Showing 153001 words to 156000 words out of 173794 words

Chapter 52 - GURBIN IDO Karyayyiyar Rai By Huguma

wani waje daban,har yanzu bata waiwayeni ba,ni kuma bansan muhallinta ba bare naje na nemi yafiyarta" sai ta kama habar zaninta tahau fece majina.

Dariya hade da mamakin furera suka kama yuuma,saidai ta danne kawai taci gaba da kallonta tana cewa

"Allah sarki,ai sai a godema Allah da yasa aka gane kuskuren da akayi,alhamdulillahi,Allah ya yafe mana"

"Ameena....ameena" ta shiga amsawa tana sharce hawaye,wanda kusan hawayennata dukka akan naggenta da suka dinga mutuwa ne,asarar data tafka.

Sai data gama dukka koke kokenta ta miqe zata tafi sannan tace

"Umm....nace ba,ai sai a bani kwatancen gidan nata,can inda take a gomben ko?,sai a leqa aga dakin nata,a kuma nemi yafiya,bai kamata a matsayina na uwar riqonta ba kuma ya zamana bansan inda mazauninta yake ba"

"Tooo....anzo wajen" yuuma ta fada,ta shafa addu'ar da takeyi sannan tace

"Yanzu kam bana ce miki ga inda muhallin maimunatu yake ba,tunda ba zuwa nayi ba ko sanda ake bikin,ban samu na leqa ba" gaban inna furera ya fadi,har yanayin fuskarta yadan sauya

"To,ikon Allah,to kuma su can gidan surukan nata fa?" Kai yuuma ta sake girgizawa

"Shima bana ce ba,tunda nafi shekara rabona da garin gombe,sannan koda can ma kinsan ba ni nake kai kaina ba,yafendo ke aikomin da mota ta daukeni daga nan qofar gidan zuwan wancan" shuru furera tayi,ga qoshi ga kuma kwanan yunwa,yanzu ya kenan?.

"To ai inaga ta zo da sauqi ko,me zai hana ki waya da ita ki gaya mata surukarsu nason ganin dakin diyarta,idan yaso nima basai motar tazo ta daukeni ba?". Binta da kallo yuuma tayi galala,sai kuma ta gyada kai

"Haba furera,dama dai na tashi zuwa ne"

"Zan iya jiran tafiyar taki indai ba zatayi tsaho ba"

"Allah ya bamu aron rai" ta amsa mata a taqaice,sabida takaicinta daya fara kama yuuma,murna ta cika inna furera

"To alhmdlh,don Allah a qoqarta muje anan kusa yuuma,na gode Allah ya qara zumunci" ta fita tana zabga mata addu'a tare da hango nesa a kusa,duk daba haka taso ba,so tayi gobe ko jibi ta dage.

A tsakar gida sukayi kacibus da daada,sai tabi fureran da kallo cike da mamakin abinda tazoyi gidan,harara suka zabgawa juna,inna furera tayi gaba tana yada habaici

"A hayye na gaba kam ai yayi gaba,na baya ko tsintar hula ba zaiyi ba,yo mu da muke jinin sa'a da nasara,haihuwa me rana,ta jefa mu gidan arziqi,ai an rabu ne kuma ba'a rabu ba,yuuma gidan karamci" sak daada tayi tana duban dakin yuuma,ta sani cewa yuuman ba munafuka bace,da sai tace wani abun suke qullawa,hakanan ta san yuuman bata daukar raini ko cin kashi bare tace zata je tayi mata tatas kan ganin furera da tayi cikin gidan,amma duk da haka sai ta kasa daurewa,ta ajjiye faifan dake hannunta ta nufi dakin yuuma.

Yuuman na tsaka da nade abun sallah daadan ta shigo,ta daga kai ta dubeta

"Mamaki nake yuuma da ganin fitowar furera a dakinki,me tazo yi?" Tambayar sai ta bata mamaki da haushi,salon yadda tazo mata da maganar mai kama da titsiye

"Kunfi kusa ai,nima tare na ganku,sai kije ki tambayeta ai" daga haka taci gaba da aikinta,shuru daada tayi,don bata da sauran ta cewa,sai kuma ta juya ta fice daga dakin sukuku,yuuma taja qaramin tsaki,sun dauka ita din sakarai ce da zata biyewa shirmensu daga ita har fureran?,kallonsu kawai takeyi amma tasan halin kowa.

