Showing 147001 words to 150000 words out of 173794 words

Chapter 50 - GURBIN IDO Karyayyiyar Rai By Huguma

wanka.

Abu kaman wasa sai gashi gaba daya daren yazo masa a wani irin birkice,sau biyu yana sake wanka,a wannan karon dai wankan ibada ne,tsakiyan dare da kuma kafin sallar asuba,me yasa mafarkinta ya hanashi bacci?,me yasa mafarkinta ya hanashi sukuni?,yana gaban mudubi a zaune yana lissafa tsaho shekaru da watannin daya dauka baiyi rayuwa da mace ba,sai ya furzar da iska daga bakinsa,tabbas wannan abun da ya farun yana da nasaba da dadewar da yayi da nisantar rayuwa dasu,bawai wani abu bane na daban.

Dab da liman zai tada sallar asuba ta buda idanunta,tana budesun abubuwan da suka faru a daren jiya suna dawo mata fes cikin kanta,sannu a hankali ta waarasu cikikin dakin,yana nan a yadda yake har hasken data kunna kafin ta kwanta,saidai sanyin dake busawa ya fara mata yawa saboda iskar asuba data gauraye duniya.

Hannunta ta daga tana shafa saman mararta a hankali,sakayau take jinta,babu wannan ciwon,hakanan babu feelings din gaba daya,sai ta sauke ta juya hannun damanta,idanunta suka sauka akan amna dake baccinta cikin kwanciyar hankali,hannunta ta dora kan fuskar yarinyar da wasu lokuta take mata yanayi da fuskan mahaifinta,batasan ya akayi murmushi ya kubce mata ba,sai ta miqe ta zauna sosai tayi kissing goshinta,sannan ta sake gyara mata kwanciyar gami da ja mata bargon sosai.

Bandakinta ta wuce,ita dinma sai da tayi wanka don bata yadda da kanta ba,sannan ta dawo ta saka prayer jilbab and skart da takanyi amfani dasu musamman a sallar asuba irin haka,ta tada sallarta.

Ko data idar qur'aninta ta dauka,bata wasa da tilawa ko don saboda haddarta,ta buda daga inda ta tsaya jiya ta dora,cikin qaramin sauti da kuma lallausar muryarta dake koyi da qira'ar shaik khalilul khusari.

A nutse ya turo qofar dakin a hankali,sautin karatunta ya baqunci kunnuwansa,sai ya maida qofar kawai ya rufe ba tare daya katse mata karatun ba,ya juya yana barin wajen,sautin karatun yana bin kunnuwansa har zuwa sand yayi nisa a wajen.

"Itama matarka ce" zuciyarsa ta raya masa sanda yake shirin wucewa zuwa saman sa ba tare daya biya sassan unaisa ba,wannan tunanin ya sanyashi sauya akala,ya isa qofar falon ya murdata,sai ya jita a kulle, knocking ya soma,saidai babu alamun za'a bude masa,mutum ne da bai fiya tsawaita abubuwa ba,don haka yana qara biyu ya juya yayi gaba,taku hudu cikin na biyar yaji an bude qofar,ya waiwaya a hankali idanuwansa a kanta.

Kana kallonta zakasan a birkice take,don hatta gashin kanta a hautsine yake,hakan na nufin a yadda ta shigo jiya a haka ta kwanta bugu da qari kuma har yanzun bacci take,bugunsa ya tadata

"Lokacin salla zai wuce" daga haka yayi gaba,ya soma haurawa zuwa saman,unaisan kuma ta bishi da idanu,abubuwa da yawa take rayawa a ranta,indai har shirinta na jansa zuwa gareta ya tabbata,to batasan yadda sauran abubuwa kuma zasu kasance ba.

Tana gama azkar dinta amna ta farka,sai ta rakata toilet tayi brush sannan tayi alwala,komai ta iya perfectly,da alama ta samu background me kyau.

Sallar ma sanda tana yi tana ankare da ita,gyaran dake ciki da kusakuran basu da yawa,ta jinjinawa amma sosai,ta kuma sake ganin kimarta da martabarta,hakan kuma ya tabbatar mata da cewa ita din uwa ce ta gari.

