta , a kuma matsayin sa na Wanda yake son Yayan ta Hauwa ,
Wacce ta kuma ɗauke ta tamkar mahaifiyar t a rayuwa . Kuka take sosai har da cira tana
shashsheƙa ,sam bata lura da isowan sa inda take ba . Hannun sa taji ya zagayo da shi saman
kafaɗan ta yana rungumo ta jikin sa . Kiyi Hakuri ." Taji ya furta mata Maganan , wanda kalmar
hakuri tafi komai bata mamaki , Hakuri? Yau Aydaan ne ke furta mata Wannan kalmar ? To me
yasa ? Ta tambayi kan ta ,kamin ta ba kanta amsa da cewa " Saboda yana Son Yayan ki mana ,
Hummm kawai sai ta kuma fashewa da kuka wanda bai san dalilin kara sakin kukan nata ba .
Hannun sa yasa yana Shafa bayan ta alamun rarrashi ,wani ɓacin rai na Dada kulle zuciyar ta .
Ko rarrashin mutum bai iya ba ,saboda bakin Miskilanci , wallh na tausaya ma kai na kuma
zuciyata bata mun adalci ba ,haka SO bai mun Adalci ba ... Muryar sa ta kuma ji ya katse ta
yana cewa " Bakya so na ko? Haushi ne ya kamata Cikin Sauri ta fara raba jikin ta da nashi
tana miƙewa tare da shirin basa Wuri .
Hannun ta taji ya riƙe kana shima ya miƙe daga Tsaye . Ina zaki tafi ina magana? . baƙar
magana taso faɗa masa ,amma hada ido da suka yi taga Babu wasa a tare da shi sam bata san
lokacin da ta furta "Yunwa nake ji ,abinci zan ci . Hummmm Girgiza kan sa yayi alamun "Okay
,kamin ya ce muje Dirning room tun ɗazu ai an kammala komai . Me ke maki ciwo yanzu a jikin
ki?. Ɗago da sexxy eyes ɗin ta tayi tana kallon fuskar sa ,wanda ji tayi kaman tace Ban sanin ba
, Amma sai Tace " Babu ". Murmushi yayi don har yanzu in ya fahimta Haushin sa take ji . SO
kenan.! Abun da ya furta a sarari ,wanda ya sata saurin kallon sa ban fahimta ba ,me kake nufi .
Murmushi yayi yana dafa ta tare da ɗan rage tsawon sa yana dai daita tsawon sa da nata
,hannun sa yasa yana pointing Ƙwayar idon ta kamin yace " Soyayya ta nake gani mana a
ƙwayar idanun ki gasu nan ,abun gunun burgewa... Janye jikin ta tayi da ƙarfi cikin jin ɓacn Rai
kana tace " Ni bana wani Son ka . Kamin yayi wani magana ta wuce shi fuuuu tana nufar
Dinning room . Murmushi yayi yana bin bayan ta da kallo har ta mace You look so Romantic
wow .! Ya furta Maganan tare da biyo bayan ta .
**
Ƙwana uku kenan da fara shiga cikin jin dadin Rayuwar Hauwa ,yanzu kullum gidan Cikin
nishaɗi ake da Walwala . Tun safe ta tafi babban Asibiti na Gomnati na wannan Garin , wanda
tasha bakar wahala sosai kamin ta samu ganin likita . Shiru Hauwa tayi tana Sauraren Maganan
Doctor Aslaam . Kiyi Hakuri ,ki kuma ƙwantar da Hankalin ki , inshallah every thing will be Okay
. Ƙwallah ne ya ƙwanta a saman idanun Hauwa,kawai sai ta saki Murmushi tare da cewa "
Doctor na saba rungumar ƙaddara mai kyau ko marar ƙyau , Dr Ni nasan ba zan Rayu ba ,
mutuwa zanyi , kai fa da bakin ka kace mun Ciwo na ya kai mataki na Uku ,kama yi mmkin
yanda nake cikin lafiya haka . Ba wai nazo nan bane don ka kwantar mun da hankali akan Abun
da nasan dole Mutuwa zanyi , sai dai na jira lokaci ,magani zaka taimaka mun ka rubuta mun
wanda zai sa naji sauƙin raɗaɗin ciwon zuciyata kamin lokacin tafiya na yayi . Ta ƙare Maganan
tana goge Hawayen fuskar ta , zuciyar Dr Aslam sosai ya karaya tausayin Hauwa ƙwarai ya ka
masa .