A hanya fureran keta sumbatu ita kadai,Allah yasa dai kada yuuma taja mata lokaci ko kuma taqi zuwa da ita

"Idanma taqi idanuna zan murje na tafi gembu,nayi musu kwance kwance har sai na samo kwatancen gidan,don ko da tsiya koda arziqi saina fanshe wahalata,ato" da wannan tunanin ta koma gida hankalinta kwance.


********Tunda hajiya munubiya ta tafi take ta juya maganganun da sukayi da ita,ranta ke mata wani irin ciwo da suya,sadakarta aka bayar shine abu mafi ciwo da qona rai a wajenta,musamman da hajiya munubiyan ta gaya mata dukka familyn dr khalid akko kallon da suke mata kenan,zuwa yanzun ta soma gasgata cewa amma da anni basa qaunarta,don ta lura da wani kulawa da soyayya ta musamman da suke nunawa maimunatun tun zuwan da sukayi a shekaran jiya,sannan abubuwan da suka afkun da yadda aka turata kitchen hado masa abinci maimunatu na zaune, bayan itace qasanta,ta fita daraja ta fita mulki da kudi,babu ko tantama akwai abinda aka kitsa a shigarta kafin ta fito

"Bari na baki wani sirri guda daya,kinga wannan mijin naku,a gabanmu ya tashi,babu wani hali da dabi'arsa da bamu sani ba,bari kiji,indai kinaso ki tsira da mutunci da martabar ki,to karki ragawa kowa,ki tsaya a tsayenki sosai,ki nunawa kowa ke din daga madaukakin gida kika fito,shi kuma ja'afar,kada ki yarda ki bada kanki ta sauqi,mutum ne shi da ya tsani yaga ana nuna masa soyayya,ke ko matarsa data mutu wadda ya kusa zama mahaukaci a kanta ko nace yama zama.....don duka yake wani lokaci harda cizo idan ciwon ya motsa masa....." tsoron da unaisa bata taba jinsa ba yanzu ya darsu a ranta,zancan da aketa fada wai wai yau sai gashi daga bakin matar qanin babansa

"Eh....Allah dai ya kiyayeku kawai ya tsare kada wata warana ya illataku.....ina gaya miki,ita kanta baqar wahala tasha a wajensa saboda nuna masa soyayya da tayi,to ki watsar dashi,kija girma da mutuncinki,ina gaya miki idan na rantse ko kaffara banyi,idan ya fahimci kedin babbace kuma me aji,da kansa zakiga yana shanshanarki,a nan zaki murza zarenki yadda kikeso" sanda ta yima anty talatu wannan bayanin cewa tayi

"Ban yarda da maganganun matar nan ba"

"Saboda me anty?,don me zata zo ta gayan qarya ko ta shiryamin zance?,bayan suna da alaqa dashi?,ita ba kishiyar babarsa ba bare nace qiyayya da kishi ya sanyata aikata haka ba,sannan ba mai jini a jiki bace bare nace sonshi take take shiryan gadar zare,hasalima 'yarta daya kuma an sanya ranar aurenta,saura watanni biyu bikinta,bamu taba gamuwa ba sai ranar dana kai qararshi gaban anni, gida zata tafi amma saboda ni ta tsaya,da qyar ma nayi convincing dinta tazo gidana mukai wadan nan maganganun" wannan hasashen na unaisa ya sanya anty talatun itama hankalinta ya karkata

"Kuma gaskiya kika fadi,mu jarraba mu gani din".

Ajiyar zuciya ta sauke tana komawa inda ta tashi dazun ta zauna,tana lissafa adadin kwanaki ko watanni idanma ta kama shekarar da zatayi kafin ja'afar yazo hannunta,tabbas zata tsaya akan kowa har sai sun fahimci girma da martabarta,amma batajin zata iya daukewa ja'afar qafa,babu tabbas.
[11/15, 6:34 PM] +234 813 615 2119: 59

Ya tadda schedules da yawa a company,don yana shiga kamfanin tun daga first floor PA dinsa ke biye dashi yana lissafo masa,yasan cewa laifinsa ne,tun jiya ya kamata ya buda email dinsa ya duna schedules dinsa na yau amma baiyi hakan ba,hakan kuma baya rasa nasaba da abinda ya faru jiyan,ya kuma tabbata da qyar ya tsallake rijiya da baya

"Finally.....you have a trip" dakatawa yayi daga zuba wayoyinsa da yakeyi a muhalli na musamman da aka tanada masa saboda ajjiyesu,ya waiwayo yana dubansa da shanyayyun idanunsan nan dake ma kowa kwarjini

"To where?"

