Showing 36001 words to 39000 words out of 79618 words
Chapter 13 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf
Malam ba'a yi haka ba? Ba fa muji meke damun ta ba ? Kuma yanzu Turai
ta sauya ,tana Son Aaliyah da duk jinin Abba a yanzu . Umma tayi maganan cikin Sanyi ,
Aaliyah me ya faru? Ta tambayi Aaliyah cikin nuna kulawa . Umma Auren dole Su Baba Salihu
suka Ɗaura mun da Wani .... Aure.??? Baba yayi maganan cikin ɗaga Murya , ina wannan
bazata saɓu ba.!
#Mmn teddy*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema
Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba
Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan
Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House
ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
23
Baba ne ya kalli Aaliyah yana cewa " Tayaya zasu yi miki Auren Dole , idan suna taƙama su
iyayen ki ne ,nima matsayin Uba nake a wurin ki koda bani na kawo ki Duniya ba . Malam ka
bar wannan zancen don Allah , Aaliyah faɗa mana ke kin san yaron ne ? . Kallon Umma Aaliyah
tayi kamin tace " Eh na san shi ,aikatau nayi a cikin Gidan su ,har part ɗin shi ma ... Nan Aaliyah
ta fara basu labarin Aydaan , Wanda tun da tace Gidan Moddibo Hauwa ta fahimci Wane ne .
Shiru tayi tana jin Wani irin yanayi tsikar jikin ta na tashi . Sai da Aaliyah ta gama maganan ne
Baba ya dafe kai yana cewa " Wannan tabbataccen Yaron Suka Wanke ki suka miƙa masa?
Tabbas zaki dawo ba'a hayyacin ki ba Aaliyah , kuma Indai ina da Rai ba tare da amincewar ki
ba bazan taba yarda a miƙa ki gidan Aydaan Moddibo ba . Tsayawa Aaliyah tayi tana Son
tambayar Baba dama yasan Aydaan ne ? Sai kuma tayi shiru tana nazarin kalaman sa. Ita dai
a wannan lokaci taji yana mawa Abba Sababi ne ta Wayar sa , wanda kamin tayi Aune taga ya
mika mata Waya suna magana da Abba . Jiki a sanyaye ta mike tana cewa ' Baba Bari na
koma.! A'a Aaliyah ki taho dakin Umma ko ruwa ki sha kamin ki tafi . Wani irin kallo Baba ya
watsa mawa Hauwa , Wanda tayi Saurin kasa da kan ta . Kama Hannun Aaliyah tayi tana
shigewa Ɗakin Umma da ita .
Aaliyah ne da shigar su ta fara neman wurin zama ,wanda kamin ta zauna Hauwa tace " Ke
dakata.! Bana kirawo ki bane don ki zauna ... Aaliyah kalli idona ki faɗa mun matsayina A wurin
ki . Cike da mmkin sauyawan Hauwa Aaliyah idon ta na cikowa da Ƙwallah tace " Ke Adda ta ce
, Yaya na Uwa ɗaya uba ....ya isa ban tambaye ki wannan ba . Kin san da hakan ? Hauwa tayi
maganan tana kallon Aaliyah wanda tayi saurin gyada Mata Kai . Motsa Baki Hauwa tayi tare da
fara cewa " ke da Bakin ki a kwanakin baya kika taho kika same ni da cewa " Na faɗa miki duk
wani Abu da zai ɓata mun rai game dake ,domin ki kiyaye ,nace miki babu komai, To Aaliyah
yanzu Akwai . Na'am Adda Hauwa me nayi miki? Aaliyah tayi maganan tana narke mata ,domin
tana Gab da fashewa da kuka . A'a bance kimun kuka ba , Aydaan .! Ki sani idan kika kuskura
ko sau Ɗaya kika ɓata ma Aydaan tamkar Ni Hauwa kika yi mawa , Haka idan kika guje shi
kusani tamkar Nine kika guje mawa." Aaliyah idan kika azabtar da Aydaan Wallh bazan yafe
miki ,ki fita ki bani Wuri Kiyi duk Abin da kikayi niyya .