Basu koma wani baccin ba,ko surutu da hirar amna ma ba zata bari su koma ba,don haka ta jata kawai suka wuce kitchen.

Break fast me kyau ta shirya,wanda ya dauketa awanni kusan uku kafin ta kammala,har masu aikin unaisa suka gama hada nasu break din suka fice suka bata wajen,sau tari dama idan girki ya hadasu lokaci daya ita ke tsaftace kitchen din,koda sun gyara baya mata dai dai,saita shiga ta sake killace komai.

A dining ta shirya komai,kamar ita da wasu zasuci abincin,hakan kuma zabin amna ne,ita ta dinga dauko warmers din daga kitchen din tana ajewa saman dining din,bedroom dinta suka wuce ita da amnan don yin wanka.

Tun suna wankan ta dameta da tambayar daddynta,don haka suna fitowa ta fara shirya amnan,tayi kyau sosai cikin fara shirt da gray color din skinny jeans,ta hade mata uban sumarta tsakiyar kai,tana ta qamshi yarinyar ta cilla ta fice zuwa sassan daddyn nata,sai sannan maimunatu ta samu sukuni,ta zauna gaban mirror ta buda manta ta fara shafawa,ta shirya kanta cikin favourite shigarta na chiffon fabric,sun ray pleat design da rigansa drawstring data zauna mata a jikinta ta mata kyau sosai.

A jikinta dama taji sai amna ta jawoshi sassan nata,aikuwa tana tsaka da hade sumarta cikin band amna ta turo qofar da sauri

"Anty moon,daddy xai fita,kizo kiy serving dinsa,yace bai yarda nima na iya girki ba,wai ba tare mukayi ba" dariya ce ta kusa qwacewa maimunatu,ta cikin madubin take kallonta tana saka band din,sannan ta janyo siririn mayafin kayan ta yafa saman kanta ba tare da taji shakkan fita dashi ba,tunda babu wani abu a jikinta daya fito,dukka yanayin dinkin me sakin jiki sosai ne

"Muje in gaya masa,amna ta ta zama 'yammata,she can cook" dadi ya cika amnan,ta saqale hannun maimunatun suka rankaya zuwa falon.

A tsaye suka sameshi,ya bawa qofar da zasu fito baya,hannuwansa cikin aljihun wandon suit dinsa,wata iriyan suit mai daukan ido da hankali,koda bakasan tsadan sutura ba zakasan taja kudi,komai nashi designer ne me tsada,duk da bata ga fuskarsa ba amma ta baya tana iya hangen sumarsa da tasha gyara sosai,qafafunsa dake saye cikin safa sun nutse a cikin center carpet din dake wajen

"Daddy ka zauna mana" amna ta fadi tana zame hannunta daga na maimunatu ta kuma nufeshi.

A hankali ya waiwayo,a kanta idanunsa suka fara sauka,haka ma ita,duk yadda taso ta zamewa kallonsa amma sai da idanuwansu suka hade waje daya,duk da haka tayi namijin qoqarin kau da nata idanun,wani irin nauyinsa yana cikata,abubuwan da suka faru a daren jiya suna dawo mata cikin kwanyarta daya bayan daya,sai taji ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba, nauyinsa da kuma nauyin idanuwansa na sake qara mata kasala da kuma nauyi,duk da abinda takeji a jiya cikin jikinta babu shi a yanzu,amma har yanzu cikin jikinta tana jinsa a mace yayi wani irin laushi,sai ta zame saman one sitter din dake daura da ita ta zauna akai,tana kwaranyar da dubanta ga tv ba tare da tana fahimtar abinda ke gudana ba.