"the construction work of the estate in lagos should be checked sir" juyowa yayi gaba daya yana dubansa

"Did something happen?"

"Kamar akwai qorafe qorafe sir....but sir Jabir will explain to you" shuru ya danyi kana ya kada kai

"Okay....you can go, I need thirty minutes to get ready before entering the first meeting, tell them,and.....send me Mr. Martin"

"Okay sir" ya amsa a ladabce yana juyawa dauke da project planning manual dinsa.

Iska ya furzar daga bakinsa yana murza hannayensa guri guda,yana son duk yadda za'ayi ya fita da amna zuwa wani guri da zai zame mata baqo ko na kwana uku ne,He promised her,kuma duk yadda zaiyi baya yadda yayi mata alqawari ya saba mata,bama ita koma waye zaiyi mu'amala dashi,amma kuma yaga alama kamar dama ba zata bashi damar hakan ba,sabbin sabgogi sai danno kai suke,zai yi qoqari ya duba,koda a wannan karon zata kama ya tafi lagos din da ita ne zaiyi wannan qoqarin.

Shigowar secretary dinsa ya katse masa tunani,dauk da basket din da shi sam yama manta dashi

"Sir,It's your food,you forgot it in the car" duban basket din yayi yana shafa gaban kanshi,daya hannun nasa kuma riqe da biro,kallon saman ido yayi masa yace

"Drop it here" a ladabce ya qaraso ya dora masa shi saman table din nasa saidai kuma daga gefe guda,wai ko xaiyi abinda zai dan wanke kansa a wajensa,saboda yasan me laifi ne shi a wajensa,saidai har yanzu baice masa komai ba,shurunsa kuma bashi da sauqi sam a wajensu.

Dubansa ya sakeyi,kamar zai magana sai kuma ya shareshi yaci gaba da rubutu akan file din dake gabansa,ya danyi jim yaga ko zaice wani abu amma yaga baibai ta kansa ba,sai ya danyi gyaran murya

"Sir,akwai baqi dakeson ganinka...."

"Ka gaya musu,yau bazan samu damar ganin kowa ba,tell them in a polite way,they're our client.....don't repeat it again" J ya fada da kakkaurar muryar dake nuna gargadi da kuma jan kunne ba tare da an fito an maka filla filla da laifin da kai kanka kasan ka aikatashi ba.

A ladabce ya kada kansa

"I will not repeat it sir,am sorry" bai amsa masa ba yaci gaba da aikinsa,shi kuma ya juya ya fita.

Files din dake gabansa ya gama dubawa,wadanda zai sakama hannu ya saka musu,ya tattare takaddun da zaiyi amfani dasu sannan ya shige toilet din dake manne cikin office din nasa.

Yana fitowa jabir na shigowa office din,kai tsaye kamar kowanne lokaci da bashi da shamaki da shigowar

"Good morning" ja'afar ya fada yana sauke hannun rigarsa da yayi rolling up don kada ruwa ya taba

"Morning dude,mun tashi lafiya" jabir ya qarasa maganar yana zama saman kujeru guda biyu dake gaban table dinsa

"Alhamdulillah....ya jikin madam?" Goshinsa ya murza

"To,da sauqi,yau kam ko breakfast ban samu ba,,she can't cook"

"Allah ya bada lafiya" ya fada yana dawowa mazauninsa.

Hannu ya miqa zai dauka wani file,sai ya ture murfin daya daga cikin warmers din,cikin qanqanin lokaci qamshi ya cika wajen

"Wow,wannan fa?,daga ina?" Jabir ya fadi yana leqa warmer din,tambayar ta dan ja hankalin ja'afar,ya daga kai yana kallon abincin shima qamshin na cika qofofin hancinsa,kafin ma yace wani abu jabir ya buda warmers din ya fara serving kansa tare da ja'afar din a different plates,ya kammala ya tura masa gabansa shima yaja nasa.

