Showing 156001 words to 159000 words out of 173794 words

Chapter 53 - GURBIN IDO Karyayyiyar Rai By Huguma

mata ba,a hankali ya saci kallon maimunatu wadda har yanzu bata bar jagula abincin ba,kamar ma bata wajen,don fuskanta baiyi kama da wadda taji abinda amna ta fada ba,tunda ta taya amna murna ta kame kanta.

Da idanu ya yima yarinyar sign na ta tambayeta hadi da dauke kansa ya azasu bisa wayarsa,amma kunnuwansa suna saurarensu

"Anty moon.....zaki bimu nida daddy ko?,zai kaimu yawo sosai,zamuje har kifs beach garden,qawata tana ban labari suna zuwa ita da dad dinta duk sanda suka je".

Qaramin murmushi mara sauti tayi,tadan dafa kan amna

"A'ah amna......saura kwanaki mu koma school,banason nayi missing komawata makaranta" haka kawai yaji amsar tata wani iri,bai zaci zata ce hakan ba,amma sai ya basar yana miqewa daga wajen sanda amna ta soma magiyar ta bisun,da taga kuma ya tashi sai tayo wajensa,wai wayowa yayi,ya dora hannunsa saman kanta ya tofa mata addu'a sannan yace

"Ki kwanta anan amnee,ina da aiki da yawa da nakeso na gama kafin mu wuce" da yake cikin murna take sai batayi wani rigima ba ta yaddan,ya juya yana barin falon,yayi hakanne don baison ya sake shiga dakinta kada wani abun ya sake giftawa da zai hanashi cikakken bacci,don jiyan da qyar ya qwaci kansa.

Yana fita ta miqe tana gyara gurin,tayi mamaki sosai da yawan abincin da taga yaci,don kusan rabinsa shi ya cinye,tana aikin amna na sake mata magiya,sai data bar komai ta kama hannunta ta sanya cikin nata

"Kinaso a kori antynki daga school?" Kai ta girgiza da sauri

"Good girl,to kinga indai bakison hakan,dole na koma makaranta da wuri,next time sai muje tare"

"U promised?" Kai ta gyada,duk da bata da tabbaci tasan ta amsa ne kawai,amma kuma bata da mafitar data wuce ta amsa din.

Washegari gaba daya bai zauna a gida ba,ita kanta amna din bata ganshi ba kwata kwata,su biyu suka wuni,wannan ya sanya koda dare bata yi wani wahalar abinci ba,sai tayi musu jallop na taliya kawai wadda aka wadata da veggies,bayan sallar isha'i kadan amnan tayi bacci saman qafafun maimunatu suna tsaka da kallon wani film,sai falon yayi shuru saura ita kadai.

Shirye shiryen tafiyar shine ya tsaidashi yau a waje,bai dawo cikin gidan ba sai qarfe tara da mintina ashirin har da doriya na dare,har ya gota sassan unaisa sai ya dawo da baya,yayi knocking qofar,minti kusan daya sannan aka bude qofar.

Cikin matuqar girmamawa ta xube a qas tana gaidashi,daya daga cikin masu aikinta ne,masu aikin da ba'a nema izninsa ba kafin zuwansu gidan,abinda yasa ua dauke wuta kaman baisan da xamansu ba,ita kanta unaisan ba wani tunawa yake da lamarinta sosai ba bare wadanda ta ajjiye,komawa baya tayi ta lafe sanda yake shigowa,yana gama shigowa tayi wuf ta fita a sashen.

Zaune take saman three sitter dinta,tana sanye da doguwar rigar atamfa,sai dankwalin kayan dake aje a gefe,kanta dake cike da gashin doki da aka yiwa kitso tamkar nata yana a bude,ta miqe qafafuwanta tana kadasu,hannunta dafe da wayarta da alama chart takeyi,gefanta teburin glasa ne dake hargitse da ragoyin abinci gorar ruwa data lemo dukka da tasha.