Yadda ta rage tsahonta ta hanyar zama haka ya bita da idanuwansa,kyakkyawar zagayayyar fuskarta da tayi wani iri garai garai ta kuma yi fresh ta fito tarwai a tsakanin duhun kalar vail din dake kanta,kamar yadda jajayen siraran lips dinta ke qyallin lips balm

"Ina kwana" ta gaidashi da sak irin muryar data dinga gigitar dashi cikin mafarkansa na jiya,sai daya lumshe idanunsa yana hadiye wani abu sannan ya motsa bakinsa

"Lafiya Lau" tayi tsammanin zai mata magana kan abinda ya faru da ita a jiya ko wani abu makamancin haka,amma sai taji baice komai ba,hasalima ya tattara hankalinsa ga diyarsa

"Fita zanyi amna,am late,ina da alqawari da mutane,banason na saba" ya fada with softness lokacin da amnan ta dage sai ya zauna yayi breakfast dasu,haka ya juya suka fice tare yana lallabata ita kuma tana tuburewa.

Baki maimunatu ta tabe,bata taba ganin mutum irinsa ba,idan komai ya faru ma yana iya nuna komai din bai faru ba,shariya ginshira da kuma izza,ita dama bata wani damu yaci din ba,banda amna ta dage ma ba nemansa take ba iyakar zamanta a gidan,sai taci gaba da zamanta a nan tana jiran dawowar 'yar rigima anma suyi break din tare.

Ba'a rufa minti uku ba sai ga amnan ta dawo dauke da kwalin sabuwar waya

"Ga wayarki inji daddy......sannan yace na hada masa abincin a foldable basket,yau da girkina zashi office" hannu tasa ta amsa wayar ta aje gefe,tana dariyan maganan amna,tunda dai yau ta tayata yanka veggies ta damu kowa da zancan ita tayi girki,sai ta miqe ta shiga kitchen din,ta hada komai a basket din ta riqowa amnan,har zuwa dab da inda motarsa ke kunne yana jiran amnan.

Tana hangoshi yadda yake duba agogon dake daure ga tsintsiyar hannunsa,sai ta gyara tsaiwarta sosai,ta kuma tsaya a wajen data tabbatar bazai ganta ba,so take ta qare masa kallo irin wanda bata taba ba tsahon saninta dashi,tanason ta gano dame yafi sauran maza da yake da kwarjini izza da kuma qasaita har haka?,saidai tun batayi nisa da bin qwaqwafin nata ba ta fara ganewa cewa tabbas da bambanci,sai ta lumshe idanunta tana sauraren sautin bugun zuciyarta,ta cikin idanuwanta kuma tana hango wancan lokacin da ya sanya yatsunsa biyar saman fuskarta,ta bude idanunta da hanzari kamar a lokacin abun ya faru,ta saukesu a kansa sanda ya saki wani qasaitaccen miskilin murmushi yana jan kumatun amna bayan ya karba kwandon hannunta.

Qaramin tsaki taja tana kauda kanta daga dubansa,haushinsa yana saukar mata,sai ta juya a nutse tana barin wajen,ta tsani duk mutumin dake busa hayaqi qwarai,har batason hada muhalli dashi,batasan ya akayi take manta wannan a kansa ba.

Koda ta koma sabgarta taci gaba dayi cikin gidan ita da amna,bata tashi tunawa da wayar ba sai da azahar bayan ta idar da sallah amna tayi bacci, fiddota tayi daga kwalinta ta budeta,sabuwa ce dal,sannan daga gani ba qaramar waya bace,mamaki ya kamata,me ya sami tata wayar?,bata sani ba,iya abinda zata iya tunawa kawai shine sanda wayar ta sulale ta fadi daga hannunta sanda ya tareta ya sanyata a wata iriyar koma.

Baki ta tabe ta miqe ta jonata a charge,sannan ta dawo ta kwanta saman kujerar ta buda daya daga cikin novels din afra dake wajenta,wanda batasan ta hado dashi cikin kayanta na makaranta ba,sai yanzu data qarasa zazzage akwatin,don baifi kwanaki goma sha hudu suka rage musu komawa makaranta ba.

Guraren qarfe uku da rabi taji ana knocking sassan unaisa,sai ta gyara kwanciyarta bayan ta duna lokaci,taci gaba da karatunta,sosai littafin yake daukar hankalinta,batasan ya akayi ta qulla alaqa me qarfi da films na soyayya da litattafansu ba,zama da madaukin kanwa,afra ta koya mata qarfi da yaji.