Ko sau daya jabir ya kasa riqe bakinsa daga yabon abincin,da gaske kuma yake,dadin abincin yakai masa ko ina,duk yadda ja'afar yaso basarwa qamshinsa da kuma yadda jabir keta santi akai yasa ya gaza daurewa,sai ya rufe file din,yaja abincin shima ya fara ci.

Loma biyu kacal ya yadda da abinda jabir din ke fada,saidai ya dake ne ba tare daya nuna ba

"U have a great cooker" jabir yayi furucin yana gyada kai

"what is happening with our Lagos contract?" Ja'afar ya kauda wancan maganar ya sako masa wannan,baice komai saboda yadda girkin ke dibansa,ya fiddo wayarsa yayi dan danne danne ya turawa ja'afar gabansa,sai ja'afar din ya bishi da kallo,ya fuskanci sosai yakewa abincin santi,kaman zai magana sai ya fasa,ya dauki wayar yana duba abinda yake son nuna masa.

Ya jima yana nazari bayan ya tsaida nashi cin abincin,har jabir ya gama ya wanko hannunsa a toilet ya fito


"Da zaka kyautamin yaa J ai da an samin kwano a gidanka kafin my fa'emm ta warware" sai sannan ya dauke idanunsa daga kan wayar,ya watsa masa harara

"Lokacin aiki ne wannan,ba zancan family ake ba yallabai"

"Magana anan fa ta zama dole,kana samun irin wannan kabakin ya kamata a ga canji a jikinka,kadan aje tumbi haka"

"Irinka ne ni da zan kwanta?,so kake wataran ka kasa aikata komai a gad....." Shuru kuma yayi ba tare daya qarasa ba,kaman wanda wuta ta daukewa

"A gado ko?,kuma hakane fa dude,ku da yake expert ne ta wannan fannin zaku fimu sanin sirrin farin shiga" jabir ya fada dariya sosai na kubuce masa.

Karamin tsaki yaja yana tura masa wayarsa da qarfi gabansa,banda jabir din yayi hanzarin saka hannu ya tareta da babu abinda zai hanata faduwa qasa,har yanzu dariyarsa yake kafin yace

"Na duba mana ticket na tafiya lagos jibi in sha Allah"

"Hakan yayi" ja'afar ya fada yana miqewa tsaye don shima ya wanke hannun nasa,ya wuce jabir daketa qunshe dariya har yanzu.

Sai gab da la'asar sannan ya samu kansa,sanda ya dawo office ya taras da miscall har uku,bai iya biba sai daya dawo daga sallah,yana zaune daman cussion yana dan sauke gajiya yabi bayan kiran.

Sosai tayi zurfi cikin tunani lokacin da take kwaba qullin alkubus din data yiwa amna alqawarin yi yau,amna na gefanta tana faman zuba mata surutu kaman yadda ta saba,zaune saman sink daura da tap din dake kitchen.

Tabbas fuskar hajiya munubiya ta gani tana fitowa daga sassan unaisa,unaisan na biye da ita,amma duka ba wannan bane yafi tsaya mata ba a rai,maganganun da kunnuwanta suka jiye mata

"Duk sharrin ammansa ne d wannan makirar tsohuwar,na gaya miki kiyi da gaske,kiyi kamar kinayi,ki kuma zuba ido sosai,zakiga dukka abubuwan da na gaya miki" me amma ta tsare ma haj munubiyan?,me kuma anni itama ta tsare mata?,meye alaqarta da unaisa da har ta zabi ziyartarta a kebantaccen lokaci irin wannan?,bayan basu jima da haduwa a gida ba?,bama wannan ba duka,ame zata zuba ido?,kwata kwata zuciyarta bata kwanta da zuwan haj munubiya ba,duk da bata ganta ba amma ta fita daga gidan ba tare data nema kowa ba.

"Anty moon ana kira,Allah yasa daddy ne" amna ta fada tana tattara hankalinta,ko daya maimunatu bata ma fuskanci wayarta bane saboda sabon ringtone dake kai.