Hauwa Kiyi hakuri , tabbas Maganan ki gaskiya ne , wanda ciwon su yakai wannan limit ɗin cire
masu rayuwa ake yi , don Ni likita ne nasan hawa hawa na cuta da kuma worst ɗin shi . Yanzu
wannan tablets din su zaki na rinƙa sha ,duk lokacin da Tarin ya ƙwace miki zaki ji dai-dai .
Amma likita a tunanin ka zan iya ƙara Shekara Nawa a duniyar nan duk da kasancewar nasan
kai ba Allah bane ba .
Shiru Doctor yayi kamin yace " Hauwa ba zaki ƙara shekara ba ,idan kin yi ƙamari ki ƙara
Cikakken Wata Daya ,Kiyi hakuri na faɗa miki gaskiya ne saboda na lura ke macace mai
tawakalli . Uhmmm Na gode Likita , Hauwa tayi Maganan tana miƙewa jikin ta a sanye ta fi ce
daga Office Ɗin . A lokacin da na bar wannan Duniyar ,wani Hali ne Ƙanwata zata shiga?
Aaaliyah..!! Sunan da ta furta kenan kamin ta ja numfashi daƙyar tana tarar napep . Tun da ta
shiga take tunani har ta isa gida . Baba ta tadda Tare da Umma a tsakar gidan , wanda tayi
sallama cikin Sauri Umma ta amsa tana cewa ' Hauwa Gashi yanzu Baban ki ya sayo miki
kayan buɗe Baki kasancewar duk ranan Litinin da Alhamis dama kina azumi . Cike da jin dadi
Hauwa ta kalli Baba kamin tace " Baba na Gode . Ba komai Hauwa'u Allah yayi miki Albarka .
Amin Baba . Tayi Maganan tana shirin wucewa sai kuma ta dawo tare da cewa " Baba Don
Allah dama nace gobe ina son naje Gidan Abba na gaida su Inna Turai . Auuuu ehh Gaskiya
ne ,ai hakan na da kyau Hauwa , Allah ya kaimu goben Lafiya ."
Ɗakin ta ta nufa tare da shigewa . Da fari maganin Da Doctor Aslaam ya bata ta fara shan su
,kamin ta koma ta zauna tana jawo akwatin ta . Hannun tasa tana budewa gami da fiddo da
Wasu hotuna guda uku . Fuskar Aaliyah ne ya fara bayyana a na farkon wanda tana ganin
hoton ta saki Murmushi zuciyar ta na mata wani sanyi . Adda Hauwa nake So.! Keee Aaliyah
kina nufin Kina son ta fiye da Abban ki da Maman ki duka ?. Eh mana Ina son Adda Hauwa fiye
da kowa.! Maganan nan tasu ce ta dawo mata na yarinta , Hawaye ne suka fara zuba mata
kaman yau ne zata barsu bari na har Abada . Aaliyah Ina Son ki Nima , kuma zan bar ki bawai
don bana Son ki ba , A'a A hakan zan yi farin ciki tun da ban mutu ba sai da naga Rayuwar ki
tayi inganci , bana Son Kiyi kuka ko bayan bani ....Ta tasa hoton tana Maganan a sarari hawaye
na cigaba da zuba mata . Rungume Hoton tayi tana kuka sosai tare da cewa " Ina Son ki
Ƙanwata . A hankali ta aje Hoton kamin ta yi duba ga hoton na biyu . Hoton Aydaan ne ya
bayyana Fuskar nan nasa cikin miskilin murmushi ,wanda aka samu yayi daƙyar , a lokacin baifi
shekaru 18-19 ba . Aydaaannnnn nasan zaka kula mun da Ƙanwata Sosai ,ita din farin ciki na
ne , Kamin Alƙawari ba zaka bari tasha Wuyar rayuwa ba, Maganan take kaman zautacciya ita
kaɗai sai wannan hotunan nasu . Zan tafi na barta a hannun Allah a kuma hannun ka ,ina
addu'ar duk wata Soyayyar da kake mun ya taru ya nukku ya koma kan ta . Aje Hoton nasa tayi
tana duba cikon dayan Hoton wanda ya kasance hoton ta ne , ita da Aydaaannnnn dukan su da
uniform na makaranta ,fuskokin su dauke da fara'a kaman ba shi ba . Hauwa ya kama ta ki bar
su suyi rayuwa cikin jin dadi su ma , Hannun ta tasa tana raba hoton gida biyu tare da cire
ɓangaren ta ,tana cire na Aydaan ...!