: Chapter 59
59

.........Murmushi Dr Bilkisu tayi, cikin sigar lallashi tace, “Kiyi haƙuri dubawa kawai zanyi, dan idan yazam yaji miki ciwo ne ba'a ɗauki mataki ba nan gaba zaki iya fuskantar wata matsalar da ba'a fata. Gara tun yanzu yana a ɗanyensa a ɗauka mataki kinji ƙanwata. Badan Anaam taso ba ta bar Dr Bilkisu ta duba, dan sosai ta dinga lallaɓata da nuna mata illar rashin dubawar harta amince. 

   “Ya ALLAH”. Dr Bilkisu ta faɗa da sakin rigar Anaam ɗin takai hanunta saman goshi tana murzawa. Sosai ranta ya sosu, sai dai kuma ta fahimci matsalar daga jikin Anaam ɗinne. Amma duk da haka an nuna mata mazantaka da yawa da ƙawazuci.

   A tsorace Anaam dake kallonta tace, “Doctor wajen ya daina aiki ko?”. Murmushin da babu niyya Dr Bilkisu ta saki, ta girgiza kanta da kallonta. “A'a bai daina aiki ba ƙanwata, kawai dai anyi ɓarna ne da alama angon naki tsohon tuzurune halan shiyyasa ya gagara binki a sannu. Gaskiya yayi miki ɓarna da yawa da dole sai anyi ɗinki”.

   “Na shiga uku”.

Anaam ta faɗa tana fashewa da kuka. “A'a kinga kwantar da hankalinki baki shiga uku ba. Mata da yawa sunci karo da matsala fiye da taki ma a dalilin first night, ban san mike damun mazan ba da suke muku irin wannan zuwan haka, ko soyayyace ke ingizasu oho, koda yake suma iyaye akwai laifinsu, zaka kai yarinya buduwa gidan miji amma kaita tsumata da kayan mata. Sune suke saka gushewar hankalin mafi yawan mazan har su aikata mummunar ɓarna ga yarinya, a yanzu haka inada irin cases ɗin nan da yawa ga wata can ma kwana uku kenan da mata ɗinki har huɗu kaɗan ma ya rage ita mijin ya kasheta dan a sume aka kawo mana ita tana bleeding kamar mai haihuwa” (Iyaye wlhy da gaske matsalar nan tana cutar da yaranmu, maganar mai ɗinki da bleeding ɗin nan da nake muku ya faru a gaske ALLAH har kuka naima yarinyar, amma koda aka binciki mijin iya gaskiyarsa ya faɗa cewar ya fita hayyacinsa ta yanda ya gagara jin tausayinta balle tuna ita din virgin ce, koda yarinyar ma akaji ta bakinta daga baya akan ko tasha wani abu ne bata ɓoye ba ta sanar da irin kayan matan da aka dinga ɗirka mata har ji ta dingayi kamar ta jawo auren koma ta bashi kanta kafin a ɗaura. Ya ALLAH, iyaye mata a duba dan ALLAH a gyara, ƴarki budurwa ce bata san komai ba, koda ɗan kayan fruit kika gyarata da su zuma da mazarƙwaila sun wadatar ai, sai maganin sanyi da a kullum bana gajiya da tuna muku shine mafi muhimmanci kafin kikai ƴarki gidan aure ki tabbatar bata tare da imfection yafi maganin matar nan da za'a iya cutar miki da yarinya a dalilinsu. Dan mazan da yawa sukan kasa controling kansu ne harsu fatattaka miki yarinya a banza taje yoyon fitsari ya sameta. Dan waccan yarinyar da nake gaya muku sai da yakai ko fitsari bata iyayi da kanta saida taimakon robon fitsari tsahon wasu wattani. Shin riba akaci ko faɗuwa kenan🤦🏻?).

     Kuka sosai Anaam ta dingayi har ba'ajin sautin muryarta a yayin da ake mata ɗinkin, tabbas ita din ragguwace bata wasa ba. Ko yaya abu ya sameta ta dinga raki ke nan balle wannan da ya zame mata makafin ajewa a tarihi dan bata taɓa riskar azaba makamancin hakanba. Shareff yasha tarin ALLAH ya isa da inda tarasu za'ai waje guda buhu-buhu zai ɗiba ya kaima Mommy ajiya saboda tarihi😝😆.