Fashewa da Kuka Aaliyah tayi kamin ta juya da Gudu tana ficewa daga Ɗakin ko sallama ba
tayi mawa su Umma ba ta fita tana kuka . A hanya sam kan ta ya kulle ,me Adda Hauwa take
nufi? Shin tasan Aydaan ne? a'a Babu ta yanda Za'ayi Tasan shi . A haka ta isa gida ,tana shiga
Ta nufi Ɗakin Abba . Zubewa tayi har ƙasa tana basa Haƙuri tare da cewa " Na tuba Abba , na
amince Wallh zan masa biyayya zan zauna da Aydaan ,amma kuce Adda Hauwa ta daina fushi
dani Don Allah. Inna Turai ne ta riƙo ta tana cewa " Ita Hauwan ke fushi dake ? Gyada Mata Kai
tayi tana fashewa da Sabon kuka . Dafa ta Inna tayi tare da shafa bayan ta tana rarrashin ta ya
isa . Zata daina kinji?.
Saurin riko Hannun Inna Turai tayi tare da cewa " Inna Adda da gaske zata daina fushi dani? .
Gyaɗa Mata Kai Inna Turai tayi tare da cewa " Ai kin san bata taɓa fushi dake ba , Yau ma dai
ta nuna miki kisan darajar Auren ki ne . Mu tafi ɗaki muje kici Abinci . Miƙewa Aaliyah tayi Abba
na Murmushi cike da jin sanyi a zuciyar sa ta fice daga Ɗakin tare da nufar Ɗakin Inna Turai .
**
Basu samu isa Garin Ibadan ba sai Safiyar goben ranan . Koda suka isa Gida Kowa part ɗin shi
ya nufa tare da kimtsawa ,kana kusan Awa biyu Aydaaannnnn ya fito yana nufar Ɓangaren
Ammiee . Anan ne take ƙara Sanar masa da Isowan Amaryar sa a gobe , Wanda Batasan Tuni
Abban Ibadan ya sanar masa ba . Ammiee ne tace dashi yaje ya duba jikin Summy ,don har
yanzu jikin nata sai a hankali ,ciwo sosai take yi . Jin hakan yasa shi nufar part ɗin Hajiya
Rahina . A Falo ya tadda Momy Rahina don saukowar ta kenan daga Bedroom din Summy .
Hannun ta dauke da glass cup da alama ruwa ta bata sannan ta fito . Washe baki yayi cike da
jin dadi da faharin ya zama sirikin ta tace " dawowar yaushe ?.. murmushi yayi yana gaishe ta
kamin ya haura upstairs don nufar bedroom din Summy .
Da shigan shi Bedroom din ya ga ko ina ta rufe ruguf , a hankali ya taka yana nufar window tare
da yaye labulan , Tun shigowar sa taji ƙamshin turaren sa ,wanda a ko'ina taji bazata yi
makowar mai shi ba . Wani irin Raɗaɗi take ji tana ɗago idanun ta tare da Ware su daƙyar dai
dai yana isowa. Hannun ta ta ɗago masa tana miƙa masa , Wanda a hankali ya miƙa nasa
yana haɗawa da nashi ,tare da matsowa kusa da ita yana hayewa saman gadon ,dama sun
saba. Matsa hannun nata yayi a hankali yana jin Zafin jikin nata yayi tsanani . Ɗago da Lulun
idanun sa yayi yana zuba su a kan fuskar ta , wanda suna haɗa ido tafara zubda Hawayen da
suka dade da daskare mata a zuciya . Kuka take sosai har dasu Ajiyar zuciya . Wanda duka
yasan dalilin yin masa hakan ,bai wuce kishi da bakin cikin Auren sa da Aaliyah . Kallon ta yayi
yana cewa " Meke damunki Summy? Ina ke miki ciwo ? . Ɗago da idanun ta tayi da suka yi Jah
kaman zata masa magana sai kuma ta kasa . Please ki faɗa mun ? Me yasa kika ƙi bari a kaiki
asibiti?. Aydaaannnnn ina Son ka.! Bazan iya jurar ganin nayi kishi da ko wacce ya ma ce ba
,zan iya komai , bazan iya kishi da Yar Talaka ba kuma abun Haushin ma yar Aiki na.!