**
A hankali take cin Abincin nata Hankalin ta ƙwance duk idan ta kalli fuskar Aydaaannnnn sai ta
kauda kan ta Gyefe . Shi kuwa ƙurr da ido yayi mata yana kallon ta ,komai nata sak na Jidderh .
Ganin yanda komai taci sai ta raba biyu ta aje wani a gyefe yasa Aydaaannnnn cewa " Wannan
na waye kike ajewa kuma?. Adda Hauwa mana .! Babu yanda za'a yi itama ta ci irin wannan?
Tsayawa yayi yana kasa bata amsa ta ina hakan ziyuwu? Shine Abun da yake cewa a zuciyar
sa . Kasan mene Yah Aydaan? Tun Ina yarinya Komai Adda Hauwa taci sai ta kawo mun , kaga
lokacin da kuke makaranta tare ina Wannan chocolate ɗin da kake bata , Kullum sai ta rago ta
kawo mun , tun ina ƙarama nasan sunan ka amma a bakin ta na saba ji . Kana Son Adda
Hauwa sosai .shi yasa Nima nake daga maka ƙafa A duk abin da kake mun , amma kar kayi
zaton soyayya ce ,a'a kawai ina Son Wanda yake son Adda Hauwa ne . Murmushi yayi kamin
yace" Oho Haka ne? To mai zai hana mu dawo Da Adda Hauwan Gidan nan sai mu zauna tare
. Saurin kallon sa Aaliyah tayi kamin ta fara tunanin Maganan nasa , Wannan me yake nufi
kenan...! Ɗan rainin Wayo kawai ,Ganin bakin ta na motsi yasa Aydaaannnnn cewa Magana
kike yi ne , fadi da ƙarfi bana jin ki sosai your voice is low .....!
#Mmnteddy*️SEXXIE'S HOUSE️*
#Mmnteddy
Forty-four
44
*Littafin na kudi ne Regular group ₦300 Vip group ₦500 spc ₦1000 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number
08081202932/09061466409...*
___________________
Nuna masa tayi ba wani Abin zata Faɗi ba , hakan ya bashi damar cigaba da cewa " Kin ga
kema ai zaki fi sakin jiki sosai . Hummm idan dan Ni zaka yi hakan to me zai hana ka mayar
dani Gidan ku kawai ,naga Acan zan fi samun sakewa sosai ,don nan din ne bana So . Aaliyah
Wai mutane nawa kika damfara ne ? Me kuma yasa kika Ɗauki Wancen sana'ar ....Don Allah
nidai kawai shikenan . Ta katse shi tana miƙewa daga Zaunen da take . Me kike nufi Har kin ci
abincin ya ishe ki . Uhmmm ya ishe Ni . Murmushi yayi yana cewa " Ni yanzu ma na fara
saboda kin san ina cin Abinci Sosai. Wuce shi tayi a zuciyar ta kam cewa take " Ko ban ƙoshi
ba ai na ji na ƙoshi da komai ,ka tasa Ni da Wasu maganganu marasa ma'ana Humm haba .
Rasa inda zata nufa ne yasa ta komawa Inda ta tabbatar nata