Sosai tayi mamakin ganinsa a sassan nata,karo na farko kenan tsahon zamanta a gidan,duk yadda taso ta danne farinciki da mamakinta amma sun gaza boyuwa,tana daga zaunen tace masa

"Bismillah ga waje....." Ta datsi maganar tare da qwallawa dayan ne aikin nata dake cikin bedroom dinta tana gyaro mata shi kira,sai gata jiki na rawa,ta zube itama tana gaidashi,da hannu kawai ya amsa mata ba tare da ya dubi sashen ta ba

"Ki hado masa abinci da abun sha" ta bata umarni kai tsaye,sai ta miqe da hanzari ta fice,cikin zuciyarsa yake jin qyanqyamin maganarta,yar aiki?,ta kawo masa abinci da abin sha?,definitely batasan shi ba,batasan komai a kansa ba,ta yaya zai fara tsara zama da irin wannan?.

Daga kai tayi ta dubeshi still yana tsaye hannayensa saye a aljihunsa

"Have a seat" ta sake maimaitawa,tana jin wani dadi da izza tana shigarta,ko har ta fara cikin nasara ne ya biyota da kansa?,indai ko hakane lallai zata nutsu ta yanka qa'idojinta da sharudda wanda zasu dace da rayuwarta ba matsi balle takura.

Baice mata komai ba,yafidda hannuwansa daga aljihu tare da daurin kudi sabbi ya matsa gaba kadan ya ajjiye mata su

"I don't have your account digits....zan xanyi tafi....so koda zaki buqaci wani abu" sai ya ciro dan qaramin qawataccen complimentary card dinsa milk da aka yiwa ado da zaiba ya aje mata

"You can contact me" dauke idanunta tayi daga kan card din ta mayar fuskarsa,wani abu na mata yawo a zuciya,wannan tafiyar da yake fadin zaiyi a qa'ida ace da ita zai tafin,amma sai wani girman kai ya taso mata,meye nata na damuwa ko nuna zakwadin tafiya?,bayan sun zagaya duniya da kyau,kudi sosai daddynta ke fitar musu duk sanda suke son su fita wata qasar,kada ma tayi magana ya rainata yaga kamar so take yaje da ita ne, shikenan sai ta amsa tayin da haj Aaya tayi mata na zuwa inda itama kafin sun dawo,don haka ta koma ta jingina da kujerar tana cewa

"Allah ya kiyaye hanya" labbansa kawai ya motsa alamun amsawa,sannan ya juya yana ficewa daga sashen hadi da bar mata qamshin turarensa.

Ajiyar zuciya ta sauke sanda ya ida ficewar,ta lumshe idanu tana zuqar daddadan qamshin nasa,ashe yadda take hangensa da tsada daga nesa yafi haka wuyar samu ma daga kusa?,amma dai ko yaya ne ita ba zata sake bada kanta ba,zata ci gaba da amfani da girma da martabarta,har sai ya fahimta ya kuma kawo kanshi.

*******Tun da ta farka da safen amna ta kasa komawa barci,wai batason tayi barci daddy ya tafi ya barta,tunda yace flight din safe ne zasu bi, maimunatu nata mata dariya tana kuma shirya mata kayanta,dai dai da yadda tace haka daddy yake shirya musu idan zasuyi tafiya,ba wasu kaya masu yawa ba masu.kuhimmanci kawai ake dauka,sauran abinda basu da,yafi ganewa ya siya musu a can.

K'arfe tara da minti ashirin ta kammala komai harda break fast dinsu,ita dince kawai.batayi wanka ba,tun jiya bata ganshi ba,tana daki dai ya shigo sunyi magana da amna,kafin ta fito sun gama ya fita,kamar ta shareshi amma sai taga bai kamata ba,kodon diyarsa dake qaunarta,don haka ta dauki kwando ta shirya komai dai dai da yadda amnan zata iya dauka

"Muje na rakaki ki kaiwa daddy" daman zaman jira take,ta kuwa sauko da saurinta,maimunatu ta dauki kwandon suka fito tana tsokanar amna,kada dai ace daddy ya tafi ya barta,ta qyalqyale da dariya

"Daddy baya fadin alqawari fa ya saba anty" kai ya jinjina tana murmushin yadda yarinyar tasan halin mahaifinta,duk da shekarunta basufi hudu ba.