Kuma yar Aikin gidan mu .! Wani irin ba dadi yaji , wannan yasa shi yi mata Wani irin kallo
kamin yace " Nine nace ina Son ta ai , so ina ke miki ciwo?. A Maimakon ta basa amsa kawai
sai ta fashe da kuka ,nasani ai . Aydaan ka tsane Ni me nayi maka? . Ke Summy , Wai ke
bakya duban Ni Ƙannin ki ne? Me yasa zaki Soni? .So babu ruwan sa da Wannan , Amma zaka
iya kashe Ni ta hanyar yimun Allura yanzu ai kai likita ne ." Kallon ta yayi cike da jin dan
tausayin ta . Hannun sa yasa yana Rungume ta jikin sa , wanda nan naga Abun mamaki shigar
da kan ta tayi saman ƙirjin sa tana shaƙar ƙamshin jikin sa tare da masa Wani irin kuka can
ƙasa² na tada Sha'awar masoya . Sarai tasan waye Aydaaannnnn shi yasa duk wani Abu da
zata ja hankalin sa take yi . Hannun sa yasa yana shafa suman kanta har zuwa Bayan ta tare
da hura mata iska a Gyefen kunnen ta a hankali ,is Okay my Summy ,ya Isa ina Son ki kema .
Sauke Ajiyar zuciya tayi tana saka hannun ta tare da shafa saman ƙirjin sa tana wasa da
ƙwantattun gashin ƙirjin shi . Lumshe ido yayi tare da saurin riƙe hannun ta cikin wani irin
yanayin murya yace " Stop it". Yayi maganan tare da miƙewa yana cewa " Bari na Dauko first
aid box na yi miki allurao . Ga shi nan ai , Ammie tun juya ta shigo dashi .
Juyawa yayi yana kallon inda ta nuna masa , nufar wurin yayi yana dubawa tare da Ɗaukar
Wasu alllurai yana haɗawa wuri guda tare da jan shi a ƙaramin sirinji ....Takowa yayi zuwa inda
ta miƙe zaune . Tsayawa yayi yana kallon ta , kamin yace ' Bani Hannun ki nayi miki?. Kallon sa
tayi a shagwaɓa tace " A'a Ni ba'a mun Allura a hannu kamun a baya kawai . Cike da yagewar
ido da yafi nata yace " Okay juya ,kuma kar ki mun raki . Juya masa tayi yana sa hannun sa tare
da Sauke Skirt ɗin jikin ta , Wani irin abu ya haɗiye , hannun sa yasa yana shafa tudun Bayan ta
, Kusan mintuna biyar yana kasa sa Sirinjin . Ita ko lumshe ido take , tana fara jin tana tsiyaya .
Wani irin magana take a harde kaman wanda ake saka mata shocking . Aydaaannnnn Please...
Please Aydaaannnnn , Aydaaannnnn ...! Hannun sa yasa yana shafa Gadon bayan ta cikin
Wani irin Salo ,yana jin yanda Alƙalamar sa ke harbi kana yace " Mun kusa saura kwana nawa
ne ? Just mu kara hakuri kar muyi sabon Allah . No Aydaaannnnn Babu komai fa . Kai ai miji na
ne zaka zama . Wani irin kallo yayi mata bai san lokacin da ya zura allurar ba tana gantsarewa
tare da sakin yar ƙaramin ƙara . Hannun sa yasa yana lailaya mata kamin yace " zan Aiko miki
da magani ki tabbatar kin sha . Yayi maganan a gadarance kun dai san shi da isa da mulki ga
uwa uba Miskilancin hummm. Juyawa yayi yana ficewa da ga Bedroom din tare da nufar
Farfajiyar gidan .