    Sosai ya dinga kaikawo dan yana iya jiyo kukanta da kiran Abie da Mamie da take famanyi, har da wasu a ALLAH ya saka matan da take ambata da ja masa ALLAH ya isa. Sosai hankalinsa a tashe yake dajin ɗunbin tausayinta da takaicin kansa. Da yanada damar dawo da ciwon jikinsa da yayi ko zai samu sassauci a zucyarsa, dan itaɗin wata abace mai daraja a zuciyarsa da baki ko alƙalami ƙaryarsa zanawa. Ita ke kukan amma tare suke raba raɗaɗin a zuciya. Koda aka kammala Dr Bilkisu tasa aka kaita wani ɗaki danta huta yana shigowa ta fashe da kuka wai bata son ganinsa Dr Bilkisu ta koresa. Duk da haushinsa da Dr Bilkisu keji kasa daurewa tai sai da tai dariya. “Tunda patient ɗina bata bukatar ganinka jeka abunka mun sallamaka Alhaji Al-Mustapha. Dan gaskiya kai mai laifine mai girma a wajenmu ɗin”.

   “Gutun murmushi ya ɗanyi iya laɓɓa sai dai bai fitan ba. Ya jingina da bango hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya zuba mata idanu. Bargo taja ta rufe har fuskarta ita a dole bata buƙatar ganinsa ɗin dai. Dr Bilkisu ta janye daga kallonta tana ƙara sakin ƴar dariya itama. Inaga ka bata dama ta huce sai muyi magana a office”.

   Kansa ya jinjina mata kawai. Ta juya ta fita. Cigaba yay da tsaiwa a wajen har bayan minti biyu da fitarta sannan yabi bayanta, har sannan kuma Anaam bata buɗe fuskar taba ɗin.



    A office ɗin doctor batare data kallesa ba ta miƙa masa takardar data gama rubutu a jiki. “Taji ciwo ne, amma mun mata ɗinki. Na fahimci cewa ƙaramin jiki ALLAH ya bata, amma shekarunta sun kai ga hakan. Sai dai kuma yanayin halittarta tana buƙatar bi a sannu, domin masu irin yanayinta zakaga ko'a wajen haihuwa ana shan fama dasu matuƙa saboda jikinsu bashi da wani ƙwarin gaske, sauƙinta ma ita tanada wannan ƙaramin jikinne, da irin raɓo-raɓo ɗin nan take akwai matsala, hakan na nufin ko anan gaba za'a bita a hankali inba hakaba kullum zata dinga shan ɗinki kenan. A yanzu dai zan riƙeta anan gaskiya har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ta samu nutsuwa yanda ya kamata saina baka ita da sharuɗɗa masu tsauri. Muna buƙatar waɗan nan drugs ɗin dana rubuta anan.”

    “Uhhim”.

Kawai ya faɗa yana miƙewa. Dr Bilkisu ta bisa da kallon mamaki, irin miskilan mutanen nan na bata tsoro, sai sun tafka tsiya ka rasa ta inda zaka auna yaya ma sukai. Kiji fa ta gama masa bayani akan kuskurensa ya bita da ‘uhhim’ kawai tsabar miskilanci. Bai san ta ɗaga masa ƙafa bane kawai saboda Dr Jamal. Amma da yaga yanda ake ruwan masifa yau, duk da kwarjininsa shima ya taka rawar gani wajen cika mata ido ko fushinta ta gagara nuna masa akan fuskarta.

    Pharmacy ɗin asibitin ya nufa domin sayo magungunan, sai da aka gama haɗawa zai ɗauka waya dan musu transfer yaji babu wayar a jikinsa, kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Dole ya bar musu maganin akan zaije ya dawo. Ɗakin da take ya sake komawa, saboda yana son jin ko tana buƙatar wani abu. Samu yay tana barci a yanda ya suka barta, ya kai hannu ya yaye bargon data lulluɓe har kanta tare da kaiwa tsugunne gaban gadon. Duk da barci take kumburin idonta bai hana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login