Dab da zata tsinke ta daga,saboda sai data tsaya ta dauraye hannunta ta kuma gogeshi

"Assalamu alaikumm" yarrr yaji tsigar jikinsa ta tashi,sai ya zame kadan yana sake jingina sosai da kujerar,ya kuma dauke dukka qafafuwansa ya dora kan center table din yayi crossing nasu.

Har zata sake maimaita sallamar tata jin shuru,sai tashi muryar ta ratso ta cikin wayar,ta kuma isar da saqo zuwa ga qwaqwalwarta cikin lokaci qarami,har cikin bargonta taji sautin nasa,tsigar jikinta ta zuba itama

"Wa'alaikumus salam" ya amsa mata muryarsa can qasa kamar wanda ya tashi a barci,a hankali ta cira wayar daga kunneta ta juya ta miqawa amna,idanunsa na a lumshe muryar amna ta maye gurbin tata muryar da yake sanya ran ji

"Daddy i missed you, please daddy ka dawo da wuri,anty moon tana maka favourite dinka,daddy zaka dawo?" Murmushi mara sauti ya kubce mata

"In sha Allah amnee"

"Thank you dad,daddy pizza please"

"Amnaaaa" yadan ja sunanta,da sauri ta tareshi

"Please daddy say okay"

"Okay" ya amsa mata kamar yadda taso,sai ta shiga murna tana masa godiya.

Duk yadda yaso ya daure amma sai ya kasa,hakanan ya samu kansa da cewa

"Bata wayar" da sauri kuwa amna ta miqa mata,saita tsare amnan da ido tana son bin ba'asi,murya can qasa da sigar rada tace

"Daddy" amsar wayar tayi,kamar zata sanya a kunneta sai kuma ta latse wayar ta ajeta gefe taci gaba da kwabinta,dubanta amna keyi cikin rashin jin dadi kamar zata saki kuka, murmushi maimunatu ta saki,yarinyar ba zata gane ba,matuqar zata ci gaba da jin muryarsa to akwai damuwa,har yau bata fita daga tarkon maganin data shama kanta ba,lallabawa take

"Daddy yana aiki,ba'a son a dinga disturbing nasa,ko kinaso yayi ciwon kai?" Da sauri ta girgiza kanta

"Okay,budemin ledar can maza a dafawa daddy abinci" sai kuwa ta hau bude mata fararen ledojin,saboda dasu xatayi amfani,cikin ranta tana mamakin tsabar wayo na yarinyar da har ta iya daukan wayarta ta zuba numbers din daddyn nata ta kira,wanda already ta dade da haddace ta.

Daga wayar yayi daga kunnensa yana kallo cikin mamaki,yaji sanda yarinyar ta bata wayar,it means kashe masa waya tayi?,sai yaji wani abu ya tsaye masa a rai,karon farko kenan da wata diya mace a duniya ta taba yi masa hakan,ransa ya sosu sosai,ya furzar da iska daga bakinsa

"me hakan ke nufi?,ta dauka shi sa'anta ne?,she doesn't know who I am" ya fada yana jin zafi har cikin ransa(a hayye,mai yi ne yau akayi masa,ashe dai babu dadi😝).
[11/16, 10:55 AM] +234 813 615 2119: 62

Har suka gama cin abincin bata sake ba,tana ta juya cokali cikin abincin,har yanzu fuskarta babu cikakkiyat walwala,hakan yasa amna ta kasa sakewa.

Yatsun hannayensa ya hade guri guda yana duban amnan,ya tabbatar albishir din da zaiyi mata a yanzun zai sanyata ta ware

"Are you ready?" Kusan tare suka daga kai,saidai ita maimunatu ta basar kamar hankalinta bai wajen

"For what daddy?" Ta tambaya with full excitement tana kallonsa kamar wata babba yadda ta tambaya din,hannunsa ya sanya a aljihun rigarsa ya fidda ticket ya nuna mata

"Trip to Lagos" ihun murna ta saki harda miqewa tsaye,yadda ya zata din kuwa haka ne,nan da nan ta sake,ta fara zayyano masa ina da ina zasuje,yana zaune yana kallonta kawai,duk sai data gama murnar sannan ta zauna tana fadin

"Daddy,ins ticket din anty moon" shuru yayi, yarinyar ta iya tambayar qure,baisan me zaice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login