***
Tsawon dare Aaliyah ta kasa barci ga damuuwar Adda Hauwa ga kuma damuwar daga Yau
gobe Ibadan aka kuma yi da ita . Me yasa Adda Hauwa zata Faɗi mun haka ? Me yasa abun da
bata taba mun ba ?. saurin miƙewa Aaliyah tayi daga Zaune tana faɗin Wallhi na gane na gane
yanzu . Adda Hauwa itace Jidderh n da yake magana , tabbas itace ,saboda yace muna kama
ba kaɗan ba .... Dafe kai Aaliyah tayi tana rushewa da kuka mai taɓa zuciya. Shine wanda Adda
Hauwa zata yi fushi dani akan sa , Wayyo Ni Aaliyah , Me yasa Zaka shigo mun rayuwa ta . A
haka ta wuni tana kuka har aka fara korar sallar subahi .
**
Kaman yanda Aaliyah idanun ta suka gagara rintswa haka ɓangaren Aydaaannnnn ,duk dashi
na farin ciki ne ,duk ya kosa safiya tayi a taho masa da Matar sa ,wanda yake ganin Abun
tamkar a mafarki . Sai bayan ya dawo sallar subahi sannan ya rintsa , inda a barci mai dadi ya
dauke sa . A cikin barcin sa ne yayi mafarkin Aaliyah ta haifa masa cute bby girl , Wanda sukayi
kama sak har daƙwa²n idanun . A haka ya tashi cikin matsanancin Farin ciki , Privacy ya nufa
don lokacin ƙarfe Goma na safiya . Bayan ya kamala karin kumallo sa ne , ya mike tare da nufar
Ɓangaren Ammiee Anan yake jin tun Safe An tura Jirgin yawo Heliƙwafta na malam bahaushe
don dauko Amarya . Hajiya Barmani tace bata buƙatar Ganin dangin Aaliyah ko mutum daya
,wannan ne yasa Momy Rahina Da Momyn Aaman su kadai tafiya don ɗauko Amarya , jirgi
suka bi don zuwa Garin Yobe.... To ko ya abun xaya kaya.....!
#Mmn teddy*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema
Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba
Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan
Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House
ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
24
Nufar Ɓangaren Hajiya Barmani Aydaan yayi don Abba ne ya kira sa yana Sanar masa da Abun
da bai san dashi ba sai a Wannan lokacin ...Wai Hajiya Barmani ta ce " Ba za'a kai Aaliyah
Sabon Estate din su ba , Anan Gidan Zata zauna a ɓangaren sa. Wannan yasa Shi nufar
Ɓangaren Hajiya Barmani , inda da Shigar sa ya tadda Summy Hibba , da Sauran ƴammatan
Gidan . A'a Aydaaannnnn Ango na . Kallon Hajiya Barmani yayi kamin yace " Waye Angon
naki? . Murmushi Hajiya Barmani tayi kamin tace " To ƙwarai ni kuwa , Don babu Abun da zaka
nuna mun ƙuruciyar ma na Fika. Ran sa ba Dadi ya shigo Falon nata ,amma jin Wannan
maganan nata yasa shi Darawa tare da cewa " Humm To Ni Angon Aaliyah ce. Saurin kallon sa
Sumayya tayi yayin da Hajiya Barmani tace " Akul kar Wannan ya ƙara fitowa daga Bakin ka na
haneka Kul". Kai Angon mata biyu ne , Yau dai za'a Fara kawo wacce kake kallon ta a mata ,
don Ni nasan Waye Talakawa da mugun abu ,babu Mamaki an gama da kai ne ,an kai sunan ka
an tsaface ka Allon Ƙarfe . Ɗago da Lulun idanun sa yayi yana sakin mawa Hajiya Murmushi
bawai don bai ji zafin maganan nata ba a'a . Sumayya itace Ƴar gata kuma Ƴar dangi ƴar uwar
ka ta jini ba Wancen abun ba da ba zata taɓa nuna .... Hajiya Don Allah ki bar wannan maganan
.! Ni bashi ya kawo Ni wurin ki ba ". Ƙwazin.! Hibba ta kira Sunan Aydaan cikin Sanyin murya
tana Ɗago da idanun ta tare da kallon Aydaaannnnn . Ina jinki ,yayi maganan yana Bin fuskar ta
da kallo .