Daga second matattakala ta biyu ta tsaya ta miqa mata kwandon,sai ta tsaya tana duban amnan tana ci gaba da haurawa har takai qarshe sannan ta sauke idanunta daga kanta tana juyowa don barin wajen taje ta qarasa abinda batayi ba.

Waiwayowar da zatayi suka hada ido ta ita,sanye take cikin wanu straight leg trousers da shirt spaghetti hand,siriryar silver chain ne a wuyanta da qaramin dan kunne barima, qafarta high hill ne,fuskarta ta wadata da makeup sosai.

Kallon kallo suka yiwa junansu,sa'annan unaisan ta zarce da yima maimunatu kallon qurilla daga sama har qasa.

Wasu soft nigh gown ne a jikinta farare tas tas kamar ba dasu ta kwana ba, gashinta mai laushi da santsi nannade cikin wata hula me zubin shower cap,kwantacciyar qananun sumarta ta gaban goshinta zuwa qeya dukka ta fito ta sake qawata fuskarta kamar ba daga bacci ta tashi ba,jikinta na fidda qamshin turaren baccinta data jima da warewa musamman saboda bacci kamar yadda afra ta koya mata,fararen santala santala hannunta dukka a waje suke saboda yanayin hannun rigar dan qarami ne sosai, tsintsiyar hannunta cike suke da duwatsuntan nan asalin wadanda ta gada daga daadarta,ko sau daha bata taba sha'awaf ciresu daga hannunta ba,sai suka kuma sake mata kyau suka haske farar fatarta dake luwai luwai fes kuma jajir da ita,kullum duwatsun kamar sake gogesu akeyi saboda sheqin da sukeyi,qafarta wani farin slippers ne mai taushi da aka yiwa wani adon gashi gashi daga sama.

Da qyar unaisa ta hadiye wani abu me tauri,haushi sosai ya cikata ganin yadda maimunatun tayi gaggawar dauke idanunta daga kanta tayi gaba kamar batasan wacece ita din ba.

"Agwai" ta kirayeta da sunan da tasan zai bata ranta,sai tayi kamar bata jita ba ta sakeyin gaba

"Hey dake nake magana" nan ma shuru,taci gaba da takawa zuwa sassanta,zuciya ta ingiza unaisan,sai tayi saurin takawa ta kuwa sha gabanta

"Don baki da kunya kina ji ina miki magana?,wato kin samu sake saboda kina zaton kin hada miji dani ko?,mijin da kike hoto a wajensa?,ba kowan kowa bace ke illa 'yar qauye mazauniyar riga,ki kiyayeni wallah,bakisan wacece unaisa ba,diya ga ministern ilimi" wani kallo maimunatu ta watsa mata,karon farko tun zuwanta gombe da taji wani ya bata mata rai,har ran nata ya sosu har haka

"Duk da nike bafulatana amma ban taba daukar tallan nono ba har kawo rana irin ta yau,kiwo kuwa wannan ado ne ga dukka cikakken bafulatani,koda ma ace nayi tallan nono ai ba aibu bane ba kuma gazawa bace,saboda dan halak baya manta tushe,tushiya kuwa masomin dukka wata daawa ce da tayi tsiro ta fito al'umma ke kallonta......" Daga wannan ta kewaye unaisa ta qarasa shigewa falonta ta kuma rufe qofar ta abinta,take unaisa ta sake hasala,sai ta juya zuwa stairs din ja:afar,sai kuma ta sake ja ta tsaya,idan ta hau tace masa me?,kada mutuncin ta ya zube a idanunsa,bari,zatayi dealing da yarinyar a cikin gidan da kanta,dole tayi.laushi,kuma dole tayi mata biyayya,badai tafiya zaya yi ya barsu ba su biyun a gidan ba?.
[11/16, 10:55 AM] +234 813 615 2119: 61

Tunda suka gama komai ta sake wanka ta kuma gyara amna,ta shirya ta cikin wani Three quater mai kyau da shirt dinsa,itama ta shirya kanta,abinci ta zuba musu amma amna tace sam ita sai daddy ya dawo,duk yadda ta lallabata amma amnan taqici,yau kam kwanciya takeso tayi,tanason ta kalla qarasa kallon dramas dinta,idan da sauran lokaci ta duba karatuttukanta,bata son ma su hadu dashi kwata kwata,tana tunawa da abinda ya faru jiya,ji take kamar ta maido lokacin ta goge dukkan abinda ya farun.

