Showing 21001 words to 21427 words out of 21427 words

Chapter 8 - Wasa Da So by Aisha Muhammed Sani

ka yi ta
karshe kennan."


Daga idon Hameedan har Adam hawaye ne kawai ke zuba,sai ita tai dauriya tare da
fadin, "Ba zai mutu ba insha Allah likita,zai samu abun da ya ke so."

Adam na jin hakan tuni ya tashi daga kan gadon tare da fadin, "Da gaske ki ke
Hameeda?.

Daga ma sa kai kawai ta yi tare da rufe fuskarta.

Adam bai san lokacin da ya rungume Hameeda ba tsabar murna.

Likata kuwa fita yayi kawai yana murmushi sannan ya sanar da su Abba da Momy duk
abin da ya fahimta ga me da hakan,ba karamin farinciki Aunty tayi ba da jin hakan.


Tuni aka sallami Adam.

Suna komawa ba jimawa Muhsin da kan sa ya zo yana taya Adam Murna tare da fadin ai
bakomai daman Allah ya yi Hameeda ba matar ba ce ya dauki hakan amatsayin kaddara
kuma ya sanar da iyayensa komai sun fahimta.


Ancigaba da shagalin biki kamar yadda aka fara amman fa Adam baya barin Hameeda ko
ina ta yi yana biye da ita duk wanda ya masa magana yakan ce masa, " *Ni fa ku
barni nasan illan wasa da so gwanda nai tatttalin abuna, dan da tuni an gama kayar
dani*."

Shi dai Adam gani ya ke za akwace ma sa Hameedar sa.

Dariya kawai su ke domin su kan su sun dau babban darasi akan rayuwar Adam Da
Hameeda.


An daura Auren Adam da Hameeda, Dady ya ba su wani karamin gidan sa achan su ka
tare.

Mubarak kuwa soyayya ta kullu tsakanin sa Da Hameeda suma an fara shirin Auren
su.....


Bayan shekara biyu......

Hameeda ce ta fito da wani lukekyn cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta na shagwabe
fuska tare da cewa, "Honey ni fa ice cream zan sha."

Adam da ke kallo A TV juyowa ya yi ya na, "Ah Mama Lutiya yau Yan abun sun motsa
kennan yau ba ni ba hutu daga wannan sai wancen."


Zama Hameeda tai tare da fara kuka tana, "Ni wallahi in ba zaka siyomin ba sai na
baka Babynka daman ni na gaji."

Dariya Adam ya yi, ya tashi ya na, "yoo ni nama isa?, ai tashi muje."

Rikyeta ya yi suka fita tare.


Haka Rayuwa ta cigaba da kasancewa cikin farinciki Da anashuwa tsakanin Adam da
Hameeda.


*ALHAMDULILLAH,ALHAMDULILLAH YAU DAI ALLAH YA YI NA KAMMALA WANNAN LITTAFINA MAI
SUNA WASA DA SO,ABIN NAYI KUSKURE ACIKI ALLAH KA YAFEMIN,ABIN DA NAI DAIDAI ALLAH
YASA YA AMFANAR DA AL UMMA, AMEEN YA ALLLAH🙏*

_Nagode sosai masoyana wajen bani hadin kai acikin wannan littafin nawa inan ta fe
da sabo amman kan ya zo ga wanda na fara nan ni da kawata eyman maj suna *Yaya
Imran* fatan zaku cigaba da bibiya kamar yadda akasa ba_

Duk mai shawara,sharhi,neman karin bayani ta nemeni ta wannan number👇

08103080717

Urs xayyeesherth

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login