Ƙwazin Wannan Abun da kake is not Good , Bai dace ba , Anty Summy tana Son ka ,me yasa
kake kokarin fifita Soyayyar Ƴar aikin mu akan na jinin ka? Mun taso tare , Tun muna yara muke
So da ƙaunar junan mu , but Why now zaka ce baka Son jinin ka ko nace kana fifita wacce Da
ita da Dabbobin gidan nan basu da mara ba . Don dabbobin mu sun fi mana ita amfani , su ko
ba komai zamu yanka muci Namar su tayi mana Dadi. Ita kuwa fa? Sai dai ƙarin Ɗawainiya da
Jidali iyaye.....Keeeee..! Ya Wani daka mata gigitaccen Tsawa wanda tun da take dashi bai taba
masu irin wannan Tsawan ba ,don ko ina na Wurin sai da ya amsa . ina Wasa dake ne?? Ni
sa'an Wasan ki ne? , Saurin girgiza Kai Hibba tayi tana kokarin sa kuka , Kamin yayi magana ne
Summy da ta gama tunzura tace " Saboda An kawo aibun ta shine kake Wannan maganan ? Ai
maganan Hibba gaskiya ne , Nima kamin Tsawa amma sai dai ta tsaya iya nan don babu duka
". Saboda me kika ce haka? Yayi maganan yana maida kallon sa ga Summy dake farfar da ido
na musifa . Saboda Ni Yayar kace ,bakai ne ka riƙe mun hannu ba a yarinta, nice Wacce na
kama hannun ka kana yaro mu tafi makaranta , Aydaaannnnn baya na ya goya ka ba sau Ɗaya
ba Sau biyu ba... Soyayyar ka jarabta ta ne a gare Ni ...a kullum bani da burin da ya wuce na
ganni tare da kai , amma kai da yake butulu ne mai manta alheri , kasha faɗa mun baka SO na
sau nawa ? . Me yasa me yasa Aydaaannnnn duk matan duniya ka rasa wacce zaka hada Ni
kishi sai Aaliyah?? .
Saboda Ina Son ta , kuma ba zan daina Son Aaliyah ba har ranan da zan ban doraar duniya ,
saboda ina jin ta tamkar jini na dake gudana cikin jiki na.' Hajiya Aaliyah zasu sauka a yau a
cikin gidan nan ,amma ban yi Alƙawarin zan barta takai gobe ba ,ba tare da na Kaita Gidana .
Yana Gama Faɗin haka kamin Hajiya Barmani tayi magana ya juya fuuuu yana barin Falon ....
Zuciyar sa na masa Wani irin Zafi ...zaki maimaita ke yayata ce ,tabbas sai kin maimaita
wannan kalmar , Kuma zaki sha mmkin Waye Ni Aydaaannnnn , baki Sanni ba har yanzu.
Bayan fitan sa ne Hibba ta kalli Summy tana cewa " Anti Summy you make a mistakes ,
Maganan ki yayi kaushi da yawa ,kin san Fa Waye Ƙwazin? Baya da kirki ,baki masa ba ma
yayi miki bare kin masa . Na tausaya miki kar ki manta