Daki suka koma duka ita da amnan,saidai lokaci bayan lokaci tana zancan rashin shogowarsa,daga qarshe dole tasa maimunatu ta bude mata qofa ta tafi dubashi.

Yafi awa da shigowa cikin gidan amma ba wanda ya sani,sabida tarin ayyukan da yakeso.ya hattama,bayason barinsu su zame masa kaya,ga tafiyar dake gabansa jibi,wadda yake saka ran sai ya huta sosai kafin ya dawo din.

Idanunsa ya dauke daga kan system din yana duban amanan,gaba daya yarinyar ta narke fuskarta tana dubansa,sai ya sakar mata murmushi,yana jin dadi har qasan ransa,shigar tayi mata kyau,kuma ko ba'a gaya masa ba alamu sun nuna tana samun kulawa tare da jin dadin zaman gidan,kafin tace komai ya hade hannayensa waje guda

"Am sorry angel" dole ta saki dariya,ta tako da gudu ta fada jikinsa tana dariya,gefansa ta zauna tana qorafin dai

"I say sorry ko?" Ya tuna mata yana dubanta,dariya tayi tana tura kai lallai sai ta karanta abinda yake rubutawa a fuskar system din

"Daddy ka ajjiye don Allah muci abinci" sosai yaji dadin tayin data masa,don yunwa yakeji,ya kuma yo takeaway amma ya gaza ji,sai tattarashi yayi ya ajjiye,saboda kwata kwata taste din bai masa dadi ba,har yanzu taste din breakfast din safe yana jinsa akan harshensa,wannan yasa ya kasa jin dadin kome,amma kuma baison yarinyar ta fahimta haka,bayason raini,saidai kafin ya sake kowanne tunani amna tayi caraf da hannunsa,ta kuma riqeshi gam,babu damar ci gaba da aiki,dole yabar komai ya miqe yabi bayanta tana gaba janye da hannunsa.

Yankewa tayi kawai ta fara karatun bayan shigarta daki kada bacci ya dauketa bata karanta komai ba,har ta zauna sai kuma taji sha:awan shan gwanda,don haka ta miqe tayo kitchen,ta dudduba freezern gaba daya babu ita,da alama ta qare kenan,dama kuma last hisham ne ya siya ya bayar a kawo mata,ranta babu dadi ta rufe freezer din ta dawo daki,sai ta yanke kawai ta kirashi ta roqeshi ko zata samu wata,tana matuqar sonta.

A bakin qofar dakin amna ta sake masa hannu

"Daddy ka kirawo anty moon,yau tayi aiki sosai,zan dauko mana spoons da plates kafin ku qaraso,na iya zaka gani,anty moon ta koyamin" sai ta juya da hanzari ta bar wajen cikin zumudi ba tare data tsaya sauraren me zaice ba.

Da kallo ya bita har ta bacema ganinsa,baisan wanne irin qauna bace tsakaninta da ita ba,yana ganin zumudi sosai a fuskarta da farinciki duk sanda zasuci abinci tare,kansa ya girgiza yana sakin qaramin murmushi a fuskarsa sannan ya maida kansa ga qofar dakin.

Gaba ya matsa kadan ya dora hannunsa akan handle,sai a sannan ya tuna da abinda tayi masa dazun,hakan yasa ya qara hade fuskarsa,sannan ya murza qofar a hankali ya tura qofar dakin.

Tsaye take a gaban gadonta inda litattafanta suke ajjye,ta bawa qofa baya,sanye da farin high waisted skinny leggings da baqar armless robber shirt,gashinta data daure da siririn band mara fadi yana ta reto a bayanta,kanta babu dankwali,hannunta riqe a qugunta,ta kara wayar tata a kunnenta

"Ya hisham don Allah,Allah yasa ban takura ka ba" ta fada cikin karyar da murya,saboda batason matsanta masa da gasken,don dai batasan wanda zata kira din bane sai shi

"Kada ki damu matar yaaya,za'a kawo in sha Allah"

"Na gode sosai ya hisham,you are such a kind person" fusgar wayar da akayi da wani irin zafin nama yasa bata samu daman jin me hisham ya fada ba,sosai ta tsorata ta kuma juyo a razane,don ko kusa ko alama bataji shigowar mutum ba.

Dab da bayanta yake a tsaye,abinda yasanya ta kusa fadawa jikinsa kenan sanda ta juyo din,cikin sauri ta zare idanunta daga nasa,saboda wani kallo da yake mata,wani irin abu ne ke gilmawa cikin idanuwansa,yayin da qirjinsa ya cika da wani irin qunci fushi da kuma bacin rai,abinda ya sanya launin qwayar idanunsa canzawa kenan cikin qanqanin lokaci.

Taku biyu ya qara ya kawar da dukka tazarar dake tsakaninsu,fuskarta ta sauka tsakiyar qirjinsa saboda yadda ya bata tazara wajen tsaho,yayin da shi kuma habarsa ta sauka a tsakiyar sassalkan gashinta,da sauri tayi taku biyu baya saboda sake bata ratar daya hade a tsakaninsu,bata sauke diddigenta a qasa ba ya maara mata baya,sake jaa tayi da baya ya sake maida qafarshi inda ta sauke,bata gushe ba tana matsawa yana binta har ta qure da bangon dakin.

Idanuwanta dake cike fal da tsoro ta daga ta kalleshi,sai taji tsoronta ya ninka na baya,fushin data hanga saman fuskarsa da yadda idanuwansa suka sauya ya sake tsoratata,ci gaba yayi da aza mata kallonsa yana kuma sake hade gap din dake tsakaninsu,dab da ita ya tsaya ya daga hannunsa, abinda ya sanya maimunatu qanqamshe hannayenta tana jiran jin saukar duka ko mari,duk da batasan ainihin laifin data masa ba,amma wani sashe zuciyarta na gaya mata kashe masa wayan da kikayi daxu,ba abinda zuciyarta ke hasaso mata sai irin marin data taba karba daga wajensa shekarun baya da suka shude,da qyar idan yau ba za'a maimaita ba.

A hankali ya sauke hannuwan nasa yana morewa kallon fuskarta dake cike da tsoro,duk da idanuwanta a kulle suke amma hakan bai hana kyanta fita ba, siraran jajayen lips dinta nata motsi,koda ba'a gaya maka ba kasan kuka take shirin saki,bai gama wannan tunanin ba kuwa hawaye suka ratso rufaffen idanunta,bin hawayen yayi da kallo,sai yaja baya a hankali,ta gama karya lagonsa,baisan dalili ba bai kuma san me yasa ta shiga sahun mutanen da hawayensu ke saurin karya shi ba,ba abinda wannan ya tuna masa sai shekarun baya sanda ya mari marainiyar fuskarta,abinda ya tsaye masa a rai tun a wancan lokacin fiye da komai,zuciyarsa yaji tayi laushi,amma kuma bacin ran dake can qasan ransa har yanzu yana motsawa.

Daga hannunsa yayi yana kallon wayar da ya qwace din,number hisham din ce,sai ya danneta ya shiga wajen block yayi blocking nasa sannan yayi deleting number kwata kwata daga kan wayar,bai tsaya a nan ba ya sake shiga contact nata,numbers din dake kai ba masu yawa bane,duka duka na 'yan gidansu ne sai na wasu mutum hudu afrah besty teema ummu,numbers dinsa ya saka ya shiga wajen kira,number batayi appearing ba,alamu dake nuna cewa kenan bata da number dinsa?,yaja qaramin tsaki can tsakiyan ransa,sai ya samu kansa da yi mata saving number,ya kuma sanya mata full name dinsa

_*ja'afar marwan akko*_,ya daga kansa a nutse ya sauke a kanta,tana tsaye manne da bango kamar zai tsage ta shige,fuskarta duk danshin hawaye,sauka idanunsa sukayi saman qirjinta wanda shape dinsa ya fita sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login